← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 51

Sashe 25

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ashe kece babu lafiya baby baifadaminba kawai yafadamin numbern dakin ne,
Sannu ya jiki?

'Daga kai tayi ahankali tana cewa,

Alhmdllh.

Shiru dukkaninsu sukayi babu wacce numfashinta bai fita da sauri sbd ganin 'yar uwarta.

Suhailat cikin jikin rumanah din take satar kallo dan kuwa batasan haka take kishin mijintaba saidataga cikin dan kuwa Allah ne kadai yasan irin ciwo da radadin datakeji axuciyarta saidai tana qoqarin fincikewa sbd batason zubarwa da kanta qima a gurin mijinta da 'yayanta harma da rumanar datake kishiyarta.

Rumanah kuwa jitayi duk atakure take da wanzuwar suhailat din gashi nurse tagama abinda takeyi ta fice.
Hakanan takejin bata iya kallonta sosai sbd ganin take zuciyarta da shaidan zasu hasaso mata maheer atareda suhailat din Wanda hakan na matuqar girgiza zuciyarta.

Cikin kulawa suhailat ta miqe ta bude basket din ta hada mata black honey tea sai pancakes da toasted chicken datai laushi sosai ta zuba matasu a plate tareda aje matasu yanda zata iya ci.

Cikin sanyin murya rumanah tace,

Nagode amma inaso zanshiga toilet....

Wayar suhailat dince tayi ringing ta sauka da sauri sbd mum 'dintace batareda taji mai rumanah din ke fadaba ta fita dan amsa wayar.

Ganin ta fita yasa rumanah sauke qafafunta qasa ahankali ta sauko ta nufi toilet din dake dakin ahankali sbd jiri.

Tana kaiwa tsakiyar dakin wani irin jiri ya dibeta daidai shigowarsa dakin.

Saida tajita jikinsa tayi saurin sakin ajiyar zuciya sbd ta sadaqarda cikinta yagama zubewa idan ta fadi.

Bude idanuwanta data rintse tayi takallesa cikin fargaba sbd ganin kallon dayake mata murya na rawa tace,

Toilet zanshiga.

Yanda ya dauke gira daya yasa tasan menene azuciyarsa tayi qasa dakai cikin tsananin sanyin murya tace,

Yi hakuri bansan zan.....

Just shut up"""yafada yana daukarta gaba 'daya ya bude toilet din suka shige.

Sauketa yayi ahankali kamar kwai
Ta dago takalli fuskarsa taga ba wasa tasaki 6oyayyan murmushi cikin zuciyarta tana cewa,

Ko fushi kyau yake masa.

Brush ya miqa mata ta karba tayi tana kallonsa sbd kallonsa yanxu matuqar nishadi da nutsuwa yake bata tana gamawa ya miqa mata towel tareda jawota jikinsa yazare mata kayan jikinta itadai ido kawai take binsa dashi sbd yau ko ta6insa nutsuwa yake bata.

Da yake shower ce bai shigaba ita kadai tashiga tayi wankan shikuma yana tsaye gaban mirror yana goge inda rigarsa ta baci da ruwan allurar dayaje yiwa wani patient kafin yashigo dakin.

Tana gama wankan ta dauki towel ta daura tareda zare shower cap din kanta ta tsaya gaban madubin da yake dubawa tana fuskantarsa.

Wasu kayan yasanya mata saidai bada bra ba duk saiyaji ransa yabaci da yanda kayan patients din sukai mata kyau amma bai nunaba yasake gyara mata gashinta ya dauketa suka fito tana kallonsa gira 'daya ya dauke yace,

Wannan kallon fa matata tana nan so be carefull bata hadani da komaiba.

Murmushi daya bayyana fararen haqoranta tasaki tareda sake qanqamesa tana fitarda sautin murmushinta ahankali
shima murmushin gefen baki yasaki suna kawowa tsakiyar dakin sukai ido hudu da suhailat dake zaune tayi musu kallo 'daya ta dauke kai tana qoqarin danna kira awayarta.

Saurin saukowa jikinsa rumanah tayi sbd taji nauyin suhailat din sosai koba komai ka girmama mai girmama kansa ta zauna bakin gado tana suuke kanta qasa.

Kallo 'daya yayiwa suhailat yagano halinda take ciki yaji tabasa mugun tausayi sbd baisan lokacinda ta dauka azauneba gashi sun dade aciki gashi qila batasan yana cikiba.

