← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 30

Sashe 23

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ke! Dallah rufemin baki in har ke kinmanta da waye ubanku ni ban manta ba, in har ke bakya guje masa masifar da bala'in mahaifinku ni ina guje masa, Boy karka bari shed'an ya yi tasiri akanka har Mahaifinka yaji wannan maganar wallahi zai yi masifar sa6a maka watakila har tashafe ni karufawa kanka asiri karufa mini ni uwar da na haifeka.
''Da kyar Ansar yafurta shikenan Mum komai yawuce zan je na basu hak'uri, cike da farin ciki Hajja fatee tashiga sa masa albarka.
Ansar yafad'i haka ne don kawai ya kwantarwa Hajja fatee da hankali ba wai hakan ne har cikin ranshi ba.
Ya mik'e jikinsa a mace yanufi part d'inshi yayinda Basmah tanufi kitchen ta had'a mishi abincin Hajja fatee tabisu da kallo tana mamakin irin tsananin shak'uwar da ke tsakanin Ansar da Basmah.

_Anaal_
*9:33pm*

Tana zaune a parlourn Granny abin duniya yataru ya yi mata yawa, rashin ganin Ansar ba k'aramin halin damuwa yajefata ba, gashi har _9:33pm_ tayi tasan kuwa a irin wannan lokacin mayuwacin abu ne Ansar ya zo tadauki wayarta tayi checking balance taga ko na plashing batada sai kawai ta haddace digit d'inshi tayi masa please call me''
Alokacin yana kwance a parlour yajingina rabin jikinsa a kujera yaji shigowar text a wayarshi da ke ajiye akan ''center table kallo d'aya ya yi mata yadauke fuska, yawan kawo haske da takeyi tadauke yabashi haushi Basmah tayi sallama tashigo d'auke da tire mai d'auke da foodflask ta ajiye a gefen center table a kasalance yafurta Basmah miko min wayata.
Wance daga ciki tafad'a tana kallonshi da yatsa ya yi pointing d'in wance yakeso ta tadauko masa.
Tadauko ta mik'a masa yana yadanna text d'in yaga Anaal ce tayi mishi please call.

Hannunshi har makyaryata yakeyi wajen kiranta, Anaal har tafitarda ran zai kira unexpected taji phone d'inta yadauki k'ara cikin zumud'i ta amsa kiran _Hello_ tafad'a cikin sanyi murya mai cike da damuwa.
"Saida ya lumsashe idanunshi daga bisani ya bud'e su yakike my Lucky?
Lafiya lau tun d'azu nake baza idanu zuwanka gashi har 10:00pm ya kawo jiki banganka ba hope lafiya ce ta rik'eka?

Huh! Abubuwa ne sukayi min yawa amma gobe insha-Allah zan shigo ya Granny?
Granny tana d'akin watakila tayi bacci naga tasha magani, kuma bacci yakesata sosai.
Ke kadai ce kenan?
Eh!
Ya gyara kwanciya can! K'asan mak'oshi yafurta nayi missed naki sosai sai kace ba d'azu da rana mu ka rabu ba.

''Anaal ta rausayarda kai ta kalli bakin k'ofar d'akin Granny taga ba kowa, tace nima haka Ya Ansar yau rana d'aya da ba ka zo da dare ba duk sai naji ba dad'i ko abincin nakasa ci.
Ansar ya yi k'ayatatcen murmushi had'e da cewa nima bancin abincin ba ban fahimci inajin yunwa ba, saida ki ka ce ba ki cin abincin ba kitashi kije ki zubo abincin ki zo mu ci tare.
Mamaki ne ya lullu6e Basmah ta yi zugun tana kallon Ansar sai aikawa kanta tambaya takeyi da wacece ya Ansar yake waya, da har tayi saurin gusarda b'acin ranshi da wuri haka?

