← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 71

Sashe 49

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida tashafa fuskarsa, tata6a wuyansa taji babu zazza6i sosai, sannan tayi kissing goshinsa, ta gyara zamanta akan gadon itama ta zauna tayi shiru, tsawon awa uku suna haka,Amma Bai farka ba.

(banyafewa duk wacce ta karanta min batare data biyaba)

******

Zaune suke a Dakin Ummah itada Walida, Walida ta kalleta Tace"amarya, har kin fara wani irin haske kina sheqe"

Murmushi tayi, ta daga murya tace"Hajja Dan Allah kibani wayar inkira mama inji ko sunje"

Hajja datake daka mata gumba tace"kede kawai kice abaki waya kikira shahab, Nina Rasa wacce irin amarya cema babu waya"

Walida tayi qasa da muryarta tace"ai yanzu Zaki samu waya, saikin shiga tukunna"taqare maganar cikin wata manufar

Harararta Aisha tayi tace"kyaji dashi"

Hajja ce tad'auki wayar takawo mata, cikin sauri takira mama, saide Alokacin wayar tana daki, ita Kuma tana can tareda Ramadan adakin Shahaab.
Saida tagama dakan gumbar, sannan tahada mata wani magani cikin Dan qaramin bokiti tace"gashinan maganin Sanyi ne, saiki dinga Sha kullum"

Hankalinta yana kan waya tace"to Hajja"

Saida tayi wa mama 3missed call, bata dauka ba, sannan tabawa Hajja wayarta

******

Sai Bayan sallar magrib yafarka, Adede lokacin Kuma Ramadan yadawo daga masallaci, mama kuwa acikin Dakin tayi sallah.

Yatsina fuskarsa yayi tareda dora hannunsa akan goshinsa ya runtse Idonsa, cikin sauri Ramadan yace"Shahaab katashi?"

Mama kuwa jikinsa tafara ta6awa tana fadin" Alhamdulillah, Bari inkira likita"

Kokarin tashi yake zaune, Ramadan yayi saurin riqeshi tareda saka masa fillo a bayansa yanda zaiji dadin zama, kallon mama yayi, cikin shagwa6a yace"mama kaina yana ciwo"

Cikin sigar lallashi tace"nasani, yi hakuri, yi hakuri kaji, nakira doctor yanzu zaizo"

Bata dade da rufe bakintaba kuwa doctor yashigo, sake dubashi yayi ya kalli mama Yace"Hajiya mama jikinsa yayi sauqi sosai," yasake russunawa cikin ladabi yace"Allah yaqara afwa yalla6ai"

Shahaab ya Jinjina Kansa alamun amsawa, mama tace"amma Dr. Yacemin fa Kansa yana ciwo, kana ganin babu matsala ne?"

Cikin sauri yace"babu damuwa Hajiya, inde kun bashi magungunan Dana bayar dazu, zai warware, saide a kiyaye abinda zai sake 6ata masa rai"

Cikin sauri tace"insha Allah"
Dr. Nafita, mama tabi bayansa ta wuce part dinta domin kawo masa abinci.
Ramadan kuwa tashi yayi yabude fridge din dakin yadauko masa fresh milk, yazuba masa acup yabashi, ahankali ya Kar6a yasha yar kadan, sannan yabashi sauran ya ajiye.

Idonsa ya Lumshe, yafara tunanin irin abinda yafaru tsakaninsa da munirat dazu, Ramadan ya kalleshi yace"yakamata katashi kayi sallah"

Babu musu yatashi yashige toilet, saida ya watsa ruwa a gurguje, sannan yafuto jikinsa daure da towel, wardrobe Ramadan yabude yadauko masa kayan sakawa, yabashi tareda fadin "in fadama gaskiya?wallahi bazan iya baka auren qanwata ba, saboda na tabbatar adaren farko saita ga likita"

Harararsa yayi, tareda karban kayan yasaka, sannan yace"idan baka Bani ba, ai gashinan Abokina yabani"

Yana fadin haka yatada sallah, saida ya idar sannan ya Ramadan yace"abokina a koda yaushe kaime sa'ah ne,kanada babbar mace, me Hankali, ilmin boko, wayewa,tareda budar ido wato munirat, sannan gashi yanzu zaka auri yar qaramar yarinya, wadda komai ma saika Koya mata, batada wayewa, batada budar ido,akwai kyan diri, uwa uba meson ka tsakani da Allah wadda ba dukiyar ka tagani ta nuna tana yinka ba"

Shahaab daya zauna agado ya zubawa Ramadan ido yana jin bayanansa, yasaki ajiyar zuciya yace"hakane Kam, Nima na lura Aisha batasan komai ba, saboda kaga yanayin society din data tashi,saide Yaya zanyi? Allah yariga yasakamin soyaiyar ta acikin zuciyata, dole nine zan dinga Koya mata komai harta saba wataran ta dinga yin wasu abubuwan da kanta, Amma nikaina shaida ne, batasan komai ba yarinyar hatta a 6angaren soyaiya ma, nine nakoya mata kiss,Amma last time data min, wallahi jinayi kamar zan mutu....inda ace, tasan ire iren wadannan abubuwan, maganar Allah banajin zan dinga fita wani waje Bayan aurenmu"

Ramadan yazaro Idonsa yace"kiss?yaushe hakan tafaru?"

