← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 30

Sashe 25

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ansar yadanno hancin motarshi afarfajiyar gidansu zuhra ba don ranshi naso ba ya zo gidan sai don matsanta mishi da Hajja fatee tayi.
Yayi parking yanufi wajen Abbah, bayan sun gaisa Abbah ya tambaye shi ba'asin abinda yahad'ashi da zuhra Ansar bai 6oye mishi komai ba tirya-tirya yabashi labari.
Nasiha sosai Abbah ya yi mishi akan yak'ara hak'uri dama aurin gida ya gadi haka.
Ansar ya bishi da toh ba wai don ya aminta da kalmar hak'urinan da Abbah yace ya yi ba saida yasha ataye{green tea} sannan yanufi cikin gida kaitsaye part d'in Hajiya saudat yanufa, da sallama yashiga parlourn gidan mutane gidan suna zaune tsabar wulaqancin ba Wanda ya amsa mishi ya durk'usa ya gaida Hajiya saudat adak'ile ta amsa duk da wannan tsohon wulaqancin da akayi mishi bai sa ya yi k'asa da guiwa ba.
"Yanemi kujerar da ke facing zuhra ya zauna cikin tattutasan lafazi yafara magana Hajiya dama zuwa nayi na ba Ku hak'uri akan abinda yafaru jiya sharrin shed'an ne da kuma laifin zuhra da tarufe ido tak'are min zag.....kai mallam dakata! Hajiya saudat ta daka masa tsawa cikin hargowa ta taso kamar za ta dake shi, idanunta suka k'ank'ance tsabar masifa da bala'i ta d'age lebb'e sama tafara zazzaga masa rashin mutuncin ba shakka Ansar ka cika cikakke maras kunya ka dake 'yar tawa don tsabar iskancin da kazar uba ka debo k'afafunka ka zo gidanan bakinka d'auke da Kalmar ban hak'uri.
"Toh da hak'uri ta mutu sadaka nawa tabaka?
Kai! Bari ka ji tanuna shi da yatsa ka gaugauta bud'e fatun kunnuwa ka guda 2 da Allah{s, w, t} ya albarkace da su ka saurarani da kyau domin gargad'in na farko na kuma k'arshe zan kashe maka.
"Zuhra ba baiwar ubanka bace da za ka ware kwanji ka daketa
Ansar ya zaro ido cike da firgicin yana kallon Hajiya saudat.
Zuhura ta kad'a kai tana yatsinar fuska tace fad'a mishi dai Hajiya shi ana shi rashin basira yadauka ni baiwar gidansu ce.

"Idan ma yadauka yasauke domin ba ki gadi bauta ba Hajiya saudat ta kar6e zance wannan ya zama maka auta ya zama maka d'an fari duk ranarda shed'ancinka ya tashi kasake dukan zuhra wallahi, ta'allahi! Sai na kafa tarihi akanka nan da ka ke ganina ba k'aramar 'yar tasha bace.
''Ansar ya ta6e baki yace ae naga alama.
Ba ka ma ga alama ba sai tsautsayi yasake d'ebarka ka dake zuhra alokacin za ka zahiri, kai! bari nayi maka ta mahaukata ko aureta ka keyi ka daketa sai nai maka wanka tsalki, ballantana ba uban da ya zarga mata igiyoyin aurenka, ina fatan ka fahimcin karatun nawa?
"Gyara zama Ansar ya yi yana kallon Hajiya saudat anatse na fahimta Hajiya kiyi min gargad'in mai cike da kaukausar murya, watakila ke daga bakinki kadai yafito ni kuma zan fad'a miki abinda yake k'asan zuciyata ya d'an numfasa.
"Hajiya zan iya shanye komai amma ba zan lamunce ana cin zarafin iyayyena ba ta hanyar zunduma musu zagi, ni dai naga zuhra nace inaso ba Wanda yahad'ani da ita tun kafin rayuka su b'aci kafin ta kai har kiyi min wankan tsalki ni zan yi wa kaina domin na sauk'ak'a miki debo ruwa, Hajiya na hak'ura da zuhra Allah ya had'a kowa da rabonsa na alkhairi.

