← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 51

Sashe 44

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basaika datse alaqar dake tsakaninmuba nasan bana ranka ko gabanka kayi qoqarin barina da aurenka har zuwa yanzu da baka sallameni bayan haihuwataba sbd itace amfanina daman shiyasa kace haka sbd sanin sirrin zuciyata saidai........

Fixgoto yayi da qarfi zaiyi magana ta fixge jikinta tana sakin wani irin kuka mai qarfi da ciwo sbd zancensa ya girgiza duniyarta gabaki 'daya ya kasheta jitake zuciyarta kamar zata babbake ta kama da wuta sbd masifar dake ci mata zuciya.

Cikin tsananin damuwa suhailat ta dauki abeel ta nufi palon qurya tafadawa ammy dake zaune cikin tunani abinda yake faruwa.

Da sauri ta taso tana shigowa palon ya juya zai fice ammy tayi saurin riqo rumanah dake kuka kamar ranta zai fita takira sunansa ya tsaya cak batareda ya juyowa sbd qaran kukan dake sake hargitsa nutsuwarsa da tafasa zuciyarsa.

Rungume rumanah tayi tana qoqarin rarrashinta saidai kukane takeyi sosai Wanda ke nuna tsananin ciwo da baqin cikin da zuciyarta ke ciki.

Kasa tsayawa yayi ya rintse ido da qarfi ya fice yanajin baqin cikin kukanta da maganganunta.

Suhailat dake tsaye ji tayi jikinta ya qara wani irin sanyi da kukan da rumanah keyi ahankali ta fice daga sashen sbd ganin suna buqatar tattaunawa tsakanin 'ya da uwa dan jin tayi tazama baquwa acikinsu su duka din har maheer 'din.

Shiru ammy tayi da ita rungume a jikinta batareda tace mata komaiba sbd halinda take ciki tana buqatar tayi kukan ko dan ta rage nauyin dake zuciyarta,

Maganar gskia ko ita bazataso rumanah ta zubar da jiniba sbd sauyi suke fatar samu daga gareta...

Itace sarauniya ta farko a tarihin qasar gabaki 'daya data hau sarauta batareda jinin sarauta a jininta ba bama 'yar qasarba baquwar haure daga wata qasar,

Qaddara ta koro iyayenta daga gida suka fada wani gari inda daganan Allah yasake jefasu hannun masu kamun bayi aka kamosu zuwa nan qasar aka haifeta amatsayin baiwa
Wata qaddarar tasa ta auri yariman masarautar,

duk wannan qaddarar data koro iyayenta ta zamtowarta cikin lissafin masu mulkin qasar ne wannan kawai ya tabbatarda akwai abinda Allah ke nufi da hakan Wanda suke fatar sauyine na alkhairi mezaisa suso ganinta tana aikata abinda sauran sarakunan suka aikata.

Tasan tabbas maheer yayi hakan ne dan bazai iya bari ya rasataba dan idan ta cigaba da zubarda jinin karagar mineelik zata shiga jikintane sosai ta yanda zasu rasata har abada.

Dakinta tashigarda ita ta kwantarda ita kan gadonta ta rufeta tareda shafa kanta ta fice taje palo ta zauna tareda kallon Jakadiya data shigo duba assultana jin shiru dan tuni aka zagaye sashen ammyn da tsaro kasancewar tana cikin.

Dafe goshi ammy tayi cikin tsananin damuwa da rashin sanin mafita tace,

Kije kisanarda sarkin fada haroun assultana ta 'daga hukuncin zuwa wani lokaci batajin dadi yanxu.

Cikin girmamawa da jimami tace,

To""ta fice taje ta sanar atake akai sanarwar aka watse tareda tsananta tsaro sashen ammy.

Har dare tana sashen ammy kwance ko motsi bata yi
tayi wani irin sanyi idanuwanta sunyi jajir.

Shigowa ammy tayi cikin nutsuwa ta zauna bakin gadon tareda sauke numfashi ahankali cikin kulawa da sanyin murya takira sunanta.

Bata motsaba ta bude idanuwanta dasuka kumbura batareda ta amsaba.

Duk wani 'da na halak bazai iya kallon makasan mahaifansa ya qyalesuba matuqar yanada halin daukar mataki ko fansa akansuba..
Saidai kuma dangana da bariga Allah ta wata hanyar shine sasanci da kawo qarshe ga kashe kashen.,
Ummu-rumanah har abada haqqin asma'u da bulama bazai bar ko 'dayanmuba koda kin yafe mana saidai kuma ina sake roqon yafiyarki a maimakon mu duka 'din,
Wlh rumanah ina kallonki amatsayin 'yar dana haifa,
Ina qaunarki da sonki har cikin zuciyata fiyeda wasu daga cikin 'yayan dana haifa shiyasa bazan iya bari naganki cikin wata muguwar rayuwa.

