← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 30

Sashe 3

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ansar ya rabawa su Nadeeya tsaraba da ya yo musu trolley guda yacikawa Zuhura da had'ad'u Arabian gowns da hijabai different colours had'e da shoes da handbags ga kyau ga tsada misalin 'karfe _2:30pm_ yanufi gidansu Zuhura yana Shiga layin gidansu idanunshi suka hasko masa wata matashiyar budurwa wance shekaru ta ba za su haura 17yrs ba tana sanye da Hijab har k'asa sky blue colour ta yane fuskarta da niqan, tana tafiya a hankali kamar mai tsoron taka k'asa yanayin tafiyarta cikin natsuwa yak'ara tafiya da imaninshi kasa d'auke idanunshi ya yi daga kanta hakan ne yabashi damar rage gudun mota yasoma tafiya slow-slow yana kallonta har tak'araso daf da motarshi ta ra6a ta gefenshi ta wuce kanta a sunkuye tana kallon k'asa tsintar kanshi ya yi da bin ta da kallo ta cikin mirror da ke jikin motarshi idanunshi na kanta har sai da ta6acewa ganinshi sannan ya yi nasara dawowa cikin natsuwarshi.
"Cike da mamakin kanshi ya ja mota da k'arfi ya nusa cikin unguwar, horn yadanna a bakin gate d'in gidansu Zuhura maigadi ya bud'e masa gate, tsayawa ya yi ya gaisa da Abba buzu maigadi saboda tun jiya da Granny tabashi labarin kirkin mutume ya ji aranshi ya kwanta masa parking lot yanufa ya yi parking.
"Yafito daga mota ya hango Fahad yafito daga cikin gida kai Fahad zo nan"! Ya kwadawa Fahad kira bayan Fahad ya zo ya bud'e boot d'in mota yanuna mishi nasu tsaraba ga tsarabanku nan kowane ku da sunanshi akai Fahad yashiga yi masa godiya ya kinkime kayan Indan kashiga ciki ka turo min Zuhura ina part d'in Granny.
Fahad ya amsa da to..yawuce cikin gida yayin da Ansar ya ja trolley d'in da tsaraban Zuhura yake ciki yanufi part d'in Granny ''Ammah kadai ya tarar a parlour tana linkewa Granny kayanta da ta kwaso daga igiyar shanya, gaisawa suka yi Yanemi sofa ya zauna Ammah ina Granny"?
Tana d'akin ko a kirata ne"?
Noo.....ki barta kawai ae ba yanzu zan tafi ba
Shikenan.... Ammah tafad'a had'e da kwashe kayan da ta linke tanufi cikin d'akin Granny Ansar yafito da phone d'inshi ya kira wani friend d'inshi Sageer da suka yi karatu tare a U.k ya shagala da firar da yake yi da Sageer.

Ba ko sallama Zuhura tafad'o parlourn sai saukar numfashinta Ansar ya ji a kunnenshi yad'ago a rikice tana tsaye daf da shi tana zuba murmushi sallama ya yi da sageer yasauke idanunshi akan sutura da ke, sanye a Jikinta Black colour skintight da red colour d'in top a tsakiyar gaban top d'in anyi tsaga dai-dai saitin Nonuwa wannan yasa boobs d'inta a baiyane Fitinanai k'amshin na fita daga Jikinta kanta ba d'an kwali gashinta yasha gyara yana lullu6e da gashin attachment ya kwanto har gadon bayanta sai kace nata.
"Ansar yasauke ajiyar zuciya had'e da janye idanunshi daga kanta a zuciyarshi yasoma aikawa kanshi tambayoyi anyya kuwa Zuhura tana da hankali"? wannan wace irin masifa ce kalli wad'annan watsatsu kaya da tasaka"?
Yaushe Zuhura ta sauya kyawawa d'abi'aunta da nasanta da su"?
Yasaukar hannanye ta ya ji a kafad'arshi tana matsa mishi jijiyoyin wuyanshi abun ka da lafiyayye namiji wanda baya tsallaka iyakokin ubangiji cikin d'an k'ank'anin lokacin ya tsince kanshi cikin wani yanayi gaba d'aya Jikinshi ya mutu.
"Kamar Wanda aka tsakara yadawo hayyacinshi _A'uzubillahi minal shed'anin rajim_ yafad'a had'e da ture hannayenta daga wuyanshi ya mik'e tsaye Wawan tsaki ya ja cike da jin haushi yace wai meke damunki ne Zuhura"?
Yatsine fuska ta yi had'e da dusuna duwawunta akan kujera na yi maka kama da Wance take cikin damuwa ne"?
"Sororo ya yi baki bud'e yana kallonta daga bisani ya zauna nesa da ita ga tsarabanki nan na kawo miki ki bud'e ki gani ko na iya za6i"? Yak'arasa magana da murmushi akan fuskarsa.
"Tana yatsina tasauko daga kan kujera ta janyo trolley d'in ta zuge zip tasoma fitowa da handbag's wow! Gaskiya Honey ka iya za6i gaba d'ayansu favorite colour's d'ina.
Ansar yasaki murmushin jin dad'i harda su kada kai tana dauko shoes ta tabe baki, tad'ago tasauke idanunta akan fuskarshi cikin gadara tace Amma Ya Ansar wad'annan shoe's d'in ba nawa bane"?
"Na ki ne mana yafad'a with full confidence k'ara yatsine fuska ta yi lalle ma Ya Ansar kana nufi har ka manta da size d'ina"?
Sosa k'eya ya yi alamar jin kunya ni fa na dauka 37 ne size naki"?
To in Kadauka ka sauke 39-40 shine size d'ina.
Murmushi Ansar ya yi domin tun ba yau ba yasan halin Zuhura na rena arziki ba kasaifa yake mata kyauta ta ya6a ko tanuna farin cikinta ballantana har yasamu kalmar godiya daga bakinta, wannan yana d'aya daga cikin mummuna d'abi'aunta da yatsana ga kuma wasu sababbi da yadawo ya tararda ita d'auke da su.
"Watsar da takalmin ta yi a gefe tashiga zaro raguwar kaya da ke ciki zaro ido ta yi miye wannan"? Tana magana ne had'e da d'ago hijab, da mugun mamaki Ansar yake kallonta bangane miye wannan ba ke bakida idanu ne"? Yak'arasa magana cikin b'acin rai Zuhura kuwa ko a jikinta sai ma jefar da hijab d'in da ta yi Ya Ansar ba zan 6oye maka ba ni bana saka irin wad'annan kayan duk wata sutura mai nauyi bana shiri da ita, saboda banason zafi shiyasa tsakanina da Hijabi sai in zan yi sallah bana saka Arabian gown ko last year da Daddy ya je Makka yasiyo muna Arabian gown ni nawa *Anaal* na ba wa domin anan gidan ita kadai ce take saka irin wad'annan kayan.
"Tun lokacin da tafara magana Ansar yake mata kallon mamaki da takaicin wai yaushe notun kan Zuhura ya kwance"?
Gani yanayin da yake ciki yasa ta tabe baki tace ni ina mamakin anyya kuwa wad'annan tarkace a U.K kasiyo su domin kwata-kwata ba su yi min kama da kayan da suka fito daga U.K ba"?
"Ran Ansar yak'ara b'aci yashiga girgiza kai ya isheki Zuhura nace ya isa hakanan Yafad'a cikin tsawa da tafarfasa zuciya, wad'annan kayan su naga damar siya miki tunda ba za ki iya amfani da su sai ki ba wa Nazeeya ba wai kidinga gushesu a gabana ba.
Taso mishi ta yi kamar za ta cinye shi d'anye Sam babu ladabi balle d'a'a tafara magana kai wane irin mutum ne Ya Ansar"? Daga nace banaso wad'annan tarkace shine za ka rufe ni da masifa"? to ni wallahi ba uban da ya Isa ya yi min dole
A tsorace Ansar ya mik'e tsaye jikinshi har wani Mazari yake idanunshi sun canza kala zuwa jajaye.......

