Sashe 19
Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A lokacin yadawo daga masjid kenan yana cire jallabiya yaji ringing wayarshi, share kiran ya yi saida yagama cire Jallabiya sannan yanufi bed ya kwanta yana d'aukar wayan kiran na tsinkewa.
Har ya yi niyyar ya ajiyen wayan sai kuma wani tunani yafado masa ya duba miss call d'in sam bai yi tsanmani Anaal ce takira shi ba.
Da sauri ya yi calling nata back.
Anaal najin wayarta tad'auki vibrate dama tasaka wayan a meeting ne jikinta har rawa yakeyi tayi received.
_Hello''! Ya Ansar_
Hi Lucky ya akayi ne?
Dariya tasa yau kuma nice Lucky?
Kwarai kuwa domin ke Mae Sa'a ce ko kinsan cewa ke ce mace ta farko da na ta6a raba dare ina waya da ita, dawowa na daga masallacin kenan gashi kuma ina waya da ke.
Anaal ta kad'a kai kuma ni ce Mace ta farko da kafara hanawa bacci ba.
Gaba d'aya suka sa dariya.
Ae dole kayi dariya Ya Ansar kayi bacci abinka kabarni da sauraron minsharinka yanzu haka da headache na tashi tak'arasa magana cikin shagwa6a.
Wani irin nishad'i ya kai masa ziyarar bazata ya lumshe idanu oh! Sorry my Lucky zan zo miki da extra ki d'an kora kinji?
''O'o ni banason magani.
Shikenan sai nazo zan nemo abinda zai warkarda ciwon kan. Yanzu ki je shirya kada kiyi latti kice ni ne sanadi.
Tana dariya ta katse kiran wani irin dad'i takeji yana ziyarta ta.
Cike da nishad'i tashiga bathroom tayi wanka tana fitowa, ta goge jikinta tashafa lotion iya powder ta goga tasaka uniform, ta d'auki schoolbag d'inta tanufi parlour ta iske Granny tana sauraron Labarun BBC a 'yar k'aramar radio ta cikin girmamawa ta gaidata, Granny ta amsa had'e da cewa har kinfito?
''Eh Granny
Toh Allah yabada Sa'a ki je cikin drawer purse d'ina na nan ciki kidauki N200.
Na gode Granny akwai raguwar canji jiya ya isheni nayi k'udin adaidata har nayi breakfast.
Shikenan adawo lafiya saboda ke ba Karin kumallo ki ke yi ba ballantana nace kisha koda 'yan ruwa shayi ne.
Dariya Anaal tayi karki damu Granny nariga na saba in ba 10:00am tayi ba bana iya cin komai.
Ke ki kasani da tsirfarki ta tsiya, sai kitafi kada kiyi latti a narke a banza ke ba wani abincin kirki ki ka cin ba.
Tafice tana dariyar Granny kaitsaye BQ tanufa ta wajen Ammi ta jima wajen Ammi kafin tayi sallama da ita tanufi bakin gate wajen zaman Abbah bayan ta gaidashi yabata k'udin breakfast da na adaidata shi kan batace bazata kar6a ba domin tasan sai ya tuhumeta ina tasami k'udi shiyasa tarufawa kanta asiri ta kar6i k'udin.
7:06pm tafito daga gida tun daga nesa ta hango motar Ansar inda suka saba had'uwa, tun kafin tak'arasa tafara murmushi.
Jeeddah Aliyu*SONKI NE SANADI*
_A Romantic love story 2017_
Na Hauwa shehu Aliyu
*®NWA*
www.jeeddahaleeyu.blogspot.com
*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*
15
Da yake gilasai motar tinted ne ita bata ganinshi amma shi yana ganinta. Kamar yanda take murmushi shima murmushi yake har yafi nata, tana Isa ta bud'e k'ofa tashiga had'e da sallama sautin wakar Indian ne ya amsa mata ta kai duba wajen Ansar sai faman kad'a kai yake yana bin wakar sai kace tare da shi akayi ta.
