← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 51

Sashe 17

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Qura mata ido yayi yana mamakin hawayenta sbd dukkanin alama na ciwon datajine abinda baitaba ganiba ga suhailat duk kuwa wuya da azaba yanada wuya suhailat tayi hawaye
Ita kuma wannan hawayen nata na shagwabane tunda daga Dan wannan ciwon sai hawaye.
#mamuhgee
[10/07, 04:54] 80k: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_haske writers association_💡

*20*
Not edited
Dagowa tayi takallesa tana qoqarin tsayarda hawayenta
Suna hada ido ya miqe tsaye ya nufi bedroom dinsa batareda yace qalaba ko waiwayenta.

Kallon hannunta tayi dake radadi sosai tasaka 'dayan hannun ta share hawayenta ta miqe ahankali taja hular rigarta ta rufe kanta ta nufi qofa ta fice.

Tana saukowa ta tararda Carolina a palo tana qoqarin fara aikin gyaran gidan sbd su amah zasu school.

Kallonta Carolina tayi cikeda mamakin ganinta tana saukowa daga saman a wannan time din saidai kuma ba abinda yashafi aikinta bane sai kawai taci gaba da aikinta
Itama rumanah nauyin Carolina din taji yasa takasa yimata magana ta nufi dakinta tashige.

Toilet tashige tayo alwala daqyar sbd ciwon hannunta tafito tayi sallah tana gamawa ta fito ta nufi kicin saidai duk yanda taso tayi aiki kasawa saidai takoma daki ta zauna ta qurawa hannun ido tana tuno yanda ciwon yasamu.

Lumshe ido tayi tuno kalamansa"""inada nauyi ne?"""
Sai a lokacin mamakin maganarsa yake shigarta
Tasake tuno qaqqarfan jikinsa saikuma tayi saurin lumshe idanuwa sbd kunyar ganinsa dataji saikuma taji sanyin qamshin turarensa yashiga hancinta tayi saurin bude ido taga babu kowa zuciyarta ta buga da qarfi.

Mikewa tayi ta nufi jikin window ta tsaya
Wani sabon qamshinsa taji yashiga hancinta har zuciyarta ta rufe fararen idanuwanta ahankali tareda budesu takoma bakin gado tasake zaunawa har lokacin hancinta da idanuwanta sunkasa daina jiyo qamshinsa
Zuciyarta takasa sukuni
Rashin sukunin hakan yasata miqe tafito jiki asanyaye ta nufi kicin.

Duk yanda taso yin aiki a kicin kasawa tayi sbd rashin nutsuwar datake ciki gashi hannun yafara kumbura saidai batajin zafin kamar yanda takejinta cikin rudu da rashin sanin abinda yake damunta.

Kallo Carolina tabitadashi ganin kamar tana cikin damuwa gakuma hannunta daya kumbura cikin tausayawa tace taje daki ta huta tana kwatanta mata da hannu.

Murmushi qarfin hali tayi zatayi magana doorbell yayi qara atare suka kalli agogo da Carolina sukaga qarfe bakwai da minti goma,

Wanke hannu Carolina tayi ta fito cikin din ta nufi qofa ta bude.
Dawowa tayi riqeda leda fara ta kalli rumanah tace taduba mata chips data zuba ta nufi sama.

Knocking tayi ahankali saidai ba amsa hartagaji bail budeba harta aje saidai tadawo qasa dashi takalli rumanah tace magani ne batasaniba ko urgent yake buqatarsa gashi bata shiga bedroom dinsa ta miqawa rumanah tace ta taimaka mata taje gurin sultana tafada mata kozata kirasa awaya tasanar masa.

Qura mata ido rumanah tayi sbd sanin bata tada sultana idan tana bacci ataqaicema lokacinda take tashi bacci baiyiba saidai zuciyarta na fargaba da idan yana buqatar maganin ne a gaggauce.

Karbar maganin tayi ta fito palo ta nufi dakin sultana saidai kuma tasamu kanta da tsayawa cak sbd qila yana cikin wani haline yake jiran maganin.

Juyawa tayi ta nufi saman tana qoqarin danne faduwar gabanta harta isa ta shiga palon ta nufi qofar bedroom din tayi knocking.

Shiru ba amsa tasake yin knocking din still ba amsa
Kasa juyawa tayi ta rabe qofar dakin gabanta na tsananta faduwa hakama takasa tafiya sbd fargaba.