Kallan mamaki yamasa yace"hakan baya faruwa a tsakanin masoya ne? Kokuma bayan shi nacema namata wani abu ne?"

Cikin tsokana Ramadan yace"wannan abu aduhu, a baqar leda, waya Sani?"

Girgiza Kansa yayi, Adede lokacin mama takawo masa abinci ta zauna sannan tafara bashi, babu laifi yaci daidai gwargwado, Ramadan yabashi magani yasha, sannan mama tace"meyafaru ne akacemin munirat tafuto tana kuka?"

Ransa ne ya6aci, lokaci daya yayi kicin-kicin da fuskarsa yace"mun samu Sa6ani ne mama,Allah yasa baki hanata tafiya ba"

Mama tace"aini batazo ma inda nake ba,yanzu saboda kun samu Sa6ani da'ita saita tafi batareda tasanar Dani ba?nasan bazai wuce akan batun aurenka neba, inbanda munirat ai itace babba, Sai abunda tace zakayi, saboda kamar ita aka yiwa abu marar dadi, Amma idan ta kwantar da Hankalin ta Aisha ai kamar yarta take,Ina Rasa control dina wani lokacin Ina fada mata maganganu saboda nariga nasan cewa Dama can kudinka yasa ta aure ka, to Amma Yaya zanyi? Tunda kana sonta, dole haka zan haqura ai, bansan meyasa bata dauka ta a matsayin mahaifiya ba"

Ahankali yace"hakane Kam, inda ace tana daukar ki kamar momynta, da bazata turo mutane tace suzo su kashe ki ba"

Spoon din hannunta ne yazame yafadi qasa, gaban Ramadan yafadi, dagashi har mama, hada baki suke suna fadin "kisa Kuma?"

Nan take ya basu labarin komai,mama da hawaye yake kwaranya a'idonta tace"amma har saki biyu Shahaab? Meyasa bazaka nemi shawara ta ba?"

Cikin 6acin rai yace" mama duk Wanda yanemi yayi shamaki tsakanin ni dake wannan kadanne daga cikin sakamakon dazai Kar6a ahannunsa, bazan iya hadaki da kowacce mace ba,naji haushin kaina daya kasance Bana Dukan mata,Amma dayau sainayi mata duka kafin tabar gidannan"

Dukan sa mama tayi akan murdaddan dantsan hannunsa, cikin sauri yasaki qara, cikeda shagwa6a yace"mama akwai zafi fa"

Hawayen idonta ta share sannan ta dora kanta akan kafadarsa ta rungume shi sosai, Ramadan ma qwallah ya goge yace"gaskiya hukuncin daka yanke Shine daidai, duk mutumin da bazai so mahaifiyar ka ba, babu amfanin zama dashi, ko a addini mahaifiya aka fara ambata kafin mahaifi,bazai iyu mu hada soyaiyar iyayenmu mata data kowa ba,uwa uwa ce ako'ina"

Mama ta Kalle su tace"Allah yayi muku Albarka "daga Nan ta dauke sauran abincin tafice daga d'akin

Tana fita Ramadan yace"wannan dalilin ne yasa nake sake nunama muhimmancin Aisha awajanka, yarinyar tana sonka sosai, Kuma kun dace yanda baka zato, shiyasa tun farko nake cusa ma ra'ayin ta"

Shahaab yace"gashinan Kuma kacusota dayawa tana nema ta zautar Dani ba"

Kafin Ramadan yabashi amsa mama takawo masa magani acikin wani cup guda biyu, daya maganin Sanyi ne, dayan Kuma na tsumi ne, zama tayi ta ajiye maganin tsumin sannan tabashi na sanyin tace"gashi, Aysha Sulaiman ce tabani shi indinga baka kana Sha, maganin infection ne"

Babu musu ya Kar6a yashanye, yana bata cup din, tabashi dayan maganin tsumin tace"shanye wannan dinma"

Jiyayi kamar yayi ihu, tana ganin yanayin fuskarsa ya sauya tasan zai iya yimata gardama,baikuma Isa yarusa mata aikintaba,danhaka cikin sauri takai cup din bakinsa, bata dauke ba saida taga yashanye, sannan tamiqe tsaye tace"to saida safenku, zanje inkira qawata, tunda muka sauka ban kirasu ba"

Ramadan yace"to mama saida safe"

Shahaab kuwa runtse Idonsa yayi, Ramadan ya kalleshi yace"abokina Yaya ne?"

