← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 30

Sashe 12

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

''Yakoma jikin kujera ya lafe ya zuba mata na mujiya{idanu} tana karatu yana aikin kallonta duk da jikinta yabata ita yake kallo ba Qur'ani ba hakan bai sa tad'ago ta dube shi saida takai dai-dai ayan da yadace ta tsaya sadakallahul azim"! Tafad'a had'e da tad'ago kanta.
"Mik'o min Qur'ani na.
Kamar daga sama muryarta yadak'i dodon kunnenshi a kasalance ya mik'a mata ta miyar a jakka.
"Taciro Ahalari me su'al wa jahab ta mik'a masa. Ya kar6a yana jujjuya shi ka bud'e shafi na farko ta umarceshi.
''Ya naga wannan kina nufi da shi zan yi karatu"?
"Kwarai kuwa saboda yafi sauki ganewa.
Toh ai ni nayi wannan.
Humm.....za ka maimaita ne sai naga kamon ludayinka koda zan canza maka wani ka bud'a shafi na farko za mu fara karatu nafara jin baccin.
"Saida yai murmushi sannan ya bud'e shafin na farko, kamar yanda ta karanta mishi Qur'ani batare da ta duba ba haka tafara karanto mishi wannan.
Shafi d'aya ta karanta mishi ta dasa aya.
Iya nan za mu tsaya gobe za ka yi mun bitarshi sauran littafai sai gobe zan zo maka da su.
''Na gode malama amma kuma sai naga kamar wannan da ki ka fad'a min ya yi kad'an ki k'ara mun mana yak'arasa magana yana wani langwa6e kai.
''Girgiza kai ta yi bazan k'ara ba kuma sunana Anaal ba malama sai ka kiyaye.
"Huh....malama kenan ni fa d'alibinki ne fa ta ya zan dinga fad'ar sunanki kaitsaye ba ko dan sakayawa"? Ai sai ki dinga kallona a matsayin d'alibi marar d'a'a.
''Amma kuma ni nace Ka fad'in sunan nawa Dan Allah Ya Ansar karka ce za ka dinga kirana da malama Allah ba zan ji dad'i ba tak'arasa magana kamar za tai kuka, batasan hakan da ta yi ba ta yi masifar burge Ansar ya lumsashe idanunshi yadauki tsawon d'ak'ik'a 2-3 idanunshi a lumshe daga bisani ya bud'e su fasss"! akanta.
"Kamar me koyon magana yafurta zan yi tunani akai malama tah.
''Cuno baki ta yi tana jujjuya kafad'arta alama shagwa6a ba sai gogan naku yasaki baki da hanci ya shagala iya shagaltuwa da kallonta.
''Da sauri ta mik'e tsaye ta sunkuce Jakarta sai da safe ka gaida su Nadeeya ko juyawa bata k'ara yi ba tashige d'akin tabarshi zaune.
"Sai da yadauki tsawon lokacin a zaune kafin ya mik'e yafita yau ma bai nemi Zuhura ba yai tafiyarsa a gate ya tsaya ya yi wa Abbah sai da safe yafice.
"Cike da nishad'i yake driving yana murmushi har ya iso gida murmushi bai gushe daga kan fuskarshi ba.
"Yayi parking motarshi a parking lot gani securities birjik da kak'in custom ga kuma blacks cars d'in Daddy a Parke ya tabbatar mishi Daddy ya zo.
"Ya kai duba ga wrist watch d'in hannunshi 10:15pm yanufi part d'inshi yasan irin wannan lokacin Daddy ya kwanta sai dai da safe koda zai same ganinsa.
''Yana rage kayan jikinshi ya fad'a bathroom yasakewa kanshi shower yana fitowa ya tsane jikinshi da towel ya Shafa lotion yasaka pyjamas d'inshi yak'ara gudun Ac ya haye gado ya karaton addu'a kwanciya bacci ba wai don yana jin baccin ba. Kasancewar baccin zai iya d'auke shi "at any time.

"Ya lumshe idanu muryar Anaal ke yawo a kunnenshi in juya hagu yak'ara juyawa side d'in dama daga karshe yadauki pillow ya jefa a k'irjinshi ya matse shi gam he had a sleepless night duk lokacin da ya yi yunkuri rufe idanu Anaal yake gani yayinda kunnenshi ke jin sautin amon muryarta Yajuya side d'in damansa, Yak'ara zurmawa a tunani ba shi ne yai bacci ba sai around 2:30am.

_"Washe Gari_
_11:00am_

Ansar yafito cikin shirinsa na tafiya office black trouser ne a jikinsa da red colour long sleeve ya tsuke wuyansa da black necktie k'afarsa sanye da cover shoe black in colour jikinsa na fitar da k'amshin turaren "mesmerized Cologne kafad'arshi na rataye da briefcase hannunshi d'aya yana sakad'e cikin aljihun wandonshi, fuskarshi d'auke da murmushin abin sallarsa sai walk'iya Yake.
"Shigar ta yi masifar yi masa kyau Ansar irin mazanan ne masu murd'ad'e jiki he's very giants man kallo d'aya za ka yi masa kagano ba duk namiji zai iya karawa da shi ba.
"Direct parlourn Mum Fatee yanufa tsit parlour yake ba kowa k'amshin turaren wuta ya gauraye parlourn.
''Ya ajiye briefcase da hannun kujera ya nufi staircase ya hango Mum Fatee da Housemaids a kitchen suna had'a breakfast. yafasa haura stairs yanufi kitchen d'in ta baya ya rungume Mum Fatee "Good morning Mum"!
''Morning Boy katashi lafiya"?
Am Fine Mum"
That's Good My Boy Daddy yadawo har yai bacci yana tambayarka.

