← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 71

Sashe 9

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aisha bata qara mata magana ba, tagama tsefe kanta, Sannna tadaureshi da Dan kwali, Dan batada ribom ko daya

******

Zaune suke shida mama dakinta, yanda Dakin ya tsaru, saika rantse Dakin wata budurwa ne, Kansa yana kan cinyarta, so yake yafada mata yanaso idan yagama ginin companyn yabawa munirat to Amma yana tsoro, danhaka saiya sauya shawara yace "mama akwai kayan Azumi dazan raba, idan akwai Wanda kike so akaiwa saiki fadamin Inyi musu magana"

Mama tace "A a Shahaab, banason komai, abu daya nakeso awajanka kawai"

Cikin Sanyi jiki ya kalleta, yana tsoro karta ce masa yaqara aure, yace "mekikeso mama?"

Tace "nariga na fitar da rai da ganin Qawata Aysha,inajin Sai a darussalam zamu hadu,lokacin danaje gidansu neman ta, mutanan unguwar sun fadamin babanta yakoma jigawa da aiki,danhaka inaso kasamu lokaci, kaje jihar kaginamin gidan marayu acan, inajin Aysha tarasu, bansan Kuma tayaya zan taimaki wani Nata ba, qila tarasu tabar marayu, idan Allah yasa yayanta suna daga cikin Wanda za'a kawo su gidan marayun shikkenan kaga Nima na taimaka mata, qila haka Allah ya qaddara mana nida ita, Allah baiyi zamu cika alqawarin mu, muhada Yayanmu aure ba"

Shahaab ya Lumshe Idonsa, yabude, shifa wannan maganar hadin auren ne yasa bayason aga matar Nan, to Amma Yaya zaiyi? Ahankali yace "to, za'ayi"

Tace "yaushe?"

Kallan ta yayi yakasa magana, Nan da Nan ranta ya6aci tace "nifa Naga alama bakasan nemomin qawata Shahaab, Kuma muddin a kaga Aysha, saika auri yarta inde mace ta Haifa, saide in ta aurar da'ita ne, daga min cinyata tunda ban'isa insaka kayi ba"(😅)

Sake rungume mata cinyoyi yayi,tamkar zaiyi kuka cikin shagwa6a yace "Allah bazan tashi ba, to yanzu ni mama yakike so inyi, aiki yamin yawa, da wanne zanji? Ga company's, ga office dinmu, ga gida"

Kallan sa tayi yana magana kamar zaiyi kuka, ahankali tace "Shahaab, koba Dan qawata Aysha ba, zaka samu Lada kaima idan kayi"

Cikin gajiya da maganar yace "zansa ayi"

Cikin damuwa tace "to yaushe zakaje? Zanbaka kudin ma, nide fatana kawai ayi"

Jikinsa ne yayi Sanyi lokaci daya, lalle mama da gaske take, sake rungume ta yayi yace "mama kibar kudinki, awanne gari kike so ayi a Jigawan? Wanne Gari qawar Taki take?"

Tace "bansan garinda takeba Shahaab, kawai kayi a inda kaga ya dace"

"to mama zan shirya naje cikin satin nan tunda zan raba kayan Azumi, zanyi magana da Ramadan acikin jerin garuruwan da za'a raba kayan azumin, su saka da Garin jigawa, ni sai naje Jigawan da kaina, in raba musu kayan azumin, inyi maganar gina gidan marayun da Gwamnatin Jihar "

Ahankali mama tasaki wata irin ajiyar zuciya tace"nagode MAHMUD, Allah yayi Maka Albarka"

Tamiqa hannunta Qasan fillo, tad'auki kudi bandir daya tabashi tace "ungo wannan nakane"

Murmushi yayi, dimples dinsa suka futo, yatashi daga kan cinyarta, yayi kissing kumatunta, sannan yace "nagode mama" yatashi yatafi part dinsa cikin murna yana jin dadi kamar tayi masa kyautar miliyoyin kudi.

Bayan Ansha ruwa yana zaune agaban mama, munirat na Gefe tana danna waya kamar kullum, wayar Ramadan yakira, cikin zolaya Ramadan yace"kaga Angon munirah ita kadai "

Murmushi yasaki yace" Ramadan, a cikin kayan daza'a raba na dinnan, atura mota biyu zuwa jigawa, a Kwai aikin da zanje inyi acan, Nima inaso inshiga cikin masu rabawar araba Dani, inason in Dan wara jinin jikina"

Hakanan munirat ta tsinci kanta da faduwar gaba, batasan dalili ba, har saida ta daina danna wayar datake tazuba masa ido tana kallon sa, menene Kuma zai kaishi wata jigawa? Waye nashi a jihar?
Ganin babu Mai bata amsa Sai shi, shiyasa tabar maganar har zuwa lokacin da zasuje kwanciya.

