← Book details Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 30

Sashe 24

Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bari na tambaye ki idan magge za ta kama bera ya takeyi?
''Shiru tayi tana tunanin daga bisani tace kwantarda kai takeyi ta dinga sand'a tayi wuf! Ta cafke wuyanshi.
K'ara kyalkyalewa da dariya Ansar ya yi yasakin hannun Basmah guda yadungure mata kai yanda ki ka ga magge tayiwa bera haka zan yiwa Anaal, na cafke zuciyarta na dasa mata zazzafar soyayyata ta yanda duk lokacin da na furta inasonta jikinta na mazari za ta amince da ni.
Hum....you're very smart Ya Ansar.
''Yes! I'm yafada cikin jin dad'in yabon nashi da Basmah tayi
Lallai ba ko kwankwato Anaal za ta fad'a tarkonka baiwar Allah har nafara tausaya mata, saboda ba za ta iya fito-na-fito da zuhra ba.
Mtcsww! Ya ja tsaki in ana maganar sarauniyya mata kidaina sak'o zancen zuhra domin tenure ta yak'ara.

Dariya Basmah taci kamar cikinta zai fashe Allah sarki duniya ashe akwai ranarda za ta zo da za Kadàina son zuhra?
Gashi ta zo kuma kingani da idonki ke ni fa sai daga baya nagano son Anaal ne sanadi dusashe soyayyar zuhra a zuciyata.
Basmah ta mik'e tsaye had'e da cewa sai da safe saboda na fahimce in ana firar Anaal Sam baka gane dare ya yi, Ansar ya mik'e yana dariya mu je na rakaki suka jera had'e da ficewa daga parlourn suna tafiya Ansar yana cigaba da bata labarin Anaal, saida yakaita har main parlourn sannan yadawo part d'inshi sai ke ji kamar Anaal d'in ce yagayawa yana sonta, ashe gaskiyar bahaushe da yake cewa barin kashi ciki baya maganin yunwa gashi dae ba Anaal ya fad'awa ba amma yaji sauki a zuciyarsa.

_Washe Gari_
_7:15am_
Kamar yadda yazamewa Ansar jiki kai Anaal school ko yau hakan ce tafaru, bayan yakaita yadawo yak'ara kwanciya sai misalin k'arfe _10:30am_ yafito cikin shirin tafiya office yana sanye da material Mae taushin gaske transparent brown in colour k'afarshi sanye da brown sandal yana, rataye da briefcase fuskarshi lullu6e da fara'a yashiga parlourn Hajja fatee yana shiga mum na fitowa daga bedroom d'inta ya gaidata cikin girmamawa ya ajiye briefcase d'inshi bisa kujera yanufi dining area, Hajja fatee da kanta tayi mishi saving tana Mae k'ara jaddada masa yaje gidansu zuhra yabata hak'uri sai binta da toh ya yi, yana gama breakfast yadauki briefcase d'inshi dai-dai lokacin Basmah tafito _Good morning bros_
_morning my 'yar lukuta yau bakida lectures ne?_
Ina da amma sai 2:00pm
Okay ya yi kyau in kindawo da wuri ki had'a min fruit salad.
Toh tafad'a had'e da bin bayanshi har parking lot tarakashi cikin sigar tsokana tace ka gaida Lucky.
Saida ya murmushi sannan yace za taji yaja mota yanufi gate maigadi ya bud'e masa yafita.

