← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 71

Sashe 52

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka kawai yaji ransa ya6aci, mezatai a dutse? Yanzu haka tana can kowa yana kallon ta, haka yadinga tsaki shi kadai kallonma kashe wa yayi, yasake Kiran waya yayi oder kayan furnitures komai da komai Wanda za'a zubawa Aisha, harda na part din mama gaba daya, dakuma nasa Dakin, sannan yatashi yaje ya kwanta.

(littafin kudi ne, ban yafeba idan kika karanta shi free)
******

Cikin kwanakin da basu wuce ashirin ba,Idan Kaga Aisha dole kasake kallon ta,Tasha gyaran jiki yanda ya kamata, magungunan mata kuwa Anty Mariya ce take hada mata su masu kyau tana bata ciki harda na qarin breast, Nan da Nan kuwa suka sake cika suka tsaya qyam, tayi haske tayi kyau sosai, kamar ba'itaba, gyara kawai ake mata saikuma nau'in girke girke datake sake Koya mata, tsawon wannan lokacin bata kira Shahaab ba, Shima daya gaji da tambayar Hajja yanda za'ayi ya sameta yaga de batada niyar hadashi da'ita, saiya denakira, yau kwana biyu kenan da kawo lefenta akwatunan ta goma Sha biyu, yanaso yakira yaji ko kayan sunyi mata kyau Amma Kuma babu yanda za'ayi ya sameta awaya, tareda Anty Mariya suka taho gida, Alokacin biki yarage saura kwana uku, Ummanta Sai kallon ta take tana ganin yanda taqara yin kyau sosai,dogon gashin Nan Nata yasha gyara Sai qyalli yake, Hajja kuwa kasa rufe baki tayi Sai Fara'ah take,tana qara yiwa Anty Mariya godia, daga Nan Hajja tajata suka shige daki zata nuna mata kayan lefe, itama Aishan Dakin Ummanta tatafi Dan tabar Hajja da Anty Mariya Sud'an gaggaisa, batayi tunanin har ankawo lefen ba, Ummah tabiyo ta daki tace"kin kira Mahmud kuwa tunda kika tafi?"

Cikin sauri tace"Ummah bamuyi waya ba, itace ta hanani kiransa tace nabari yafara haduwa Dani tukunna zaifi doki na"

Murmushi Ummah tayi tace"ai komai yazo qarshe, kikira shi idan kin huta, Dan kullum saiya kira wayar Hajja Ina jinsu suna fada"

Murmushi tayi tace"to Ummah"

Wani magani ta Dauko tabata tace"kitashi kije bayangida kiyi tsugunno da wannan, kibari yashiga jikinki sosai"

Tace"to Ummah"

Sai dare tashiga Dakin Hajja anan taci Karo da akwatuna, saitayi turus ta tsaya daga bakin kofar, Hajja ta kalleta tace"kayan lefen ki ne,shekaran jiya aka kawo su"

Shigowa tayi ta zauna batare data budeba tace"sunyi kyau sosai"

Hajja tafara budesu tace" keda baki dubaba? Bari ki gansu, harda sarqar gold aciki kusan Kala uku, saina dauke miki su na 6oye saboda Yan kallon Kaya kar a dauke a nemeta arasa, Dan kullum Sai mutane sunzo ganin Kaya, Amma ni me sunan qawa banga rigar nono ko daya acikin kayan naki ba"(🙈)

Bakinta tata6e tace"shikkenan kawai,inajin anmanta, Hajja kibani waya nakirashi,"

Hajja tace"um kirashi Kam, yanda yake bugomin safe, rana, dare, Gara ki kirashi Nima nahuta" ta qarasa maganar tana bata wayar, sannan tafice tabar mata d'akin

Yana ganin Kiran yayi rejecting, yakira, tana dauka da yaji muryarta ce yasaki wata irin ajiyar zuciya a6oye,cikin nutsuwa tace"ina wuni"

"lafiya" yabata amsa a taqaice, tanajin haka tasan cewa fishi yake, murmushi tayi tace"fishi?"