Tayi dariya o'o su Indian boy ko sallama Ba'a amsawa?
Yayi dariya yarage volume ya dube ta yi hak'uri my Lucky duk lokacin da nake sauraron wak'ar nan ni kadai nasan halin da nake shiga.
Hmm,,,ta tabe baki kana jin abinda suke fad'a ne?
Bai bata amsa ba sai kawai ya ja mota.
Cike da nishad'i ya dube ta yace
_inasonki tamkar bugun numfashina a duk lokacin da na rufe idanuna kyakyawar fuskarki nake gani. Banida buri da yawuce naji ki kwance akan k'irjina, nafara sonki tun daga ranar da idanuna suka fara tozali da ke ina sonki sosai fiye da son nake yi wa kaina_
Tun lokacin yafara magana har ya yadasa aya jikin Anaal rawa yake kamar mazari tsoro da rud'ani suka lullu6e ta.
Ansar yacigaba da cewa _juyo ki dube ni ki yi min murmushi nan naki mai sanyaya zuciya, ba....._ ya Ansarrr da k'arfi cikin kururuwa Anaal ta kira sunanshi a tsorace ya hadiye sauran kalamansa yana mata kallon tsoro.
A zafafe tafara magana kanka d'aya kuwa? Ka kuwa San abunda bakinka yake furtawa? toh wallahi indan ma mafalki ka ke yi ka falka wannan hauka da shirme har ina? Au dama shine dalilin da yasa kace mu zama friends ashe akwai wata, mummuna manufa a k'asan zuciyarka?
Toh ni wannan cin amana ba da ni ba wannan ae abin kunya ne.
Ansar ya dube Anaal baki bud'e daga bisani ya kece da mahaukaciyar dariya har yana had'awa da dukan steering, da kyar yai controlling dariyan cikin pity face yace nifa ina fassara miki abinda wak'ar take nufi ne Allah sarki poor girl ke kin dauka da ke nake?
Ae ko giyar wake nasha Anaal babu kalma son a tsakaninmu. Ni fa banta6a yi miki wani kallo fa ce na k'anwata ta jini Anaal ina ba ki kulawa ne a matsayinki na wance batada 'yan uwa domin ba lallai bane wasu matsalolinki ki iya tunk'arar iyayyenki da su ba, shiyasa nake tunani ni ne zan maye miki gur6in yaya Auwal na rok'eki kada ki sake wannan mummuna tunani a tsakaninmu.
''Tsananin kunya ya lullu6eta, takasa koda motsa d'an yatsa gaba d'aya ta susuce gani haka yasa Ansar ya kira sunanta cikin laushin murya _Anaal_
Kasa amsawa tayi sai ma rufe fuskarta da hijabi da tayi abin ya bashi dariya sai kawai yadinga kwasan dariya shi kadai har ya iso gate d'in makarantarsu batasaniba saboda fuskarta na rufe.
_Anaal mun iso ko yau ba za ki je school d'in bane mu koma gida?_
Da sauri ta bud'e fuska amma bata bari suka had'a ido ba ta bud'e k'ofa tafita yadinga kwalla mata kira tayi biris da shi sai da yaga shigarta cikin school sannan yaja mota yatafi yana dariyar shirmenta.
"Direct Anaal tawuce class ta ajiye schoolbag d'inta tana fitowa taci karo da zeenat, 'yar buzuwa ashe kin shigo?
Mtcsww''! Anaal ta ja tsaki rai 6ace tace banaso iskancin zeenat sau nawa ina kashe miki gargad'i kidaina kirana 'yar buzuwa?
Oho"! Nasani miki da alama yau akwai wanda yata6a ki bara na ajiye schoolbag d'ina nadawo tashige class tabar Anaal tsaye.
