← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 30

Sashe 29

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Har tadasa aya Ansar yana kallonta adage yana Shafar d'a siriri gemunshi, kingama...?
Ta gyad'a kai.
inaso k'ibud'e kunnenki da kyau ki saurarani nasoki zuhura ban kuma ta6a tsanmani zan daina sonki ba, munana halayenki su suka jagorancin goge sonki a zuciyata ba zan 6oye miki ba domin banga amfani yin hakan ba Zuhura ayanzu banasonki na tsaneki bana fatan duk wani dangantaka da zai hadani da ke ko zan mutu wallahi ba zan aurenki ba domin kinficemin arai.

Ni da ke Sam bamudace ba ki je kiyi rayuwarki nima nayi tawa, so tsuntsu ne ayanzu tsuntsun sonki yatashi na kuma tabbata ba zai ta6a dawowa kanki ba don haka ki shafamin lafiya kifita daga rayuwata.

Tashin hankali Wanda ba'asa masa rana Zuhura jin maganganu Ansar take kamar, saukar aradu wani k'aton k'ololo yatokare mata mak'oshi duhu ya mayewa ganinta numfashinta yana k'ok'arin barin gangar jikinta, ashe akwai irin wannan ranar da za ta zo Ya Ansar zai bud'e baki yace bayasonta ya tsaneta.

Ki tashi maza ki ja k'awar cin mushenki kubarmin office tun kafin nai miki wulaqancin Wanda atarihin rayuwarki ba'a ta6a yi miki irin shi ba.
fad'uwa tayi daga kan kujera ta zube guwaiyu biyu-biyu k'asa tarusa kuka tashiga rok'oshi karka yimin haka Ya Ansar wallahi insonka in narasaka zan iya mutuwa Dan Allah kayi hak'uri kayafemin.

Kin riga kin makaro Zuhura tuni na yage sonki daga zuciyata ayanzu cike take da k'iyayyarki, da tsanarki Mae zafin gaske duk abinda zai faru saidai yafaru ba zan aureki ba na fahimce kinada sha'awar zama office d'ina sai ki yi ta zama har abusa k'aho.
Ya kwashe wayoyinshi da makulin mota da sauri Zuhura ta tashi ta rik'eshi gam-gam tana kuka haik'an! Da kyar ya yi nasarar yakiceta daga jikinshi azuciyarshi yace shegiya sai k'arfi tsiya kamar namiji, yafice da sauri har yana had'awa da gudu.

Leebeauty ta tafa hannaye huh! Dad'i na gobe saurin zuwa Wanda baiji bari ba zai ji hoho! Sai ki tashi mutafi ke kan tak'are miki, ayanzu ke da kazar da aka tsumata aruwa bakuda banbancin.
"Haba! Leebeauty ki tausayimin mana ahalin da nake ciki bai kamata kidinga fad'amin bak'ak'en maganganu ba.
Uhm... Sai kiyi ni ki tashi mutafi domin inada abinyi ba gadin office na zo yi ba.
"Dole ta mik'e tana mashalo kamar wance tasha syrup suna fitowa suka ci karo da Abdallah cikin kuka tafad'a masa wulaqancin da Ansar ya yi mata, harara Abdallah yadanna mata ya zage ta tass! Yak'ara da cewa Ansar yamin dai-dai gara da yabarki sai ki je can! Ki k'arasa da fitsara da rashin kunyarki, kuma duk ranarda nak'ara ganin k'afarki a company nan sai na karya miki ita heartless kawai.

Rana zafi inuwa k'una Zuhura tarasa tudun dafawa da matsanancin kuka takoma gida Hajiya saudat naji abinda yafaru ta harzuk'a matuk'a tasha alwashi sai tadawowa da Zuhura farin cikinta.

