← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 30

Sashe 16

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da sauri Ansar yake scrolling pic's d'in mtcsww"! Ya ja tsaki had'e da ajiye wayan a hannun kujera, yadauki nashi ya yi dialling digit d'in Anaal wayarta a rufe mtcsww"! Yak'ara zuba tsaki.
"Basmah tashigo d'auke da plate tajanyo k'aramin center table ta daura plate d'in akai tak'ara komawa kitchen ta dauko mishi drinks da ruwa.
''Yana cin had'in salad d'in yana lumshe ido saida ya cinye tass ya ture plate ruwa kawai ya sha yaciro chewing gum mai k'amshin strawberry daga pocket d'inshi ya 6are ya jefa baki.
"Basmah ta mik'a mishi hannu nima zan cin Ya Ansar.
Me za ki ci mayya"?
Tana dariya ta furta chewing gum.
Ciro d'aya ya yi ya jefa mata ta cafke.

Yakoma jikin kujera yalafe idanunshi a lumshe ya furta Basmah me ki ka sani game da Anaal"?
Da mugun mamaki baki bud'e Basmah take kallonshi takasa furta komai sai kallonshi take yi. Shi kuma sai tauna chewing gum d'inshi yake yi hankali kwance.
"Ajiye zuciya Basmah ta yi ta mik'e daga mazauninta ta koma kusa da shi ta zauna bisa hannun kujerar da ya ke zaune.
"Ya Ansar wannan tambayar naka ya sakani cikin rud'ani akwai wata alaqa ne tsakaninka da Anaal"? Banaso zuciyata tafara kintsa mini abinda ba shi bane ma'ana zargi.
"Yad'ago ya dube ta a d'age ki fara amsa mini tambaya na firstly in yaso daga baya kya iya naki tambaya.
"Langwa6e kai Basmah ta yi _Anaal yarinya ce Mae hankali da natsuwa tana da tsananin hak'uri, sai dai miskila ce tabugawa a jarida ba abinda yafi burgeni da Anaal irin iliminta ba irin bin Anaal da banyi ba akan mu qula k'awance amma tak'i sai dinga fuskewa kamar dae banyi mata ba duk da wannan har yanzu ina k'aunarta_ tak'arasa magana kamar za ta yi kuka.
Tun lokacin da Basmah tafara magana Ansar yake zabga murmushi, hannun Basmah yarik'o don't worry 'yar lukuta zan had'a ki k'awance da Anaal kinsan duk gidanan tamu tafi zu wa d'aya duk abinda nakeso kema kinasonshi koh"?
"Basmah ta yi dariya tak'ara dank'e hannunshi can kasan makoshi ta furta Ya Ansar do you love her''?
Zaro ido ya yi who"?
Anaal mana tafad'a tana kallon kwayar idonshi.
Tabe baki ya yi had'e da girgiza kai capital No we are just a friends.
"Sauke ajiyar zuciya Basmah ta yi thank God da har zuciyana yafara saqa mini, irin k'alubali da za ka fuskanta daga wajen Dad da Mum kasan ba abinda suka tsana irin Wanda bashi da shi.

"Ansar ya mik'e tsaye karki damu k'anwata insha'Allah ba abinda zai Shiga tsakanina da Anaal ko kin manta da irin d'inbin son da nake wa Zuhura''?
Ban manta ba Ya Ansar amma kuma zuciya tana canza sheqa daga nan ta koma nan.
"Ban da tawa zuciya domin Zuhura takeso ita kadai na d'auki Anaal ne tamkar ke.
Murmushi Basmah ta yi tace ni dae yanzu yaushe za ka had'a mu k'awance''?
''Tabe baki ya yi ke fa kin fiye gaggawa.
Har Basmah tabude baki za ta yi magana ya katse ta sai na dawo Basmah karki 6ata min lokacin da wannan surutun naki yasa kai yafita Basmah tabishi da kallonshi.
"Yana fita bai zarce a ko ina ba sai inda yasa6a jiran wucewar Mae niqan, so yake ya gasganta zarginsa shin Anaal ce ko ba ita ce ba.
''Cikin Sa'a bai fi _5 minutes_ da zama ba sai gata ta ta tsallako titi yau ita kadai ce, da sauri ya 6alle k'ofa yafito Anaal naganinshi tadauke kai kamar bata ganeshi ba ta ra6a shi za ta wuce cikin sark'ewar lafazi Ansar ya Kira sunanta Anaal''!
"Ta tsaya cak da saurinsa ya k'arasa kusa da Ita Anaal shine za ki wuce ni ba ko gaisuwa ko kina tsanmani don kin rufe fuskarki da niqan ba zan gane ki ba''?

