← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 30

Sashe 21

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Anaal ta rausayar da kai tana kallonshi sauk'in kanshi ya burgeta matuk'a suna isa inda yasaba ajeta ya yi parking, alokacin yak'arasa shanye Coke d'inshi yasauke glass yajefarta gwangwani.
Yadawo da ganinshi kanta, ita ma shi take kallo yasake mata shu'umin murmushi ya akayi ne an Lucky nah? Naga sai wani kallona ki ke yi ko nayi miki kyau ne?
''Tayi murmushi had'e da cewa ina yaba kirkinka ne a zuciyata. Na jima banci karo da mutum Mae kirki irinka ba.
Ga ka da sauk'in kai komai naka Mae sauk'i ne ba ka d'auki rayuwa da zafi ba, na gode da irin kulawarka akaina ina Mae maka albishir tuni ka maye gur6i yaya Auwal a zuciyata yaya Auwal yariga ya6ata ko su Abbah sun fitarda da rai sake ganinshi shekaru 16 da 6atanshi tun ina 'yar shekara 1 ya6ata har yau ba Wanda yaji labarinshi, tana k'arasa magana idanunta suka ciko da hawaye.

"Girgiza kanshi yashiga yi karki yi kuka Lucky shaquwarmu daga Allah ne, nai miki alqawalin daga yau zan tayaki da addu'a indan yaya Auwal yana raye Allah da yabainarshi.
_''Ameen_ tafad'a tana kallonshi lokaci d'aya suka sakewa junansu murmushi ta bud'e k'ofa tafita yabita da kallo har ta6acewa ganinshi sannan yaja mota.

_zuhra_
*4:00pm*
Zuhra na kwance a parlour akan kujera tana chat wayarta tayi ringing, tayi picking had'e da karawa akunne _Hello Leebeauty!_ kinsan banida wadatace k'udi amma zan kira Ya Ansar yakaimu ta d'an yi shiru tana saurare abinda leebeauty take fad'a tayi dariya haba! Leebeauty kema kinsan k'udi ba matsala bane, a wurin Ya Ansar kedai ki shiriya da wuri za mu biyo gidanku mu d'auke ki.

_okay ya yi kyau sai nazo_ ta kashe kiran tashiga dialling number Ansar ringing d'aya zuwa biyu Ansar yadauka _Hello!_ yafad'a akasalance
Hi! My luv yakake ya office?
_Lafiya Alhmdllh_
Ya akayi ne?
Dama my luv shopping nakeso ka kaini kayan kwalliya na sun k'ara banida k'udi a hannuna kuma Alhaji ya yi tafiya.
Ansar ya girgiza kai yana mamakin zuhra ita dai bata buri da yawuce yadinga kashe mata kudi, gashi bata jin maganarshi kuma ba gode mishi takeyi ba.
shikenan naji zan zo na kai ki da k'arfe nawa za ki je shopping d'in?
Ka zo around 5:30pm ya yi.
Okay ba matsala sai nazo
Ya yi hang up.

_5:30pm_
A gidansu zuhra ya yi masa ya tsaya bakin gate ya gaisa da Abbah, sannan ya zarce parking lot ya yi parking yaciro wayanshi ya kirata yafad'a mata yazo saida ta6ata 8-10 minutes kafin tafito sanye cikin wata arniyar fitted gown na material golden colour shara-shara da shi yalafe a fatar jikinta wuyan rigar shown me your back ne anjara duwatsu a Ingiya kamar sark'ar wuya {necklace} a wurin shown me d'in.
D'inki ya yi kyau saidai babbar matsalarshi yanda ya baiyanar da ilahirin surorin jikinta k'afarta sanye da hills blue in colour,hannunta d'auke da wata 'yar k'aramar purse ita ma blue ta yane kanta da d'an siriri mayafi har ana iya hango dogon kiston attachment d'in kanta, ba laifi tayi kyau matuk'a a fuska saidai sutura jikinta ce za ta dusashe kyaun da tayi.
Domin duk Wanda yasan ciwo kansa sai ya yi tir da ita, yayinda samari 'yan bana bakwai za ta tafi da ruhi da gangar jikinsu musanman yanda Allah ya yi mata kira ta jiki zuhra akwai diri hips d'inta kadai abin kallo ne ga gaba ga baya.

''Tana rausaya kamar ganye bishiya yana kad'awa alokacin iskan damina, tun kafin tak'araso Ansar yafara cika yanayi batsewa ranshi ya yi mugun 6aci wai matar da zai aura ce wance za ta zame masa uwar 'ya'yanshi anan gaba ita ce cikin wannan bak'ar shiga.

Jeeddah Aliyu*SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*17*

Hankalinta kwance ta bud'e mota tashiga k'amshin turare ta yadak'i hancinsa ya lumshe idanu Wanda suka kad'a sukayi jajir saboda 6acin rai.
_sorry my luv na barka kanata jira_
Harara ya zuba mata cikin hargowa yafara magana wai ke zuhra wace irin yarinya ce me taurin kai da naci?
Sau ina gayamiki banaso irin banzaye tufafin nan da ki ke sakawa?
Na fahimcin kinfiso sai na nuna miki 6acin raina k'arara akan wannan mummunar d'ab'ia taki....Dallah dakata Ya Ansar akan wane dalilin za ka dinga yi mun ihu aka?
Aure na ka ke yi da za ka kafamin doka na bi, duk tsiya da azarbabinka ka jira har a zarga min igiyoyin aurenka alokacin ka ke da iko akaina ba yanzu da nake gidanmu ba don haka ka saurara mun.
''Ke ashe bakida tarbiyya har ni za ki kalla ki gayawa magana?
An gayamaka magana kai da karufe ido kafad'amin son ranka fa? Ko angayamaka tsoro nakeji? Idan ma haka kadauka kayi gaggawa ka sauke domin ni ba uban da nake tsoro.

