← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 30

Sashe 14

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Anaal tafito daga gida jikinta sanye da school uniform a hankali take tafiya ga k'atuwar schoolbag d'inta rataye a bayanta, bakin titi tanufa tasami adaidata da zai kaita school.
''Tun kafin tak'araso Ansar ya hangota yasaki ajiyar zuciya had'e da hamdallah. Yana kallonta har ta ra6a shi ta wuce yana ganin takai titi yaja mota ya bi bayanta, Horn yadinga dana mata juyowa d'aya ta yi ta kalli motar tadauke kanta batare da tagano wanda ke cikin motar ba saboda gilashi motar tinted ne.

"Ansar yana gani tayi nassara tsayar da wani mai adaidata ya yi saurin saukar da gillasai _ke Anaal bakyaji ne tun d'azu ina miki horn"?_
"Muryar sa Anaal tagano saida gabanta yafad'i a d'an rikice tajuya ta dube shi Ya Ansar tafad'a abaiyane tadawo da ganinta ga mai adaidata malam dan Allah minti 1.
"Okay hajiya amma ki yi sauri.
Tajuya tanufi motar tadafa k'ofar da ke saiti da shi ta d'an tura kanta cikin motar _ina kwana Ya Ansar_
Lafiya kishigo nayi dropping naki.
''Shiru ta yi tana kallonshi tarasa kalma da za ta furta masa gani shiru nata ya yi yawa yasa yace kishigo mana kina 6atawa kanki lokacin.
"Ba yanda ta iya dole tajuya sukuku kamar kazar da kwai yafashewa a ciki takoma wajen mai adaidata tabashi hak'uri.
"Ta bud'e k'ofar seat d'in baya ta ajiye schoolbag d'inta ta zauna a seat d'in gaba ya ja mota suka halba kan titi.
Shiru ya biyo baya Anaal tana nazari me Ansar yake yanufi da ita yayinda Ansar yake tunani shin me ke shirin faru d[truncated by WhatsApp]*SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*11*

Anaaal yakira sunanta cikin tautasan lafazi Na'am tafad'a had'e da kallonshi nasan za ki yi mamakin faruwar wasu abubuwa tsakanina da ke, toh ba abin mamaki bane in ki ka yi la'akari da kyakyawar alaqa da ke tsakanina da Abbah.
''Ya d'an yi _shiru na kamar _5 seconds_ daga bisani ya nisa yacigaba da cewa banaso ki matsantawa kanki da tunani, ni na d'auke ki kamar K'anwata ta jini duk abunda ki ke da buk'ata kada ki boye min ki d'auke ni matsayin Friend wanda ba za ki iya boye masa duk wata damuwa da ki ke ciki, kamar yanda nima ba zan boye miki halin da nake ciki ba.
"Anaal ta yishiru tana wasa da gefen hijabinta gaba d'aya kalaman Ya Ansar sun daure mata kai ta ya za'ayi tayi k'awance da namiji ko namiji Ansar Galadima gaskiya abun da wuya wai gurguwa da aure nesa.

''Anaal kin yi shiru ba ki bani amsa ba ko bakyaso na zama abokin shawararki"?
Girgiza kai ta yi cikin sanyi murya tafara magana ba haka bane Ya Ansar na yarda da kai 100% saidai ba ka tunani wannan sabuwar alaqa tamu ba zai kawo matsala ba"? Domin ni ina gudu duk wani abu da zai kawo fitina daga gareni.
"Murmushi ya yi bana tunani faruwa hakan in ma kina jin tsoro me zai hana mu dinga huld'a mu a 6oye"?
Jikin Anaal yadauki rawa da kyar ta iya furta a 6oye kuma"? To wai me yasa za mu dinga 6oye alaqar mu al'hali mu ba wani mugun abu mu ke aikatawa ba''?
Ansar yak'ara dafe steering cikin dabara da wayo yace saboda kina jin tsoro amma ni bayanshi banada wani dalilin kwakwara, amma kuma in kin amince kowa yasan cewa akwai k'awance a tsakaninmu ni a wurina ba matsala bane.

