← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 30

Sashe 8

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ga mamakinsa sai yaga Ammah tana dariya sai da ta yi mai isarta sannan, tace Muhammadu ba cassette bane Anaal ce.
"Rass-rass.....gaban Ansar ya yanke ya fad'i zuciyarshi tashiga bugawa da sauri-sauri sai kawai ya yi murmushin yak'e yace ikon Allah ni na dauka a DVD plate ne.
''A'a bashi bane k'anwarka ce Anaal k'ara shiga rud'ani ya yi shi dai yana jin sunan nan a bakunan mutane gidanan, dai-dai da sau d'aya bai ta6a cin karon da mai wannan sunan _shin wacece Anaal"?_ lallai yakamata na nemo sanin akan wannan Anaal mai zazzaqar murya. A karo na biyu yak'ara juyawa jiki a mace yafita yana zuwa ya mik'awa Abbah murhun garwashin, ya ja kujera ya zauna yashiga tunanin wacece Anaal"? Ko ma wacece ita Allah yabarkace ta da dad'in murya gashi ta iya karatun Qur'ani kowane harafi tana bashi hakk'insa zuciyata tana mararin had'uwa da ke Anaal n.........muhammadu"!
Abbah ya katse masa zancen zucin da yake yi.
"Na'am,,,,,,Abbah.
Muhammadu ka tayani murna k'anwarka Anaal saura surah d'aya ta hadace Al-qur'ani mai girma.
Ba ka ji farin cikin da nakeji ba muhammadu nikan zuwa Najeriya ya yi min rana 'yata ta albarkatun da ilimin addini da na zamani.
Allah yasakawa Alhaji sa'eed da gidan aljanna ya yi min alheri da har na ko ma ga ubangijina ba zan manta da shi ba.
"Shi dai Ansar mutuwar zaune ya yi sai yanzu ya fahimcin Anaal 'yar Abbah da Ammah ce.
To ya akayi duk zuwan da nake yi gidanan ko a bisa kuskure banta6a had'uwa da ita ba.
Ansar ya had'iye yawu yace Ameen Abbah ai yi wa Kaine ita kuma Anaal Allah yasa mata albarka a karatunta yasa abunda za ka ci amfani sa ne.
Ameen muhammadu
''Yayinda Abbah yacigaba da cewa waton Muhammadu ba yabon kai ba wallahi ina alfahari da 'yarta sai dai kashhh.....akwai abunda yake cin min tuwo a kwarya.....Abbah yad'an shed'a damuwa ta baiyana k'arara akan kyakyawar fuskarshi. Daga bisani yacigaba da cewa sanin kanka ne Muhammadu mu baqi ne kowane lokacin za mu iya komawa k'asarmu, Agadaz a can Agadaz muna zaune ne a wani k'auye dajin Allah Jama'a mazauna wannan k'auye ba abinda mu kasani sai kiwon awakai da rak'uma muna rayuwa tamkar wad'annan awakai da rak'uma kasan dalilin da yasa nace da kai haka"?
"Ansar ya girgiza kai.
Abbah yace saboda ba mu da wadatace ilimin addini islama balle aje ga ilimin boko shi ka ajiye shi a gefe domin ba mu basan menene shi ba.
''Zuwanmu Najeriya mu ka fahimcin menene addinin musuluncin har mu ke gudanar da ibadunmu adai-dai shiyasa nake da burin Anaal tana, gama sakandire na aurar da ita saboda ina fargaba komawa Agadaz da ita mahaifina zai iya aurar da ita ga jahilan k'auye.
Abbah yak'arasa magana kamar zai fashe da kuka.
"Sauke numfashi Ansar ya yi yace wannan ba abin damuwa bane Abbah insha Allah, kafin tak'arasa karatun nata Allah zai kawo mata mijin aure. Sai dai Abbah wani hanzari ba gudu ba a yanda naji kana yaba hazaqarta me zai hana kabarta ta je makarantar gaba da sakandire kafin Allah yakawo mijin sai ka aurar da ita.
"Jikin Abbah yadauki rawa yana girgiza kai kul,,,,,muhammadu karka sake yi min maganar makarantar gaba da sakandire nan, banda tambad'ewa da lalacewa da rusawa 'ya'ya mutane tarbiyya ba abunda suke koyarwa. Ai ni na d'auki darasi daga kan yaran gidanan ada kafin su je makaranta nan duk fad'in unguwar nan ba 'ya'ya da suka fi su natsuwa da ingantattaciya tarbiyya sa6ani yanzu da ake buga misali da tarbarbarewa tarbiyya akansu.
''Ansar ya gyara zamanshi yak'ara fuskanta Abbah ya yi k'asa da murya ni a nawa gani Abbah duk mutume da ka ga ya je highschool ya sauya kyakyawan halinsa zuwa mummuna to dama can yana da burin yin hakan. A yanda naji kana yaba hazaqar Anaal bai dace ace karatunta iya secondary ya tsaya ba.