Kisan bashine mafitaba bashine zaisa kiji sanyi a mutuwarsuba saima lalata rayuwarki dazakiyi ta hakan sbd har abada bazaki yafewa kanki abinda kikayiba zaki tsinci kanki cikin baqin ciki da damuwar da muma muke ciki ayanxu,

Mijinki yana miki sonda bazai iya bari ki fada wani mummunan haliba bawai yanayi ne dan karki kashe mahaifinsa saidan yana tsoron hakan zai qarasa gusarda imaninki ne.

Amatsayina na uwa ba sultana matar sultan mahaifiyar maheer ba nake baki shawarar karki kashe mahaifin mijinki ki bar iyayensa da haqqin ran iyayenki wlh Allah zai kamasu sbd baya taba barin haqqin wani akan wani dan haka kiyiwa magana nazari.

Miqewa tayi jiki asanyaye tabar dakin tana fatar rumanar tayiwa zancenta kyakkyawan fahimta.

Qofar da ammy ta fita ta qurawa ido idanuwanta nasake kadawa sbd zancen ya shigeta saidai fadanta da maheer ya kasa barin zuciyarta ta nutsu da daga bakinsa wainnan kalaman suka fito tabbas zuciyarta bazata tsaya wasi wasin daukarsu ba,,

Meyasa zai fada mata kalaman dasukafi dalma zafi gurin tarwatsa kunnuwanta da zuciyarta?????
Meyasa zaiyi fushi ya iya furta mata kalaman rabuwa da ita bayan alqawarin dayayi mata badan mutuwaba dashi da ita bazasu rabeba????
Wasu irin hawaye masu radadi suka gangaro mata ta rintse ido tana qoqarin danne kukan dake qoqarin zuwar mata.

A cikin daren takoma sashenta tareda guards inda ta bada gargadi mai qarfi akan batason ganin kowa.

Kwana biyu tayi bata fito ko qofar part dinta ba..
Abincin safe rana dare haka ake kwashesa bata fitowa saidai ammy tazo dakanta har bedroom tasata cin abinci dole.

Duk iya yanda take jin kewa da soyayyarsa na cin zuciyarta dannewa tayi sbd har lokacin zuciyarta cike takeda zafi da radadin kalamansa shima kwana biyun bai nemeta ba hakan yaqara quntata yanayinta.

Nuratu data rungumi qaddara da hannu bibbiyu akan mahaifiyarta still itace ke kulada rumanar amintacciyar baiwarta duk da da farko anso hanata ko kusantar inda rumanah take saidai rumanar ta hana sbd tasan suna tsananin buqatar juna sbd sukadai suke ganin junansu amatsayin jininsu tunda mamani sunanta matacciya.

Sultan kuwa a rubuce ta aikawa harooun da takardar a tsananta tsaro a sashensa kowama yanxu ta hana yashiga gurinsa
Hakan kuwa akayi nan take aka cika umarninta tareda bada gargadi ga duk Wanda yaje kar abari yashiga.

Kwance take kan doguwar royal chair 'din shaqatawa dake qaramin palonta dakeda manyan qofofi guda biyar dasuke ta bayan garden din shashaqatawarta,

A rufe idanuwanta suke saidai Sam ba baccin takeba iskar gurin mai sanyi take kado mata ta shara sharen labulayen winduna da qofofin palon dan ragewa kanta zafi da quncin datake ciki.

Ahankali ta jiyo kukan jariri na shiga kunnenta ta bude idanuwanta a hankali sbd tasan kukan abeel ne tunda kaf masarautar babu jariri bayanshi.

Tashi zaune tayi cikeda kewar 'danta da tausayinsa na rashin 'dan uwansa dakuma 'dumin jikin mahaifiyarsa
Miqewa tayi ta nufi qofar bakin window ta tsaya tana hango cikin bedroom din suhailat da itama ta iska ke daga farin labulenta....

Rungume take dashi a tsaye tana jijjigasa cikin tsananin kulawa da damuwar kukan nasa
Ta 'dagosa tafa duba fuskarsa cikin qaunarsa tayi kissing kumatunsa tana cewa,

Abeel please kayi hakuri mummy bazata sake baka maganin zazzabi ba kaji pls my little prince forgive mummy......