Jin shiru sosai yasata qara kwankwasawa cikin nutsuwa tana qoqarin sake kwankwasawa aka bude dakin hakan yasa saura kadan ta fada masa tayi saurin daidaita tsayuwarta tareda sauke kanta qasa daqyar ta furta,

Ga saqo aka kawo.

Batareda yakalletaba ya karbi maganin cikin maqoshinsa yace,

Wait.

Cak ta tsaya ya bude ledar yaciro maganin yaduba ya miqa mata.

Dagowa tayi suka hada ido danasa dake kafe da ita tasaka hannu takarba hannunta yakalla batareda yaqara cemata komaiba ya rufo qofar.

Hannunta daya kalla yasa ta fahimci mai hakan ke nufi takalli ledar maganin tasaki fuska akaro na farko datayi murmushin daya fito daga zuciyarta tun bayan rasuwar iyayenta.

Saukowa tayi ta nufi dakinta ta ajiye maganin ta zauna duk bayan minti qalilan tana waiwayowa takalli ledar.

Qarfe takwas su amah suka tafi school bayan fitarsu da awa 'daya ya sauko cikin wasu blue black Balenciaga's suit dogon gashinsa a daure qamshin turarensa na annick goutal mai sanyi ya ratsa palon sosai wayarsa ce kawai ahannunsa sbd meeting zaije ba ba asibiti ba saiyadawo zaije hospital din.

Itakadaice a palon itama fitowarta kenan cikin doguwar riga ash zata dakin sultana sbd lokacinda ake gyaran dakinta yayi.

Sunkuyar dakai tayi sum sum tashige dakin sultana.

Tana shiga ta tararda ita zaune kan couch tana waya cikin girmamawa ta durqusa tagaida da kai ta daga mata sbd wayar datakeyi.

Tashi tayi tafara qoqarin gyaran dakin cikin dauriya sbd tsananin azabar da hannunta ke mata saidai bazata iya barima sultanar tasaniba.

Shigowa dakin yayi da sallamarda shikadai yaji abarsa ya nufi gurin ammyn ya sumbaci hannunta data miqa masa yana cewa,

Saba'ul khair ya ammy.

Murmushi tasakar masa tareda katse kiran ta ajiye wayar tana cewa,

Barka da fitowa yarima maheer.

Kallonta kawai yayi batareda ya amsaba yace,

Zan fita sainada dawo.

Allah yatsare but did you take your breakfast?

Kai kawai ya daga mata ya juya haryakai bakin qofar dakin ya tsaya batareda yajuyo ba cikin husky voice dinsa yace,

Bani fruits din gaban ammy.

Yawu ta hadiye cikin faduwar gaba sanin da ita yake saidai bazata iya dauka da hannu dayaba dole sai biyu gashi batason ammy tasanda ciwonta.

Kallonsa ammy tayi cikin mamaki ganin baya tabacin abinda bashi aka kawowaba.

Cikin sanyin jiki ta aje pillon dake hannunta ta je gaban ammy ta dauki dan glass bowl din amma tuni hannunta ya gaza bowl din yafadi qasa ya fashe.

Da sauri ammy takalli fuskar rumanah din
Da sauri ta durqusa zata bada hakuri sultana takalli hannunta cikeda mamaki da kulawa tace,

Rumanah hannunki akumbure,
Ciwo kikaji shine kike aiki?

Numfashi ya sauke a maqoshinsa kafin ya ficewarsa sbd dama abinda yakeson ammyn ta fahimta kenan.

Ita kanta tagano dan ammy tasan taji ciwo yasata daukar Abu mai nauyin da bazata iya dauka da hannu dayaba saidai batasan dalilinsa nayin hakanba.

Qura mata ido ammy tayi cikin sigar fada tace,

Meya samu hannunki ya kumbura haka kamar ma karywa ko targade.

Kallon qofar daya fita tayi asace kafin ta sunkuyar dakai cikin sanyi tace,

'Yar buguwace nayi.

Yanayinta sultana takalla taga alamun ba gskia tafada mataba sbd tasan rumanah tun tana jaririya saidai tasan bata taba yimata qaryaba.

Qofar itama takalla sbd taga lokacinda rumanah tasaci kallon qofar lokacinda maheer yafita kenan yana sane da ciwon,
Kodai dama da gangan yasata daukar Abun?

Maida kallonta kan rumanar tayi cikin kulawa tace,

Menene kika bugu dashi?

