← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 30

Sashe 4

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Cike da takaici Granny take kallonshi daga bisani ta girgiza kai tace ni a suwa da zan tsawata mata Ansaru"?
A matsayinki na wance ta ke da iko da ita saboda kina matsayin kaka a wurinta, kin ga kenan kinada matsayin da za ki tsawatar mata.
Huh,,,,,,,Ansaru kenan da ace na isa na fad'a aji da tuni ya yi tasiri akanta tadaina wannan shasshanci a wani gefen in ka yi la'akari ba laifinta bane, irin tarbiyyar da uwarta ta tabata kenan.
''shiyasa akoda yaushe nake la'anta baqin hali irin na saude.
"Ansar yasauke numfashi ya maida ganinshi wajen Zuhra wance ta ja ta yi tsaye tana musu kallon mai cike da wulaqancin, suna had'a Ido ta ja dogon tsaki tajuya a fusace.
ke! Zuhura zo nan,,,,,Ansar yataka mata birki cikin d'aga murya cak.....tai tsaye sai dai batada niyya dawowa ki zo nace zan yi magana da ke yasake bata umurni a harzuk'e tajuyo indan na dawo me zan maka"?
Kasanni sarai bana iya jure wulaqancin musanman na d'a namiji.
kisani muddin ki ka sake ki ka fita wallahi zan barki bari na har abada.
A tsorace Zuhra tasauke idanunta akan fuskarshi, numfashinta na kai komo jiki a sa6ule tadawo cikin parlourn tai tsaye tana kallon Ansar idanunta tap da hawaye sai mutsu-mutsu take da baki.

"Nemi waje ki zauna Ansar yafad'a fuskarshi a had'e zama ta yi hawaye da take k'ok'arin dannewa suka sulalu akan kunce ta.
''Granny ta dube ta ja tsaki batun yau ba Zuhra nake kuka da irin wannan watsatsiyar shiga da Ku ke yi gara ma Nazeeya da ke domin ita tana saka mayafi sa6anin ke da ki ke fita tsirara da sunan wayewa.
''Ansar ya kar6e zance ta hanyar cewa ina wayewa Granny ga talla tsiraici"?
Bani na fad'a ba Ansaru haka suke cewa a duk lokacin da na zaunar da su ina musu nasiha.
Wannan ba wayewa bane Zuhra asalima duk mai hankali da tunani Wanda yake da wadatace ilimin islama zai danganta hakan da Jahilci domin wayewa tana samo asaline da mutume da yake ka re hakokin Allah ta'allah. Kiji tsoron mahalincinki Zuhra ki dube kanki Sam ba ki yi kama da 'ya'ya musulme ba.
su Kansu Wanda Ku ke kwaiwayo da su ba bu indan addininsu ya yarje musu su yi watsaysiyar Shiga.
Gashin attachment ne akanki Najasa ne Zuhra kin dauka ki sakawa kanki shin a haka ki ke bautawa ubangijinki"?
kalli faratanki zaqo-zaqo kin fente su da jan farce ki dubi girman Allah Zuhra ba don ni ba ki canza wad'annan mummuna d'abi'u da ki ka kwaso domin rankatakaf zuri'ar Galadima babu mai wannan d'abi'a sai ke da Nazeeya.
"Zuhra takasa furta uffan sai sharar hawaye take yi zuciyarta na tuk'uk'i tun da take duniya ba'a ta6a ci mata fuska ba irin yau burin Granny yacika yau Ansar ya wulaqanta ta a gabanta.
Granny ta kya6e baki tace Kadàina wahalarda yawun bakinka Ansaru domin wad'annan maganganu naka suna shiga kunnenta ne kamar ana busa zare a kunnen bebe tun da tana sonka kacigaba da yi mata Nasiha watakila Allah yasa adace tagano talla tsiraici ba abu mai kyau bane babban takaicin na shi ma sa'eedu ya zama shanyaye mijin tace duk lokacin da na yi mishi korafi akan shigar da yaran nan ke yi sai dai yadinga kad'a kai kamar k'adangare yana kyaci kamar zai d'auki mataki, ba kuma abunda zai iya saboda anriga an gama da shi Granny tak'arasa magana tana huci.

