← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 71

Sashe 5

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jan zuciya tayi tace "ai tashen balaga takeji,Kuma wallahi Mamuda bazan haqura ba saika Nemo min qawata kokuma kaje ka siyomin ruwan Roba"

Jabir da dariya ta kamashi saiya silale yabar gidan, Abba kuwa shiru yayi yana tunani, toshi yanzu Ina zaije neman wannan qawar ta Hajja? Shida ba aljani ba tayaya zai dinga yawo gari gari yana neman Aysha Yakubu sagagi, toma Aysha Yakubu nawane a Nigeria?🤔
Har gara ruwan ma, danhaka ya kalleta yace "kiyi hakuri to, zan siyo miki ruwan, wanne iri kike so?"

Babu kunya tace "Faro" (🤣)

Yace "to kiyi hakuri yanzu zanje nasiyo miki" daga Nan yajuya yafita daga gidan, itama ta dakawa Aisha Harara, Sannna tashige cikin dakinta.

SHAHAAB littafin kudi ne, Naira 300 kacal babu yawa,kibiya kafin free page su qare, zaki turo 300 ta wannan account din

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaki turomin shedar biya ta Number ta 08033300034
🌸SHAHAAB🌸
(Romance)

Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name

Like my Page On Facebook 👇🏻
https://www.facebook.com/amnahel

5&6

Baifi minti talatin ba ya dawo hannunsa d'aukeda baqar leda, yana zuwa yawuce Dakin Hajja yakai mata ruwan, budewa tayi taga faro ne guda biyu, tasaka hannu ta bude dayan tafara Sha, Sai da yaga fishin dake kan fuskarta yadan Kauce, sannan yatashi yafuto daga d'akin.

Aisha yasake yiwa fada sannan yashige dakinsa

******
ABUJA

Atamfofi ne a gabanta da shaddodi masu shegen kyau, d'ad'd'agasu takeyi tana magana cikin Isa "kayan sunyi kyau, Kuma sun kawo min su daidai kamar yanda nayi oder"

Ta kalli daya daga cikin ma'aikatanta tace "jeki kiramin munirat"

Cikin ladabi ta amsa sannan tajuya, Bayan wasu mintuna tadawo tace "Hajiya tace gatanan zuwa"

Jijjiga kanta tayi cikin ranta tana fadin lalle munirat ta'isa,intura aikiranta Amma saboda ta nunamin ita yar zamani ce batazata biyo yarinyar sutaho tare ba, saita nunamin itama tanada iko saboda tana auren Shahaab

Saida aka dauki kusan minti talatin sannan taqara so part din na mama,aqasan kafet din ta zauna tareda fadin "Gani mama"

Saida takusa minti goma, ta tabbatar ta6ata mata lokaci kamar yanda Itama tayimata, sannan tatura mata kayan tace "ga kayanki Nan, kidauki kikai wajan dinki"

Cikin ladabi ta d'auka tareda yimata godia, Sannna Takoma part dinta

Tana zuwa dakinta ta zubar da kayan tafada kan gadonta tareda fashewa da Kuka, ita kenan suturar dazata saka ma batada ikon dazata siyo da kanta taza6i irin Wanda take so saide sirika tasiyo takawo mata?

Yaya zatayi da wannan tsohuwar ne? Bata Rasa komai a gidan mijinta ba, wannan matar ita kad'ai ce ta tsaye mata, tarasa Yaya zatayi da'ita, wayarta ta janyo takira qawarta Mery, saide jin wayar Tata akashe yasa takira mamanta, cikin kuka ta zayyane mata komai, daga qarshe mahaifiyar Tata shawara tabata akan hanyoyin dazata dinga samun kudi ta hannun Shahaab, saita dinga siyar kalar kayan Dayayi mata, jin wannan shawarar ne yad'an sanyaya mata ranta.

******

Zaune yake a Babban office din companyn sa na takalma dake lagos, Sai wasu mutane guda biyar dasuke fuskantar sa, cup din tea ne a gabansa Sai turiri yake da alama yanzu aka had'ashi

Wata takarda ce agaban su Mai d'aukeda zanen taswira ta wani qaune dake jihar oyo, daya daga cikin su ne yake tsaye, gaban wata babbar TV dake manne abangon office din, yana Sanye cikin suit kamar yanda gaba dayansu itace Sanye ajikinsu, saide Shahaab yacire jacket dinsa yasakata a jikin kujerar dayake zaune, yad'ora Kansa a jikin kujerar ya kishingida kujerar Sai juyawa dashi take, Hankalinsa gaba daya yana kan matashin dake yin bayanin wajan daki-daki, wani ruwa matashin ya nuna yace "kwata kwata bangaren da zamu Gina company bashida ruwa, Amma a opposite dinsa akwai ruwa sosai Wanda yake wucewa, saide akwai titi a tsakani, sannan kamar yanda muka tattauna da gwamnan jihar, yabamu tabbacin cewa inde zamu ninkawa masu gonakin wajan kudin gonarsu to zasu siyar mana da gonakin, saboda Nan ne yafi da cewa da Gina company shinkafa, dazaran mungama zamu yi gada, wadda motocin zasu dinga bi ta wannan kan gadar, mukuma saimuja ruwan ta qarqashin gadar, wannan shine zanan wajan dakuma yanda yake, ga Kuma yanda tsarin ginin company zai kasance Bayan an kammala ginawa "

