← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 30

Sashe 30

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ajiyar zuciya tayi ta tsince kanta da zance zuci Abdallah da Ya Ansar akwai inda halayensu yazo d'aya ashe wata rana zan iya kamuwa da sonshi kamar yanda na kamu da son Ya Ansar...?

"Kidaina wahalarda kwakwalwarki da tunani ke da Abdallah ba Ku dace ba, ki yiwa kanki kiyamunlaili ki rabuda shi.

_Ba zan iya ba_
Tafad'a kaitsaye had'e da d'auke fuskarta tana kallon titi.

Shikenan ni zan sanarda shi domin ba zan zuba ido ina kallo ki cigaba da yaudarar d'an uwana domin nasan babu sonshi azuciyarki.
Cike da d'ibin mamaki tadawo da ganinta akan fuskarshi kai kuwa wagayamaka banasonshi..?
Cikin natsuwa yajuyo ya dubeta yasaki k'ayatatcen murmushi zuciyarki ce tafad'a min.

"Firfito da idanu tayi tana kallonshi cike da tsoro ya akayi yasan sirrin da ke zuciyarta Tun daga lokacin bakinta ya mutum mutus ga wani mutuwar jiki da ya lullu6e ta, yana isa school d'insu ya yi parking inda yasaba yi tabud'e k'ofa akasalance tafita.

Ya dakatarda ita ta hanyar furta sai nadawo d'aukar ki kuma ki tabbata kin jirani, kada barazanar Zuhura ta tsorata ki domin ayanzu bata cikin tsarina ina fatar kin fahimcin inda na dosa..?
''Bata tanka masa tajuya tashiga gate d'in makaranta.
Tana shigewa yaja mota yatafi, ana tashi yazo daukarta cikin yanayi na tsoro tashiga motar tashi tsoronta d'aya kada tsautsayi yagita Zuhura taganta ta tabbata kashinta yabushe.

_*Few Day's Later*_

Fuskar Ansar had'e kamar baita6a dariya ba Yashiga parlourn Daddy da ke farmhouse, ya yi tsaye turus yana k'arewa Abdallah kallo Mai cike da haushi Abdallah da ke waya da Anaal yad'ago ya kalleshi kauda fuska yacigaba da wayarsa mtcsww!..Ansar yaja tsaki yak'arasa shiga parlourn yanemi kujera da ke kallon Abdallah ya zauna, muryarshi adak'ile yafara magana ka katse wannan banzar waya marar amfani da ka ke yi mu yi magana ta fahimta.
Girgiza kai Abdallah ya yi had'e da furta Baby zan kira ki anjima domin naji inda maganarmu ta kwana kinji...?
Yayi shiru yana saurarenta yasaki murmushi _I love you_ bai jira jin ta bakinta ba ya kashe wayarshi domin yasan ba amsa mishi za ta yi ba.

''Wace irin maganar fahimta ce za mu yi...?
Ina fatar contract ka samu mana yak'arasa magana yana dariya.
Ansar ya yi ajiyar zuciya ya mik'e yadawo kan hannun kujerar da Abdallah yake kai d'an uwa bansan yanda za ka d'auki maganar tawa ba watakila kasaka fahimta aciki ko kuma sa6ani hakan.... Ya d'an nisa daga bisani yacigaba da cewa Abdallah so nake ka rabuda Anaal ka fita daga harkata ni kuma nai maka alqawali duk abinda ka keso, daga gareni zan maka.

Abdallah yasaki baki yana k'arewa masa kallo mai d'auke da mugun mamaki, yahadiye yawu ko zan iya sani dalilinka na bijiro min da wannan maganar mai Kama da dafin kunama...?
Za ka iya amma kafara amsa min firstly za ka iya rabuwa da ita ko kuwa..?
Zan iya in har ka zo min dalilinka mai k'arfi.
Ba dole bane sai kaji dalilina ba
Uhm"! Tun da bara ka iya fad'ar dalilinka ba nima ba zan iya rabuwa da ita ba sonta yanzu nafara.

Murmushi takaicin Ansar ya yi yad'age gira sama yana ma Abdallah kallon wulaqancin, anyway zan biyanka ladan rabuwa da ita da za ka yi daga Naira million 1 har zuwa million 10 zan iya mallaka maka na kuma sanka farin sani akan k'udi za ka iya yin komai domin, son da ka ke mata bai taka kara ya karya ba.
"Zancenka gaskiya ne zan iya komai akan k'udi amma ba zan iya siyarda soyayyar Anaal ba alfarma d'aya zan iya yi maka amatsayinka na d'an uwana shin miye dalilinka nayin hakan...?
Anaal tayi maka wani laifi ne ko kuma iyayyenta...?

