← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 71

Sashe 54

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kar6i kayan tafara kokarin sakawa, yayinda Hajiya zaliha ta wuce kitchen tahado mata fruit Wanda ta hadashi da maganin mata, sannan ta fasa mata madara peak ta ruwa aciki, takawo mata tace Tashanye shi tas, cikin ladabi ta karba tafara Sha, dadin dataji ne yasa ta shanye shi duka, Nan da Nan ta nemi yunwar da takeji tarasa, Hajiya zaliha tace"toki kwanta kihuta, anjima za'a tafi dinner, idan me kwalliya tazo saiki shirya ku fara"

Tace"toshikkenan Anty Nagode"

Cikin jin dadi Hajiya zaliha tafice tareda rufo mata Dakin, tana zuwa falon taga Shahaab a tsugunne yana gaida mutanan jigawa, shadda ce ajikinsa milk colour, wadda taqara qawata kyakykyawan zatinsa, Bayan sungama gaisawa da baqin yadan daga Kai yana Kalle Kalle ko zaisa Aisha Amma shiru ne babu bayani, Kuma babu Wanda yace masa tana daki yashiga,Mama kuwa da tasan ma'anar Kallen Kallen dayake saitace"ka manta wani abu ne?"

Cikin sauri ya Girgiza Kansa yace"a a mama"

Sannan ya kalli agogon hannunsa yace"bari inje"

Cikin sauri yatashi yafice daga falon,jabir yayi sauri yabi bayansa.

Hajja tayi murmushi Dan itama ta gane wayake nema.

Bakinta cikeda naman kaza Wanda aka kawo musu hade da lemuka da abinci, tace"Aysha, takwararki fa yake nema"

Abba da Ummah sukai murmushi, yayinda Walida da faty suka hada ido suma suke qus-qus daga Gefe,sauran baqin maza da'akazo dasu kuwa daya daga cikin su ya ajiye lemon dayake Sha yace"to Hajiya Atura masa ita mana"
Mama kuwa saita basar dasu ta hanyar fada musu cewa"tana daki na, shirya wa take, inajin bata gama bane"

Nan da Nan kuwa taga sun yarda da maganar Tata, tasan halin danta Sarai, yanda yarinya Tasha gyara idonta idon Shahaab tsaf zai iyayin abun kunya ga surukai Baja-Baja agida, Gara tayi zamanta adaki idan ankai masa ita saiya ganta(😇).

Firarsu sukaci gaba dayi anan Hajja take tambayar Ina surukarta matar Shahaab, Nan take mama tafara Basu labarin mutuwar auren Shahaab da munirat, sosai labarin yadakesu kasancewar sude a qauye abune me girma kaji zancen kisan Kai.

Aisha kuwa tana ganin fitar Hajiya zaliha tatashi ta kunna kallo, Nan Hankalinta yayi kan kallon tun tana fahimta har bacci yafara fizgarta daga qarshe ta gyara kwanciyar ta tafara bacci, bata tashi ba Sai wajan karfe biyu da kwata, cikin sauri tayi sallah, tana zaune tana azkar Walida da faty suka shigo suka kawo mata abinci, tana faracin abincin suka fara bata labarin zuwan Shahaab,Sai dariya suke, faty tace"ni wallahi tausayi ma yabani, yad'an kakkalli mutanan falon yaga bata Nan Kuma abun tausayi mama tana cewa wayake nema saiya ce babu komai, inda nice ai saide suga nagudu wajan mijina"

Walida tace"to Rasa kunya, shi din cemiki akai ya haqura ne? Rabu da abinda kake so kinji, yanzu haka muna fita zai lalla6o wajan matarsa"

Aisha tace"kude wallahi kuncika sa ido, a falon ma Kuna zaune gulma kuke? Ninasan Bani yake nemaba, idan nemana yake bazai 6oyewa mama ba, fada mata zaiyi"

Faty tace"wallahi ke yake nema, abinda mutane yagani a falon gamu Nan reras shiyasa yafita da sauri? Bafa waya kuke ba, rabonki dashi tun ranar Daurin aurenku, Shima Ina ganin ku ba magana kukai ba, Shima narasa dalilin sa naqin siya miki waya"

Walida tace"tunda kikaga haka may be bayason tayi waya da maza ne, kin Kuma San waya da daukan Hankali, tana haduwa da wani saurayin yanzu zaija hankalin ta kamar yanda Shima ya janyewa inusa hankalin ta"(😄)

Dariya sukayi, Aisha tace"wallahi Bahaka bane, zai siyamin, yace Sai lokacin da muka tafi honeymoon Dubai, dakaina ma yace zan za6i wadda tamin"

Walida da faty suka hada baki sukace"wowww!"