Cikin damuwa yace" mama batasan halin danake ciki ba take Bani wannan abun ne?"

Ramadan yace"maganin infection nefa,ko bakada shi ai baida matsala maganin"

Cikin sauri yace"Shima dayan data qara Bani duk na sanyin ne?saida nace su saka sati biyu ayi-ayi ayi abunnan, Amma suka daddage itada qawarta, Wai sati uku, Kuma yanzu gashinan tana Bani wannan abun, Yaya takeso nayi ne?"

Dariya Ramadan yasaki yace"to yanzu kuka zakayi?ai itama mama gata takewa Aishan,tsuma mata Kai take yi"

Fillo yadauka yadokawa Ramadan ajikinsa, haka sukaci gaba da zance, har suka gangaro kan batun yanda shirye shiryen auren zai kasance

(keda Allah idan kika karanta batare da kin biyaba)

******

Saida tayi wanka ta shirya, tasa ma'aikata su shirya abinci sukai part din Shahaab saboda Ramadan, sannan tashige daki takira wayar su Hajja, saida ta gaisa da kowa sukayi mata bangajiya, sannan sukaci gaba da magana da Hajja,yawanci zancen nasu duk akan labarin Yan makarantar sune, daga Nan Kuma suka koma kan batun auren Aisha, saida dare yayi sosai sannan sukai sallama, Hajja ta kalli Aisha taga idonta a rufe, a fili tace"mesunan qawa har anyi bacci"

Aisha kuwa tana jinta tayi shiru, ba bacci take ba, kewarsa take, tana so Yakirata, tana so taji muryarsa ko kadanne, bataso Hajja tasan idonta biyu, Dan tsaf zata Dauko mata wata hirar ta hanata tunanin sa.🙈🙊

Acan Abuja kuwa kallo Ramadan ya kunna musu, saida suka gama ganin labarai sannan Ramadan yaci abincin da aka kawo,shirin kwanciya sukayi, yakashe musu wutar Dakin sannan yakoma kan gadon ya kwanta, yana kwanciya matarsa takira wayarsa, yad'auki wayar yafita daga d'akin yana sanar da'ita zai kwana tareda Mahmud ne, baijin dadi.

Shiru shiru Shahaab yaji Ramadan bai dawo Dakin ba, dama tunanin ta yayi masa yawa, cikin sauri yad'auki wayarsa yakira layin Hajja, Alokacin Hajja tafara bacci taji waya tana ringing dalilin haka ne yasa tafarka, Aisha kuwa cikin sauri tad'auki wayar, tanaso taga waye yake kira a wannan lokacin kusan karfe daya saura na dare?
Tana ganin number sa, tasaki wata irin ajiyar zuciya, cikin sauri ta dauki wayar

"kinyi bacci?" shine abinda yafara fada mata

Saida tasake yin qasa da muryarta yanda Hajja bazata jita ba, sannan tace"idan wayar tana hannun Hajja fa?"

Yace"ainasan tayi bacci"

Saida tasake yin qasa da murya sannan tace"yanzu suka gama waya da mama fa"

Mamaki ya kamashi, ya dauke wayar daga kunnan sa ya kalli lokaci, sannan yamaida ta yace"su basa gajiya da zance ne?shine tasa mama tazo ta dinga dura min wasu irin magunguna, Kuma idan nace ayi aurenmu da wuri tace Bahaka ba"

Cikin sauri Aisha tace"itama mamanka cede"
Murmushi yayi yace"ni kaka nake yi da'ita, tunda tabani auren jikar ta,Nima nabar dan, nakoma jikanta kamar ke,fadamin meyasa bakiyi bacci ba? Tunani na kike? "

Ahankali tace"Um.."

Ajiyar zuciya yasaki yace"kiyi hakuri, Dana dawo nagaji ne dayawa, saina kwanta bacci bansamu damar kiranki ba,kin haqura?"

Cikin shagwa6a tace"Uhm...
nide ban haqura ba"

Yanda tayi masa maganar cikin shagwa6a hakane yasa yaja fillo ya rungume a qirjinsa tareda Lumshe Idonsa, ahankali cikin lallashi yace"tome kike so?"

Cikin sauri tace"saika cemin kana sona sau Dari"

Murmushi yasaki yace"shikkenan?"

Tace"eh"
Chapter 49 · 0% Book details