← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 30

Sashe 10

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_6:07pm_
Ansar ya yi parking motarshi inda yasaba jiran wucewar mai niqan, cikin Sa'a baifi 7 minutes da tsayawa ba sai ga ta saidai yau ita kadai ce.
Yau Ansar ya k'udurta aransa sai ya yi mata magana, har wani gyaran voice yake tana kawowa daf da shi yayi k'undubala had'e da 'kunar ba'kin wake yafurta _sannu malama"_
Ga mamakinsa sai ga ta ja ta yi tsaye cikin _ba wani sannu malama ka tabbata ka zo d'aukar karatu da wuri domin Granny ba ta Lattin gashi kana cika bakin kafita_ tana k'arasa magana tajuya a rikice Ansar ya bud'e mota yafito _Anaal"!_ yakira sunanta a rud'e na'am Ya Ansar"!
Yak'arasa kusa da ita yana dariya mai ban sha'awa sannu da zuwa malama Anaal ya makaranta ya karatu"?
"Saida ta lumshe idanunta sannan ta bud'esu "Alhamdulillah"!
Ansar ya gyara tsayuwarshi yasaka hannunshi na hagu cikin aljihun wandonshi fuskarshi na fitar da k'ayatatcen murmushi wanda yak'ara fitowa da kyaunshi da kwarjininshi.
"Gaskiya Anaal ke miskilace a kullum sai kin wuce ni anan wajen dai-dai da sau d'aya ba ki ta6a nuna kinsanni ba.
Dariya Anaal ta yi mai dad'i ta ratsa kunnnuwa Ansar ba Shari ya lumshe idanu daga bisani ya bud'e su yana mai cigaba da kallonta har yanzu dariya take yi.
Ta d'an tsagaita da dariya "still da sanyaye murmushi akan fuskarta, Allah Ya Ansar kabani dariya.
"Toh bani abata yafad'a yana kallon kwayar idonta domin ita kadai yake iya hangowa daga cikin niqan.
"Sosai yanzu tasa dariya bata ce da shi komai ba tajuya tacigaba da tafiya yabita da kallo tashige lungu da yasa6a gani tana shiga take yagano shortcut ce na zuwa gida, yafi sauri bisa ga ta mik'e hanya street.
''Tana 6acewa ganinshi yasaki murmushi had'e da hargitsa laulausa gashin kanshi. Cikin nishad'i ya shure wata empty robar ruwan da ke k'asa.
"Ya ja motarshi yanufi masallacin da yasaba sallah bayan ya gama sallah yanufi cikin gida zuciyarshi cike da burin sake tozali da Anaal.
"Dama Anaal itace mai niqan itace mai zazzaqar murya gaskiya Anaal 'yar baiwace ji ko dariyarta mai dad'i, kamar ta dawama yi min ita. Da wannan yadana "Horn Abbah ya bud'e masa gate ya yi parking yafito yana murmushi yanufi wajen Abbah
Yana zuwa miqa masa hannu suka yi musabaha Abbah yana fara'a yace Muhammadu ya gida ya aiki"?
"Lafiya qalau Alhamdulillah! Abbah.
Masha Allah"! Yau ka zo da sa'a domin har na dafa mutumin naka {green tea} Ansar ya washe hak'ora madallah Abbah mu k'arasa na d'an kora.
Yana kur6a green tea suna ta6a fira saida ya shanye cup 3 sannan ya mik'e Abbah zan shiga daga ciki.
Toh Muhammad a fito lafiya"
Allah yasa Abbah yafad'a had'e da juyawa yanufi part d'in Granny.
Da sallama ya tura k'ofar shiga parloun Granny da Anaal suka amsa masa, yanemi sofa da ke facing nasu ya zauna Anaal tacigaba da murzawa Granny maganin da ta ke Shafa mata na ciwon k'afa.
Granny har yanzu k'afar bata sake bane"?
Bata sake ba Ansaru gatanan ina fama musanman yau ta matsa min sosai.
"Tausayinta yakama Ansar yace ki shirya Granny gobe zanzo mu je asibiti, ko za su canza miki magani.
"Uhm... Ba inda zan je Ansaru nasan halin likitocin nan sarai ba wadatacen imani ne da su ba cikin mugun engine d'inan za su sakani su dinga gasa ni kamar sun same kaza.
"Granny na dasa aya Ansar da Anaal suka bushe da dariya ba mai kama wani, Granny ta kama baki tana kallonsu kaga ja'irai yara ni ku ke yi wa dariya"? tun lokacin da naji Ansaru yace zai dinga zuwa d'aukar karatu nasan cewa ba wani karatu da zai yi ya zo ne bud'e Sabon rumbun dariya a parlourna.
"Ansar da Anaal suka k'ara sa dariya Anaal har da dafe ciki hawaye na tsiyaya daga idanunta.
"Ya Allah! Granny tafad'a had'e da mik'ewa da kyar bari na ba ku wuri maimakon karatu ku sha dariya ta nufi bedroom d'inta Anaal ta tashi da sauri ta kama hannunta sakamako gani yanda take taka k'afar da kyar har bedroom tarakata sannan tadawo, tarar da Ansar yana dariya ta yi tsaye had'e da crossing hands nata a k'irji tana kallonshi a zuciyarta tace kai wannan d'an taliki akwai dariya har na siyarwa.
"Ya tsagaita da dariya nashi ya dube ta fuskarshi d'auke da yalwatatcan murmushi malama ke nake jira fa.
"Tarausayar da Kai ta tak'o zuwa gabanshi ta zauna nesa da shi kad'an....