_2:30pm_

Ansar yafito daga office yana tare da Abdallah wai kai ina za ka je ka ke wannan saurin? Abdallah ya watsawa Ansar tambaya.
Bayan na gayamaka akwai magana Mae matuk'ar mahimmancin da nakeso nayi da kai.
Ina ruwanka da inda zan je kai da ka ke fita gantalinka na ta6a tambayarka?
Huh...Abdallah yata6e baki abin naka ne da matuk'ar daure kai, kullum a irin wannan lokacin ka ke fita ae dole na tuhumeka.
Bakada ikon tambayana domin ba zamanka nakeyi ba
Shikenan Allah ya kiyaye hanya in kadawo kanemi domin maganar ta k'aruwa ce.
Ameen sai kajira in nadawo kayi maganar taka yak'arasa magana had'e da shiga mota kaitsaye makarantar su Anaal yanufa bai wuce _5 minutes_ da tsayuwa ba tafito tare da su zeenat tayi sallama da su tanufo motarshi ta bud'e k'ofa tashiga fuskarta d'auke da murmushi ta gaidata shi.
Ya amsa yana kallonta Lucky ya karatu?
Alhamdulillah!
Ya ja mota suka d'auki hanya ya dubeta cikin kulawa yace jiya fa nasami matsala da mutuniyarki da alama k'arshen rabuwarmu ne yazo.
Cikin kid'ima da firgicin ta zaro ido kana nufi yaya Zuhura?
''Kwarai kuwa ita nake nufi.
_innalillahi wa'inna illaihim raji'um_ kai kuwa Ya Ansar me ya yi zafi haka wane laifi ta aikata maka da ka za6i kabarta adai-dai lokacin da Ku ke yunk'uri zama inuwa d'aya?
Ya yi ajiyar zuciya yashiga bata labarin abinda yafaru bai 6oye mata komai ba.

Mamaki ne ya baibayeta daga bisani ta dubeshi cikin natsuwa da kwantarda murya, tabbas yaya Zuhura ta tafka babban kuskure duk da haka bai kamata kace kafasa aurenta ba ko don albarkacin tsawon lokacin da ta share, tana jiranka ga kuma dangantaka ta jini da ke tsakaninku.
Ka dai k'ara hak'uri kacigaba da lurarda ita har Allah yasa tagane.
K'atuwar harara ya wulga mata cikin b'acin rai yafara magana banta6a tsanmani Lucky bakya k'aunata ba sai yau yarinyar da tak'are min zagi uwa da uba ita ce za ki ce na cigaba da zama da ita, wallahi ko ita ce autar mata na barta.
"Na shiga uku Ya Ansar me kawo maganar rashin k'auna anan?
Daga kai har yaya Zuhura kuna masifar son junanku a tunanina bai kamata abu d'an k'ank'ani ya zama silar rabuwarku.

Mtcsww..ya ja guntun tsaki kurciya ke damunki Lucky ke k'aramar yarinya ce, banda shirmen kurciya irin naki ta ya za ki danganta zagi a matsayin d'an k'ank'anin abu?
Ya Ansar kenan ni a ganina in har son da ka ke yi wa yaya zuhra na gaskiya ne za ka iya shanye duk wani cin zarafi da takeyi maka domin tun asali kasan halinta kasan wacece ita duk da haka ka za6e ta, sai yanzu da tafiya tayi nisa za ka bijiro da irin wannan babbar magana.
Kinga Lucky in har ba za ki iya gayamin maganganu masu dad'i da sanyaya zuciya kibarni naji da b'ac[truncated by WhatsApp]*SONKI NE SANADI*

_A Romantic love story 2017_

Na Hauwa shehu Aliyu

*®NWA*

www.jeeddahaleeyu.blogspot.com

*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*

*21*

_ina alfahari da ke Ummi A'isha Allah yabarmu tare tawan_

Note:- _masu yi min magana a pc na turo musu SONKI NE SANADI daga farko Dan Allah kuyi min uziri ba zan iya ba ku nema a blog d'ina da fatan za Ku kar6i uziri na karku danganta hakan da wulaqancin_

Ikon Allah Anaal tafad'a baki bud'e ka ga bawan Allah ni fa banina kai zomo kasuwa ba rataya akabani. Da can kasan za ka iya ji da b'aci ranka wayace kafad'amin? Tak'arasa magana tana murgud'a baki.
Ta k'asan ido ya dubeta ya yi murmushi
Saboda nasan za ki kwatarmin da hankali ta hanyar dad'ad'a kalamanki.