"Jikin zuhra yadauki rawa idanunta suka fito turu-turu numfashinta yafara kai kawo, murya na rawa tace haba! Ya Ansar yanzu adalilin wannan d'an k'ank'anin abu za ka barni?
"Kallo mai cike da k'ask'ancin yake mata ke a wurinki yake D'an k'ank'ani amma ni awurina yazarce duk yanda ki ke zato, wallahi a yadda nakeji zuciyata tana k'una da tafarfasa ko aurenki nakeyi zan iya dank'ara miki saki d'add'aya har saki 3 sai gashi kin taki sa'a mahaifiyarki da bakinta tace ba uban da ya zarga miki igiyoyin aurena da yau kinga tsiya ta zahiri.

Jeeddah Aliyu[6/28, 8:49 PM] YAYA HAYAT: *SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

_wannan shafin naki ne qanwata ta kaina Khadijat Abdullahi shehu{Hajja ce} na gode da irin k'aunar da ki ke nuna min_

*22*

Hajiya saudat tasaki baki galala tana kallon Ansar bata ta6a tsanmani wannan kalma za ta iya fitowa daga bakinshi ba, sakamakon yanda tasan yana matuk'ar son Zuhura.
Kukan Zuhura ne ya katse mata zance zuci, ta dubeta ta daka mata tsawa ke! Daiña rok'onshi ko giyar wake yashi bai isa yace yafasa aurenki ba. Bayan yasan kin share tsawon lokacin kina zaman jiranshi.
"Zuhura ta dube Hajiya tana kuka haik'an Hajiya kinji abunda yafad'a wallahi da gaske yakeyi, na shiga 3 na lalace Hajiya ba zan iya rayuwa ba Ya Ansar Dan Allah ki bashi hak'uri tak'arasa magana had'e da rik'o hannun Hajiya saudat.
"Buge mata hannu Hajiya tayi wai ke wace irin banza yarinya ce? Namiji ki ke wa kuka ashe duk iskancin da yake miki ke ki ka siya da k'udinki, don yafasa aurenki sai me? Shine autan maza da za ki zubarda hawayenki a wofi?

Mtcsww! Ansar ya ja tsaki ya mik'e da gudu Zuhura tanufi wajenshi ta zube gabanshi tana kuka kamar ranta zai fita, ta cukume k'afarsa ka dubi girman Allah Ya Ansar ka yi hak'uri kayafemin in kafasa aurena zan iya haukacewa kai kadai zuciyata takeso sharrin shed'an ne na gane kuskurena ba zan k'ara sa6awa umurninka ba.
Kallon sama da k'asa ya yi mata yafincike k'afarshi da k'arfi, ba hauka ba idan kin iya ki had'e zuciya ki mutu ba abinda yashafe ni. Yajuya cikin zafin nama yanufi k'ofar fita Zuhura ta zabura da gudu ta bi bayanshi tana kwalla masa kira.

Nazeeya ta dube Hajiya wance tun zamanta parlourn sai yanzu ta tofa albarkacin bakinta anya Hajiya Ya Ansar banza yabar yaya Zuhura kuwa? kalli yanda ta daka da gudu ta bishi, sai kace zararriya.
Takaicin yak'ara turnuk'e Hajiya tace ba abinda ya yi mata tsabar dakarci da komawa baya ne yake dawainiyya da ita.
Ta6e baki Nazeeya tayi idan kuwa haka ne yaya Zuhura na cikin wahala ni yaushe zan d'auki soyayar k'ato nasa araina har yasame damar wulaqantani haka.

Yana isa parking lot Zuhura na karasawa ta ware hannayenta ta tare masa k'ofar mota, ka ji tausayina Ya Ansar karka juya baya wallahi inasonka fiye da tunaninka.
Tsanarta ce tak'ara baibaye shi na tsaneki Zuhura tsana mai tsananin gaske na gwanmace na mutu da na aure jahila, dak'ik'iya irinki yatureta yashiga mota ya ja ta da k'arfi dai-dai Anaal tafito daga BQ wurin Ammah, Zuhura ta bi motar da gudu tana kuka had'e da kururuwa afirgice Anaal ta watsarda kayan da ke hannunta ta daka tsalla ta koma gefe atunaninta Ansar zai bankad'e ne sakamako yadda ya ja mota yanufo ta gadan-gadan, tun kafin yak'arasa Abbah ya bud'e masa gate.