''Shikenan Granny zan yi iya nawa k'ok'arin na lurar da ita yajuya wajen Zuhra da ke shasshekar kuka yace yi hak'uri Zuhra nah zo mu je compound mu yi sulhu kinsan na tsani kukanki.
"Kamar jira take ta tashi da sauri ya bi bayanta Granny ta bi shi da kallon tausayi, tasan lamarin so ne kawai ba wai don Ansar yadace da Zuhra ba domin ta ko ina halayyan su yasha banban da na juna.
''Nufin Zuhra tashige part d'insu da gudu Ansar ya cinmata yasha gabanta, yana kallonta k'asa-k'asa yanzu don mun gaya miki gaskiya Zuhra shine za ki fushi"?
Ashe gyara kayanka zai zama sauke mu raba"?
"Tad'ago cikin hawaye ranta na soya tafara magana ba zai zama ba Ya Ansar amma kasani ko za ka yi min fad'a ka jani privately ba wai a gaban Ganny ba domin da kunnenka ka ji yanda take aibanta mahaifiyata.
"Ae dole ta aibanta mahaifiyarki saboda ita ce baqar uwa asarar dangin a zuciyar Ansar yafad'i haka a baiyane kuma sai ya yi k'asa da murya I'm very sorry babynaa kema kinsan Granny ta tsufa komai yafito daga bakinta fad'a kawai ta ke yi bata masa birki.

''Inasonki Zuhura sosai shiyasa nake kishinki banaso abunda zai 6ata miki rai har ki zubur min da hawayenki
tun da kinaso saka iri-iri wad'annan kayan at last ki dinga daura after dress akai, domin nasan ko nace ki saka hijab ba sakawa za ki yi ba indan mu ka yi aure sai ki dinga yi min kwalliya.
Ni da kaina zan dinga siyo miki english wear's har sai kince sun ishe ki muradina yakasance wannan kyakyawar halitta ni kadai nake kallon abata ba da 'kartti wajen ba.
Yak'arasa magana yana murmushi
"Dariya Zuhra ta yi shikenan zan dinga sakawa ko don na farantawa zuciyar da nakeso.
"Kiran sallah magarib ya katse musu zance nasu Ansar ya dube ta cike da shau'kin so yace shiga gida ki yi sallah nima zan tafi masallacin maybe nadawo maybe kuma sai gobe.
"Bara na kawo maka buta ka yi alwala noo,,,,,,ki barshi kawai zan yi a wajen Abbah
Huh,,,,,,Ya Ansar nagano ka kadai kace za ka je shan green tea kai ko d'acinsa ba ka ji
"Dariya ya yi mai sautin gaske ki je Ammah ta koya miki yanda ake had'awa inan mu ka yi aure kidinga dafa min.
ita ma dariya ta yi sai kace ba ita bace yanzu nan tagama kuka har da su shassheka.
Ansar ya juya yanufi bakin gate, cikin d'aga murya tace "Honey please in kayi sallah kadawo Allah ban gaji da ganinka ba.
Batare da yajuya ba yace naji zan dawo amma fa sai nagama shan mutume nawa{green tea}
Yana zuwa gate yatararda Abbah yana alwala ya ja kujerar roba ya zauna Abbah ya gama alwala ya mik'a masa buta tare suka jera zuwa masallacin sai da akayi sallah isha sannan suka juyo gida.
''Still a bakin gate suka k'ara yada zango Abbah yashiga room d'inshi na maigadi yafito da tarkace kayan ataye ya ajiye su kusa da k'afafuwan Ansar d'an k'aramin murhu waya yadauka ya dube Ansar yace muhammadu bari na debo mana garwashi, nasan yanzu Ammah ta isa sauke tuwo da sauri Ansar ya tashi tsaye ya kar6i murhun yi zamanka Abbah kawo na kar6o mana yanufi BQ Wanda a yanzu yazama muhallin Abbah da iyalansa shi ya kwana a bakin gate a d'akin maigadi matarshi ta kwana a BQ 'yarshi kuma ta kwana part d'in Granny.
Yana k'arasawa ya iske Ammah tana kwashe tuwo ya yi sallama had'e da gaida ta Muhammadu Kaine atafe"?
"Eh! Ammah ya gida"?
Lafiya lau Muhammadu tak'arasa magana had'e da kar6a murhun ta zuba mishi garwashi kace ko yau ka zo shan mutume naka"?
"Eh Ammah ae ni yanzu na zama buzu saura kawai Ku koya min buzanci da yanda ake nad'a rawani Allah Ammah wannan rawanin yana burgeni yak'arasa magana yana dariya.
Ammah na tayashi kamar daga sama yafara jin zazzaqar murya mai matuk'ar dad'i tana rera karatun Qur'ani mai girma cikin suratul Al- araf tsit,,,,,,,ya yi kamar anyi ruwan sama andauke ya ba za fatun kunnayenshi biyu yana sauraron wannan muryar mai zak'i da gard'in gaske baisan lokacin da ya lumshe idanunshi ba.
''Lafiya Muhammadu ko kana buk'ata wani abu ne"? Muryar Ammah ce tadawo da shi natsuwarshi cikin jin kunya yashiga girgiza kai yajuya ya koma wajen Abbah.
"Har ya kamalla shan green tea zuciyarshi na azalzalarshi akan ya tambaye Abbah wacece yaji tana karatun Qur'ani iya saninshi daga Abbah sai Ammah yasani baisan suna da 'ya ba yana kuma gudun kada Abbah ya fassara shi bai-bai dole ya mik'e ya kira Zuhra a waya tafito sai around _10:00pm_ ya baro gidan har zuwa lokacin zazzaqa muryarta tana shawagi a dodon kunnenshi.......