Jiya da nadawo daga gidan Granny naga Prado's d'inshi a parking lot lokacin naga dare ya yi shiyasa ban shigo ba bara naje mu gaisa yajuya yafice da d'an gudunsa ya haura staircase.
"Controller General Basheer Galadima yana kishingid'e jikinsa sanye da farar Jallabiya da sallama Ansar yashiga parlourn, Daddy oyoyo Ansar yafad'a kamar k'aramin yaro.
"Controller ya tashi zaune yana murmushi Ya kuma ware hannayenshi Ansar na zuwa yashige k'irjinshi hugging d'in Juna suka yi tightly Boy ya aiki da hak'uri da jama'a hope komai yana tafiya yanda yadace"?
"Alhamdulillah Daddy ni kaina banta6a tsanmani abubuwan za su daidaita kamar haka ba.
"That's Great I'm proud of you my Boy dama nasan za ka iya handle d'in company nan ka kuma tafiyar da shi yanda yadace, Allah yai maka albarka.
"Ameen Daddy.
Ansar yasaki Daddy ya zauna kusa da shi sai doka murmushi yake shi dai duk duniya in kacire Allah da manzonshi ba abunda yakeso sama da iyayyenshi, bashida burin da yawuce ya kyautata musu kasancewar shi kadai suka Haifa d'a namiji gaba d'aya hope d'insu yana kanshi.
"Gyaran murya controller ya yi alamar zai yi magana mai mahimmancin, kwanaki baya sa'eed ya kirani akan zance aurenka da Zuhura so yake ayi kafin azumi nace yabani lokacin zan yi magana da kai naji naka ra'ayi.
Ansar ya tsince kanshi da fad'uwar gaba ya rikice yashiga in da in da Dad...ddy...azumi fa"? Gaskiya ya yi sauri ni anawa tsari sai Zuhura ta gama karatu zuwa lokacin na kamalla gini na.
"Murmushi controller ya yi shikenan Boy tunda haka ka za6a inda rai da lafiya kamar gobe ne.
''Mum Fatee ta yi sallama tashigo ta dube suna murmushi firar me akeyi shine ba'a jirani ba"?
Controller ne yabata amsa cikin sigar wasa fuskarshi d'auke da murmushi ina ruwanki da ko firar me mu ke yi keda ki ke shigewa d'akin da 'ya'yanki kuna shawara abinku na ta6a tambayarki abunda ku ke tautaunawa akai"?
"Au.....Daddy tanan ka 6ullo to ae shikenan sai kutashi mu je ku yi breakfast in tayi tsami ma ji.
Ba abunda za ku ji domin wannany firar ta tsakanin d'a da uba ne ko Boy"? Controller yak'arasa magana had'e da kallon Ansar Dariya sosai Ansar ya yi yace haka ne Daddy.
"Zaro ido mum fatee ta yi lallai Boy haka ma za ka fad'a in dai Daddy ne tafiya zai yi yabarni da kai gidanan mu had'e maka kai ni da Girl's d'ina.
"Ansar yana dariya ya mik'e tsaye ya rik'on hannun Mum Fatee zo mu je Mum zan sanarda ke amma in ku ka had'e min kai ai na Shiga tara.
Controller da Mum suka sa dariya cike da farin ciki suka nufi dining area, Ansar ya ja ma Controller kujera ya zauna sannan shima ya zauna mum Fatee ta yi musu serving.
"Suna gama taking breakfast Ansar yai sallama da su yanufi office.

_8:00pm_

Kamar yanda jiya Ansar yadira gidan Granny yau ma hakan ce tafaru, saida ya tsaya a main gate wajen Abbah yasha green tea sannan yanufi part d'in Granny a parlour ya iske Granny tana kallon sunnah tv.
"Bayan sun gaisa suka shiga firar duniya Ansar yana yi yana kallon k'ofar d'akin Granny ko zai ga Anaal tafito.
Kamar daga sama ya ji muryar Zuhura Granny Ya Ansar ne ya zo naga motarshi a parking lot"?
"Ta bankad'o curtain tashigo tana gani Ansar tasaki murmushi idonka kenan my love yanzu abunda ka yi min fissibillah"! Kana gani yadace"?ko ba komai na ba ka hak'uri.
Kallon hadarin kaji Ansar yai mata yadaure fuska tamau ya had'e rai.
"please Ya Ansar I said am sorry ta zube gabanshi tashiga zuba masa magiya.
Ko kallo bata isheshi ba sai ma kauda fuskarsa da ya yi.
Bud'e curtain aka yi had'e da sallama cikin sauri Ansar yajuya ya kalli bakin k'ofa, sanye take da hijab sky blue in colour iya gwiwarta duk da fuskarta ba make-up ta yi masifar yi ma Ansar kyau.
"Ina wuni Ya Ansar"?
Anaal ta gaida shi
Muryarshi har wani shacking take yi ya amsa da la...fi..ya....malama Anaal ya gida ya karatu"?
Ta rausayar da kanta tace Lafiya qalau Alhamdulillah.
Ta juya cikin tafiyarta a natse tashiga bedroom d'in Granny yayinda Ansar ya rakata da ido saida tabacewa ganinshi sannan yadawo da dubanshi ga Zuhura wance takafe shi da nata idanu...

Jeeddah Aliyu
*SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*10*
Chapter 12 · 0% Book details