Hannu yakai yakamo hannunta tareda miqar da ita ya matsota gabansa yana kallon cikin idonta datake qoqarin 6oye halinda take ciki cikin kulawa yace,

Are you ok?

Kai ta 'daga masa batareda yakallesaba
Yayi kissing forehead dinta yace,

I will be in my office""yasa kai yafice yabarsu.

Jawo abincin rumanah tayi tafara ci hannunta na rawa sbd rawar da zuciyarta keyi.

Suhailat ma batareda takalli fuskar rumanah din ba tace,

Zantafi office am getting late Allah yasauwaqa.

Tana gama fada ta dauki handbag dinta ta fice hawayen datake riqewa suka gangaro mata ko office dinsa bata biyaba ta wucewarta saidata isa office dinta ta rufe siririn kuka ya balle mata amma dannesa tashigayi sbd bataga dalilin kukanba tunda dama tasan tanada kishiya meye abin jin zafi dan taganta da ciki bayan itama Allah yabata nata 'yayan ba juya yayitaba.

Saidata samu nutsuwa tayi masa text tace ta wuce office and she's very late so shiyasa bata biyo office dinsaba.

Tana ficewa rumanah ta aje breakfast din sbd dama turawa kawai takeyi.

Yana gama karanta text dinta ya aje wayar tareda lumshe fararen oily eyes dinsa.

Yinin ranar dukkaninsu a darare sukayisa sbd kowanne da abinda ya maqalewa zuciyarsa.

Baibar asibitin ba yau sai qarfe goma na dare lokacinda rumanah tayi bacci kenan.

Koda yakoma gida suhailat bata nuna damuwar komaiba a fuskarta itada 'yayanta su maqalqalesa suna masa oyoyo
Yayo wanka bai sauko cin abinciba sbd yaci pizza tareda rumanah a asibiti.
Koda suhailat taji cewar yayi dinner murmushi kawai tayi tace,

Ok bari nacewa Carolina tasaka a fridge.

Kodata dawo dakin yana kwance wayarsa a kunnensa yana magana da antynsa wadda yake biwa tana qara basa haquri akan abinda yafaru shidai kunnuwane kawai nasa baya iya zuba dogon zance.

Kwantawa tayi ajikinsa tareda rungumesa ta rufe ido alamar bacci
Yayi mamaki sbd basu cika kwana daki dayaba koman dare wani lokacin dakinta take komawa ta kwana.
Koda yagama wayar tayi bacci yakalli fuskarta kafin ya lumshe idanuwa fuskar rumanah daya baro tana barci tafado masa yasake rungume suhailat ajikinsa yana kamar rumanah ce ajikin nasa.

Washe gari ma tare sukaje asibitin saidai ko zama batayiba gaisawa kawai sukayi ta wuce gurin aikinta sbd ganin irin kallon da maheer kewa rumanah sbd sai yanxu cikinta yafito dakyau sbd kayan da aka canxa mata sunso kamata saikuma basu kama 'dinba.

Bayan wucewar suhailat nurse 'din dake kula da ita ta fita sbd idan yashigo fita sukeyi.

Kallon 'dan cikinta yayi batareda ya amsa gaisuwartaba ya dauki file dinta yafara dubawa.

Qamshinsa daya cika dakin ta shaqa tana lumshe ido cikeda qaunarsa mai zafi dake cin zuciyarta.

Yana gama dubawa ya kalleta a miskilance yace,

Did you bleed today?

Girgiza masa kai tayi kala kallonsa ya juya yafice baisake cewa komaiba.
Numfashi tasauke a sanyaye ta zame takwanta.

Kwananta biyar a asibitin akayi discharging dinta tunda suka kamo hanyar gida numfashinta ke fita da qarfi
Jin tayi tafison komawa Libya gurin ammy hankalinta zaifi kwanciya acan.

Suhailat ma tunda tasan zasu dawo gida anyi discharging dinta jikinta yake sanyaye.

Carolina tagyarawa rumanah dakinta tun na farko sosai.

Qarfe goma sha biyu suka iso tareda driver sbd shi theatre zaishiga.

