← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 30

Sashe 28

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mushirikin murmushi leeabeauty tayi tace ina mamakin yanda ki ka yarda da Ansar Galadima, ko kinmanta da halin d'a namiji ne...? Namiji hankaka ne gabanshi fari bayanshi bak'i amma tun da kin yarda da shi miye nawa aciki.....?
Ba shakka leebeauty na yarda da Ya Ansar 100% ba wata 'ya mace da zai so fiye da ni, na mallaki duk wani abu da Ya Ansar yakeso awajen 'ya mace ta ya Wanda yakeda ni me zai yi da Anaal, karki manta Anaal 'yar Matsiyata ce 'yar masu gadi duk duniya ba abinda iyayyen Ansar suka tsana irin fak'iri Anaal kuma fak'iriya ce, ta ko ina nayi mata zarar Ya Ansar kuma yai mata nisa.

Zuu kenan lallai idanunki sun rufe Sam bakya hango abunda nake hangowa, na yarda kina da Body structure da Ansar Galadima yakeso amma abin tambaya anan shin kina da kyakyawar tarbiyyar da Ansar Galadima yakeso matarshi ta kasance da ita ko kina da ilmin islama da yake burin matarshi ta mallaka....?
Shiru Zuhura tayi takasa bata amsa
Toh tun da kin kasa bani amsa ni bara na bawa kaina bakida ko d'aya daga cikin abubuwa da na lissafa, Anaal kuma tana da su Kidàina taqama da kyakyawar sura wani namiji ba ruwanshi da wannan.

Komai za ki fad'a ba zan yarda ba Co's ba yanda za'ayi Ya Ansar yaso Anaal never! wallahi, ta6e baki leebeauty tayi cike da takaicin tajuya tanufi k'ofar fita daga garden, Zuhura tabita da harara daga bisani tadawo da ganinta ga Anaal ke kuma bana ko shakka hanya Ya Ansar yarage miki ko ba haka bane tafad'a cikin tsawa..?
"Ha...ka...ne Anaal ta amsa cikin rawar murya.
''Daga yau wannan yakasance na farko na k'arshe da za ki sake shiga motar Ya Ansar muddin kinason kanki da arziki, ki nisance shi ba ke ba shi ko karatu da ki ke fad'a masa na kashe karki sake naganki ko naji labarin anganki da shi kinji ko bakiji ba....?
Na....ji
Kin samawa kanki lafiya da Matsiyatan iyayyenki, tajuya tafice tabar Anaal na kuka nashiga 3 ni Anaal nadaukowa kaina ruwan dafa kaina zuciyata ba ki yi min adalcin ba kin kamu da son mutume da yafi k'arfina, ashe Ya Ansar bayason mace mai irin Body structures d'ina yatsani farar mace mafi alheri atare da ni na rufawa kaina da iyayyena asiri na datse duk wata hanya da zata had'ani da shi.
Ta share hawayenta ta mik'e tanufi part d'in Granny sauk'inta d'aya Granny batanan tafita unguwa tawuce bedroom tafad'a bisa gado tayi kwance rub da ciki ta bud'e Sabon shafi na kuka, fuskarta tayi jajur idaunta sukayi luhu-luhu abunka da farar fata.

Da tagaji da kukanta ta mik'e tashiga bathroom tayi wanka da alwala ta gama sallah tad'aga hannayenta sama idanunta na fitarda hawaye tashiga rok'on Allah ya yaye mata son Ya Ansar ta Shafa addu'a ta mik'e ta linke pray mat tasaka gown na atamfar deviva wax bata damu tashafa mai ba takoma ta kwanta ta d'auki wayarta tacire battery tayi mata mugun 6oyo, ranar kasa zuwa islamiyya tayi da Granny tadawo ta tambayeta meke damunta sai cewa tayi batada lafiya Granny ta tausaya mata sosai harda su bata panadol extra batasan bashi bane ainihin maganin ciwon Anaal ba.

_Dare_
9:00pm

Ansar yafito daga bedroom zuwa parlour yana sanye cikin kayan bacci, yaciro wayarshi daga charging yanemi kujera ya hakince digit d'in Anaal yakira ga mamakinsa sai yaji wayar rufe.