"uhm" shine kawai abinda yace
Kwanciya tayi a gadon tazare wayar daga kunnan ta, ta dora bakinta akai tasakar masa kiss guda uku, Sannan ta maida wayar kan kunnan tace"Daya agoshi, daya akumatu, daya akan lips dinka"

Murmushi yasaki yace"keko....,kinma raina min Hankali, ni zakiyi wa wayo? Kikama hanya kitafi wani gari, keda kike da hidima a gabanki, me zakije kiyi awani gari har kusan sati uku? Kuma koki kirani, inma mutuwa zanyi inmutu ke babu ruwanki"

Cikin sauri Tace"A a, bazaka mutu ba,insha Allah kana Nan araye tare Dani, saina Haifa Maka 'yanbiyu ka gansu kayi rayuwa tare dasu"

Wannan kalmar ta haihuwa daga fada masa, itace tasa yamanta da laifin data masa, yasaki ransa, cikin sauri yace"da gaske Zaki haifamin Yara maamah?"

Fari tayi da idonta tace"insha Allah"

Ajiyar zuciya yasauke yace"ina sonki sosai, kinga kayan naki komai yayi?"

Tace"nagani sunyi kyau sosai, kayi kokari, Allah yaqara budi, Allah yasa gaba kafi haka, sunyi kyau, Kuma sun birgeni, Amma Wanda yasiyo kayan yafimin kyau fiyeda kayan...."

Cikin jin dadi yace"da gaske?"

Tayi qasa da murya tace"sosai"

Murmushi yayi yace"zakiga babu bra aciki, saida mama ta tambayeni menene size dinki nace bakya gida, Bama waya, idan kinzo Garin Sai muje ki siyo Wanda tamiki, nikuma nafada mata haka ne kawai danta rabu Dani,da niyya naqi sanar da'ita"

Tace"meyasa to?"

Qasa yayi da muryarsa cikin sigar rad'a Yace"tonariga nasan size din abuna, tun lokacin Dana riqesu a hannuna naji yanayin girman su, kawai de banso a saka brezian ne, nafison ki zauna Ahaka, banason abinda zaimin shamaki dasu...."

Cikin sauri tace"dan Allah nide kayi shiru...."

Dariya yayi yace"nayi shiru, shikkenan? Ya shirye shiryen biki?"

Bakinta ta turo gaba tace"yanzu zan fara,inaso zamuyi Walima nida malaman makarantar Dana koyar,sannan zansa gobe ayi saukar alqur'ani, zan basu sadaka idan sun gama suyi mana addu'ah Allah yabamu Zaman lafiya Kuma yabani haihuwa Mai Albarka, yanzu zaka Bani kudin Walima, da kudin fita daga dandali, da kudin gyaran jiki, da kudin uwa da uba"

Jan zuciya yayi, yarasa Yaya akai yarinyar Nan Takeda Hankali da hangen nesa, ko kadan shi baiyi wannan tunanin ba na saukar alqur'ani, Amma gashi yarinyar yar cikinsa tana cewa za'a musu, wanne irin so take masa ne? Dame ya kamata yasaka mata? Cikin tsokana yace"hardasu kudin uwa da uba? To ai mama ce zata baki wannan Bani ba,itace uwar, Kuma itace uban, kudin gyaran jiki Kuma babu maganar sa, aure saura kwana uku wanne irin gyaran jiki? Ki zauna Ahaka yanda kike,karki gyara min komai ahakan kinfi kyau, Shima na fita daga dandali kiyafemin shi kawai"

Kamar zatayi kuka tace"tabdi, duk wadda zatai aure fa mijin ko abokan sa suna bayarwa, Kuma ni sai kace a a, to Yaya zanyi da mutanan da zasuzo walimar?"

Cikin sauri yace"yanzu de abun Bana zafi bane,zan turo miki number Ramadan ki kirashi shine Abokina zai baki duk wannan kudin, akwai number mama itama ki tambayeta na uwa da uba,nikuma zanbada kudin gyaran jikin, Dana saukar alqur'ani da za'ayi, Amma ai gyaran jikin na kwana uku ne, tunda bikin saura kwana uku, Dan haka kudin kwana uku zan turo"

Cikin sauri tace"ai baka bada kudin anko bama, harshi"

Yace"kuma de? Kinga kimin lissafin komai kawai kifadamin, wannan Garin naku bidi'ar tayi yawa maamah, fadamin nawane kudin gaba daya?"

