Sashe 27
Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zeenat ce tayi karfin halin dafa kafad'arta tace hak'ik'a 'yar Agadez kinfad'a tarkon so Mae wuyar fita, inaso Kisani ba wai don akwai baiko tsakanin Ansar da Zuhura zai hanaki sonshi kada wannan ya sanyaya miki guiwa duk Wanda yasan alamomin so tabbas yasan ke da Ansar kunyi zurfi a son junanku a rikice Anaal tad'ago jajaye idanunta ta watsa su akan fuskar zeenat numfashinta na hawa da sauka.
Zeenat ta gyad'a mata kai ki yarda da duk wani furucin da zai fito bakina, Ya Ansar yana sonki Anaal kawai dai bai furta miki bane amma ga dukan alamu shima yana sonki don haka ki kwatar da hankalinki akwana atashi wata rana zai fad'a miki sirrin da ke zuciyarshi.
Ramlat ta kar6e zance ta hanyar cewa kinga saura 2 weeks mu fara exams rashin kwanciyar hankalinki zai iya shafar exams d'in da za ki rubuta, idan Allah ya k'addara sai Ansar ya aure Zuhura ba za ki rasa gur6i ba zai iya aurenki saboda shi mijin mace hudu ne.
kidaina haramtawa kanki Ansar domin Allah bai haramta aure a tsakaninku ba, koda ace akwai dangantaka ita jini tsakaninki da Zuhura ballantana babu ki rufe idanunki ki toshe kunnayenki karki daka ta munafukai kicigaba da son Ya Ansar har Allah yanuna mana ranar da shima zai furta yana sonki.
Da wannan gurguwa shawara Anaal ta zauna akai daram! Ta shiryawa tunk'arar kowane k'alubali ta sha arwashi mutuwa kadai ta isa ta ja Katanga tsakaninta da Ansar duk abinda zai faru saidai ya faru Mae rabata da Ansar sai Allah.
_hour's later_
Anaal tsaye a inda Ansar yasaba zuwa d'aukarta, tun tana tsaye har ta koma zaune ba Ansar ba labari har d'alibai 'Yan uwanta suka watse tass! Kowane ya tsufa agidansu amma ita tana zaune ta rafka tagumi lokacin-lokacin tana share hawaye da bayan hannunta.
Ta kira wayarshi yafi akirga tana rufe.
Daga k'arshe dole ta hau adaidata tanufi gida.
Da dare ta zuba ido ko zai zo shiru bai zo ba .ranar ko kad'an bata runtsa ba bacci yak'auracewa idanunta damuwa ta lullu6e ta ciwo so ya yi mata katutu a zuciya.
Jeeddah Aliyu
[6/28, 8:49 PM] YAYA HAYAT: *SONKI NE SANADI*
_A Romantic love story 2017_
Na Hauwa shehu Aliyu
*®NWA*
www.jeeddahaleeyu.blogspot.com
*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*
*24*
_Few day's later_
Ansar yagaji da shan k'amshinsa yadawo da kanshi, ana tashi school Anaal tana fitowa ta hango motarshi, wani irin sanyi dad'i ya ratsa k'asusuwan jikinta ba shiri ta k'ank'ame hannun Ramlat jikinta na bari tace _wayyo friends Ya Ansar d'ina ya zo ina zan sa kaina wayyo dad'i zai kashe ni_ dariya sosai Zeenat da Ramlat sukayi Ramlat ta fizge hannunta tace kinshiga 3 'yar Agadez ba ko jan aji kinfara zumud'i.
Wane aji zan ja? Ae yanzu ba sauran Jan aji tun da nayi sake zuciyata kamu da sonshi babban takaicina kada ya yi sauri hal6o jirgina.
Hmm..toh gaskiya yakamata ki kiyaye ki koyi ta yanda za ki dinga boye sirrin zuciyarki wannan zumud'i da ki ke yi kamar mayye ya yi bak'o nan take zai gano ki.
Zeenat tak'arasa magana tana Mae kallon fuskar Anaal.