Koda suka iso gidan tuni kayanta dayayi shopping online suka iso har ankai mata dakinta
Itadai suhailat tana bedroom dinta sbd ita bata iya munafurciba arayuwarta bazata iya tsayawa tana rawar jiki akan abinda tasan ba haka bane cikin zuciyarta,
Abinda tasani shine bazata qi rumanah ba bakuma zatai munafurcin nuna mata soyayyar qaryaba saidai zata mutumta ba sbd mijintane ya ajiyeta kuma as along as babu Wanda ya wulaqanta wani acikinsu to zasu zauna lafiya babu takura saidai batai alqawarin ringa zaunawa suna fira tareba gwaradai nesa nesa da juna saisunfi mutunta junansu.

Carolina ta tarbota daga mota suhailat na dakinta suka shigo kai tsaye daki rumanah ta nufa ta zauna bakin gado tareda sakin ajiyar zuciya ahankali.

Ta jima a zaune kafin tamiqe tashiga toilet tayo wanka tazo tasaka doguwar riga mara dogon hannu ta daure gashinta ta saka qaramar hula mara nauyi tayi sallar ishai da akai tana gurin wanka tana idarwa ta fito palo tana qoqarin sakin fuskarta ta nufi kicin inda tajiyo muryar suhailat tana waya taje daukar Abu a fridge.

Gama wayar suhailat tayi ta juyo tana Murmushi tace,

Patient ya jikin?
Barka da dawowa gida.

Jiki alhmdllh naji sauqi sosai
Ina su amah banji hayaniyarsuba gashi naga lokacin dawowarsu daga school haryayi nisa da wucewa.

Sundawo tun dazu suna study room sbd Anfara musu exams.

Jinjina kai tayi tareda ficewa tabar kicin din
Itama suhailat tana gama abinda takeyi ta fice.

Yini guda adaki tayi abinta ko abinci ma daki Carolina ke kai mata.
Ita kuwa suhailat abinda ke gabanta kawai takeyi ba damuwar komai.

Baidawo gidanba sai cikin dare lokacin kowa gidan yayi bacci sama ya nufa dakinsa kai tsaye yashiga yayi wanka harya gama shirin kwanciya ya kwanta babu suhailat bare rumanah da dama baisa ran zata iya zuwaba.

Washe gari koda yayi shirin office harya wuce rumanah na dakinta bata fitoba saida dukkaninsu ta tabbatarda suntafi gurin aiki ta fito.

A dining ta yi breakfast dinta ita kadai tana gamawa tadawo palo ta zauna tana kallo duk da hankalinta ba akan kallon yakeba duka.

Ahaka dai ta wuni ita kadai sai Carolina dake dan tayata fira sama sama sbd ba laifi Carolina din tafi sakewa da ita akan suhailat sbd tafi sake mata.

Suhailat ce tafara dawowa da yamma lokacin tana palon zaune tana gyaran farcenta sanyeda blue skinny jean da red loose top sai gashinta dake dunqule cikin hula red cikin sakewar fuska sosai tayi mata sannu da zuwa.

Cikin sakewa itama ta amsa tana cewa,

Duk kadaici ya dameki babu kowa sai Carolina kuma ita bawani sakewane da itaba.

Nikuma naji dadin kasancewa da ita sbd ba laifi muna sakewa da juna sosai.

Dakinta ta nufa tayi wanka ta sanyo white skinny jean da white chiffon shirt tareda black hula ta fito palon ta zauna kusada rumanah tana cin pancakes suna kallo.

Sallar magrib tasa rumanah barin palon ta nufi dakinta.

Sallah tayi magrib tayi bata fitoba saida tayi sallar ishai ta shiga wanka tana fitowar Carolina tayi knocking ta sanarda ita ana jiranta suci dinner.

Straight skirt tasaka black da black d&g shirt hasken fatarta yafito sosai cikin black shigar ta dauro siririn black scarf tafito tana fidda siririn qamshi ga cikinta daya fito cikin kayan sosai.

Tana fitowa kallo daya suhailat tayi mata ta dauke kai tana murmushi tace,

Ok everybody time for dinner.

Suka miqe fammah na maqale da hannun rumanah suka nufi dining suka zauna.

Abinci sukeci cikin nutsuwa itadai dama tafadawa Carolina noodles With veg zataci saigashi bata wani ci sosaiba saima papaya drink datake ta sha.

Coat dinsa riqe ahannu yashigo palon yana waya.
Chapter 25 · 0% Book details