← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 71

Sashe 35

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ramadan yana kusa da mama, acan Gefe Kuma Shahaab ne yayi masifar kyau cikin manyan Kaya, Ramadan yasake kallon girman wannan company Amma cikin ransa yana mamakin irin son da Shahaab yakewa munirat, tun ranar dayace zai mallakawa wani mutum Mai mutuqar muhimmanci yasan cewa ba kowa zai Bawa ba face munirat.

Bayan gama bayanin company da abundaya qunsa aka Bawa Shahaab damar magana domin nunawa mutanan dasuka halarci taron jin dadinsa dakuma godia agaresu.

Tashi yayi cikin nutsuwa yafara da gaida mutanan wajan sannan yad'ora da cewa "a rayuwa inajin dadin yanda mamana take Bani kulawa, da yanda ta tsaya tsayin daka wajan ganin ta inganta min rayuwa ta, banida abinda zance da mama face godia, sune jin dadina itada matata munirat"

Munirat tayi wani fari da idonta tana sake hura hanci,wajan yayi tsit kowa yana jin yanda Mahmud din yake magana kamar bayaso, saida yasake kallon kowa sannan yaci gaba da cewa "saide wannan company, ban ginashi da sunana ba, tun farko akwai wadda nayi niyyar mallakawa, ita din mace ce mai mutuqar muhimmanci a gareni, zan'iya sadaukar da rayuwata domin ta.... Dalilin hakane yasa na mallaka mata wannan company, ba kowa bace face AISHA"

Daukacin mutanan wajan Nan da Nan suka dauki tafi.
Ramadan yajuya ya kalli munirat da gumi ya wanke wa fuska, ya kalli Shahaab yasaki wani irin murmushi, yasan mutane dayawa zasuyi tunanin mama yabawa company duba da yanda yafara da yabon ta, sannan Kuma da kasancewar ta itama sunanta AISHA, wata irin dariya ce ta kama Ramadan yayi qasa da Kansa ya tuntsire da dariya domin Gano inda maganar abokin nasa tanufa.

Dam dam, gaban munirat yafadi, lokaci daya gumi ya wanke mata fuska, mutanan data gayyata kuwa gaba dayansu juyowa sukai suna kallonta jin labari yasha bambam

Shahaab kuwa yana gama wannan jawabi yad'auki takardun company, wajan da mamallakin company zaiyi sign yakalla, shiru yayi yarasa wanne irin sign zaiyi mata? Baisan Yaya take signature dinta ba, danhaka yabi shawarar zuciyar sa yayi mata sign da ASH~HAB

(yau Shahaab yataro December awajan munirat 😂🏃🏻‍♀️Dan yawuce march)

Littafin SHAHAAB na kudi ne, duk wadda taqi biyan kudi ta karanta bazan ta6a yafe mata ba, har abada, ki biya naira 300 kacal ta account dina

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta

Katsura shedar biya ta wannan number 08033300034

Mrs Usman ce✍🏻

Page

27

Mama tagirgiza kanta, tasan de bada ita Shahaab yake ba, domin kuwa idan itace bazaice Aisha Kai tsaye ba.

ta juya ta kalli Ramadan, taga yanata dariya,ahankali ta rage muryarta tace "wacece Aisha?"

Cikin sauri Ramadan ya kalleta, dahar zaice Aisha ai tana tare dake mama, Sai yayi tunani Gara taji daga bakin Shahaab din, tunda yasan dole zaiyi mata magana cikin fahimta, Girgiza Kansa yayi yace "jinake ke yake nufi mama"

Mama ta kalleshi tayi murmushi, tasan Dama bazai fada mata gaskiya ba, Amma babu abinda bai saniba akan Shahaab tunda tare suke komai.

Cikin iya kissa munirat tatashi tana dariya wadda tafi kama da yaqe, Sai firfita take da hannunta ta silale tabar wajan,
Qawayanta suka Mara mata baya.

Mama kuwa bata tafi ba, saida aka gama taro da'ita, har zuwa lokacin Ramadan yana tare da'ita, mutane Sai zuwa suke suna gaishe ta, saida mutane suka Dan ragu, sannan Ramadan ya rakata mota tatafi gida.
Mama tana zuwa gida tasamu Aisha afalo tana kallo, tana ganin Zuwan mama tatashi tsaye, cikin ladabi tace "mama sannu da zuwa"

Mama ta zauna a kujera tana cire agogon dake daure a hannunta tace "sannu Aisha, yagida? Kina zaune ke kadai bakya gajiya da wannan kallon ne?"