Jeeddah Aliyu
*SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*5*

Ansar yana zuwa gida ya kwa6e kayan jikinshi yashiga bathroom ya yi wanka yafito sanye da bathrobe, tsaye ya yi gaban mirror yana tunani Jikinshi a mace ya dauki robar lotion ya shafe skin d'inshi.
Yasanya pajamas ya fashe jikinshi da turare mai sanyi k'amshin ya kwanta had'e da kashe light ya yi switch on d'in tv Kallo yake yi sai dai gaba d'aya hankalin nashi baya ga kallon ya yi nisa a tunanin 'yan mata 3 Zuhura, mai niqan, da Mai zazzaqar murya ya lumsashe idanu yana shafar sumar kanshi a hankali _me ke damuna miyasa nake tunanin wad'annan 'yan matan guda 2"?_
Mtcsww....,,,,ya ja tsaki har k'arfe _3:00_ na sulasuli dare ya yi Ansar na kwance sai faman juyi yake yi yakasa bacci ya tashi zaune ya lankwashe k'afafunshi a tsakiyar gado yadafe k'ok'on kanshi idanunshi sun kad'a sun yi jajir alamar rashin samun baccin.

''Ya sauka daga gado yashiga bathroom yadauro alwala yafito yashiga jera nafila, har akayi kiran asuba sannan ya dakata da nafilla da yake yi yanufi masallacin ana sallame sallah bai tsaya sauraron wa'azin da liman ya ke gabatarwa ba yadawo gida. Tsananin baccin da yake ji idanunshi har wani yaji-yaji suke mishi ya haye gado yak'ara gudun Ac bai jima da kwanciya ba baccin ya kwashe shi.

_Zuhra_
Chapter 4 · 0% Book details