Sannan faty tace"kinsan Allah?, kima shirya,yanda mutumin Nan yakashe kudi wajan aurenki, to ajikinki zai fanshe, nasan jikinki saiya fada miki, tas saiya huce gajiyarsa infada miki, barema yanzu babu matarsa, aikuma Saita Allah"

Cikin mamaki ta kalli faty fuskarta d'aukeda tsananin mamaki tace"kamarya babu matarsa?"

Nan take suka fada mata labarin da mama ta basu akan rabuwa auren nasu, jikinta ne yayi Sanyi sosai, tausayin sa ya kamata, Kuma koda wasa bai ta6a fada mata cewa yasaki munirat ba, itade tunda take dashi bata ta6ajin ya kushe matarsa a gabanta ba, ko maganar ta ma ba yayi, yana kokarin ganin ya mantar da'ita cewa yanada aure, Kuma hakan shine daidai, shine tabbacin mutum yasan darajar matarsa saboda bai 6atata awajan yarinyar dayake nema ba, ajiyar zuciya tayi tace"Allah yarufa asiri,idan akwai alkhairi a zamansu tare Allah yadawo da'ita dakinta, idan Kuma babu Allah yasa tabarmin abuna nikadai"

Dariya suka saka gaba dayansu,haka sukaci gaba da firarsu suna kallo kad'an kad'an, har Mai kwalliya tazo, anan tace subasu waje zata yiwa amarya kwalliya,idan angama Nata Sai ayi wa qawaye dasu mama, haka suka futo daga d'akin tareda rufo musu qofar.

Hajiya zaliha ce tadawo Dakin ta kawowa Aisha kayan sakawa, wani material ne Mai kyau dinkin doguwar Riga, taimaka mata tayi tasaka kayan, dinkin kuwa yayi Mata d'as ajikinta, sannan tafuto daga d'akin, suka fara kwalliyar, andauki lokaci sosai Ana wannan kwalliya, sannan akayi mata dauri Mai kyau, dogon gashin kanta akayi mata wani irin style dashi.

Ba'a gamawa mutane kwalliya da dawuri ba kasancewar a nutse takeyin komai,aikuwa tuni motocin dazasu kaisu wajan dinner sunzo, mama da Hajja kuwa basu tafi ba saida Shahaab yazo mama takama hannun Aisha tasaka ta acikin motar dazasu tafi, sannan itama driver yadaukesu itada Hajja, su kansu ma'aikatan gidan sunsan Ana biki a gidan domin kuwa mama saida tabawa kowa pass din shiga.

Tunda tashiga motar kanta yake qasa takasa kallon sa, batasan meyasa ba, haka kawai ta tsinci kanta da kunyar sa, wani irin kwarjini yayi mata badan kadan ba, tun shigowar ta yake waya bai daina ba har saida tafiya tayi nisa,hukumar suce tad'auki nauyin yin dinner, shi Kansa direban daya dauki amarya da ango Shima daga hukumar aka turo shi, yanaso yajata jikinsa Amma Kuma yana son jan girman sa saboda wannan ma'aikacin nasu dayake driving, ahankali yamatsa kusa da'ita tareda Dan daga net din data yafa akanta, yana kallon fuskarta yafara tasbihi ga Allah, tabbas yasan tayi kyau sosai ranar Daurin aurensu, Amma Kuma daya ganta yau, saiya ga ranar Daurin auren ba komai tayi ba, Dan qaramin bakinta ya kalla yaji kamar yahade bakinsu, shiyasa yaji taqaicin rashin Ramadan akusa, yaso ace shine yake driving, da saide yarufe Idonsa, Amma babu abinda zai hanashi hade bakinsa da Nata, idonta dayake Lumshe ya kalla, gashin idonta ya kwanta yayi luf...,ahankali yad'ora lips dinsa akan kumatunta yasakar mata kiss, cikin rad'a yace"kinyi kyau"
Sannan yasaki net din, yajuya yana kallon titi kamar bashine yayi abinda ya aikata yanzu ba, azahiri kallon titi yake, kasancewar shine yake zaune agefen Dama ita Kuma tana hagu, hakan ne yasa yazura hannun sa na hagu ta bayanta, yayinda hannunsa na Dama yake danna waye, shi Kansa baisan meyake danna waba (😲)