Murmushi tayi tace"mama agida Bama kallo, shiyasa yanzu yake birgeni, Amma idan bakya so insha Allah zan Dena"

Cikin sauri tace"a a, yi abinki, idan nahanaki kallo menene ribata? "

Cikin ladabi tace"to mama nagode, nakawo miki abincin danayi miki?"

Murmushi mama tayi tace"saida kika yi girkin de, tojeki kawomin "

Cikin murna ta wuce kitchen tazubowa mama dambun shinkafar datayi Wanda yaji kayan hadi harda su hanta yanata turiri, mama tace "masha Allah, Aisha kece kikai wannan?"

Murmushi tayi tace"nice nayi mama, ko nazauna nabaki?"
Tace"A a karki damu, zanci dakaina,Amma ki ajiyemin shi da daddare zan sake ci, yanzu de jeki kiramin Munirat"

Cikin sauri ta kalli mama, itafa batason shiga sabgar wannan matar tasa,ko kadan batasan abinda zai hada su, cikin sanyin jiki tace"mama ai bansan part dinba"

Mama tayi murmushi tace"a a, baki ta6a zuwa bane?"

Daga mata Kai tayi,mama tace" a a baki kyautaba Aisha, masu suna Aisha fa sunada kirki, ko baki San Nima sunana Aisha ba?"

Kallon tayi tace"bansani ba mama, ashe haka sunan ki"

"haka sunana, Kuma nasan duk me suna irin nawa tanada kirki, saboda haka kede baki kyautaba da baki ta6a zuwa kun gaisa da munirat ba,karki damu da halin ta,haka take, Nima haquri nake da'ita,idan kika fita zakiga wani part daga hannun damanki, kije kice mata tazo in jini"

Tace "to mama"
sannan ta juya tafita.

Ta danyi tafiya medan Nisa sannan ta qaraso part din, wasu ma'aikata tagani a tsaye daga Gefe, gulma ta rufe musu ido ko lura da Aisha basuyi ba, daya daga cikin su yace"ai yau yalla6ai yayi maganin wannan matar tasa, muda mukaje muka tsatstsara wajan muka share, mu akai komai akan idonmu, kamfanin fa ta fadawa mutane ita zai Bawa, habaaa! yalla6ai yana tashi saiya Bawa Hajiya Mama kamfani, bakuga yanda take gumi ba"

Wani zai sake magana Aisha tace"dan Allah inane qofar shiga part dinnan?"

Juyowa sukai suka kalleta, saikuma suka fara kuskurin kunya, suna tunanin taji abinda suke fada Kuma suna tsoron taje ta fadawa mama, ita kuwa suna nuna mata ta wuce, tana shiga part din taga yasha bambam da'irin na mama, tsaruwar Kam harta yi yawa, idan anan part din take 6ata lokaci zatayi wajan kallon part din kawai.
Munirat tagani a zaune da wasu mutane su su hudu, Dan kwalin kanta yana riqe ahannunta, ta hargitsa gashin dokin kanta, masifa ta rufe musu ido basu maji shigowar Aisha da sallamar taba, ikee tace "waima wacce shegiya ce wannan Aishan?"

Kai tsaye munirat tace"uwarsa ce mana, da'ita yake"
Ajiyar zuciya ikee tayi sannan tace"ni narasa abun damuwa anan munirat....tun farko fa kece kikai wasa da damar ki da har Zaki Bari yadinga fifita wannan tsohuwar sama dake"

Hauwi tace "Allah natuba mezatai dawani company yanzu? Taci zamaninta tana neman shiga naki zamanin keda mijinki, Shima da niyya yabata ai, yasan tana mutuwa kudin de nasane"
Qanwarta Maryam tace"amma Anty ya Yaya Mahmud zai mana haka? Mommy tana can gida fa tayi gayya, tun jiya muke hada abincin baqi saboda mutanan data gayya ta"

Munirat ta goge Hawayen idonta tace"Dama mamarsa ta tsaneni, narasa Mena tsare mata, da kunne na naji yana cewa zai Bani, Amma nasan inde yafada mata Dama zata hanashi yabani,tunda gashinan anrubuta sunanta akan takardun ai shikkenan,Kuma wallahi Saita gane...."