Jeeddah Aliyu
*SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*9*

Kanta na sunkuye tana wasa da fingers nata ta furta ina littafai ka"?
A maimakon yabata amsa sai kawai ya tsareta da idanu jikinta yabata yana kallonta a tsanake tad'ago eyes nata ta zube su a nashi, kallon-kallon suka shiga yi kasa jure kallonshi nashi ta yi sakamako d'an banzan kwarjini da yai mata ta sadda kai k'asa.
"Nace ina littafai ka"? tak'ara watsa masa tambaya karo na biyu.
''Ya Shafa gashin kanshi har zuwa ga d'an siririn gemunshi yana kallonta, ta k'asan ido yana murmushi.

''Anaal ta kwa6e fuska tafara magana da zuciyarta wannan karatu ya zo ko kallon mutane"? Ni fa na tsani kallo ya wani kafe ni da idanu ba ko k'intawa. "Ya Ansar please ina littafanka dare yanayi fa"?
Ya d'age giran ido yana kallonta banida su yafad'a kamar mai rad'a.
''What's doe's mean"?
Babu ko ke bakisan kalma babu bane"?
''Amma kuma ka ce karatu ka zo dauka"?
''Yeah!
Kuma bakada littafai"?
''Ya gyad'a kai
Kana nufin ba ka shirwaya karatun ba zuwa kawai ka yi"?
''Nop
"Tabe baki Anaal ta yi saboda Ansar yafara kaita bango, iya tsawon rayuwarka kata6a ganin wanda yaje gona ba fatanya kuma yace noma ya je yi"?
"Murmushi ya yi ba sai ya ara a wajen makwacinsa ba, ko ke bakisan mutum zai iya aron abunda bashida shi ba"?
Au.....kana nufi ni ce ma Zan ba ka aron littafi"?
Eh man ko bara ki bani bane"?
Batare da tabashi amsa ba ta tashi tashiga bedroom d'in Granny ta iske ta kwance tana jan casbaha, tad'auki Jakarta na islamiyya.
''Tafice ta zauna mazauninta na tun asali Qur'ani za mu fara ko wane littafi"?
Ansar yasaki murmushi shi dama qira'arta yakeso yak'ara ji ba wani karatu da ya zo yi, mu fara da Qur'ani.
''Daga sama za mu fara ko daga k'asa sai mu yi sama"?
''Mu fara daga sama yafad'a cikin zumud'i.
Taciro Qur'ani daga Jakarta ta mik'a masa za mu fara daga fatiha.
Ya gyad'a kai cikin zazzaqar muryarta tafara karanto basmallah kanta na sunkuye tacigaba da karatu har ta kai karshe suratul fatiha.
''Tafad'a suratul Baqara a wannan karon Ansar kasa jurewa ya yi saida yad'ago ga mamakinsa sai ga ba Qur'ani a hannunta da kai take rero masa karatun.

