← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 30

Sashe 17

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tajuya fuskarta d'auke da k'ayatatcen murmushi _thanks_ tafad'a had'e da langwabe kai.
''Ya mayar mata da Martani murmushinta _you're welcome Dear_
Tadauki Schoolbag d'inta yaciro k'udi ya mik'a mata mak'e hannu ta yi, ya murtuk'e fuska ki kar6a mana.
Ko na jiya ya Ansar da kabani suna cikin schoolbag ban kashe ko kwadala a ciki ba.
Wannan kuma ke ya Shafa ki kar6a tun kafin raina ya 6aci. Girgiza kai tashiga yi kamar mai shirin yi kuka Ya Ansar Allah ba abinda zan y.....katse ta ya yi ta hanyar d'aga mata hannu ya balle k'ofa yafito ya ja schoolbag d'inta da k'arfi dole tasakarsa masa ya zuge zip yasaka k'udin a cikin ya mik'a mata tak'i kar6a ya ajiye a k'asa yashiga mota yaja yabarta tsaye tana mamakin wannan k'arfin halin nashi.
Lokacin tashinsu school ya yi tana fitowa gate taci karo da shi bata yi mamaki ganin nashi ba. Saboda taji a jikinta zai zo.
''Tun daga lokacin Ansar ya mayarda kanshi driven Anaal shi yake dropping nata school ya kuma yi picking nata shaquwa mai ban mamaki tashiga tsakaninsu.

"Ansar bai zai iya yini d'aya cur batare da yaga Anaal ba. kamar yanda ita ma in bataganshi ba batada kwanciyar hankali har sai ta kira shi a waya taji muryarshi sannan take samun natsuwa. dukansu a tunaninsu shaquwa da amintaka ce take hadasa musu hakan.

_8:05pm_

Ansar yadano hancin motarshi a farfajiyar gidan Baba sa'eed yanufi parking lot ya yi parking. Yanayi na wanda ya kwaso gajiya yafito daga mota yana rataye da briefcase da tarin file's a hannunshi saida yanufi main gate ya gaida Abbah sannan yanufi part d'in Granny.
Da sallama yashiga parlourn Anaal kadai ya tarar zaune tana Assignment Granny na bedroom tad'ago can k'asan mak'oshi ta amsa masa sallama, suna had'a Ido ta balla masa harara had'e da murgud'a baki ta maida dubanta ga Assignment d'in da takeyi.
"Sanyaye Murmushi Ansar ya yi yanufi wajenta hannayenshi na zube cikin aljihu wandonshi. Ya yi tsaye a gabanta yana kallonta k'asa-k'asa yana shu'umin murmushi nan nashi.
''K'amshin turare shi ya baibaye k'ofufin hancinta kasala had'e da wani irin sanyi Mae ratsa k'asusuwan jiki yasauka mata.
_Anaaal_
Yakira sunanta kamar Mae ciwon hak'ora.
_Na'am_
Ta amsa had'e da d'agowa suka sake had'a idanu ta cuno baki tana gunguni.
Wai laifin me nayi da Anaal take ta murgud'a min baki?
Cike da zallan mamaki take kallonshi au baka masan laifin da kayi ba?
"Saida ya zauna a kujera da ke facing nata yace of course yes! Kema kinsan da nasan laifin da nayi da tuni na fara ba da hak'uri.
''Humm! Jiya me hanaka zuwa gidanan?
Ko kasan na kira all digit naka switch off?

Murmushi ya subuce masa yashiga shafar laulausan sumar kanshi yana lumsashe idanu.
''Lallai Anaal kinfara damuwa da ni ada na dauka ni kadai ne nasan mahimmancin ki.
Tabe baki tayi cikin rashin damuwa da furucin nashi tace karka damu wannan, yana d'aya daga cikin halayena duk dalibin da nake koyarwa in banganshi ba nakan nuna kulawa ta akai.
''Ta6e baki ya yi baisan lokacin da ya ja siririn tsaki ba. Daga haka ba wanda yak'ara tankawa d'an uwansa ita tacigaba da Assignment d'inta yayinda shi kuma yacigaba da aikin kallonta.
Phone d'inshi ya yi ringing a wulaqance yake kallon wayan mtcsww"! Ya ja tsaki har kiran ya tsinke bai yi picking ba. Batare da mai kiran nashi yagaji ba yak'ara calling nashi back still ignoring call d'in ya yi.
''Anaal tad'ago ta dubeshi wulaqancin ba kyau Ya Ansar ka daure ka amsa kiran maybe, alkhairi ne yake binka kana gudunsa tak'arasa magana tana dariya. Ya tabe baki wannan kiran banajin akwai alkhairi a cikinsa tunda kin ce nayi picking, zan yi saboda ke. Kinsan ni d'alibi ne nagari bana tsallake umarnin malama tah.

O'o....ka ji da shi. Tafad'a had'e da cigaba da rubutunta.
Me zan ji da shi 'yan mata"?
D'agowa tayi ta jefa Biro a baki tana kallonshi fuskarta d'auke da murmushi, lallai nayi k'oshin d'alibi ina matsayin malamarka ka kirani 'yan mata.
To miye a ciki don na kira ki da 'yan mata ae ke ba 'yan maza bace? Ashe kuwa in haka ne magana na yana kan hanya.
Please ka d'auki wayanka kada Mae kira yaji zafi ignoring nashi da kayi.
Kafin ya yi magana kiran ya sake shigowa afusace ya yi picking _Zuhura_ yafad'a da kaukausar murya ya yi shiru yana sauraron abinda take fad'a mtcsww"! Ya zuba tsaki don kinga mota na a picking lot saime kina bi na bashi ne"?
Oh" nayi tsanmani kina bina bashi ne da za ki dameni da kira.