"Ba ko d'aya kawai inason ka nisanta kanka daga gareta.
''Ba zan iya ba Ansar muddin ba ka fad'amin dalilinka ba.
Shiru yabiyo baya kowane su yana fama da d'acin zuciya.

"Shikenan Abdallah komai yabiyo baya kada ka zargeni ka zargin kanka domin taurin kanka da son jin abinda bai shafaka ba yajanyo maka. Yana k'arasa magana yai tafiyarsa yabar Abdallah cikin zullumi da mamakin me yake nufi da wannan Sabon fi'ili da yazo da masa da shi...?

Kasa hak'uri yayi har saida yalala6o Anaal a waya tambaya duniya nan yai mata tafad'a masa menene tsakaninta da Ansar ta tsaya kai da fata ita ba komai atsakaninsu sai mutuncin daga karshe sai cewa tayi wani abu yafaru ne da zai mata wannan tambayar, yace ba komai ya kashe waya ya zunduma kogin tunani

_1 week later_

Ansar na zaune a office d'inshi dafe da kai shi fa yanzu dabara tafara k'are masa, da farko dai yana jin kunya yafito fili yacewa Abdallah shi yakeson Anaal shiyasa ya umurce shi yarabuda ita.
A6angaren d'ayan zuciyarshi yace da shi idan baka fad'a masa ba ta ya zai barta kana kallon yanda yake k'ara cusa kansa gareta ba ka tsoron tafara sonshi jikinsa yadauki rawa ga sanyi Ac amma zufa yakeyi.

Ya yi cilli da Biro da ke hannunshi ya mik'e zubur yanufi k'ofar fita saura kiris suci karo shi da Ishaq da sauri Ishaq yaja baya maigida ba dai fita za ka yi ba...?
A maimakon yabawa Ishaq Amsa sai cewa yayi
Abdallah yana office d'inshi...?
_Eh yananan maigida yanzu ma daga office d'inshi nake yace na kawo maka wad'annan documents kayi sign_
Ansar yaja tsaki mtcsww had'e da furta banida lokacin yature Ishaq yawuce cikin zafi nama yashiga elevator da zai sada shi da office d'in Abdallah da gudu Ishaq yafad'a elevator d'in yana mai cigaba da tambayar Ansar lafiya maigida naganka a hargitse kamar akwai d'ibin damuwa atare da kai..?
Saida ya yamotsa sumar kanshi sannan yace bari kawai Ishaq wannan d'an iskan yanason ya tarwatsa min rayuwa inason Anaal fiye da son yake mata akan wane zai nace mata bayan yasan shi da ita Sam basu dace ba.

Ishaq yasauke ajiyar zuciya domin shi tuni yagano take-taken maigidan nashi son Anaal yakeyi, maigida ban fahimcin wa ka ke nufi ba..?
Wa nake nufi bayan wannan tsohon d'an iska Abdallah ni nasan ba son tsakani da Allah yake mata ba, akwai wata mummuna manufa a k'asan zuciyarsa.
Kafin Ishaq ya yi magana elevator ya tsaya suka fito Ansar yana gaba cikin tafiyar masu k'arfi Ishaq yana biye da shi da d'an gudunsa.

"Da k'arfi yabanki k'ofar office d'in Abdallah yashiga Abdallah da ke zaune yana waya da girlfriend d'inshi zeely yad'ago atsorace yana kallon Ansar ba shiri yakatse wayar.

Lafiya Ansar za ka banko min k'ofa...?
Wallahi ni har ka tsorata ni.

Abdallah zuwa nayi na rok'e ka abinda banta6a yi ba arayuwata domin ni mai sa'a ne duk abinda nakeso sai na mallakesa ko ta halin yaya amma wani abin mamaki awannan karon wanki hula yakaini dare.

Abdallah nasan son da ka keyiwa Anaal bai taka kara karya ba na rok'eka Kadàina 6atawa kanka lokacin kafita harkata

Kadàina bani umurni kaitsaye kamar wani d'anka mace allura ce cikin ruwa me rabo kan dauka, domin tuni na fahimcin sonta ka ke yi tsabar girman kanka da miskilancin tsiya yahanaka fad'amin amma kasani *Kayiwa kanka*

Jeeddah AliyuCopied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
Chapter 30 · 0% Book details