Jeeddah Aliyu
[6/28, 8:49 PM] YAYA HAYAT: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*25*

_HBD my beautiful shaning angel *ZARAH B~b* wish you long life & prosperity Allah yakawo miji nagari_

Cike da takaicin ya ajiye wayar haushin kanshi yaji yanda yakasa chanzawa Anaal waya tun lokacin da yaga 'yar kwamarta{lol Nokia} yakeso yasiya mata waya 'yar zamani hidimomin da sukayi masa yawa yasa ya manta, domin da ganin wayarta ba lallai bane tayi rik'on charging ya k'udurta aranshi ya zama dole ya chanza mata waya.

_Washe Gari_

Anaal bata tsaya jiran Ansar ba gargad'in Zuhura yashige ta, tahau adaidaita tafi school su Ramlat naganin yanayinta suka San ba lafiya wai kare yasha taba titseta sukayi har saida tafad'a musu musabbabin damuwarta amaimakon su Ramlat su goyi bayanta tabar Ansar saima sake k'arfafa mata guiwa sukayi hannunta zeenat tarik'o karki yi sauri karaya 'yar Agadez dama dole ki fuskance irin wannan k'alubali don haka sai kin jajirce kirage wannan masifafen tsoron naki, ki zama jaruma ta haka za ki mallaki Ansar Galadima karki manta matsoracin bai ta6a zama gwani.

Ramlat ta kar6e zance ta hanyar cewa wannan somi ta6i ne ki ka fara gani dole sai kinsaka juriya da hak'uri sannan za ki cima gaci, kinason Ansar so ba na wasa ba Inkika hak'ura da shi yin hakan zai iya zama barazana ga lafiyarki.
Jin su kawai Anaal takeyi ba wai don za ta yi amfani da shawarar su ba.
Ana tashi daga school tana fitowa gate ta hango motarshi mtcsww! Taja tsaki ranta a6ace ta chanza hanya daga cikin mirror ya hangonta mamakine ya kamashi me Lucky take nufi...?
Laifin me nayi mata da safe tayi tafiyarta bata jirani ba yanzu kuma nazo daukarta ko kallo ban isheta ba.

Bai gama tunanin ba yaga ta tsallaka titi da sauri ya 6alle k'ofa motar ya bi bayanta yana isa wajenta tana tsayarda Mae adaidaitasahu, bai kamata ki hukunta ni da laifin da banida masaniya akai iya Sanina ba laifin da nayi miki infact koda nayi miki laifi yakamata kiyi min uziri domin ni d'an Adam ne dole wata rana ki sameni da aikata ba daidaiba.
Batare da ta dubeshi ba tace ba laifi da kayimin kawai inason na d'auke maka wahalar kaini da daukoni school da ka ke yi yakamata ka huta kaji da naka hidimomi.
Tana k'arasa magana bata jira jin ta bakinshi ba ta shige adaidaita tsananin mamakinta yahanashi yunk'urin tsayarda ita sai kawai yabi bayan adaidaita da kallo yana cizo le6e jikinshi asanyaye yasake tsallaka titi yakoma wajen motarshi.

Duk abinda yake faruwa akan idon su Ramlat cike da haushin Anaal, zeenat ta ja tsaki mtcsww! Banta6a sanin 'yar Agadez batada wayo ba sai yau in banda rashin wayo miye na Ansar Galadima aciki da zata dau fushi da shi?
Ta6e baki Ramlat tayi tana girgiza kai kinsan me...? Zuwa mu yi musami Ansar mu warware masa zare da abawa domin guy nan yabani tausayi kalli yanda, ya yi tsaye turuss! Gwanin ban tausayi kai *so* masifa ne.
Batare da dogon nazari ba suka nufi wajenshi kafin su isa har yashiga motarshi da sauri suka k'arasa zeenat tayi knocking glass da ke side d'in da yake zaune ahankali yasauke glass d'in ganin k'awayen Anaal ne yasa yasaki murmushin yak'e zeenat, Ramlat ba Ku tafi gida bane ko drivenku baizo ba?
Ramlat tace baizo ba amma yana hanya Ya Ansar dama zuwa mukayi musanarda kai abinda yafaru domin, Anaal ba sanarda da kai zatayi ba nan take Ramlat ta kwashe labarin da Anaal ta basu tafad'a masa jikinshi ya yi bala'in sanyi yarasa abin fad'a dole ya yi musu sallama yakoma office.