"Dariya ta yi Mae sautin ka yi hak'uri Ya Ansar ban yi zaton za ka ganeni ba. Naga cewa nasha wuce ka amma ba ka ta6a nuna kasan ni ba.
Shima dariya ya yi ba gashi yau na nuna nasanki ba.
''Tafiya tacigaba da yi zan wuce gida naji anfara kiran sallah magarib.
"Okay....Ni ma da nayi sallah zan shigo ki ce da Granny ta aje min Mae dad'i.
Ba wani Mae dad'i da za ta aje ma kadai sai kashigo.

_8:30pm_

''Ansar yana zaune a parlourn Granny suna fira Anaal ta yi sallama tashigo sanye da hijab har k'asa pink in colour.
Tanemi kusa da Granny ta zauna ta k'asan idon ta kalli Ansar batasan cewa shima tun shigowarta yake aikin kallonta ba.
"D'ago idanunta tayi gaba d'aya ta dube shi yau za mu yi karatu ne''?
A maimakon ya6ata amsa sai ya kafeta da idanu d'auke fuskarta ta yi ta mayarda ganinta wajen Granny tace Granny na dauko maganinki na Shafa miki tun yanzu?
"Girgiza kai Granny ta yi kije ku yi karatunku anjima ki Shafa min Anaal ta mik'e tashiga bedroom tadauka jakkar littafai.
Tana cikin karatu sai ga Zuhura tafad'o parlourn kamar wance aka jefo. Da mugun mamaki take kallonsu Ya Ansar shine za ko gidanan ko kanemi ni"? Narasa me ke damunka a 'yan kwanaki nan ka ke share ni.
Shhh......Ansar ya aza yatsanshi a lips alamar tayi shiru amma ita gimbiyar ko a jikinta sai ma k'ara kaimi ta yi wane irin shhh..."? Toh wallahi ba zan yi shiru ba har sai naji, dalilinka na shirya mini wannan wulaqancin.

_"Sadakallahu-azeem_ Anaal ta dasa aya kada ta kwasawa kanta zunubi, saboda in ana karatun Qur'anic ba'a surutu. Ta mik'e tsanm tanufi bedroom Zuhura ta bi ta da kallon tuhuma.
K'atuwar harara Ansar ya gallawa Zuhura wannan wane irin dabancin ne? Ya ana karanta Qur'ani za ki zo ki cika mutane da surutunki na banza da wofi?
''Idanu Zuhura ta zaro Ya Ansar ni ka ke kira da suna dabba? don kawai na nuna damuwata akanka?
''Eh! Na fad'a ke dabbace domin abunda ki ka aikata dabba ne kadai zai aikata shi.
Shikenan Ya Ansar naji ni dabbace amma inason kasani komai wuya komai runtse kana nan tare da dabba, ba uban da isa yaraba ka da ita mutum zai gaji da tsohun munafuncinsa da zugaka yabari domin ni da kai mutu karaba ne takalmin kaza.
"Rai 6ace Ansar ya mik'e har yaware hannu zai wanka mata mari, Granny ta taka masa birki kai Ansar kul karka daketa duk wad'annan zafafan maganganu da take fad'a ba da kowa take ba illah ni. Kabarta kawai abinda ta girma tayi wayo tarrarda da uwarta saude tana min kenan.
Amma Granny haka zan cigaba da zuba mata ido tana gasa min magana iya son ranta haka za mu yi aure bata gani girma na?
Hak'uri za ka yi Ansaru domin kace ka ji ka gani kana sonta, rashin mutumcin da bankad'a ba ka ma ga komai ba sai ranarda igiyar aure ta gita a tsakaninku.