Jeeddah Aliyu
*SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*4*

Gaba d'aya hankalinshi ya raja'a da kallonta ya shagala sosai har bayaso yadaina kallon nata.
Hakan yasa yarage gudun mota ya koma tafiya sannu-sannu.
"Tafiyarta da shigar da ke jikinta suna masifar burgeshi, da yake glass d'in motarshi tinted ne shi yahana 'yan matan su gane yana kallonsu har suka 6acewa ganinshi idanunshi na kafe akan hanyar da suka bi yasauke k'arfafiyar ajiyar zuciya, ya ja mota a kasalance yanufi gidansu Zuhura.

Horn ya yi Abbah buzu ya bud'e masa gate yana ganin Ansar ne yashiga fara'a kamar gonar auduga Ansar ya yi parking yafito yanufi wajenshi.
''Barka da zuwa Muhammadu lafiya kwana biyu muka daina ganinka ko ka yi tafiya ne"?
Yauwa,,,,Abbah ina gari ba inda naje aiyuka ne suka yi min yawa da fatar yau za ka had'a mana ataye{green tea} na ranar naji dad'in shi sosai"?
Dariya Abbah buzu yashiga kyakyatawa daga bisani ya katse dariyar tashi kai,,,,,,lallai Muhammadu in natashi tafiya Agadaz da kai zan tafi saboda na fahimcin kana matuk'ar so ataye.
Dariya marar sauti Ansar ya yi yana Sosa k'eya yace ae Abbah na gayamaka in da rai lafiya wata rana kwatsan za ka ganin Agadaz, in kuma naje ba zan dawo ba har sai ka bani mata na aura yak'arasa magana cikin sigar wasa.

"Abbah buzu yak'ara yi dariya kai Muhammadu me za ka yi da buzuwa kai da ka ke da 'yar gaye irin 'yata Zuhra shima yabashi amsa cikin raha.
Ansar ya yi murmushi Abbah zan shiga ciki in ka had'a ataye kafin natafi zan sha.
Toh,,,,,,,Muhammadu a fito lafiya.
"Allah yasa Abbah Ansar yafad'a had'e da sa kai yashiga part d'in Granny da sallama yak'arasa shiga parlourn Granny da ke kishingid'e tana kallon sunnah tv tad'ago, had'e da amsa mishi yanemi waje ya zauna ya gaida Granny suka shiga fira daga bisani yafito da waya ya kira Zuhra ya Sanar da ita ya zo.

''Babu jimawa sai gata ta zo k'amshinta da yashaqa yasa ya yi saurin d'agowa ya dube ta, sanye take atamfar super exclusive d'ikin riga da skirt ya yi tight d'inta sosai kamar ta nisa rigar ya yake nonuwanta a fili d'an siriri veil tasa ta yane kanta duk haka bai hanawa Kalaba twisting d'in da ke kanta fitowa ba wance akayi mata combination da black & purple attachment, ta yi matuk'ar kyau Ansar yana kare mata kallo ya kauda fuska ya dubi Granny fuskarshi d'auke da b'acin rai kamanunshi gaba d'aya suka sauya fissibillahi! Granny Abunda Ku ke yi Sam bakwa kyautawa kalli shigar da Zuhra ta ke yi kuma haka take fita wani sa'in ba ko mayafi amma anrasa Wanda zai tsawata mata.
Chapter 3 · 0% Book details