Zuhura tana gani yafice tak'ara fasa ihu mai k'aran gaske, tafad'i k'asa cikin kid'ima Anaal tanufi wajenta tad'ago ta lafiya yaya Zuhura mekike yiwa kuka?
Kuka yaci k'arfinta ta dank'e hannun Anaal saboda tsabar kuka muryarta bata fita sosai _Anaal Ya Ansar yace yafasa aurena, ni kuma ba zan iya rayuwa ba shi_
"Ajiyar zuciya Anaal tayi cikin laushin murya tafara magana fad'a kawai yakeyi don yad'aga miki hankali shima ba zai iya rayuwa ba ke. Kiyi hak'uri kitashi mu Shiga gida yadda yatafi haka zai dawo da kanshi.
Da kyar Anaal ta ciyo kanta tashiga gida.

_BAYAN KWANA UKU{3 DAY'S LATER_

A parlourn Granny bakajin komai sai sautin kukan Zuhura hawaye sha6e-sha6e majina na fita daga k'ofofin hancinta cikin kwanaki 3 tafita hayyacinta walwala da farin ciki sun k'aura gareta saboda ta tabbata za'a sha artabo kafin Ansar ya amince da zance aurensu.
Ansar yashigo bakinshi d'auke da sallama daga Hajja fatee sai Granny ne suka amsa masa, tun kafin ya zauna Daddy yafara 6al6ale shi da masifa wannan wane irin shashshacin ne za ka barmu zaune muna jiranka sai kace wasu sa'annika?
Kayi hak'uri Dad koda ka kirani ina bacci sai da nayi wanka da sallah sannan na fito.
Mtcsww! Daddy ya ja guntun tsaki ya dube Ansar da masifafin idanunshi Wanda su kadai sun isa su murd'a antar cikin k'aramin jarumi sa6ani Ansar da ko darr! Bai ji ba saboda shi ma irin idanun yake d'auke da su.
Kai! D'ago ka kalleni da kyau Daddy yafad'a cikin kaukausar murya mai cike da b'acin rai, Ansar yad'ago yana kallon Daddy ido cikin ido ba ko tsoro balle fad'uwar gaba atare da shi.
"Yayin da Daddy sake dank'e fuska Boy wace maganar banza ce ka zo da ita agidanan?
Sadda kai k'asa Ansar ya yi cikin tausasa halshe yace Allah ya huci zuciyar Daddyna ba maganar banza bace. Magana ce mai Mae ma'ana nazo da ita ataimaka a dubi uzirina da idon basira.

Daddy ya kad'a kai ya yi k'yaci ya kafe Ansar da idanu kenan duk abinda aka zaiyana min akanka gaskiya ne?
Eh! Toh ba zan iya cewa eh ko a'a ba domin bansan me akace da kai ba iya abu d'aya nasan yakeda mahimmancin ko iyayyemu kusani ba wai cin fuska ko tozarci ba a'a sai don gudun lalacewar zumuncinmu. Dad, Alhaji yakira sunayensu ku gafarce ni adalilin wannan maganar da zan fad'a tun farko ni nace inason Zuhura ayanzu kuma ba zan iya aurenta ba koda daga ni sai ita mukayi saura aduniya.
"Yana dasa aya zuhra tasake barkewa da kuka, Alhaji yadaka mata tsawa ke! Dallah ki yiwa mutane shiru, shi yake iko da kanshi ne da zai yanke irin wannan d'anye hukuncin?
Daddy yad'agawa Alhaji hannu ya isa sa'eed ba don Alhaji yaso ba yahadiye sauran kalamanshi.
Zuciyar Daddy na tafarfasa yafara magana Boy idan har ni ne na haife ka nakeda cikakke iko akanka daga yau sai yau karna k'ara jin magana kwatankwacin wannan tafito daga bakinka, aure kuma da kai da Zuhura ba bashi muddin ka ga ba ka aureta ba bana numfashi kaje kafara shirye-shiryenka nan da sati 3 za'a d'aura aurenku Zuhura tayi azumi ad'akinta.
Chapter 25 · 0% Book details