← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 30

Sashe 6

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Rass-rass"!...gaban Ansar ya yanke ya fad'i. Cigaba da jujjuya kwayar idonshi ya yi akan Zuhura wance ta shagala da operating phone d'inta.
"Ranshi ya yi mugun 6aci jiya-jiya nan ya gama kashewa Zuhura gargad'i da kaukausar murya bayaso tana saka watsatsu kaya. Shine ta yi biriss da maganata lalle zan nunawa Zuhura kuskure ta.
''Leebeauty ta zungure 'kafar Zuhura ta yi pointing finger a side d'in da Ansar yake zaune zuu kalli can kamar Ansar Galadima"?.
"Jikin Zuhura har rawa yake yi ta mik'e tanufi wajenshi sai wani karkad'a hips take, kamar sabuwar karuwa "wow! What's presence surprise I don't expecting to see you here Ya Ansar.
Mtcsww"! Ansar ya ja dogon tsaki cike da takaici yak'are mata kallo yak'ara Jan wani tsaki wanda yafi na farko, ya mik'e a fusace kamar zai kai mata mari.
"Yajuya yanufi k'ofar fita ishaq ya tashi da sauri ya bi bayanshi, suka bar Zuhura tsaye sororo kamar bishiya kwakwa.
"Zayyan ya dube Rasheed ya kyalkyale da dariya I told you since abokina duk mutume kirki ba zai mu'amalamta wad'annan 'yan mata ba.
''Dallah ya isa zayyan ni fa zan dinga biye maka ba nakasa more kurciya na ba, remember I'm just 25yrs I'm still young so its my time.
"Zayyan ya tabe baki had'e da mak'e kafad'a. Rasheed ya mik'e yanufi wajen Zuhura yana shu'umin murmushi Hi! Beautiful naga wance tsamin ya 6ata miki rai karki samu damuwa ni zan kawar miki da 6acin ranki.
Kallon sama da k'asa Zuhura ta yi mishi mtcsww"! Ta ja tsaki ta6angaje shi ta wuce ta fincike handbag d'inta da ke kan table tafita fuuu"! Kamar zan ta tashi sama.
"Leebeauty ta tashi tana gunguni ta bi bayan Zuhura.

"Ansar yana fita yanufi wajen mota zuciyarshi na tafarfasa a lokacin guda tsanar Zuhura ta lullu6e shi.
''Cikin sauri ishaq yakaraso ya bud'e mishi mota, yashiga ishaq ya ja mota suka d'auki hanya.
"Ishaq"! Ansar ya kira sunan ishaq kamar zai yi kuka.
Na'am maigida.
"Ishaq zan tambaya ka dan Allah karka ji tsoron ganin idona ka bani, gansasshiyar amsa wance zata fitarwa zuciyata daga wasi-wasi.
''Ishaq ina tsananin son Zuhura tamkar numfashina, bani da wani buri da yawuce ta kasance mata ta uwar 'ya'yana. Ya d'an yi shiru had'e da shed'awa daga bisani yacigaba da cewa a matsayinka na wanda yake da kusanci mai k'arfi da ni, kana gani Zuhura ta dace da zama uwar 'ya'yana"?

"Ajiyar zuciya ishaq ya yi yak'ara dafe steering ka gafarce ni maigida akan abunda, zan fad'a ba tun yau ba nake gani Sam Zuhura bata dace da kai ba.
"Allah ya yi ka natsatse mutum ne kai mai tsananin kula da addini kana taka tsam-tsam da duk abunda zai shafi addininka sai na ke mamaki duk da kasancewar ka mai kamun kai me zai sa ka aure mace irin Zuhura.
"Ba wai Zuhura tana aikata masha'a ba _a,a_ sai don ta kasance mace mai baiyanar da surar jikinta, ga mazaje da ke titi ita a ganinta wannan ba illah bace a na ta k'azamin tunani sai take ganin saka matsatsu tufafi shine wayewa.
"Tun daga lokacin da na fahimcin haka a tare da ita sai nagano cewa kodai tana da karancin ilimin addini domin ba bu wata wayewa da addinin musuluncin bai zo mana da ita ba.
"Ko kuma tana da ilimin kawai bata amfani da shi, to kuma anan akwai babbar illah domin tasani ta kuma take sani Allah yashiryar da mu yasa tagano illah da ke tattare da abunda ta ke aikatawa.
"Ameen Ansar yafad'a cike da gansuwa da Amsar da Ishaq yabashi, 1 more question Ishaq
Ina sauraron ka maigida"