Ansar yafara gajiya da zama yaga Anaal batada niyar sallama da k'awayeta sai ma Sabon shafi ta bud'e na fira yadana horn, zeenat turata ga dukan alama yafara gajiya kitafi kawai gobe za mu k'arasa magana.
Anaal tajuya tanufi wajenshi fuskarta ahad'e sai da ta isa daf da shi ta ra6a tawuce kamar batasan da zamanshi ba, mamaki ne ya lullu6e shi musanman da ya hangonta tana tsayarda Mae adaidaitasahu baisan lokacin da yafito daga mota ba yanufi wurinta da sauri.
Muryarshi asark'e yafurta Lucky ba ki ganni bane da za ki tsayarda Mae adaidaita?
A yatsine ta dube shi ta kauda fuska tacigaba da sha'anin gabanta, yanda tasha toka yai masifar burgeshi yakafe ta da idanu kinga Lucky ni fa yayanki ne bai kamata ki yi min wulaqancin akan titi ba kishiga mota mu tafi in yaso a mota ki sanarda ni laifi da nayi.
"Tayi shiru na 5-7 second's daga bisani tajuya tashiga mota ya yi murmushi ya zagaya yashiga ya ja motar suka tafi tun shigar shi mota Anaal ta kauda fuska tana, kallon titi.
"Anaaal ya kira sunanta cikin tattausan lafazi had'e da jan sunan batare da yajira ta amsa ba yacigaba da cewa wai fushi ki ke yi da ni?
Shiru ba amsa sai ma sake mayarda hankalinta kan titi da tayi.
Ni yadace nayi fushi da ke Lucky ni da na baki umurni amatsayina na yayanki ki kasa bi, sosai raina yab'aci yanda ki ka nuna ban isa da ke ba. Sai daga baya nayi dogon nazari nagano ko kina son malam Naseer shiyasa ki ka bad'a min k'asa a ido.
Da k'arfi tajuyo tana kallonshi tayi rau- rau da idanu hawaye suka fara kara-kaini a kumatunta,dama Anaal raguwar zuciya ne da ita d'an k'ank'anin abu ya isheta kuka batada juriya ko kad'an.
Jikinshi yabashi tana kallonshi yana juyawa yaga hawaye kwance a kumatunta.
Ya gangara gefen titi ya yi parking had'e da kashe mota.
Hankalinshi atashe yafara magana haba! Lucky miye kuma abin kuka?
Ko kinsan babban tashin hankalina naganki cikin b'acin rai? Ba zan iya juri ganin hawaye akan fuskarki ba
Ki taimake ni kiyi gaggawa ki goge su, tun kafin ki jefa zuciyata cikin mayauwacin hali.
Bayan hannunta tasa ta goge hawaye saidai takasa tsayarda su, Ansar yak'ara rud'ewa jikinshi na rawa yafito da handkerchief fari kal da shi ya mik'a mata. ta kar6a ta goge fuskarta harda su fayyace majina, da sauri Ansar ya d'auke fuskarsa yana yayatsine fuska.
Ta maido masa da handkerchief d'in ba yanda ya iya dole ya amsa, ya gyara muryà yafara tsarata lucky banaso na takura ki indan aure ki ke so ki fad'amin na fitarda rai akan karatunki da nake da burin ki yi.
Ko inason aure wa kake tunani zan aura bayan na riga na mallaka maka zuciyata, kai nakeso Ya Ansar sonka yariga ya mamaye ni.
"Lucky please ki yi magana kin tsare ni da idanu ba ki ce min komai ba ya katse mata zancen zuci.
Tayi ajiyar zuciya Mae k'arfi ina mamakin yanda ka kasa fahimta ta Ya Ansar ba son malam Naseer azuciyata asalima, soyayya bata gabana burina nayi karatu Mae zurfi gaske yadda zan taimakawa dangina na tallafawa iyayyena su fita daga rayuwar gadi.
Farin cikin marar misaltuwa ya lullu6e shi cike da jin dad'i yasake yiwa mota key, ya dubeta cikin shauk'in so yace kalamanki sun gusar min da fargaba da tsoro da nake ciki ba malam Naseer kadai ba Lucky karki sake ki kula kowane d'a namiji da sunan soyayya yin hakan zai iya haifarda gagarumar matsala a karatunki.