Har zeenat tadawo Anaal batasaniba tayi zurfi a tunanin, shirme da ta tafka.
Dafa kafad'arta zeenat tayi meke damunki ne Anaal?
Tayi ajiyar zuciya had'e da kallon zeenat mekika gani ne?
Damuwa, damuwa nagani fal akan fuskarki.
Hmm! Haka dai ki ka fad'a amma ni ba abunda ke damuna.
Wai Anaal yaushe za ki rage zurfin ciki? Ni fa k'awarki ce, ki tuna daga ni har Ramlat ba ma 6oye miki duk wani abu da yashafe mu saboda mun yarda da ke sa6anin ke da har yanzu ba ki aminta da mu ba, gaskiya k'awance da ke Anaal akwai wahala ina amfani irin wannan zama ki sauya halinki ace ko abu zai kashe ki ba za ki iya bud'e baki ki fad'awa wani ba.
Kisani Anaal barin kashi ciki baya maganin yunwa ki ta boye sirrinki mu kuma zamu cin gaba da gayamiki na mu domin mu yarda da ke d'ari bisa d'ari ke da ba ki yarda da mu ba chan ta matse miki.
Tana k'arasa magana tajuya tanufi hanyar assembly tabar Anaal tsaye sororo taja jiki asanyaye ta bi bayanta.
A wajen suka iske Ramlat domin yau tazo a makare
Ana gama assembly Zeenat taja hannun Ramlat suka nufi class batare da sun kulata ba wannan ya tabbatarwa da Anaal zeenat ta warwarewa Ramlat zare da abawa.
Tana shiga class tanufi seat d'insu cikin sanyinta tafara magana haba! K'awaye na bai kamata ku yi saurin d'aukar zafi akaina ba dama ba wani abu bane yau na tafka shirme da abin kunya shine ku ganni a haka, wallahi har yanzu kunya nakeji tamkar ina gabansa har inaji da wane ido zan sake tozali da shi tak'arasa magana tana yarfe hannaye.
Zeenat da Ramlat suka kalli juna Ramlat ta mik'e ta zauna akan desk ta dafa Anaal wanene shi wane irin abin kunya ki ka tafka har da zai dame ki haka?
Har ta bud'e baki za ta bata amsa uncle d'insu mai d'aukarsu darasin mathematics Yashigo dole Anaal ta hadiye sauran kalamanta.
Uncle d'in yana cinye period d'inshi mai darasin physics yana jiranshi a bakin k'ofa yafita shi, kuma Yashigo a takaice Anaal batasami damar sanarda su damuwarta ba sai during breakfast.
Direct shop d'in siyarda snacks da soft drink suka nufa.
Ramlat da zeenat Suka nemi dogon bench suka zauna yayinda Anaal tashiga shop taciro 1k tasiyo recharge card na N200 tadawo ta zauna taciro 'yar Nokia ta daga pocket tasaka recharge card d'in Zeenat tace Anaal ki k'arasa mana labarin da ki ka fara ba mu nakagara naji waye wannan mutume da ki ke magana akanshi.
Ajiyar zuciya Anaal tayi tashiga kwararo musu abinda yawakana da sanyin safiya tsakaninta da Ansar tana dasa aya suka sa mata dariya kamar zautacin.
Anaal batasan lokacin da tashiga tayasu dariya ita kanta sai yanzu shirme nata yabata dariya sai da sukaci dariya iya son ransu sannan, Anaal ta lallube wayarta tashiga rubutawa Ansar text massage.
_Sallam da fatar ka isa gida lafiya? Dan Allah Ya Ansar kayi hak'uri da abinda yafaru d'azu sharrin zuciya ne, domin ko makaho yashafa ka yashafa ni yasan kafi k'arfina me za kayi da 'yar masu gadi irina? A halin yanzu tunani nake tayaya zan had'a ido da kai, wallahi kunyarka nakeji fiye da tunaninka kahuta lafiya_