"A lokacin guda Ansar yasauke tagwaye ajiyar zuciya. Ishaq kana ganin wannan matsalar ta Zuhura wa ya yafi cancanta yafara tsawata mata"?
"Mahaifiyarta domin ita ce tushen tarbiyyar ta, ita ce a yanzu tafi kowa kusance da ita sai dai 'yan magana suna cewa ice tun yana d'anye ake tankwara shi, idan ya bushe sai dai ya karye.
"Indan har kwakwalwa ta ta auna dai-dai kana nufi abun da wuya ko Zuhura za ta daina saka watsatsun kaya"?
Kwarai kuwa maigida domin ga dukan alama ta yi nisa ba lalle bane a d'an k'ank'anin lokacin tadaina sakawa ba.
"Amma zan ba ka shawara a matsayinka na wanda ke sonta ka jajirce ka kawo mata illolin saka bankad'ad'un tufafi.
"Saka irin wad'annan kayan yana d'aya daga cikin dalilai da zina ta yi yawa a doron k'asa.
Maigida nasan kana matuk'a son Zuhura ka dage ka nuna mata illah da ke cikin kayan da take sakawa.

"Yak'ara sauke ajiyar zuciya Ansar ya yi ya fesar da iska mai zafi daga bakinshi, ishaq na kasance ina cikin jinse maza masu zafin kishi indan har Zuhura bata daina aikata, wannan mummuna d'abi'a lalle zan barta bari na har abada, domin ba zan ga maciji da rana tsaka nayi sakacin da zai sare ni ba.
"Ba zan aure mace da ba za ta bai wa 'ya'yana tarbiyya tagari ba, duk son nake wa Zuhura zan hak'ura da ita.

_Zuhura_

"Tun a mota leebeauty tafara zugata kai,,,,,,,Jama'a a rayuwata banta6a gani wulaqancin tsirara irin wannan da Ansar Galadima ya yi miki, a baiyanar Jama'a zai kalle ki ko kallo mai cike da k'ask'ancin ya zanga miki dogon tsaki.
"Wallahi Ansar ya gama da ke Zuu ke dai ki yi gaggawar d'aukar mataki ko kuma wankin hula yakai ki dare, yanzu dai dabara tarage ga mai shiga rijiya.
Tak'arasa magana tana kya6e baki.
"Zuhura ta share guntaye hawayen da suka zubo mata, babban abunda yake saka ni fargaba shin me Ya Ansar yake nufi da ni"?
"Me ko yake nufi da ke da yawuce yana daf da 6arar da Gwamnatinki.
"Zuu da kin ga kare yana shinshina takalmi wallahi ko na uban waye dauka zai yi.
"Ni fa ban fahimce inda wannan zaurance naki yadosa ba"? Na ji kince takalmi, kare kuma Ya Ansar bai kasance d'aya daga cikin wad'annan ababen da ki ka lissafa ba.
Dariya sosai leebeauty ta yi wance har ta k'ular da Zuhura rai a 6ace Zuhura tace look leebeauty kinsan duk duniya ba abunda yake saurin baiyanar da fushi na irin dariya, kidaina tun muna sheda juna.

''Leebeauty ta katse da dariyar da take yi I'm sorry tawan I don't mean to hurt you dariyan ne ya zo mun a bazata.
"Zuu,,,,,ni a nawa fahimta sai nake ganin kamar Ansar Galadima yana daf da canza sheqa.
Kamar ya yana daf da canza sheqa sai ka ce wani, d'an siyasa"? Ke ni fa ban fahimce inda ki ka dosa ba.
"Ina nufi Ansar yana daf da canza ki yana daf da fatali da soyayyarki.
"Wani mahaukacin birki Zuhura ta taka ta gangara gefen titi ta yi parking, duk ilahirin ga6o6in jikinta rawa yake sai kace 'yar tauri.

"Kuttt....ta hadiye wasu miyau masu d'acin gaske sai kace tasha mad'acin yanayin tashin hankalinta tamkar na wance tasami sak'on mutuwar uwa-ubanta.
"Da kyar tasamu ta yi controlling kanta ta tattara 'yan raguwar miyaunta masu d'aci ta yi amfani da su ta hanyar cewa.....

Jeeddah Aliyu
*SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*7*

Candijam ashe kuwa Ya Ansar yadauko ruwan dafa kansa, domin na tabbata fasa aure na tamkar yake da yada6awa kansa yunka.
"Tabe baki leebeauty ta yi ke yanzu za ki iya auren wanda baya sonki"?
Ke ubanwa ya gayamiki Ya Ansar baya sona"?
"Ubana leebeauty tafad'a tana kallon fuskar Zuhura mtcsww"! Zuhura ta ja tsaki had'e da Jan mota da k'arfi ta haura kan titi.

*5:44pm*
Chapter 6 · 0% Book details