← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 30

Sashe 26

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ansar jarumin namiji ko kad'an bai razana da jin wad'annan kalaman na Daddy ba, saima wani mushirikin murmushi da ya yi nan take kwakwalwarshi ta lalla6o masa mafita ya gyara zama cikin ladabi da kwarewa da sace zuciyar iyayye yafara magana godiya nake Daddyna duk hukuncin da ka yanke akaina dai-dai ne bana fatar zuwan ranar da zan yi jayaya da umarninka, amma nima yakamata ayimin uziri abar zance aurenan zuwa bayan sallah da sati 2 kafin lokacin na kamalla gini na.
Controller Basheer Galadima ya yi murmushi da ke baiyanar da jin dad'inshi indan wannan ne karka damu ina da gidaje sai ka za6i d'aya daga ciki.
''Girgiza kai yayi no! Daddy ni nafison nawa ko Zuhura tafi sonshi kayi hak'uri abar aurenan zuwa bayan sallah kamar gobe ne in ga rai da lafiya.
"Kafin Dad yabashi Amsa Granny tayi karaf tace shikenan Ansaru Allah yanuna mana bayan sallah.
_Ameen Granny_ Ansar yafad'a yana murmushi mugunta ya mik'e yace Daddy ni zan fita akwai documents d'in da nakeso amsa wajen Alhaji Faruq gidan Rina.
Adawo lafiya
Allah yasa Ansar yafad'a had'e da ficewa daga parlourn.
Jikin Zuhura na rawa ta bi bayanshi, Ya Ansar! Ya Ansar! Ya tsaya cak batare da yajuya ba ta gabanshi ta tsaya tana kallonshi tana murmushi Yayin da shi kuma yake mata kallo Mae cike da tsana fuskarshi ahad'e yace ya akayi ne?
Dama Ya Ansar hak'uri ne zan ba ka.
Ki adana kayanki watakila nan gaba zai miki amfani domin ba wannan bane right time da ya dace ki Kalmar hak'uri tafito daga bakinki ba. Yana k'arasa magana yanufi motarshi yafizgeta da k'arfin tsiya.

Mtcsww! Zuhra ta ja tsaki can! Ta matse maka Mae bak'ar zuciya da fad'in ran tsiya ubanka yariga ya kashe Boss kai baka isa ka tada shi ba. Za ka gaji da cin ranka ne kadawowa zuhra wallahi ni da kai mutu karaba ne takalmin kaza.

_1 WEEK LATER{BAYAN SATI D'AYA}_

Ansar yana zaune a office d'inshi Abdallah yashigo da file a hannunshi, ya zauna had'e da mik'awa Ansar file ka duba documents d'in gidan ne ka daure Ansar ka siye gidanan wallahi za ka ji dad'inshi koda anan gaba ne.
"Ajiyar zuciya Ansar ya yi akasalance yace wai kai miye matsalarka na matsanta mun na siye gida bayan kasan banada buk'ata da shi?
Ba za ka gane bane Ansar ajiye kadara komai k'ank'anta ta yana dad'i da amfani ni kaina narasa dalilin da yasa nakeson ka siye gidanan.
Shikenan naji zanyi magana da Dad in ya amince sai a siya.
6ata fuska Abdallah ya yi haba! Ansar komai kace sai Dad yasani wannan bayi bane, 10 millions ne bakada a account d'inka da za ka ce sai Dad yasani?

Shiru Ansar yayi yana nazari da sauri Abdallah ya katsi shi karka tsaya tunani ka zari k'udi kawai mallam ka siye wannan gidan zai maka amfani anan gaba.
Shikenan naji na amince zan siya anjima da yamma sai muje naga gidan in yaso on Monday sai abiyasu k'udinsu kace dai na KB ne?
Eh! Nashi ne.
''okay ba matsala.