''Yakoma jikin kujera ya lafe ya zuba mata na mujiya{idanu} tana karatu yana aikin kallonta duk da jikinta yabata ita yake kallo ba Qur'ani ba hakan bai sa tad'ago ta dube shi saida takai dai-dai ayan da yadace ta tsaya sadakallahul azim"! Tafad'a had'e da tad'ago kanta.
"Mik'o min Qur'ani na.
Kamar daga sama muryarta yadak'i dodon kunnenshi a kasalance ya mik'a mata ta miyar a jakka.
"Taciro Ahalari me su'al wa jahab ta mik'a masa. Ya kar6a yana jujjuya shi ka bud'e shafi na farko ta umarceshi.
''Ya naga wannan kina nufi da shi zan yi karatu"?
"Kwarai kuwa saboda yafi sauki ganewa.
Toh ai ni nayi wannan.
Humm.....za ka maimaita ne sai naga kamon ludayinka koda zan canza maka wani ka bud'a shafi na farko za mu fara karatu nafara jin baccin.
"Saida yai murmushi sannan ya bud'e shafin na farko, kamar yanda ta karanta mishi Qur'ani batare da ta duba ba haka tafara karanto mishi wannan.
Shafi d'aya ta karanta mishi ta dasa aya.
Iya nan za mu tsaya gobe za ka yi mun bitarshi sauran littafai sai gobe zan zo maka da su.
''Na gode malama amma kuma sai naga kamar wannan da ki ka fad'a min ya yi kad'an ki k'ara mun mana yak'arasa magana yana wani langwa6e kai.
''Girgiza kai ta yi bazan k'ara ba kuma sunana Anaal ba malama sai ka kiyaye.
"Huh....malama kenan ni fa d'alibinki ne fa ta ya zan dinga fad'ar sunanki kaitsaye ba ko dan sakayawa"? Ai sai ki dinga kallona a matsayin d'alibi marar d'a'a.
''Amma kuma ni nace Ka fad'in sunan nawa Dan Allah Ya Ansar karka ce za ka dinga kirana da malama Allah ba zan ji dad'i ba tak'arasa magana kamar za tai kuka, batasan hakan da ta yi ba ta yi masifar burge Ansar ya lumsashe idanunshi yadauki tsawon d'ak'ik'a 2-3 idanunshi a lumshe daga bisani ya bud'e su fasss"! akanta.
"Kamar me koyon magana yafurta zan yi tunani akai malama tah.
''Cuno baki ta yi tana jujjuya kafad'arta alama shagwa6a ba sai gogan naku yasaki baki da hanci ya shagala iya shagaltuwa da kallonta.
''Da sauri ta mik'e tsaye ta sunkuce Jakarta sai da safe ka gaida su Nadeeya ko juyawa bata k'ara yi ba tashige d'akin tabarshi zaune.
"Sai da yadauki tsawon lokacin a zaune kafin ya mik'e yafita yau ma bai nemi Zuhura ba yai tafiyarsa a gate ya tsaya ya yi wa Abbah sai da safe yafice.
"Cike da nishad'i yake driving yana murmushi har ya iso gida murmushi bai gushe daga kan fuskarshi ba.
"Yayi parking motarshi a parking lot gani securities birjik da kak'in custom ga kuma blacks cars d'in Daddy a Parke ya tabbatar mishi Daddy ya zo.
"Ya kai duba ga wrist watch d'in hannunshi 10:15pm yanufi part d'inshi yasan irin wannan lokacin Daddy ya kwanta sai dai da safe koda zai same ganinsa.
''Yana rage kayan jikinshi ya fad'a bathroom yasakewa kanshi shower yana fitowa ya tsane jikinshi da towel ya Shafa lotion yasaka pyjamas d'inshi yak'ara gudun Ac ya haye gado ya karaton addu'a kwanciya bacci ba wai don yana jin baccin ba. Kasancewar baccin zai iya d'auke shi "at any time.
Chapter 10 · 0% Book details