Hips dinta yariqe da hannun daya zura ta bayanta, ahankali tad'an motsa alamun bata so,cikin nutsuwa yayi sama da hannunsa ya dorashi akan dukiyar fulaninta guda d'aya yayi masa wata irin matsa, lokaci daya Aisha taqame a zaune, gabanta ne yafadi, cikin sauri ta juya ta kalleshi, Amma sai taga Hankalinsa yana kan waya, ganin ta firgita dayawa tana nema ta tona masa asiri yasa yasake ta, Adede lokacin Kuma suka qaraso wajan, kasancewar lokaci yaja yasa suna zuwa yakama hannunta suka shige ciki, ta ko'ina girma ake bashi, waje ya tsaru iya tsaruwa, duk Wanda ka kalla saide kaga yatsuke cikin suit,ango da amarya dakuma mutanan gida sune kawai basu saka suit ba, Amma jabir ma tasa suit din yasaka.

Suna qarasa wa ciki kawai haske kake Gani na camera tako Ina yana tashi, an gudanar da taro lafiya,anyi Rabon kayaiyaki yanda ya kamata, amarya da ango sunsha pictures da video, lamarin dayasa kafafen sada zumunta suke ta surutu akan bikin, yanda masoyan sa suke posting din vedion bikin ne yasa munirat tagani, Wanda taji kamar tahadiyi zuciya ta mutu, yayinda qawayenta dasuke gefenta suna mata dannar qirji suke sake zigata, dayawa daga cikin su tunzurata suke har hakan yasa tayi wani quduri marar kyau acikin zuciyarta.

Sai qarfe goma na dare, suka nufi gida,hannun Aisha yana cikin na mama har suka qaraso gida, anan part din mama gaba dayansu baqin suka kwana, kowa yariga yagaji, Kuma babu Wanda yake tareda yunwa kasancewar anci Ansha awajan dinner, shiyasa suna dawowa kowa ya kwanta, su faty ne basuyi bacci da wuri ba itada Walida sunata aikin danna waya suna posting pictures din amarya da ango.

Sai shadaya da wani abu Shahaab yadawo gida, yariga yasan cewa Aisha tana tare da iyayenta, shiyasa yayi tunanin tafiya part dinsa Shima,saide duk yanda yaso yayi bacci bai samu ya runtsa ba Sai gab da asuba, hakan ne yasa ya makara a sallar asuba.

Bayan yadawo daga masallaci kuwa kwanciya yasake yi yana ramakon bacci, Sai wajan azahar yashiga part din mama, Fata yake yaga Aisha Amma yana zuwa yaga bata Nan, abinci mama tabashi yaci, saida yaci, sannan ya kalleta yana goge bakinsa da tissue yace"Akwai driver yana jiransu, zai kaisu gidansu idan sungama abinda suke saisu shirya sutafi"

Cikin jin dadi mama tace"to insha Allah, suma baqin ai munyi magana dasu anjima zasu tafi, idan sukaje sukaga gidan nasu saisu shirya subi jirgin dazai tashi anjima"

Cikin kulawa yace"dawuri haka? Nayi tunanin zasu kwana biyu har muje dasu suga sabon office din Abba dayake lagos?"

Cikin farinciki tace"office ka bashi?"

Yace"Eh ai bazai ji dadin Zaman Garin ba tunda ba sabawa yayi ba, Amma idan akwai abinda zai dinga dauke masa kewa hakan zaisa ya kwantar da Hankalinsa ya zauna agarin"

Cikin jin dadi tace"ka kyauta, Allah yasaka da alkhairi, Allah yayi maka Albarka"

Cikin jin dadi Shima yace"Amin"

Daga Nan yajuya yafita.

Saida kowa yagama shirya wa sannan suka tafi gidan da Shahaab ya basu, Wanda yake kusa Dana mama, asalin gidan munirat yayi niyyar sakawa aciki, Kuma duba da yanda mama take zaune ita kadai yasa yafasa, ya zauna akusa da'ita awani part din daban, yanzu Kuma da Allah yakawo su Abba, kawai saiya basu gidan.
Chapter 54 · 0% Book details