Mtcsww"! Zuhura ta ja dogon tsaki kamar za ta gutsere halshenta, tajuya fuuu.....tana wani jujjuya mazauna ita a dole ga shak'iyiya.
Ansar yana huci yakoma ya zauna yayinda Granny tacigaba da rarrashinsa da kalamai masu kwantarda hankali sai around _10:30pm_ ya yi sallama da Granny yawuce gida har yatafi bai k'ara gani Anaal ba.

_washe Gari_

Ba zato ba tsanmani Anaal taci kora da Ansar yana zaman jiranta zai kaita school.
Jiki ba lakka ta bud'e k'ofar mota tashiga kallon d'aya ta yi mishi taga damuwa shinfid'e akan fuskarsa.
Cikin sanyayiyar muryarta tace _ina kwana Ya Ansar_
Lafiya Anaal yau kin kusa ki yi latti.
Wallahi kuwa yau bacci nayi sosai da kyar Granny ta tashe ni.
Ansar ya kad'a kai kin more 'yan mata ni jiya ko runtsewa ban yi ba yanda naga rana haka naga dare.....

Jeeddah Aliyu
[4/25, 6:22 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

13

Cikin yanayin na tausayi Anaal tajuyo tana kallonshi Ya Ansar bai kamata kadauki abunda yaya Zuhura tayi da zafi ba. Har ya yi sanadin hanaka bacci nata halaya ne haka dole sai kana hak'uri had'e da lurarda ita.
''Haba Anaal zuhura k'aramar yarinya ce da zan dinga tsara mata yanda za ta gudanarda rayuwarta?
Ba k'aramar yarinya bace amma kafita hankali da tunani matuk'ar tana sonka toh dole ta bi abinda ka ke so.
Anaal kenan lallai har yanzu ba ki San wacece Zuhura ba. In kina neman mace 'yar raini wayo marar tarbiyya, fitsarariya ki ka kawo ga Zuhura sai ki Shafa fatiha. Kina ji fa Granny ta kira da munafuka yak'arasa magana cike da takaici.

''Naji Ya Ansar anan Zuhura ta yi kuskure amma kamar yanda ka ji Granny tace, daga wajen mahaifiyarta ta koya domin ita ma ba ragawa Granny ta ke yi ba.
''Mtcsww! Ansar ya ja tsaki Allah ya kyauta dukansu ba laifinsu bane Baba sa'eed ne mai laifi shi da ya zuba musu ido suna wulaqanta mishi mahaifiya.
Nima abinda nake fad'a kenan a zuciyata. A shekaru Granny bai kamata ace tana fuskantar irin wannan cin zarafi ba.
Bari kawai Anaal Granny na zaman hak'uri dad'inta bata bari ta kwana balle ta tashi da yanzu, sun mayarda ita juji.

''Dariya Anaal ta yi ae Granny batada sauki muddin tsautsayi yasa kata6o ta za ka ji ba dad'i. Ni dai shawarar da zan ba ka kacigaba da hak'uri da Zuhura dama haka auren zumuncin ya gada. Ni shiyasa bai ta6a bani sha'awa ba, Saboda in zama bai yi dad'i ba nan take yake 6ata zumuncin.
6ata fuska Ansar ya yi ba wani hak'uri da zan yi zan nemawa kaina mafita ae ba aurenta nakeyi ba ballatana nai hak'uri infact ba ita kadai bace 'ya mace da zan dinga shanye wulaqancinta.
Zaro ido Anaal ta yi kai Ya Ansar banaso cika baki duk son da ka ke yi ma Zuhura za ka iya barita akan d'an k'ank'ani abu?
Harara ya galla mata zan tabbatar miki ba cika baki nakeyi ba, muddin Zuhura bata sauya munana d'abi'unta ba ni kuma ba abinda zai hanani sauyawa. Yana k'arasa magana dai-dai yakawo gate d'in makaratansu ya yi parking.
Chapter 16 · 0% Book details