Sashe 20
Sonki Ne Sanadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana gamawa tayi sending ta mik'awa Ramlat waya ku duba send items ku ga text d'in da na tura masa, na ban hak'uri ya yi kuwa?
A baiyane Ramlat ta karanta zeenat tace anyya Anaal alaqarki da Ansar bata sauya daga yaya da k'anwa ba?
Nima abin zan fad'a ki ka rigani Cewar Ramlat
"Amma wallahi kun bani mamaki da har idanunku suka rufe ku ka manta da matsayina wanda haka yasa ku ke, dangatani da mutume da yafi karfina toh tunda kun manta bara na tuna muku ni Anaal ba kowa bace ba kuma, 'yar kowa ba face 'yar masu gadi banida dangin iya balle na baba a Nigeria cin rani mu ka zo ni da iyayyena kamar yanda nasha jin dubanan mutane suna kiranmu da 'yan ci rani.
Tun farko ganinku da Ya Ansar ku ka fara wannan tunanin a tsakanimu, shin ban taka musu birki ba ta hanyar sanarda ku matsayi irin na Ya Ansar ba?
*SONKI NE SANADI*
_A Romantic love story 2017_
Na Hauwa shehu Aliyu
*®NWA*
www.jeeddahaleeyu.blogspot.com
*°°°In dedication to Aunty Sis°°°*
*16*
Zeenat, Ramlat kudaina had'ani da abinda yafi 'karfina Ya Ansar yafi k'arfina nesa ba kusa ba tuni ya girmewa ajina mutuncin da tausayina da yakeji sune sanadin alaqarmu kuma, har abada alaqarmu ba za ta sauya daga haka ba. Har Ramlat ta bud'e baki za tayi magana Anaal tad'aga mata hannu ya isa Ramlat mu rufe wannan zancen domin, duk abinda zan fad'a ba za Ku fahimce ni ba.
Tana k'arasa magana ta mik'e kutashi mu tafi class.
''Ke ba za ki yi breakfast bane?
Ta girgiza kai banajin yunwa in kum gama kusameni a class tajuya tai tafiyarta ta barsu da aikin kallonta.
_Ansar_
Lokacin da Anaal ta tura masa text yana meeting phone nashi a rufe sai around _12:30pm_ yafito daga conference Hall, yana zaune a office d'inshi zamanshi kenan Abdallah yashigo yana waya da girlfriend d'inshi, har yagama wayan Ansar yana kallonshi.
Mtcsww! Ansar yaja tsaki Wallahi ka ji tsoron Allah! Abdallah shin wace ri6a za ka ci in ka 6ata 'ya'ya wasu?
Kai bakajin tsoron wata rana a 6ata naka domin zina bashi ce. 6ata fuska Abdallah ya yi kafara koh?
Wai kai Ansar ba halin ka ji mutum yana waya sai kafara yi masa wa'azi?
Wannan yarinya da ka ji ina waya da ita tana matuk'ar sona tamkar ranta. Ba tilassata nayi ba shaukin so ne ya d'ibeta tayi min alqawalin komai nakeso za ta mallaka min daga ciki harda kanta, shine don ina gaula irinka za'a bani kyauta abun irin wannan nace ba zan kar6a ba.
Ni fa lafiyayyen namiji ne ina buk'atar jin dad'i a wannan zamani ba abinda ya kai mata musanman in kanada k'udi shiyasa na za6e su, don na dinga barje gumina akansu. Duk 'yar da k'addara ta fad'a kanta ta afka tarkona wallahi sai na moreta idan kuma na gama tsotse albarkatun jikinta nai mata wulaqancin da ko kare ba zai ci ba.
"Girgiza kai Ansar ya yi haushin abokinshi ya kamashi ba tun yau ba yasan halin abokin nashi da neman matan tsiya amma bai ta6a tsanmani iskancin nashi ya yi tsamari haka ba.
Abdallah lamarinka ba tsoron Allah a ciki kai ko tsoron cuta bakayi indan so ka ke ka more rayuwa kayi aure mana.