Cikin murmushi Ramadan yace "Tofa, yauda kanka Abokina? Amma dakayi zamanka, duk abinda kakeso umarni kawai zaka Bani, zanje inyi ma shi, meyasa zaka wahalar da kanka kana Rabon abincin sadaka?"

"inason yine Ramadan, may be wasu suyimin addu'ah Allah ya amsa"

Ramadan yace "hakane, Allah yasa mudace, idan Kuma Rabon wata ne zai kaika shikkenan"

"babu wannan maganar"

Abinda yace kenan.

Ramadan yace "to ai shikkenan saika koyi cire suite, tunda kace da kanka kakeso ka bayar, kaga bai kamata kayi aiki da suit ba ranar"

"okay" shine kawai abinda yace Sannan yakashe wayar

Washe gari yana gab da barin office aka kawo masa wani file akan case din gidan man fetir din wani bawan Allah da'aka kama akano,Me Kai ashirin,Bai tsaya ya duba file din yanda yakamata ba,ya turashi zuwa wani office din,suje suyi aikin komai

******
Hajja da Aisha suna tafe, rana Sai dukansu take, ga azumi, dawowarsu kenan daga gidan Alhaji Audu maqocin su, Wanda suka je masa jaje sakamakon qwace masa sabon gidan mansa da hukumar efcc tayi, daga Nan Kuma suka biya suka gaisa da jummai, Sannna suka taho gida, Hajja Sai mita take "Kai wannan bawan Allah, Allah kadubeshi su sakar masa gidan mansa, mutum Mai mutunci, me sunan qawa kiduba kiga yanda yake dawainiya da duka mutanan unguwar Nan, akawo mana wannan akawo mana wancen, Allah yasaka masa, Allah yakwato masa haqqin sa, Dan baka Isa fada da Gwamnati ba, saide ka hadata da Allah "

Aisha tayi shiru tana tunani a ranta, tasan cewa de idan ba wannan Mahmud wakilin ne yakama ba to tabbas Shima zai iya sakawa akamawa Alhaji Audu gidan mansa, tunda shi kowama kamawa yake, bashida wani motsi saina kama kayan mutane, to gaba-gaba ma tsaf zai iya kama babansa, tunda kowama tuhumar sa yake. (🙆🏻‍♀️)
Ranar haka ta wuni tana tunanin wannan mutumin, ko abincin shan ruwa bata iya dorawa ba, shi kuwa wannan wanne irin mutum ne?

******

Yau azumi anyi sati daya kenan, Sai yanzu ne Kuma abubuwa sukayi masa d'an sauqi, duk garuruwan daya ce aza6a araba kayan Azumi ko'ina anbasu banda jigawa, Shima Dan yace yanaso yaraba da Kansa ne, yanar gizo, gidan TV, dakuma gidajen redio Sai maganar sa ake, Ana Jinjina wa namijin qoqorin Dayayi,su Hajja Kam dasuka ji Ana fada a gidan redio cewa tayi
"mukam Rabon Naka baizo mana nanba mesunan mamuda"

Aisha kuwa haushi hajjan ma tabata, Wai mesunan mamuda, ko Yaya ma za'ayi ta had'a wannan mutumin da baban ta?(🤔).

Kamar kullum Sanye yake cikin suit Tayi masa kyau sosai, munirat dake fesa masa perfume, gabanta Sai qara tsananta faduwa yake, batasan meyasa ba haka kawai itade batason tafiyar Nan tashi, ta Kalle shi cikin kissa tace "my dear, nifa banson tafiyar Nan taka,I don't know why"

Fuskarta yakama yariqe ta tafukan hannunsa biyu yace "bafa dadewa zanyi ba, kema kinsan banson yin nesa dakeda mama, Amma nayi Miki alqawarin duk inda nake, kina Nan acikin zuciya ta,"
Cikin shagwa6a tafara yimasa wani irin kuka, baisan Yaya zaiyi mata ba, rarrashin ma kamar 6ata lokaci ne, lokaci daya yahade bakinsa danata, wayarsa dake kan gado ce tasa yadaina abinda yake, sakamakon Kiran Ramadan daya shigo.