Maganar ta ce ta maqale ganin Aisha a tsaye abakin qofar Dakin, cikin masifa tace"kekuma ubanme kike akanmu? Munafuka muna magana kinzo kin tsaya mana aka wato Zaki kwasa kije kifada mata ko?"

Cikin sauri tace"mama ce tace kizo tana kiranki "

Cikin tsawa munirat tace"fice kibarmin Nan kona tashi na kakkarya ki,annamimiya"

Cikin fishi Aisha ta juya tabar mata part dinta, qasa qasa tace"wallahi Bani ba saide ke"

Ikee tace "wacece wannan din Kuma?"

Munirat tace "baquwar uwarsa ce, shegen cusa kaine da yarinyar natsane ta wallahi"

Maryam tace "tabdi, lalle Anty akwai aiki a gabanki, kina zaune da wannan yarinyar a gidan Nan? To Bari kiji daga baqunta tana Dan kula da mahaifiyar sa zata zarce kulada mijinki, ke bakiga dirin yarinyar bane?"

Munirat tace "nikuwa ninaga uban diri ma,ai Ina ganin iya duniyanci awajan wannan tsohuwar, rannan daga zuwa na part din zuciyata daya Naga takama yarinyar ta rirriqe masa shikuma Sai ta6awa yarinyar nono yake"

Hade baki sukai atare sukace "nono?"

Tace "nono kuwa, tundaga ranar nasan banida maqiyiya irin mama, yaza'ai yarinya danya sharaf kamar wannan zaka turawa namiji baligi kamar Mahmud ita yana ta6a mata nonuwa,yanda nasan mijina idan yagani ma Hankalinsa tashi yake, bare Kuma ace anbashi yata6a, Sai kinga gashin tama shegiya kamar aljanna, sauqi na daya nasan Mahmud din yanmata basa gabansa, Aida yanda zai dinga Binta saina raina kaina"

Hauwi tace "tabdi, yanzun made karki zauna kisa musu ido, tashi zakiyi tsaye munirat"

Haka suka dinga tattaunawa suna zagin mama da Mahmud din Kansa.

Tana komawa wajan mama tace "mama tana tareda qawayenta, nace kina nemanta to Amma sai fada takemin"

Mama ta Girgiza kanta tace "Allah ya shirya, Dauko Mai ki shafamin a qafafuna"

Cikin sanyin jiki tace"to mama"sannan ta wuce d'akin.

Bayan ta Dauko man zama tayi ta dinga shafa mata suna hira kad'an kad'an, saida yamma taraka mama daki itama tatafi dakinta, har zuwa lokacin munirat batazo Kiran da mama tayi mataba.

Da daddare suna zaune afalo, mama ta kalleta tace"Aisha jeki zubomin sauran dambun Nan danace ki ajiyemin zanci da daddare "

Cikin ladabi tace" to mama "

Kitchen din ta wuce, anan ta tarar da masu aiki suna wanke wanke kwanukan dasuka gama amfani dashi na girkin dare, abincin ta zubowa mama sannan tahado mata da lemuka da ruwa, cikin nutsuwa ta ajiye mata sannan ta zauna tace"in baki ne mama ko zakici da kanki?"

Murmushi tayi tace"zoki Bani"

Zama tayi akan kujerar, tafara bata abincin, mama tace"Aisha girkin yayi dadi sosai, kinsan rabona da dambu na Dade, duk wadannan masu aikin basu iya irin wannan girkin ba, yawanci saide qauye"

Aisha tayi murmushi batace komai ba, mama tasake cewa"qirjin de yadena miki ciwo ko?"

Cikin kunya tace"eh yadena"

"to Bayan fa?"

Aisha tace"Shima yadena"

Kafin tasake jefo mata wata tambayar yayi sallama yashigo falon, wani soja ne a bayansa yabiyo shi da wata breaf case me kyau,wani irin farinciki ne yakama shi yanda yaga tana Bawa mama Abinci, Kota wannan Fannin bazai ta6a hadata da munirat ba, saboda tana kula da mahaifarsa ,tana daga gefen hannun Daman mama, shikuma yazaune agefen hagun ta,tareda kallon Aisha Qasa qasa, ajiye masa brief case din sojan yayi, sannan yajuya yafice,Suna hada ido tayi sauri tayi qasa da kanta, ahankali ta ajiye abincin zata tashi, cikin sauri mama tace "Aisha zauna mana, Ina zakije kina Bani abinci?"
Chapter 35 · 0% Book details