← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 30

Sashe 7

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ansar yafito daga cikin gida yana tafiyar sauri yanufi parking lot ya ja motarshI kirar kia cerato dark blue in colour, da k'arfi yafizgi motar gateman ya bud'e masa gate yafice.
"Kaitsaye unguwar su Zuhura ya dosa dai-dai wajen da yasaba ganinta anan ya yi parking, zullumin yake had'e da addu'a Allah yasa mai niqan ba ta wuce ba har aka yi kiran sallah magarib yana zaune yana jiran tsanmani daga bisani da ya tabbata tariga ta wuce, dole ya ja motarshi ya tsaya bakin masallacin ya yi sallah magarib ya jira isha.
''Bayan ya yi sallah isha ya yanke shawarar shiga gidan su Zuhura, yasha black tea wajen Abbah maigadi.
"Horn ya yi Abbah ya bud'e masa gate Ansar ya yi parking yafito yanufi bakin gate ya tarar da Abbah har miyar da gate yarufe yana zaune, yasha rawani da baqin yanki irin nasu na buzaye.
"Sallama Ansar ya yi mishi had'e da mik'a mishi hannu, suka yi musabaha daga bisani ya zauna Abbah akwai shi ko sai andafa"?
Murmushi Abbah ya yi yace sai anfada muhammadu ban yi tsanmani za ka zo yau ba da tuni na dafa mana.
"Shima Ansar murmushi ya yi ba damuwa Abbah ko yanzu za mu iya dafawa da zafinsa yana k'unar baki yafi dad'i sha.
"Abbah ya yi dariya kai muhammdu lallai ka zama cikakke buzu saura kawai nafara yi maka nad'i.
Dariya Ansar ya yi Abbah har nad'in ina so ni fa duk abunda zai fito daga gareku Abbah ina sonshi.
Dad'i ya lullu6e Abbah yasan k'aunarsu da Ansar daga Allah ne domin yanda yake musu hidima, kamar su suka haife shi daga Abbah har Ammah suna matuk'ar k'aunar Ansar suna jinshi tamkar d'ansu Auwal da ya6ata shekaru masu dama da suka shud'e.
"Kamar yanda Ansar yasaba d'aukar murhu yad'ebo garwashi ko yanzu hakan ce tafaru ya sunkuce murhu yanufi BQ wajen Ammah.
"Da sallama yashiga Ammah da ke d'aki ta amsa masa muhammadu ne"?
"Eh"! Ni ne Ammah ya gida"?
Lafiya qalau muhammadu.
Ammah tafad'a had'e da hankad'e curtain{La6ule} tafito k'ara gaisawa suka yi Ammah ta kar6i murhun ta zuba masa garwashi, yayinda Ansar ya baza kunnen ko zai ji qira'a da ya ji ranar.
"Gashi Muhammadu Ammah ta katse masa tunani ya kar6i murhun a sanyaye har ya juya ya yi tak'o d'aya zuwa biyu sai ya ja ya tsaya, cike da jin kunya yajuyo yana kallon Ammah. Ya zame masa dole ya tambaye Ammah abunda yake azabtar da ruhinsa, ko zai same sauki ya kuma fita daga halin qila wa qala.
"Muryar nan tashi asanyaye yace Ammah Dan Allah aron Cassette d'inan na qira'a da naji kina sauraro ranar za ki bani. Qira'a ya yi min dad'i inason na nemo irinshi.
Chapter 7 · 0% Book details