Mtcsww! Look Zuhura karki nemi ki takurawa rayuwata ki barni na huta mana. Ya yi shiru yana sauraronta hmmm! wannan kuka da ki ke yi ko a jikina domin nasan na munafuncin ne. Sai kin kwance min zariyan wando a kasuwa kidawo gida ki daura mun am tired I'm completely tired of your stupidity so let's me be....
Anaal da takasa kunne tana sauraron Ansar batasan lokacin da kyalkyace da dariya ba.
Kasa cigaba da magana ya yi yana kallonta da mugun mamaki, dariya take yi har da su dafe ciki. Gani haka yasa yace da Zuhura shikenan naji.
Na hak'ura mana yafad'a yana mushirikin murmushi.
No....ki yi zamanki karatu Anaal za ta fad'a min karki damu in nagama zan nemi ki.
I love you more.
Ya yi hanging up ya maida ganinshi wajen Anaal wance ke kwasan dariya abinta ya talafe kumatu yana kallonta ganin yanda ya shagala da kallonta, yasa ta katse dariya da takeyi ta rufe bakinta da tafin hannu.

''Gyaran murya ya yi me ki ke yi wa dariya Anaal?
Shiru tayi kamar bataji tambaya da ya yi mata ba.
Yakira sunanta cikin laushin murya kamar Mae rad'a.
_Anaal_
Ta amsa da
_Na'am_
Nace me ki ke yi ma dariya?
A maimakon ta bashi amsa sai tasa dariya cikin muryar dariya, tace maganarka ce tabani dariya iya jina banta6a jin ance a kwance zariyan wando saidai ace zani.
Humm......toh ae ni bana daura zani wando nake sakawa kinga kenan ba zanyi zaurance da zani ba.

mik'ewa tsaye ta yi ta dube shi kallon ido cikin ido tace duk da haka zani ake cewa.
Murmushi yasake mata naji malama tah next time zance zanin Anaal cos na gayamiki bana daura zani.
Turo baki tayi tajuya har tayi tako d'aya zuwa biyu ya dakatarda ita ta hanyar cewa wai ke ina za ki je naga sai wani rawan k'afa ki ke yi?
Jakka zan dauko mu yi karatu tafad'a had'e da kallonshi.
Ki dawo ki zauna yau ba zan yi karatu ba.
Saboda me?
Saboda yau alhamis a tsarin kowane makaranta islamiyya ana hutu, nima yau hutawa zan.
''Zaro ido ta yi yanzu a waya naji kana gayawa yaya Zuhura karatu za ka yi, shine za ka sauya ra'ayi da wuri haka?

"A waya nace zan yi karatu a zahiri kuma nace ba zan yi ba, gara kidawo ki zauna ki cigaba da assignment d'inki zai fi miki sauki da wannan tsayuwar da ki ke yi.
''Tana gunguni tadawo ta zauna a mazauninta Yayinda Ansar yafito da laptop d'inshi yasoma shigar da bayanai da ke cikin file's.
Annal tad'ago tana kallon yanda yake operating laptop d'in a yangance ta, ta6e baki had'e da yatsine fuska. Kamar ance Ansar yad'ago yaga tana kallonshi tana yatsina ya akayi ne 'yan mata naga kina mun kallon burgewa? yak'arasa magana yana kashe ido d'aya.
Murmushi tayi wanda yak'ara k'awata ainihin kyaun fuskarta, kallon tausayawa nake maka ba na burgewa ba kalli yanda ka ke operating laptop kamar wanda bashida lakka kai komai sai ka sa yanga ko ni sa nake Mace nafika kama jiki idan, haka ka ke yi a office duk ranarda Dad yakamaka zai yi suspended naka ko ya yi firing naka gaba d'aya.
"Tun lokacin tafara magana Ansar yake kallonta yana zuba murmushi. Shi dai komai Anaal take yi burgeshi yake yi musanman in tana magana jin yake kamar yana yawo a gajimare saboda tsananin dad'i da gard'i da muryarta take masa.
''Mik'ewa ya yi yanufi wajenta yadaura mata laptop a cinya ya tattaro tarin file's d'in ya aza a hannun kujerar da take kai.

Jeeddah Aliyu*SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

14

Da mugun mamaki Tad'ago tana kallonshi ya d'aga mata gira kince ina operating laptop a yangace, shine na kawo miki ke da bakya yanga ki yi min aikin nasan za ki iya.
Muryarta na rawa tace ni....ni...
Ke...ke...me? Ya katseta da hanzari ba abunda za ki fad'a sai kinyi shi ko na murd'e miki kunne.
"Turo miki ta yi ni fa malamarka ce kuma ba kyau yi wa malami rashin d'a'a.
Ina ruwana da zamanki malamata in ke malamata ce ni kuma yayanki ne. Ina da matsayin da zan saka ki aiki ki yi koda ranki bayaso.
Chapter 17 · 0% Book details