Zuhura da leebeauty suna la6e a lungu suna jira su ga ta inda Ansar da Anaal za su 6ullo akan idonsu mai adaidaita yawuce da Anaal, Zuhura ta dube leebeauty tace nafada miki k'awata ba abinda Ya Ansar zai yi da 'yar masu gadi, ita kanta Anaal gargad'in da nayi mata yashigeta mu tafi kawai office d'inshi na bashi hak'uri.
What's?
Hak'uri fa ki kace zuu...?
Abisa wane dalilin za ki bashi hak'uri..?
Shi yadace fa yabaki hak'uri ba ke ba, ki natsu ki gane inda yake miki ciwo zuu kina biyewa son zuciyarki d'a namiji yana wulaqantaki.

Kallon sama da k'asa Zuhura tayi mata daga bisani ta taso mata kamar za ta cinyeta kinga leebeauty ba shawararki nake nema ba, ballantana kifad'amin son ranki da Ya Ansar yabani hak'uri da kada yabani wannan ba matsalarki bane ni naji nagani naji zan iya sauke girman kaina na nemi sulhu da shi toh ke miye naki aciki?
Babu amma Kisani inajiye miki wulaqancin da zai biyo baya.
Huh!..leebeauty kenan ba fa yau muka fara samun misunderstood ni da shi kuma mu daidaita kanmu kada wannan yadameki ina da tabbacin shima amatse yake da son ganina soyayarmu ajinin jikinmu take mutuwa ce kadai ta isa taraba mu ba dai mutum ba wallahi.

Tana gama magana tai gaba abinta tabar leebeauty cikin tausayinta mtcsww! Taja tsaki had'e da fara zance zuci Iska yana wahalarda mai kayan kara Zuu idanunki sun rufe kink'i gane abinda ni na gano miki amma ba komai ajuri zuwa da tulu rafi wata rana zai fashe.

"Ansar na zaune a office abin duniya yadame shi tunani yake ta wace hanya zai bi domin ya gyara, tsakaninshi da Anaal yakai k'ololuwa a sonta ba zai iya jure wannan Sabuwar hanya da tadauko ta nisanta kanta daga gareshi ba.

Sallamar Ishaq ce ta katse masa tunani ya amsa chan! K'asan mak'oshi maigida kayi bak'i sunasu ganinka batare da ya tambaye su waye ba, yace su shigo domin bai ta6a kawowa aranshi Zuhura ce ba.

Ba knocking balle sallama ta turo k'ofar office d'in tashigo bodyguard d'inta tana biye da ita a baya{leebeauty}.
Tayi tsaye rik'e da kugu tana aika masa kallo Mae cike da kwayar so yayinda shi kuma yake mata na mamaki da tsana ko uban me yakawota office d'inshi adaidai lokacin da yake, cike da haushinta ta 6atawa abar sonshi rai har tana yunk'uri wargaza masa budget ya lumshe idanunshi Wanda ke cike da zallan k'iyayyarta.

''Cikin yanga da rangwad'a taja kujera tana facing nashi ta zauna, ta mak'e murya kamar mutuniyar arziki nasan za ka yi mamaki ganina a office d'inka toh ba abin mamaki bane, in kayi la'akari da irin son da nake maka ya Ansar na kasance mai 6ata maka kai hak'uri kayafemin kadauki hakan a matsayin k'addara ko kuskure insha-Allah hakan ba zai sake faruwa ba. Kasan inasonka Ya Ansar son da baki ba zai misaltashi ba, ba za gane ina tsananin sonka ba har mu yi aure ka k'ara hak'uri da ni da kamar yanda kasaba da sannu zan gyara halayena da d'abi'una nadawo yanda ka ke so.
Chapter 28 · 0% Book details