Hawayen datake ruqewane suka gangaro mata na tsananin soyayyar 'danta da qaunarsa saidai kuma bazata iya karbarsa daga suhailat na....

Tunda ta shigo rayuwarta ta sanadinta ta rasa komai,

Ta rasa jin dadi,kwanciyar hankali da soyayyar mijinta sbd ita,
Ta rasa babynta sbd jin mijinta ya aureta,
A yanxuma ta rasa jemal ne sbd ita Dan 'yayanta akaso kashewa duka tsautsayi yasa aka kashe mata jemal kuma gashi ta rasa mahaifarta har abada...
Gashi ta riqe 'dan kishiyar datai sanadin rabata da komai da zuciya 'daya tana qaunarsa tamkar itace ta haifesa,,,
Wace irin soyayyace takewa maheer??sbd tasan tana tsananin qaunar abeel ne sbd shi 'din tsotson maheer ne.

Idan suhailat ce a matsayinta na yanxu zata iya kashe mahaifin maheer?

Duk wainnan abubuwan da suhailat ta rasa ta dangana bata riqe kowa araiba gashi tana rayuwarta gwargwadon iyawarta batareda tasaka damuwar duk Wanda ya cucetaba koya tauyeta.....meyasa ita takasa hakan?
Suhailat tafita son maheer ne???

Girgiza kai tayi tareda durqusawa a gurin tana zubarda sabbin hawaye masu radadi da ciwo gabaki 'daya ta rasa nutsuwarta da sukuninta rashinsa atareda ita jitake tanason zubarda jinin duk Wanda ya cutatar da ita da iyayenta da 'yayanta SBD kalamansa dasuke yawo cikin kanta suna qona zuciyarta...
Cikin kuka tace,

Bakasan rashinka taredaniba ha'darine dan zan iya aikata abinda bakason dan Allah kadawo gareni maheer.

Suhailat data shigo palon dan kawo mata abeel tagansa sbd ta hangota lokacinda take kallonsu tayi saurin tsayawa cak jin abinda rumanar tace.

Numfashinta taji yaqara gudu tayi saurin juyawa dan ficewa tun kafin rumanar taganta
Saidai tana juyowa tagansa tsaye bayanta idanuwansa sunyi wani irin zurfi ya qureta da ido.

Tsawon kwanaki kenan itama bata sakashi a idoba 6acin ran rumanah duk yashafesu saidai Sam bata damu sosai da rashin ganinsaba sbd tasan irin radadi da zafi da zuciyarsa ke ciki na fada da abinda kafiso fiyeda komai.

Rabasa tayi zata fice sbd ahankali ya kira sunanta ta tsaya cak
Rumanah kuwa tun shigowarsa taji qamshinsa saidai bata juyoba sbd wani irin bugawa da zuciyarta keyi.

Hannu ya miqa ya dawo da suhailat gabansa cikin murya mai bada umarni yace,

Miqa mata 'danta.

Arikice takallesa itama rumanah a firgicen ta juyo takallesa.

Fuskarsa a matuqar 'daure yace,

Kibata 'danta.

Wasu irin hawayen soyayyar abeel da qaunarsa suka gangarowa suhailat takalli abeel din takalli fuskar maheer din taga babu sakewa ko kadan ta juya tana tsiyayar hawaye qafafunta na rawa ta nufi rumanah datai mutuwar tsaye cikeda mamakinsa.

Siririn kuka suhailat tasaki tareda 'daga hannuwanta ta miqawa rumanah abeel.

Cikin rawar murya rumanah ta bude baki daqyar tace,

Nabar miki shi.

Girgiza mata kai suhailat tayi tana wani irin kuka mai ciwo da qaramin sauti.

A firgice tasake cewa,

Wlh na barmiki shi....

Girgiza mata kai suhailat tasakeyi tareda ajiye mata shi kan kujera ta nufi qofa da gudu tana toshe bakinta sbd kukan dayaci qarfinta.

Dawo ki daukesa.

Cak ta tsaya tareda juyowa takallesa da sauri

Ki daukesa nabakishi bar abada 'dankine.

Da sauri tadawo ta daukesa ta rungume tareda dawowa gaban maheer din ta rungumesa cikin tsananin farin ciki tace,

For a moment I thought na rabu da abeel har abada..nagode.

Kallon rumanah data zuba masa ido yayi cikin kulawa yace,
Chapter 44 · 0% Book details