Huh.. Ta ta6e baki Indan fad'anka ne da yaya zuhra ba mai shiga saidai a ba Ku hak'uri, kamar gobe ne za Ku shirya bakaji ance fushin masoyi hutu?
Tsaki ya ja mtcsww! Lallai a wannan karon zan shayarda ke zallan mamaki.
"Dariya tayi cikin dariya tace sau nawa kanamin irin wannan cika baki?
Bansaniba yafad'a a fusace.
Anaal tak'ara kyalkyalewa da dariya tana lek'on fuskarshi Ya Ansar na yaya zuhra Allah nuna min ranar aurenku.
Ba ameen ba bakinki ya sari d'anye kashi.
Tak'ara tintsirewa da dariya, banza ya yi da ita ya mayarda hankalinshi ga driving traffic lights ya tsayarda su can! Ya hango Mae siyarda rakke yasauke glass ya kirashi yanka mun ta N500 Mae rakke jikinshi na rawa yashiga yankawa.
Anaal ta zaro ido rakke N500 bawan Allah duk kai kadai wannan zarin har ina?
Harara ya galla mata ina ruwanki k'udinki ko nawa?
Na ka iya nawa kallo tafad'a tana murmushi.
Ya kar6e rakkenshi ya d'ora ledan a cinyarta dai-dai lokacin aka basu hannu ya ja mota batare da ya kalleta ba yace Lucky taimaka ki tsaga mun
Me zan tsaga ma?
Rakke! Yaf'ada kaitsaye.
Au! Dama ba ka iya tsagawa ba ka siya?
Ban iya ba in za ki tsaga mun bissimillah! In kuma bara iya ba karki cika ni da surutu.

"Ta ta6e baki ta bud'e leda taciro rakke gudu d'aya tashiga tsagawa, tana cikin tsagawa ta dube shi ina fatan kana da labari ba'ashan rakke ana driving?
Dariya Ansar ya yi ke dallah banason iyayi in kin tsaga gutsuro min.
Ta gutsira taciro ta daga bakinta ta mik'a masa ni dai ba ruwana mutum zai sha raguwar yawuna, tafad'a tana dariya.

Ae ba yau nafara sha ba balle ki tayarmin da hankali.
Murmushi kawai tayi bata k'ara cewa da shi komai ba.
Yana isa inda yasaba drooping d'inta ya yi parking ya kashe mota, ya dubeta anatse ki k'arasa ladanki mana
Wane lada?
Ki k'arasa tsaga mun rakke Wanda nasha bai isheni ba.
"Ta girgiza kai batare da tace komai ba tacigaba da tsagawa tana mik'a masa gard'in rakke yaja su Sam sun manta a inda suke ga ra6ar Ac na ratsa su, tsawon lokacin suka dauka a wurin batare da sun saniba kiran sallar la'asar ne ya ankarar da su zaro manyan idanunta tayi tana kallon Ansar Wanda yashagala da shan rakkenshi.

Na shiga 3 Ya Ansar kiran la'asar ne akeyi?
Kasa magana yayi sakamakon dad'in rakke sai girgiza kai ya yi, guntun rakke da ke hannunta tajefa mishi had'e da cewa ashe agogon motarka dai-dai yake shine da na tambaye ka kace min ba dai-dai yake ba.
Dariya yasa kinga mallama miye abin tayarda hankali?
Bansaniba tafad'a tana kiciniyar bud'e k'ofa.
K'asa bud'ewa tayi ta juya tana kallonshi ta marairaice Dan Allah Ya Ansar bud'e min Allah sai Abbah ya tuhume ni ina na tsaya.
Ya lumshe idanu daga bisani yaware su akan fuskarta narasa dalilin da yasa duk lokacin da nake tare da ke banason mu rabu.
Ta kad'a kwayar idonta ni nasan dalilin sai ka bud'e min k'ofa zan fad'a maka.
Yana dariya ya bud'e mata tana fita tayi mishi gwalo nima bansaniba sai ka tambayin kanka, tajuya tai tafiyarta sai da yaga ta6acewa ganinsa sannan yaja mota cike da shauk'in sonta.

_8:03pm_
Chapter 24 · 0% Book details