_Zuhura_

Tun zuhra nasaka ran Ansar zai zo yabata hak'uri kamar yanda yasaba mata, sai taji shiru wai mallam yaci shirwa gaba d'aya yak'auracewa zuwa gidansu ita kuma d'an banzan girman kanta yahana tanemi shi.
A6angagare d'aya kuma Ansar yana had'uwa da taurarwarshi Anaal yakaita school yadauko ta da dare yakira ta a waya su raba tsakiyar dare suna waya cikin d'an k'ank'anin lokacin ya yi nasarar saye zuciyarta soyayyarshi mai zafin gaske ta kanainaye mata zuciya tun daga lokacin Anaal tashiga wani yanayi domin Ansar ko da kuskure baita6a Sa6ul da bakan furta mata Kalmar so ba shiyasa take tausayin kanta gashi suna daf da fara final exams batada lokacin karatu sai na tunanin Ansar.

Jeeddah Aliyu
[6/28, 8:49 PM] YAYA HAYAT: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*23*

Yammaci ne mai d'auke da sanyaye iska su Kansu bishiyoyi suna jin dad'i yadda suke kad'awa. Anaal ce tsaye a k'ofar gida tare da malamin islamiyyarsu mallam Naseer sai doka murmushi take.
Ansar yadanno hancin motarshi tun kafin yak'araso ya hangota rass!rass! Gabanshi yafad'i ba Shari yataka birki zuciyarshi tashiga tafarfasa masifafen kishi ya lullu6e shi gumi sai tsiyayo mishi yake, yaja numfashi da k'arfi yak'urawa Anaal ido dai-dai ta rufe fuskarta da gefen hijabinta da alama malam Naseer yagaya mata maganar da tasata jin kunya. Ansar yasake harzuk'a yana kallo har suka gama fira malam Naseer ya hau mashin d'inshi yawuce shi fuuu! Binshi da kallo Ansar ya yi ya ja tsaki mtcsww! Yafito daga mota Anaal na k'ok'arin shiga gida ya kwalla mata kira Lucky!
"A rud'e tajuyo saboda yanda muryarshi ta ratsa dodon kunnenta, jiki asanyaye tanufi wajenshi lah! Ya Ansar Kaine?
Harara ya zuba mata ahasale yafurta bansaniba wane k'ato ne naganki tare da shi?

Ta zaro ido tay kamar taga abin tsoro Ya Ansar ba k'ato bane malaminmu ne na islamiyya malam Naseer shi yake d'aukarmu daras...ke dallah! shiru kin saki baki sai zuba ki ke yi don yana malaminku sai me?
Ae bashida hurumin da zai zo gidanku ko kece ki ka gaiyyace shi?
Girgiza kai tayi.
Toh! Me yazo yi wajenki?
Hmm!Uhm! Cewa ya yi wai yana Uhm!....
Yana me ya katseta cikin tsawa
Tak'ara rud'ewa haba! Ya Ansar miye kuma na daka min tsawa?
Tsareta da idanu ya yi yana cika yana batsewa jin yake kamar ya kwada mata mari.
"Wai lafiya Ya Ansar kai tsarini da masifafun idanunka?
Ya motsa sumar kanshi ya yi had'e da lasa lips d'inshi na k'asa takaicinta yak'ara kamashi.

Nunata da yatsa ya yi look! Anaal karki rena min hankali za ki fad'amin abinda wannan k'ato ya zo yi a wajenki ko kuwa?
Innalillahi wa'inna illahim raji'um! Haba Ya Ansar Dan Allah Kadàina kiran malam Naseer da k'ato ba fa wani abin tashin hankali bane cewa kawai ya yi yana sona.
"Dif wutar kan Ansar ta d'auke yashiga muzurai yana kallon Anaal, tsawon _20 seconds_ yadauka ahaka daga bisani yace ke kuma wace amsa ki ka bashi?
Kanta asunkuye tace cewa nayi yabani lokacin zanyi shawara da zuciyata.
"Bakya buk'atar shawara da zuciyarki ba sai kin wahalarda shi ba ki fad'a masa bakya sonshi. Ba ki shirya yin aure ba karatu za ki yi.