''Da Sauri Anaal tace No! Banaso kowa sani saboda gudun zargi Ansar ya yi murmushi jin dad'i yace shikenan daga yau mu zama friends koh"?
''Dariya marar sauti Anaal ta yi tace haka ne.
Dai-dai Gate d'in Aminu Kano commercial ya aje ta yadube ta a tsanake k'arfe nawa za ku tashi"?
Shiru tayi tak'i fad'a masa da kyar ya shawo kanta ta amince ta fad'a masa.
''Kina da waya"? Tambayar da yak'ara watsa mata kenan.
Kamar tace A,a sai kuma ta tuna k'arya ba halinta bane.
"Ta gyad'a kai phone d'inshi yadauko ya mik'a mata saka mun digit d'inki, hannunta har rawa yakeyi tasa mishi numberta ta mik'a mishi phone d'inshi har tayi yunkuri bud'e k'ofa yakira sunanta can k'asan mak'oshi _Anaaal..._
"Yanayin yanda yaja sunan nata ya haddasa mata kasala tajuya tana facing nashi _Na'am_ ta amsa had'e da kafe shi da idanu, shima tsareta ya yi da shu'umin kallo da sauri taje kauda fuskarta shima cikin sauri yadakatar da ita No...Anaal karki juya please akwai abunda nake kallo a fuskarki.
"Narke fuska ta yi kamar za ta yi kuka Ya Ansar zan yi latti fa
Shima kamar zai yi kuka ba za ki yi ba Anaal kallon 10 seconds zan yi miki.
''Ten seconds fa Ya Ansar"? Gaskiya ya yi yawa.
''Okay five seconds ya yi"?
Eh! Tafad'a had'e da gyad'a kai
Toh ki juyo mana kamar za ta fashe da kuka tajuya tana kallonshi kasa jure shu'umin kallon da yake mata tayi ta runtse idanuta gam yayinda Ansar yasami damar k'are mata kallo wani irin abu yakeji yana masa yawo tun daga d'an yatsar k'afarsa har zuwa tsakiyar kansa.
"Ya lumshe idanu Jin shiru shi ya yi yawa yasa Anaal ta bud'e nata idanu gani nashi idanu a rufe-ruff, yasa tashiga kallonshi electric shock taji yana janta kamar zai karar da jini jikinta. Jikinta na mazari ta 6alle k'ofa tafita jin karar bud'e k'ofa yasa Ansar ya bud'e idanunshi.
Ta bud'e seat d'in baya tad'auki schoolbag d'inta a kunyace tadafa k'ofar da ke saiti da shi _Na gode Ya Ansar_
A maimakon ya amsa mata sai kawai ya wanketa da murmushi yaciro k'udi ya mik'a mata _ga wannan ki yi breakfast_
''Mak'e kafad'arta ta yi Uhm..... Uhm...kabarshi kawai Granny tabani two hundred kuma Abbah yabani na transport sun wadace ni.
''Ya galla mata harara k'udin Granny da Abbah daban wannan nawa ne ko kina nufi banida matsayin da zan miki kyauta ki kar6a''?
Batare da tace komai ba tasa hannu biyu ta kar6a had'e da cewa na gode Allah yasaka da alkhairi amma gaskiya sunyi min yawa bara iya kashe su ni kadai ba.
"Tabe baki ya yi cikin gatse yace ki kashe rabi ki jefar da rabi.
"Anaal ta zaro ido har da su dafe k'irji k'udi ne zan jefar"?
''Eh! Man yafad'a cikin rashin damuwa.
Humm....tasauke numfashi ni kan bara iya jefar da k'udi ba.
Ansar ya yi murmushi yace toh ki je ki kashe su duka tunda ba za ki iya jefarwa ba.
tajuya jiki a mace tanufi Cikin makaranta Ansar ya bita da kallo yana Shafa gejere gemunsa sai da ta6acewa ganisa sannan yaja mota yanufi gida.

_10:33am_

Ansar yafito cikin shirin shi na tafiya "office jikinsa sanye da ash colour suit da blue colour long sleeve, kaitsaye part d'in Mum Fatee yanufa ya yi taking breakfast sannan yanufi office.
_11:30am_ yashiga conference hall tsawon lokacin suka dauka a meeting d'in agajiye yafito daga hall yanufi office d'inshi Ishaq na biye da shi dauke da files.
"Yana shiga office yacire coat yanemi sofa ya zauna ya dube ishaq yace ishaq yunwa nakeji ka je ka yi min order abincin me kyau.
''Okay Boss Ishaq yafad'a had'e da ficewa wannan ya ba Ansar damar afkawa tunanin Anaal baisan dalilin da yasa yarinyar take burgeshi ba yake jin kamar in yana tare da ita kada su rabo
''Komai na Anaal ya yi mishi musanman kyawawan d'abi'unta ina ma ace Zuhura ita ce Anaal ba shakka da na kasance me Sa'a a rayuwa.
"Yanda ishaq yafita yabar Ansar cikin tunani haka yadawo ya tarar da shi yana cikin cin abincin idanunshi suka kai duba ga wall clock da ke manne a bango Office d'in nashi.
''Ba shiri ya yi dropping spoon ya mik'e tsaye ya kwashe phone's d'inshi had'e da car key yanufi k'ofar fita jikinsa ko ina rawa yafita a bakin k'ofa yaci karo da ishaq maigida Ansar ina zuwa haka''?
"Fitan gaggawa ne yakamani ishaq ba zan jima ba zan dawo ka je office d'ina akwai Documents a locker ka dauka ka kai office d'in Abdallah, kace naje ya had'e su da wanda na bashi jiya yana magana ne had'e da tafiya Ishaq yana biye da shi har parking lot. Saida ya ja mota sannan Ishaq yakoma ciki domin aiwatar da abinda maigida Ansar yasaka shi.
Chapter 14 · 0% Book details