_4 day's later_

Duk wata hanya da Ansar zai bi yaga Anaal ya bi abin yaci turu gudunshi takeyi kamar naman daji tsawon kwanaki nan ya yi su ne cikin tashi hankali.
Yamma lis! Anaal tadawo daga islamiyya ak'ofar gida taci karo da Ya Abdallah zaune a boot d'in motarshi yana waya yana ganinta ya katse wayar.
"Sannu da zuwa Baby Anaal{dama haka yake kiranta}
Tana murmushi ta amsa da yauwa. Ya Abdallah ina wuni...?
Lafiya lau Baby ya karatu?
Alhamdulillah!
Yaushe za Ku fara exams...?
On monday insha-Allah Dan Allah atayamu da addu'a.
In wannan ne bakida matsala Baby Anaal.
Na gode Ya Abdallah!
Har tajuya yadakatarda ita d'an tsaya Baby Anaal akwai wata magana nakeso da nayi da ke.
Taja tayi tsaye agabanshi Baby Anaal dama najima ina jiran zuwan wannan ranar da zan baiyana miki sirrin da ke zuciyata.
Alhamdulillah! Yau Allah yacika min burina gani gaki zan bud'e miki sirrin z[truncated by WhatsApp]*SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*Goron Sallah*:-

_*Walk humbly talk politely dress neatly Treat kindly pray attentively donate generously, may Allah bless & protect all of you my fan's*_
_Happy Eid mubrak_

*26*

Jikin Anaal yadauki rawa gabanta yafadi rass! Yayin da Abdallah bai lura da halin da take ciki ba, yacigaba da cewa Baby Anaal najima da sonki azuciyata so kuma ba na wasa ba aurenki nakeso yi kafin na sanarda ke abinda ke raina sai da na fad'awa Abbah yace na nemi yarda ki in kin amince shi bashida matsala.
Baby Anaal nafara sonki tun kafin ki mallake hankalin kanki Dan Allah ki amince da ni zan jiyarda ke dad'i da ba kowace mace take samu irinshi ba.

"Ajiyar zuciya Anaal tasauke yafi akirga wannan shi ake kira Ana wata ga wata, k'asa magana tayi sai kawai ta sadda kanta k'asa kamar mai nazari k'asa da murya Abdallah ya yi yadawo kalar tausayi karki damu kanki da tunani zan ba ki wadatace lokacin ki yi nazari da kyau duk da nasan banida makosa kowace mace nace inaso da gudu za ta kar6e ni ki je kawai ki yi tunani.
"Da kyar ta ja k'afafunta tashiga gida tun daga ranar Abdallah ya nace mata kamar chewing gum ya siya mata waya mai tsadar gaske, sai kashe mata k'udi yakeyi kamar hauka daga Abbah har Ammi sun ji dad'i al'amari musanman Abbah da yake gani Abdallah shi yafi dacewa da 'yarsa ko ba komai yasan asali da tushenta.

Ta6angare uwar gayya Anaal Sam ba bu son Abdallah aranta tana, kulashi ne don ba yanda za ta yi tsakaninta da shi daga Uhm.... Sai a'a yayinda Abdallah yadauki hakan a matsayin kunyar da take da ita.

_5:44pm_

Tun daga nesa Anaal ta hango Ansar da Abdallah zaune a k'ofar gida akan boot d'in mota dama duk yammacin matuk'ar tana zuwa islamiyya za ta dawo ta tararda Abdallah yana jiranta, matsanacin fad'uwar gaba da tsoro suka lullu6eta domin rabonta da tasa Ansar a ido kusan 1 week gaba d'aya ta dabarce had'e da susucewa, tun kafin tak'araso Abdallah yafara washe hak'ora _oyoyo my sweetest love tun d'azu nake baza ido naga ta inda za ki 6ullo_
"Hmm!...tayi murmushin yak'e kawo jakkar na rage miki nauyi k'ok'arin yake ya kar6e jakkar littafanta da ke rataye a kafad'arta, da sauri tadafe jakkar tana girgiza kai barshi Ya Abdallah na gode!
"Da k'arfi tsiya ya fincike jakkar duk abinda yake faru tsakaninsu Ansar yana kallonsu ta k'asan ido jin yake kamar ya shak'e wuyansu yaita dukansu har sai sun nemi agaji.
Mtcsww! Ya ja guntun tsaki ya mayarda hankalinshi wurin wayar hannunshi bayaso ko kad'an su gano halin da yake ciki yak'ara murtuk'e fuska ya had'e rai.

"Ina wuni Ya....An...sar tafad'a cikin sark'ewar lafazi.
Banza ya yi da ita kamar bai ji ba
Abdallah ya zungure shi kai kurma ana gaidaka.
A yatsine yad'ago kamar yaga kashi ya d'an waiga wa ke gaidani''?
Anaal ce gatanan tsaye gabanka.
Ya kya6e baki kamar Mae ciwon hak'ora ya amsa da sannu.