"Zaro ido Anaal tayi Uhm! Ya Ansar karka tsorata ni kadai ka ke nesa da ni ta wace hanya za mu ci abinci tare?
Ke dai kawai ki je ki d'ebo kuma karki kashe waya.
Uhm!
Anaal tashiga kitchen ahankali tafurta nashigo kitchen
Toh! Ki yi mana saving
Na bud'e foodflask.
Menene a ciki?
Tuwon semo ne da miyan kubewa.
Wow! Delicious ashe za mu ci dad'i?
Uhm! Haka dai kafad'a.
ta zuba tuwon semovita Leda d'aya da miya ta bud'e roban man shannu Granny ta tsiyaya tadauko plate d'in da hannu d'aya d'ayan kuma na dafe da waya tadawo parlourn, kasan me?
A'a sai kinfad'a
Har da man shannun Granny na zuba.
_iyeee lallai yarinya nan za ki ci dad'i_
Zan ci ko za mu ci kana nufi kafasa cin ne?
Dariya ya yi no! Banfasa ba sai lokacin ya dube Basmah wance mamaki yahanata motsi, Basmah yi min saving mana.

Ajiyar zuciya Basmah tayi tad'auki plate tasa mishi ledan tuwon shinkafa fari fat! da shi tak'ara d'aukar plate mai zurfi ta zuba mishi miyan agusi taji stockfish.

''Ta6angare Anaal kuma bayan ta ajiye plate tanufi fridge tadauko ruwa had'e da cup tadawo ta zauna gaban plate tana sauraron Ansar da ke zayyano mata kalan nashi abinci.
Narke fuska tayi Wanda hakan yasa ta manta da wa take waya, tasa shagwa6a Allah Ya Ansar naka yafi nawa dad'i ni ba zan ci nawa ba naka zan ci.
Tashi zaune ya yi yana dariya da ke nuna tsantsan nishad'i da yake ciki, shikenan ki jirani zan zo yanzu nan na kawo miki nawa na kar6i naki.
Uhm! Uhm! Yi zamanka nima zan ci nawa ko ba komai nawa da man shannu, naka ba bu tak'arasa magana tana dariya mai ban sha'awa.

Huh! Kinsa yawuna ya tsinke amma ba komai nima zan yi manage da nawa, sai kifara ci kinsan kinfini k'atuwar loma.
''Tasa dariya na dai ji d'in.
shiyasa nafika kwari sai da safe.
Da sauri yace ina za ki tafi?
Zan ci abinci mana.
Karki kashe waya ki ci ahaka inaso naji karar shigar loma bakinki.
Dariya sosai Anaal tayi daga bisani tayi Bismala tafara cin tuwonta.
Jin tayi bismillah! Yasa Ansar ya wanke hannunshi yafara cin nashi, tariga shi k'oshi amma sai tayi mishi wayo sai da ta tabbatar da yacinye nashi tass! Sannan ta ture nata plate tana dariya tace _yeee nai maka wayo ko rabi bancinye ba_
Shima dariya ya yi ya tara hannunshi a robar wanke hannu Basmah ta zuba mishi ruwa ya wanke hannunshi.
Tayagi tissue ta goge mishi hannu _thanks my 'yar lukuta_ yafad'a kamar Mae rada duk da haka saida Anaal ta ji _wacece 'yar lukuta?_ ta watsa masa tambaya.

Saida ya yi murmushi kafin yabata amsa Basmah ce bara na bata Ku gaisa, ya mik'awa Basmah waya had'e da cewa Anaal ce za Ku gaisa.
Wani zaro ido Basmah tayi za ka yi tsanmani kwayar idonta zai yi tsalle yafad'o k'asa cikin kid'ima tafurta A....Anaal?
Ita ce mana kiyi magana kudaina k'ona min credit a banza yak'arasa magana yana harararta.