Tace"kudin uwa da uba dubu biyu, na gyaran jiki dubu hamsin, na anko dubu ashirin,na fita daga dandali dubu biyar, na Walima Kuma duk yanda yasamu, abinda Allah yahore, nasauka Kuma zan basu dakaina"

Murmushi yayi,komai zatayi tsakaninta da Allah take fada, babu ruwanta da zuga kudi akan komai kasancewar tasan yana dashi, ya tabbatar inda watace kudin dazata yanka masa Sai yayi yawa sosai, amma ita gashi tana fadar komai yanda yake, abinda bata saniba shine ba kudi ba, inda Ana bada rai, dazai iya mallaka mata nasa, tariga tagama siyeshi da kyawawan halayenta, cikin tsokana yace"yanzu maamah duk wannan uban kudin nine zan bayar?gaskiya yayi yawa, Ina laifin ma gaba daya dubu hamsin atalauce? Albarka ake nema ai"

Cikin shagwa6a tace"Allah kowa fa Ana bashi,Kuma gyaran jiki bakai akeyiwa ba"

Murmushi yayi yace"nibance kimin gyaran jiki ba,yanda kike da kimfi kyau, kinsan yanda kikeda kyau kuwa?"

Cikin shagwa6a tace"nide gaskiya kabamu"

Yace"shikkenan, zan turo miki number Ramadan,kifada masa, zai Baku"

Cikin sauri tace"to,saida safe"

Yace"to kiss me..."

Ahankali tasakar masa kiss din, ya Lumshe Idonsa yace"nifa banji ba"

Sake yimasa wani tayi,nanma yace baiji ba, saida tayi masa sau uku, sannan sukai sallama, daga Nan tatafi gidansu Walida suka fara tsare tsaren yanda walimar tasu zata kasance.

Washe gari kuwa akayi saukar alqur'ani a gidan limamin Garin, tafadi buqatar Mahmud Nason haihuwa aka saka shi acikin addu'ah, saikuma addu'ar Zaman lafiya da kwanciyar Hankali Mai dorewa da akayi musu, Bayan angama suka nufi wajan Walima inda aka rabawa mutane snacks,kowacce take away ansaka Rabin kaza, da doughnut, meat fie, cake, saikuma lemo da ruwa, awajan walimar faty ta sameta, domin kuwa isowarsu kenan daga kano

RANA BATA QARYA

Tun safe aketa kafa rumfuna a filin ball din Garin,yayinda manyan motoci suke sake buda hanyoyi yanda motocin baqi masu zuwa Daurin aure, zasu Sakata su wala, Abba yashiga busy sosai, Sai siyan qwaryar nono yake Ana turasu gida, acan gidan Kuma Ummah da mutanan ta sunata Dama nonon tareda fura da kwakwa wadda suka gogata tun Daren jiya, amarya tana wajan kwalliya tareda qawarta Walida da Faty,gaba daya Garin cika yayi da baqi, daga kan Yan kasuwa, Yan siyasa, harma da ma'aikatansu na hukumar efcc.

Ana dab da daura aure motar daya Dauko shata tundaga dutse tafaso Kai cikin Garin, yasake girma, yazama saurayi, yayi wani irin fari kamar ba jabir din Ummah da Abba da Hajja ba, Kai tsaye yace wa direban taxi din suwuce wajan Daurin aure, suna zuwa kuwa yafuto yabashi kudinsa, ya rataya school bag dinsa Mai kyau a bayansa, Shima yafada cikin wata rumfa ya tsugunna kamar yanda mutanan cikin rumfar suke zaune, daga nesa yake hango Abba yaci babbar riga dinkin shadda fara qal, Sai Fara'ah yakeyi, Allah Allah yake adaura auren yasamu ya qarasa wajan mahaifinsa,ango kuwa baisamu damar ganinsa ba, rabonsa dashi tunda sukai waya yasanar dashi yaduba account dinsa yatura masa kudin jirgi ya shirya yazo bikin shima.

aikuwa ko minti ashirin jabir baiyi ba, aka daura auren Aisha Mahmud, da angonta Mahmud Wakili, akan sadaki naira dubu Dari biyu lakadan ba ajalan ba.

(to masu son shiga jirgi fa su shirya kar Hajja A'i tarufe qofa 🤣)

Littafin kudi ne, idan kika karanta baki biyaba nabarki keda MAHALICCINKI, Saboda nide ban yafe miki ba.

300 ne kacal

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN tareda shedar biya ta wannan number 08033300034

Mrs Usman ce✍🏻

Page 19

'Daurin auren daya kawo surutu da kace-nace a tsakanin mutanan qauyen, dayawa daga cikin su Badon sunsan waye mijin ba, zasu iya cewa anriga ansaida Aisha ne.
Inusa dayake tsugunne agefe yayi saurin goge qwallar Idonsa, rayuwa kenan, yana son Aisha ashe ita ba matarsa bace, yariga yasan tayi masa Nisa, babu yanda zaiyi yanzu saide yayi mata fatan alkhairi.
Chapter 52 · 0% Book details