Naji Ya Ansar insha-Allah zan kasance Mae biyayya ga dukan abinda ka umurce ni.
Ya lek'a fuskarta yana dariya da kyau my Lucky hakan nakeso ji daga bakinki.
Da sauri ta kauda fuska
Haba! Lucky kwana nawa rabona da naga wannan kyakyawar fuska taki ma'a6ociya murmushi, shine za ki haramta min ganinta?
Ta juya tana kallonshi ta ta6e baki ba wani nan da ka damu da fuskar da ba ka yi fushi da ita ba.
O'o! Abinda yawuce kidaiña tadashi daga ni har ke masu laifi ne, d'an juyo ki haskani da murmushinki yak'arasa magana cikin tsokana.
Mak'e kafad'a tayi had'e da furta nak'i.
Bakisan cewa in ki ka had'e da fuska bakya kyau ba? Gara kiyi murmushi 'Yan k'anana hak'oranki masu kama da na bera su fito.
Anaal batasan lokacin da ta kyalkyale da dariya ba sosai furucinshi na k'arshe yabata dariya, shima yashiga tayata har isa inda yasaba ajiyeta suna kwasan dariya abinsu.
Tana fitowa daga mota leebeauty na danno hancin motarta dai-dai lokacin Ansar yafito yana cigaba da tsokanarta tana dariya, jakkar ubanan leebeauty ta furta akid'ime had'e da firfito da idanu tak'are musu kallo tass! Daga bisani ta kyalkyale da dariya har tana had'awa da dukan steering.
Ta girgiza kai taja mota kaitsaye gidansu Zuhura ta tanufa bakinta d'auke da mugun labari.
Da kyar Ansar yabar Anaal tawuce gida shi kuma yaja mota yakoma office, hankalinta kwance ta tura k'ofar gida tashiga ta gaida Abbah sannan tanufi cikin gidan tun kafin tak'arasa k'ofar da za ta saddata da part d'in Granny ta hango zuhura da leebueaty tsaye kowace fuska kamar ta nagge. Rass! ta tsince kanta da fad'uwar gaba, ke Anaal zo nan...Zuhura ce ta kwalla mata kira kamar kazar da kawai yafashewa a ciki tanufi wajensu, tana zuwa Zuhura ta firzge hannunta tanufi garden leeabeauty ta mara mata baya batasaki hannunta ba saida ta saddata da garden, tayi wulgi da hannunta da k'arfin gaske tashiga zagayenta had'e da k'are mata k'ank'antace kallo daga bisani tafara magana cikin izza da taqama Anaal meke tsakaninki da mijina?
Leebeauty ta zo min da wani banzan labari wai taganki amotar Ya Ansar kuna nishad'i tamkar masoya, shine nakeso na gasganta hakan ta hanyar tambayarki menene had'inki da shi? Duk da nasan ba abinda Ya Ansar zai yi da ke ko tsirara yaganki ko darr! Ba zai ji ba domin bakya cikin jinsi matan da yakeso.
Jikin Anaal yadauki rawa dama gata da shegen tsoro, kamar farar kura tun kafin tafara magana hawaye yafara wanke mata fuska, tayi yunk'uri bud'e baki takasa kuka yaci k'arfinta ta durk'ushe k'asa tacigaba da kuka.
Zuhura ta dube leebeauty tana yatsina tace yanzu kin yarda da abinda nake gayamiki? D'an banzan tsoron Anaal kadai ya isa yahanata son abinda nakeso, ita kanta tasan bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane, duk yawan 'yan mata da ke garinan birjik me Ya Ansar zai yi da ita kalli skin d'inta adalilin saleema tana fara yakek'ashe k'asa yace ba zai aureta ba Anaal tafi saleema fari nesa ba kusa ba, Ya Ansar ya tsani farar mace ba abinda zai yi da Anaal sai in so yake yalasa zumar ta kuma Ya Ansar ba mazinaci bane, ba ta inda hasashenki zai zama gaskiya leeabuearty.