Cikin rawar murya ta gaisa da Anaal daga bisani ta mik'a masa waya yacigaba da magana da Anaal cikin nishad'i da Annashuwa sai kusan around 10:44pm, ya yi sallama da ita yajuya yana kallon Basmah wance ita ma shi take kallo ba ko kiftawa.
Ya yi murmushi yadai 'yar lukuta naga kina kallona kamar bak'auye yashigo birnin?
Huh..ba dole na kalle ka ba ka zo min da abin mamaki Mae rikitarda kwakwalwa. Yaushe alaqa Mae k'arfi irin wannan tashiga tsakanika da Anaal?
Saida ya yi ajiyar zuciya ya ajiye wayar da ke hannunshi ya rik'o hannayen Basmah yana kallon cikin idonta, wannan yakasance sirri tsakanina da ke ba za ki fad'awa wani ba.
Har sai lokacin da yadace ya yi da zan bankad'o sirri kowa yaji.
''Basmah tayi murmushi karka damu Ya Ansar tsakanina da kai sai Allah, wannan alqawalin ne na d'aukarwa kaina insha-Allah wannan maganar ba za ka ji ta a bakin kowa ba.
Basmah!
Na'am''
_Tun daga ranar farko da nayi tozali da Anaal zuciyata ta kamu da sonta so mai tsananin gaske har, nakanji a jikina sanadin sonta zan iya aikata koma menene domin na mallaketa ni kadai. Kada kiyi zaton kyakyawar fuskarta ce tajani wallahi ba ko d'aya domin ranar da na fara ganinta fuskarta na lullu6e da niqabi abu d'aya zan iya ce miki kyakyawar tarbiyyarta, kamun kanta, uwa-uba iliminta sune suka k'ara jefa zuciyata a tarkon sonta._
Basmah inason Anaal Sosai fiye da tunaninki rasata tamkar rasa wani sasshe ne a jikina, Babban farin cikina na kasance tare da ita har k'arshen numfashina.
Anaal ita ce ta dace da tsarina ita ce mace da nake mafalki na, mallaka ba zuhra ba. Kurciya da rashin sani su suka debeni har na furtawa zuhra kalmar so a yanzu nayi nadama had'e danasani marar adadi.

Zufa ya karyowa Basmah bata damu da ta goge ba saboda hannayenta na danke da na Ansar, ta rankwadar da kai tana kallonshi saida tagama karantarshi tass! Sannan tafara magana.

Jeeddah Aliyu
*SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*20*

Banyi mamakin jin wannan maganar tana fitowa daga bakinka ba. Domin nasa ran faruwar haka tun daga, ranar da kayimin tambaya akan Anaal zuciyata tabani akwai wata a k'asa, saboda ba halinka bane tambaya akan mace da bakada alaqa da ita.

"Ba shakka Ya Ansar na yabawa za6inka d'ari bisa d'ari saidai tana k'asa tana dabo kafi kowa sanin baqar ak'ida iyayyenmu na k'yama da tsanar talaka, anyya kuwa za su amince da Anaal musanman yanda suka d'auki dogon buri suka aza akanka?
"Nasani Basmah ban kuma manta ba shi so ba ruwanshi da k'udi da talaka, zuciyata Anaal takeso duk runtsi ba Wanda ya isa yarabani da ita. Dad da Mum suna son farin cikina don haka ba za su k'i Anaal ba domin ita ce farin cikina.

"Toh amma wani hamzari ba gudu ba ita Anaal d'in tasan kanasonta?
Girgiza kai ya yi.
Meyasa baka fad'a mata ba?
Tsoro, tsoro ne Basmah yahanani fallasa mata sirrin zuciyata.
"Dariya Basmah tasa kai Ya Ansar a yanda ka ke d'inan akwai mace da za ta ba ka tsoro?
Ba tsoron Anaal nakeji ba tsoron yadda za ta kar6i tayin soyayyata.

Toh yanzu menene mafita"?
Mafita guda d'aya ne nakeda shi ahalin yanzu nafara aiki da shi, da alama haqata za ta cima ruwa.
Ban fahimcin ka ba?
Za ki fahimta idan na fahimtarda ke na nemi kusancin da Anaal ba don komai ba sai don nayi mata kissan munmunk'e kissan da, da kyar in za ta mik'e.

Zaro ido Basmah tayi cikin kad'uwa tace kissa fa kace Ya Ansar dama ba son gaskiya ka ke mata kai kuwa me za kai ka da kissan mutum?

Dariya sosai Ansar yashiga kyalkyatawa daga bisani yace ke banza ce Basmah sai kace ba bahaushiya ba.
Banda shirme irin naki ta ya zan kashe abinda nakeso?
Basmah ta rausayarda kai ni kan ban fahimcin inda ka dosa ba d'ourani akan haske.
Chapter 23 · 0% Book details