Ubangiji ya yarje mana mu aure mata d'add'aya har guda 4 amma in za mu iya adalcin tsakaninsu, in ba za ka iya adalcin ba ka aure guda 1 ta isheka barje gumi domin zina bala'i ce kada sanadinka ya janyo mana masifa a zuri'a.
Abdallah ya mik'e tsaye yana murmushi ya dube Ansar yace karka damu d'an uwa zanyi aure very soon duk wannan abin da nakeyi akwai wance zuciyata takeso, banida burin da yawuce na mallake ta a matsayin matata ta sunnah.
Na yarda da ita za ta kai min budurcinta har gidana. Wad'annan tarkace da ka ga ina moresu a farmhouse d'in Dad ba ta aure a ciki kawai abokan jin dad'i ne. Inanan da matata kamila, malama mai nagartaciyyar tarbiyya tana jirana a gefe da zaran nagama more rayuwa za mu yi aure zan watsarda duk wani shashshancin na rungume halak d'ina.
Mtcsww! Ansar yaja tsaki 'yar iska dai irinka dama mazinacin sai mazinaciya kuma inaji maka tsoro ranarda Dad zai kamaka da karuwa a farmhouse d'insa, wallahi za ka sha mamakin irin hukuncin da zai dauka akanka.
A yatsine Abdallah ya dubeshi sai in Kaine munafukin da zai fad'a masa.
Murmushi Ansar ya yi kaima kasan ni ba munafuki bane da na iya munafuncin da tuni kashinka ya bushe banza kawai bunsuru.
Abdallah ya yi murmushi yana Sosa k'eya kanka akeji ni ka ga tafiya ya murda handle yafice tun fitar Abdallah Ansar baisan dalilin da yasa yakejin matsanancin fad'uwar gaba ba.
Ya kifa kanshi a desk yashiga nazarin kalaman Abdallah lokacin yashare Mae tsawo yana fama da tunani, ganin zai wahalarda kanshi a banza yasa ya mik'e yashiga bathroom d'in da ke cikin office d'inshi ya wanke fuskarshi yafito yana goge fuskar tashi da k'aramin towel sai lokacin yatuna wayoyinshi da ke rufe yana budewa text message suka fara shigowa rututu na Zuhura yafara karantawa _Honey na kira duka layuka ka a rufe just to tell you how much I missed you in kayi switch on please ka kirani ina matuk'ar son naji sanyayiyar muryarka Mae sanyaya min zuciya. ILYSVM_
Ansar ya tabe baki yacigaba da karanta text d'in yana cin karo da na Anaal yafara doka, murmushi kamar Wanda akayi albishir da kujerar makka tun yana murmushi sai ga bawan Allah yana kwasan dariya shi kadai, ya duba wrist watch d'in hannunshi remains 15 minutes a tashi su Anaal daga school ya mik'e ahanzarce yadauki key yajefa sama ya chafe ya bud'e fridge yaciro gwagwanin coke Mae sanyi gaske yafice.
Yaja mota cikin nishad'i yana driving da hannu d'aya, d'ayan kuma yana rik'e da coke lokacin zuwa lokacin yana kur6awa a haka ya iso gate na school d'insu yanemi wajen da yasaba tsayuwa ya yi parking.
Ya zauna zaman jiran a tashe su.
_2:15pm_
Anaal tana fitowa ta hango shi saida gabanta ya yanke yafad'i duk wannan uban sauri da take yi tunaninta ta sulale ba sai tajira shi ba koda zai zo ya tarar ta yi tafiyanta, sai gashi haqarta bai cima ruwa ba.
'kamar wance za ta fashe da kuka ta nufi wajenshi kunyarshi takeji matuk'a jin take kamar za ta nitse k'asa cikin tatata tak'arasa hannunta na rawa ta bud'e k'ofa bata bari suka had'a ido ba cikin laulausar muryarta tace _ina wuni Ya Ansar?_
Batare da ya amsa ba ya kur6a coke d'inshi kallonta yake yi ba ko kiftawa, yayinda ita kuma ta sadda kai k'asa tana wasa da yatsunta. Tsawon lokacin suka dauka ahaka shi bai tanka ta ba ita kuma bata k'ara cewa komai ba.