Qofa.

Sake kallonta ammy tayi tasan tabbas ba abinda tafada din bane taji tausayinta yakamata tace,

Tashi kije zansa maheer yaduba miki hannun idan yadawo.

Miqawa tayi ba musu ta fice sbd zata iya cewa tunda take arayuwarta batasanma ya ake musuba a alamari duk abinda aka sata shitakeyi sbd suma basu taba sata abinda yakaucewa addininta ko lafiyartaba.

Abinci taci kadan tasha magani dakuma shafa ta kwanta nan take bacci yayi gaba da ita.

Ranar Carolina ce tayi aikin komai ita kadai.

Suhailat ta farfado saidai ko motsin kirki da magana bata iyayi komai sai anyi mata koda su amah suka dawo school da yamma tareda sultana suka nufi hospital dubo mum dinsu.

Kodata tashi bacci hannun ya sauka gabaki daya babu wani zafi sosai ta sauko gado ta tube tashiga toilet tayo wanka da ruwan zafi sosai hannun da jikinta dayaso kamuwa da zazzabi suka saki tayi sallah ta fito taci abinci nan takama aikin dinner babu bata dogon lokaci suka gama home made pizza sai boiled vegetables da kuma fruits salad din yarima.

Itace ke jera abinci a dining din suka shigo
Shine agaba hannunsa riqeda riqar suit dinsa ta sama farar long sleeve dinsa kamar yanxune yasata
Kallo daya tayiwa hanyar shigowar ta sauke kai tana aje cups din hannun ta.

Shi ko kallon inda take baiyiba duk da acikin idon juna suka fara cikin karo ya wucewarsa sama.

Dagowa tayi tabi bayansa dakallo yana kaiwa qofa zai shiga ya tsaya cak
Tayi saurin dauke kanta shima baijuyoba sai yashige.

Ajiyar zuciya tasaki cikin ranta tana qoqarin daidaita numfashi.

Ammy dake kallonsu tun shigowarta tasaki numfashi tareda nufar hanyar bedroom dinta tashiga.

Wanka yayi yayi sallar magrib yana zaune kan sallayar akayi ishai yafito yaje masallaci dagacan yana dawowa ko shigowa baiyiba hospital yakoma.

Kwance take idanuwanta a rufe amma hawayen daya gani yasashi sanin idonta biyu yakalli nurses din dake tareda shi da sauri suka fice.

Shafa fuskarta yayi ta bude idanuwanta dasuke jajir ta qura masa ido zatai magana ya girgiza mata batareda yabude bakiba.

Share hawayenta tayi daqyar sbd nauyin jikinta cikin tsanani sanyin murya tace,

I love you...i love you and pls always remember it even in the future.

Lumshe ido yayi batareda yace komaiba ya sunkuya yayi kissing forehead dinta murya daqyar yace,

Time to sleep,Gud night.

Lumshe ido tayi tareda gyara lullubinta ya sake kissing dinta yafice bayan yaduba file dinta.

Koda ya isa gida babu kowa a palo sai sultana itama dan tanason ganinsa ne.

Yana ganinta yasan dawowarsa take jira yayi kissing hannunta yace,

Gud night ammy jeki kwanta nadawo.

Murmushi tayi tareda miqewa ta fuskanci qofar bedroom dinta harzata wuce tace,

Gobe inason kayi mana booking flight zamu wuce Libya nida rumanah zuwa jibi,
Kuma inason kafin natafi da ita tasan matsayin aurenta sbd idan munje ba dawowa zamuyiba acan inason tasamu sabuwar rayuwa dan haka kanada zabin iya sauwaqe mata kafin jibi muwuce.

Tana gama fada bata juyoba ta shige dakinta.

Cak ya tsaya bakin stairs din tun lokacinda tafara magana harta gama yana waiwayowa tana shigewa.

Qofar dakinta yakalla kafin ya haye yana isa daki ya kashe wayarsa data damesa da ringing batareda yaduba mai kiranba.

Tubewa yayi yafada toilet yayo wanka yana fitowa yagama shirin kwanciya ya kwanta.

Gari na wayewa ya qarfe tara saura ya sauko cikin shirinsa sbd yanada tiyata har biyu yau.

Motsi yaji dakinsu amah yasa ya tsaya tareda waiwayo qofar tareda tunanin meyasa basu tafi school ba har time din.
Chapter 17 · 0% Book details