''Abbah kai kanka kana da yak'ini akan irin tarbiyyar 'yarka take da ita bai kamata kasa shakku akanta ba. Kabarta tacigaba da karatu irin basirar da take da irin wance al'ummar musulme za su amfana da ita ne.
"Har Ansar yadasa aya Abbah yana kallonshi yana kad'a kai alamar yafara gansuwa da jawabin nashi. Abbah ya gyara zama Muhammadu ban k'i ta taka ba nima na gabarta maka da nawa uziri, ba wai ina shakka ko kwankwanto akan Anaal bane ina tausayawa irin rayuwar da za ta yi indan lokacinmu komawar mu Nijar ya yi batare da ta yi aure ba.
"addu'a kawai za ka yi mata Abbah domin Allah yana saurin kar6a addu'ar iyayye akan 'ya'yansu.
Shikenan Muhammadu Allah ya za6a mata abinda yafi zama alheri a rayuwarta.
''Ameen Abbah tana aji nawa ne"?
Tana shekarar karshe Abbah yafad'a had'e da mik'ewa yasauke green tea ya zuba a cups sai tiriri yake ya zuba sugar kad'an ya mik'awa Ansar cup d'aya.
Ahankali Ansar yake kur6a green tea saboda zafi da yake da yana sha Abbah na bashi labarin Anaal Ansar yana shanye green tea yadire cup cikin girmamawa ya dube Abbah bara na shiga ciki Abbah na gaida su Granny.
Toh Muhammad a fito lafiya.
Ansar ya amsa da cewa Allah yasa ya juya a natse yashiga part d'in Granny a parlour ya tarar da ita da littafin izziya ta kwama medical eyeglasses tana karatu.
"Tsaye ya yi yana kallonta ya kwashewa da dariya a firgice Granny tad'ago sannu a hankali ta ajiye littafin hannunta ta zare eyeglasses d'in idonta ta dubi Ansar ta galla masa harara kai shak'iyi ni ka ke yi wa dariya"?
"Dole nayi miki dariya Granny kinga yanda ki ka tak'ark'are kina karatu sai kace zamani da ki ke cikin ganiyar kurciyarki lallai tsohuwa nan kin mana wayo, nima ya zama dole na koma islamiyya.
Yak'arasa magana had'e da zaunawa kusa da ita dariya Granny ta yi ba dole na tak'ark'are ba na fi wannan dak'iki'ya matar taka wance ko Hizzib 10 ba bu akanta sai d'an banzan fad'in ran tsiya.
"Uhm,,,,,Uhm,,,,Granny karki yi wa matata sharri.
Ba sharri nake mata ba gaskiya ce nake fad'a ga malama a gida a maimakon su dinga zama tana, daura musu karatu tunda sun karkare zuwa islamiyya shiririta ta hanasu.
"Ansar ya girgiza kai takaicin ya baiyana k'arara akan fuskarsa Granny lamarin yaran ne sai addu'a especially Zuhura domin gara Nazeeya sau dubu da ita.
"Granny ta yi ajiyar zuciya mai k'arfi bari kawai Ansaru hannunka ne baya ru6ewa ka yanke ka 'yar da tuni nace ka hak'ura da auren Zuhura babban takaicina da al'amarin Zuhura rashin kula da addini lokacin sallah ya yi ta yi zamanta tana latsar waya, har sai wata sallah ta riske wata sannan ta had'e su tagama ta kai tsakiyar dare tana latsar waya batare ta yi sallah isha ba, sai da safe ta yi ta wannan bala'in da me yai kama"? Mahaifiyarsu taana kallon wannan tabargaza da suke tafkawa bata iya kwa6arsu sai kace 'ya'yan ido, shi kuma sa'eedu baya iya aiyana komai tariga ta shanye shi. Hatta da girki yaran nan basu iya ba saidai Anaal tashiga kitchen su kuma, su hakince parlour suna latsar waya basu San cewa Kansu suke kwara ba Anaal ba domin duk namiji da aure Anaal wallahi ya yi dace da mace tagari mai nagartaciyya tarbiyya Anaal ga hankali da natsuwa ga ladabi da biyayya uwa-uba ilimin addini da na zamani a rayuwata banta6a gani yarinya mai natsuwa da kamalla irin Anaal ba.
Kalle ni da tsofan nawa nake zaunawa Anaal ta daura min karatu sa6anin su da kurciyarsu sun k'asa yi a kullum cikin yi musu nasiha take akan su daure su koma islamiyya sai dai su yi mata dariya ko tsaki. Sai anan gaba za su gano amfani nasiha da Anaal take musu.
"Gumi ya tsiyayowa Ansar saboda shi baisan bankad'a na Zuhura har ya yi k'amari haka ba. Haushi da tsanarta suka lullu6e shi ya ma tsani cigaba da zancenta domin zai iya hadasa masa bugawar zuciya hakan ne yasa yakawo karshen zancenta nata ta hanyar cewa........

Jeeddah Aliyu*SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*8*
Chapter 8 · 0% Book details