Girgiza kai tayi cikin sanyinta tace ba zan iya ci masa fuska nace bana sonshi ba malam Naseer yana da matukar k'ima da daraja a idanuna, bai kamata kaitsaye na fad'a masa irin wannan maganar ba.
"Ranshi a b'ace yake kallonta kwaryar idonshi ya kad'a ya yi jajur, da kyau Lucky Yau kin nunamin banida matsayin a wurinki kinfifita wani akaina shi kina gudun b'acin ranshi ni kuma bakya gudu nawa kije kicigaba da soyayya da malam Naseer ni na amince da shukar da nayi ba Wanda ya isa ya gir6e ta.
Batare da yajira abinda za ta fad'a ba yajuya cikin tafiyar sauri yashiga motarshi ya fizgeta da k'arfi.

Anaal tayi tsaye sororo tana mamakin wannan k'arfin halin na Ansar jikinta amace tashiga gida kaitsaye BQ tanufa tashige d'akin Ammah ta tararda Ammah na cikin gida tafad'a kan mattress tayi ruf da ciki, tarasa me kedamunta duk duniya ba abinda ta tsana take adawa da shi irin fushin Ansar ahankali hawaye ke zuba daga idanunta suna sauka agefen wuyanta, cikin tausayawa kanta tafara magana da zuciyarta kaicho na ni Anaal na kamu da son abinda ba zan ta6a samu ba meyasa nayi sake zuciyata ta kaini mahalaka?
Zuciyata tana sonka Ya Ansar so Mae tsananin gaske, saidai kashe! har abada ba zan sameka ba shiyasa na yanke shawara zan mallakawa waninka zuciyata duk nasan ba wani d'a namiji da zai goge shafin sonka azuciyata.
Kuka mai sautin gaske ya kubce mata taja pillow ta daura akanta yadda ba za'a jiyo kukan nata ba, saida taci kukanta Mae isarta tashare hawayenta, adaddafe tayi sallah magarib da isha ta lalla6o wayarta ta kira Ansar wayar na ringing yak'i dauka bata hak'ura ba tacigaba da kira almost 5 missed call tayi mishi yak'i picking tayi mishi text tana rok'onshi da yadauki kiranta ya yi banza kamar bai ga text d'in ba.

"Anaal tak'ara rikicewa hawaye na abaliya afuskarta tana sake kira taji ya kashe wayarshi, ranar bata runtse ba ta matsu garin Allah ya waye su had'u tabashi hak'uri ko za ta sami kwaciyar hankali.
.
*6:48am*
Anaal tafito cikin shirin tafiya makaranta tawuce BQ ta gaida Ammah sannan tanufi bakin gate, wajen Abbah yabata k'udin breakfast.

Cikin natsuwa da kamun kai take tafiya har ta isa inda tasaba had'uwa da Ansar har ltagaji da tsayuwa ba Ansar ba labarinsa
tanemi wani k'aton dutse ta zauna tafito da wayarta daga schoolbag d'inta ta kira shi still wayarshi arufe idanuta suka ciko da hawaye kiris take jira ta fashe da kuka ta maida wayar inda tadauko ta karo na farko arayuwarta da ta6a makara _8:30am_ dai-dai ta mik'e taja sanyayu k'afafunta tanufi bakin titi ta hau adaidaita.

Har aka tashi breakfast ba abinda ta fahimta daga cikin darussa da aka koya musu bayan classes suka nufa ita da su Ramlat.

Zeenat tanufi shop d'in siyarda snacks da drinks tasiyo musu Ramlat da zeenat suna cin snacks suna korawa da drink sa6ani Anaal da ta rafka tagumi, zeenat ta dubeta cikin kulawa tace 'yar Agadez meke damunki ne?

Tasauke ajiyar zuciya Mae k'arfin gaske tayi rau-rau da ido, sani tayi za ta same kyakyawar shawara daga k'awayen nata yasa ta fede musu biri daga kai har wutsiya ba abinda ta 6oye musu cikin rauni murya da neman mafita tacigaba da cewa, ni kaina basan lokacin da nakamo da matsananciyar soyayyar Ya Ansar ba.

Narasa inda zan jefa kaina da wannan abin kunya, Ina tausayawa kaina domin koda ba soyayyar yaya Zuhura azuciyarshi ba abinda zai yi da ni tak'arasa magana had'e da kifa kanta a cinyoyinta tashiga rera kuka Mae tsuma zuciyar Mae saurare.
Chapter 26 · 0% Book details