"Sam bataji dad'in yanda ya amsa mata gaisuwa ba shi kanshi Abdallah saida yaji ba dad'i ya mik'a mata jakkarta ki shiga gida my Baby bayan salla isha zan shigo mu sha fira.
Batare da tace komai ba ta kar6i jakkarta tashiga gida.
"Haba Ansar wannan wane irin lokacin ne..? Yarinya ta gaidaka kana amsa a wulaqancin baya tuni na sanarda kai matsayin da takeda shi awurina, wallahi ka gyara wannan sabuwar d'abi'ar taka wulaqanta d'an Adam ba halinka bane.

Mtcsww!... Yasake Jan tsaki kana ya gyara zamanshi yakara gwa6e fuska Wanda yak'ara k'ularda Abdallah, kafi kowa sanin halina Abdallah banaso raini su kuma wad'annan k'ananan yara kana furta kana sonsu aji da girmanka zai fad'i a idonsu don haka kasani kana siyawa kanka rashin girma ne.

"Kai kadamu da girma soyayya ba ruwanta da wannan inason Baby Anaal tamkar numfashina insha Allah sai na aureta sai dai girman nawa ya zube gaba d'aya a idonta.

Kallo uku saura kwata Ansar yakewa Abdallah daga bisani yadiro yace ba sai in tana sonka za ka aureta ba..?
Ran Abdallah yak'ara b'aci ubanwa yace da kai bata sona...?
Hmm....Abdallah kenan dad'ina da kai shasshasha ne, ae alamar k'arfi tana ga Mae k'iba kai yanzu awannan shekarur naka ace ba ka iya bambance tsakanin so da rashinsa..?

Shiru Abdallah ya yi yana kallon Ansar daga bisani yaja tsaki mtcsww.... Ta soni ko kada tasoni ni inasonta ko ana hamaza hamata sai na aureta.
Ansar yata6e baki daga haka har suka rabo ba Wanda yasake tankawa d'an uwanshi kowane da abinda ke cikin ransa.

_washe Gari_

Anaal tafito cikin shirin zuwa school ta hango motar Ansar gabata yafad'i rass...sauri take kamar za ta tashi sama so take takai bakin titi ta yanda za ta tare adaidaita, gani abinda take shirin aikatawa yasa yafito daga mota yafara kwalla mata kira Lucky....!Lucky...! Ki tsaya ki saurareni gani ba za ta tsaya ba yasa yabita da d'an gudunsa yana cinmata ya rik'e hijabinta da k'arfi dole ta tsaya cak...wuce mutafi yafad'a cikin kaukausar murya.

Hawaye da take 6oyewa suka zubo mata sharr....dole tajuya tafara tafiya kamar barauniya yana rik'e da gefen hijabinta sauk'inta d'aya safiya ce ba mutane sosai da ba abinda zai hana tadawo abin kallo.

Ahaka suka k'arasa mota yabude mata tashiga yazagaya yashiga ya ja motar suka dauki hanya.
Menene tsakaninki da Abdallah..?
Batayi mamakin jin wannan tambayar daga bakinsa ba, atsanake tad'ago kaitsaye tace sona yakeyi da aure.

_sonki yakeyi da aure_ ya maimaita abinda tafad'a yana kad'a kai
Yakamata ki taka masa birki da wuri kada ki wahalarda shi.

"Ban fahimcinka...?
Tafad'a tana kallon gefen fuskarsa.
Ki sanarda shi bakyasonshi domin ki hutarda shi yawan hidima da yake miki.

''Huh......wa yagaya maka bana sonshi...?
Ba sai angayamin ba nakan karanta zuciya duk wani mutum da yazo kusa da ni Dan haka ina umaurtaki da ki yi gaggawa fitarda shi duhu kada kwa6arki ta yi ruwa.

Domin Abdallah yana da naci da sa'a tamkar ni yakan jajirce iya 'karfinsa har sai ya mallake abinda yakeso, shiyasa nake gargad'inki ki rabuda shi banaso alaqarki da shi karatu za ki yi ba aure ba.
Chapter 29 · 0% Book details