Zuhra! Yadaka mata tsawa had'e da nunata da yatsa kallon wulaqancin take aika masa tana yatsina da tabe baki.
''Ki natsu ki saita tunaninki dosashiyar kwakwalwarki ta hasko miki, da Wanda ki ke magana kada garin rashin tarbiyyarki ki furta abinda zai zame miki danasani marar amfani.

"Idan akan irin wannan cin zarafi da ka ke min ne Ya Ansar ba zan jin d'ar ko shakka furta maka, kowace irin kalma ce tafito daga bakina balle har nayi danasani. Ka bi ka takurawa rayuwata ka hanani shakat ni ba iskanci nakeyi ba balle kace ina wannan shagar ne don nasami customers ko akwai uban da yata6a gayamaka yaga k'ato akaina?

Wani irin k'ololo ya tokarewa Ansar a mak'oshi yasaki baki da hancin yana, kallon zuhra bai ta6a tsanmani rashin mutuncin zuhra har ya kai haka ba.
Zafin zuciya yadebe shi ya wanka mata bahagon mari sai da taga wuta jahanama{lol ta bakin yara} ya bud'e k'ofa azafafe yadank'o hannunta yaciro ta daga mota ya yar6e ta waje da6ass.....tayi fad'uwa 'yan bori.
''Tir! da wannan rashin tarbiyya naki tir! Da wannan halin naki wallahi ayau zuciyata cike take da nadama furta miki so tabbas na yarda da 'yan magana da suke cewa so makaho ne{love is blind} cikin hukuncin ubangiji yaji tausayina ya haska mini ganina. Idanu na sun waye daga makata da na shiga, ba ki dace da rayuwata ba wallahi zuhra ba ki dace da zama uwar 'ya'yana ba.

Zuhra ta mik'e da kyar idanunta sun canza launi hawaye na zuba kamar anbud'e famfo bak'ar zuciyar nan ta ta, ta motsa idanuta suka rufe ruf yanda ka ke tunani ban dace da kai ba, Ya Ansar nima abin haka yake yanda ka ke nadama akaina nima haka nake nadama saninka arayuwa na tsaneka, Ya Ansar wallahi na tsaneka bana sonka I hate you kafita daga rayuwata, mari da kayimin Allah yasa isa banyafe ba mugu bak'in azzulumi Wanda uwarshi ta haifa ba jini Mae zuciyar fir'una d'an tasha asarare...... kukan kura Ansar ya yi yadank'e wuyanta yadinga zuba mata mari baki da hancinta na jini.
_subhanalillah!_ Muhammadu me nake shirin gani?
Muryar Abbah ce ta d'aki kunne Ansar yasaki zuhra ba shiri kunya ta lullu6e shi da sauri har yana tuntu6e yashige motarshi, yafizge ta da k'arfi yanufi gate wani abin takaici gate d'in arufe yake yafito a harzuk'e ya bud'e yak'ara fizgar mota da k'arfi.

Abbah yaduk'a gaban zuhra tashi, tashi zuhra me yahad'aki da shi?
Domin wannan ba halin Muhammadu bane yi hak'uri ki tashi.
Haushin Abbah yaturnuk'e zuhra ba don da tana ganin girmanshi ba da ba abinda zai hanata fad'a mishi maganar da har ya mutu ba zai manta da ita ba. duk da haka bata barshi kara zube ba saida ta zabga Mae tsaki ta mik'e tana kuka mai sautin gaske tanufi cikin gida.
Tana Shiga main parlour ta zube tashiga kururuwa _wayyo ni Allah na shiga uku na lalace wayyo bakina hancina_
Da gudu Hajiya saudat da Nazeeya suka fito daga rooms d'insu tsananin tashi hankali ya baiyana a tare da su har suna had'a baki ta hanyar watsawa zuhra tambaya meke faruwa ne zuhra?
Accident ku ka yi ne?
Hajiya saudat ce tak'ara watsa mata wannan tambaya.
''Zuhra takasa amsa tambaya ko d'aya sai birgima da gunjin kuka ta ke yi.
Da kyar da sud'in goshi Hajiya saudat ta ciyo kanta tadaina kuka.
Tana shassheka tashiga kwararowa Hajiya abinda yafaru tana dasa aya Hajiya saudat da Nazeeya suka lailayo ashar kamar masu fad'in karatu suka aikawa Ansar.

Dama ya lafiyar kura Hajiya saudat masifafiyar mace ce 'yar tijara tun tana yarinya yara suka laqa mata suna Sauda 'yar bala'i in tana fad'a har da bakinta ke kunfa kamar tasha omo.
''Akan 'ya'yanta da uban kowa za ta iya karawa ko ubansu bata yarda yakai hannun akansu ba ballantana wani banza Ansar lallai Ansar ya tsokano tsuliyar dodo.

Jakkar uban nan duka tun kafin aure lallai Ansar yanuna min shi d'an tunkiya ne, don tsabar kazar uba zai ware dantse yadake ki a cikin gidanku ni tun da nake duniya banta6a jin wannan abin uban ba duk kwarewa iskanci irin na d'a namiji sai akai mishi mace a gidanshi yake dukanta. Sai ga wannan d'an k'ashi bishi abin kazar uba yakafa tarihi ga 'yata ke Nazeeya bani wayata na kira uwarshi naji ita ce tabashi k'arfin guiwa dukan 'yata tun kafin aure.
Chapter 21 · 0% Book details