Cikin kunnan ta ya rad'a mata "ki gyara min abuna sosai kafin nadawo"

Cikin kunya tasake boye fuskarta a qirjinsa.

Shi yana nufin tasake gyara yanda ya kamata tadawo kamar da, ita Kuma kunyar dataji tayi tunanin yaji ta yanda yakeso ne,magungunan datake Sha sun kar6eta, shiyasa yake fadar hakan

hannunta yakama cikin murmushi suka futo falo, daga Nan yayi mata sallama yatafi

Saida yabiya wajan mama yamata sallama, tayi masa addu'ah Sannna yatafi.

A Airport suka hadu da Ramadan, duk Wanda yasan shi saiya yi masa gaisuwa kafin yawuce, yau baisaka I'd card dinsa agaban suit din tasaba, a tsaye suke ko wajan Zama basu nema ba, kafin jirgi yatashi wasu daga cikin ma'aikatan efcc dakuma folice suka ruqo wani mutum kana ganinsa kasan badan qasar bane, Sai magana yake musu da Harshan turanci Amma yanda suka maqala baqin glass a'idon su babu ma Wanda yake saurarensa,hayaniyar datake tashi ne yasa suka juya shida Ramadan, suma ma'aikatan ganin MAHMUD din yasa cikin ladabi suka nufeshi, kudaden dasuke cikin jakunkunan suka juyesu aqasa, sun kamashi ne da kudi zai fita dasu wata qasar kimanin million Dari biyu na Dalar amurka cikin jakunkuna, me Yan jarida zasuyi inba dauka ba, shikam Shahaab kasa magana yayi, saboda da alama wani 6arawon Gwamnatin ne yayi amfani da Yaron domin a turashi da kudin yakaishi wata qasar.

ya kalli Yan jaridar yaga sun taru anaso yayi magana Kai kace Dama awajan suke suna jiran akama mutumin

Haquri ya basu yanemi uzuri tafiya ta kamashi, yanada ganawar da zaiyi tareda gwamnan jigawa nanda awa uku, wannan Kuma wani Babban case ne, idan ya dawo zasu zauna suyi tsatsauran bincike akan case din

Yana fadar haka yayi gaba, yana jin yanda Yan jarida suke kira "yalla6ai tambaya daya, please tambaya daya yalla6ai kawai"

Suna cikin jirgi Ramadan yana gefensa yana duba jarida, shikuwa Shahaab Lumshe Idonsa yayi, Qalubalen dasuke gabansa akan wannan matsayin dayake ciki shi yake tunani, yasan cewa tabbas baza'a Rasa masu shirya masa gadar zare ba, duba da yanda yake kama duk wani Mai sa hannu akan cin hanci da rashawa.

Kamar yanda yafada hakance ta kasance, suna sauka Kai tsaye Tahir guest palace (Annex) suka sauka, Sai lokacin dazasu ga gwamnan Sannan suka tafi, basu dauki lokaci Mai tsawo ba ya tabbatar musu za'a samu Dajin daya dace agina gidan marayun, acan kusa da Garin Kiyawa, saida aka nuna musu komai a photo dakuma wasu garuruwan ma daban, suka Kuma tabbatar masa kamar yanda ya za6a din, ayi adajin kiyawa Amma wajan da zai kasance kusa da cikin Gari suke so.
sunji dadin yanda aka kar6esu,Kuma abun yazo musu da sauqi kasancewar filin na Gwamnatin Jihar ne,Bayan sungama akayi musu photo Sannna suka koma masauqinsu

Suna zuwa Shahaab ya daura towel yashiga wanka, Bai dade da futowa ba aka kira sallar magrib, shida Ramadan suka tafi masallaci Bayan sun dawo suka Sha Fruit da sauran abubuwan buda baki

Bayan sun dawo daga sallar tarawih sun dade suna kallon labarai shida Ramadan, saida matar Ramadan din ta kirashi awaya Sannna yayi masa sallama yatafi dakinsa, shi kuwa da mama kawai yayi waya, yafada mata yanda sukai, taji dadi sosai, munirat kuwa wayarta akashe, tunda yayi try bata shigaba saiya haqura ya kwanta.

Washe gari sukaje sukaga wajan, aka auna yanda abubuwan zasu kasance, suka tsara yanda aikin zai dinga gudana, dakuma mutanen da aka damqa aikin a hannun su
Chapter 9 · 0% Book details