Anaal so take ya tayarda mota tun kafin su zeenat su fito tasan halinsu da fassara yanzu nan za su fassara ta da cewa saboda Ansar ta sulalo bata jira su ba.
Kamar za ta kurma ihu ta kalle shi, ta sauke idanunta a fuskarshi eye's ball d'inshi suka had'e da nata yasauke gwangwani coke ya cije lips yana kallonta turo baki tayi _Ya Ansar Dan Allah kayi hak'uri ka ja motar nan banaso su zeenat su gani_
''Ya tabe baki daga bisani ya yi murmushi ya yiwa mota key suka halba kan titi, ya kur6i Coke ya dube ta ta k'asan ido ya mik'a mata raguwar Coke d'in _Anaal, Anaal, Anaal sarkin kunya kar6i Coke ki jik'a mak'oshi ki ko zai rage miki wannan kunyar_
Uhm! Tai ajiyar zuciya kallo d'aya tayiwa gwangwanin ta kauda fuska, tasake takurewa cikin hijabi.
Ke kan yarinyar nan bakida mantuwa abunda yafaru tun safe ace har zuwa yanzu ba ki manta da shi ba. Lokacin da naga text naki dariya naci sosai
"Ta galla masa harara harda su murgud'a baki, tai masifar burgeshi musanman yadda d'an k'aramin bakinta yajuya.
Yasake mik'a mata Coke _na k'oshi_ tafad'a a gajarce, kina nufi ba za ki sha raguwa na ba? kina kyankyamin aza bakinki a inda na aza nawa?
''Ta kalle shi da mamaki tana nodding head nata, Uhm.... Uhm..ni ba haka nake nufi ba.
Mekike nufi da kin k'oshi?
Cikina a cike yake abinda nake nufi kenan.
Uhm... Anaal kenan abinda ki ka fad'a azahiri bashi bane a bad'ilinki jikina yabani cewa kyankyami na ki Ke, da Auwal ne yasha abu yarage miki da bara ki ce ba za ki sha ba.
Wai ni Lucky har sai yaushe zan maye miki gur6in Yaya Auwal ne? Duk wani hanya da zabi na zame miki d'an uwa na bi amma ke sai kora da hali ki ke mun, ayanda nakeji ko abincin da yafito daga bakinki zan iya ci saboda inajinki ajinina tamkar Basmah.
Ba shiri ta katse hamma da takeyi tashiga kallonshi tai yi murmushin ta mik'a hannu yabata Coke saida ya yada idanunshi akan fuskarta kafin yabata.
Tayi Bismillah ta kur6a sau d'aya sai kawai tashiga jujjuya gwangwani saida ta d'auki ''long time kafin tak'ara kur6awa a karo na uku tana kur6awa sai tayi kamar takware, ta mayarda na bakinta cikin gwangwani tafara tarin karya, duk abunda take yi Ansar yana kule da ita yashiga yi mata sannu.
_sannu Lucky ko na tsaya ne na nemo miki ruwa?_
Girgiza kai tayi ya kar6e coke d'in daga hannunta yi hak'uri my Lucky na matsa miki kinsha abunda ranki bayaso gashi garin haka har kin kware.
"Tayi murmushi batare da tace komai ba daga haka ba Wanda yak'ara magana.
Ga mamakinta sai taga Ansar yana shan Coke d'in ba abinda yasha mishi kai, a rikice takira sunanshi ya Ansarrr! Wannan coke da ka ke sha yalalace na mayarda na bakina ciki.
"Ya zaro ido na baki fa?
Eh! Tafad'a tana kallonshi.
Shine ba ki fad'a mun ba?
"A tunanina ka ga lokacin da na mayarda shi.
Wannan tunaninki ne ni ba abunda nagani yasake kur6a abinshi, da sauri tace ''please Ya Ansar Kadàina sha Àllah nasaka na baki a ciki.
"Ya tabe baki aikin gama yariga ya gama duk abunda yakai ciki, ya zama nama k'azantar da bakagani ba tsafta ni ba ruwana Coke nasha ba yawun bakinki ba.