Ajiyar zuciya Shahaab yasaki, yace" duk Wanda zamu sayi gonarsu dake wannan dajin, ba ninki biyu na kudin gonarsu zamu basu ba, zamu basu ninki uku insha Allah "

Tafi sauran mutanan sukayi, saikuma daya daga cikin su yace"amma akwai yar qaramar matsala fa oga, nafarko daji muka yanka zamu fara wannan aiki, Amma munyi bincike mungano ginin yayi daji dayawa, yakamata ace wajen ya kasance na jama'ah dayawa ta yanda muma zamu amfanesu, suma Kuma su amfane mu, hakan zaisa kamfanin mu yazama kamar wata kasuwa ce ta daban da kowa zaiyi burin zuwa wajan, duk Wanda yazo wajan, dole zaiso jin farashin shinkafar mu, daga Nan mukuma zamuyi kokarin janyo shi jikin mu harya zama Babban customer awajan mu "

Kallan su Shahaab yayi yace" why not mu qirqiri gari awajan?"

Wani ne daban yace"tayaya?"

Shahaab yace" tunda wajan daji ne, saimu qirqiri gidaje,kamar guda Dari biyu, daidai Zaman mutum daya zuwa biyu, Sai mu rabawa mutane mabuqata, Wanda muka tabbatar basuda gidan kansu saina haya, kaga saisu dawo Nan suci gaba da rayuwar su"

Nan da Nan sukayi na'am da shawarar tasa.

Sign yayi akan takardar dazasu bada kwangilar aikin gidajen, saboda yanaso aikin ya kammala cikin Dan qanqanin lokaci, ba kowa yake son mallaka wa kamfanin ba face munirat, yasan cewa zatayi farinciki sosai, bayason ita kanta tasan da aikin, saide kawai ya gabatar da'ita a matsayin mamallakiyar kamfanin.

******

Da azahar suna zaune atsakar gida cikin yar qaramar rumfarsu, Almajiri ne yayi sallama gidan, yakawo mata jarkokin da aka siya kunun Aya a kofar gida tace"dan malam koma kasake dubamin akwai wasu jarkokin,ba dukane ba"

Almajiri yace "babu jarka Sai guda daya,Kuma Haladu me p.o.s ne yaturata cikin shagonsa yatafi masallaci"

Cikin jin haushi tace "ai shikkenan, qyaleshi, Sai yaje ya kaiwa uwarsa ta dinga d'ura kalanzir aciki, dama sana'ar tace" (😂)
Ummah da Abba sukai murmushi, sude basu Tanka mata ba, suna tsoron tahuce akansu

Tashi tayi tashiga Dan qaramin kitchen dinsu na ginin qasa, tafara zuba abinci, Wanda Aisha tagama girkawa yanzu, Alokacin itama Aishan tazo zata sakawa Abba nasa abincin acikin kula, Hajja ta kalleta tace "yanaga kinata raragefe, zoki dauki abinda Zaki dauka mana, keda gidan ubanki?"

Ganin Abba yana Nan yasa Aisha bata ce mata komai ba, kawai ajiye kular tayi, Takoma Dakin Ummah tayi Zaman ta

Ko minti uku batayi ba saiga Hajja tabiyo ta Dakin, hannunta dauke da ruwan faro Wanda Abba yasiyo mata jiya, Tasha daya, dayan Kuma tabar wa mesunan qawa😂
Bata tayi tace "ga ruwanki na jiya, na jira kizo kwana da daddare naji shiru bakizo ba, shine na ajiye miki"

Kar6ar ruwan tayi tana cika tana batsewa, Hajja tata6e baki tace "yar Albarka me sunan qawa, ga niqan Aya ta can zoki tacemin ita, sonake na durashi a jarka yanzun Nan"

Murya can ciki tace "to"

Hajja tafuto daga d'akin Takoma Nata Dakin, shiru shiru tana jiran Taga Aisha tazo tayi mata aikin data sakata Amma taji shiru, daga murya tayi tace "mesunan qawa idan bazaki Dena dauremin fuska Ki futo ki tacemin ayar nanba toki dawomin da abata daki, kar akuyarki ta kunce tazo ta shanyemin kijanyomin nayi asarar ayata"

Ummah dake zaune awaje itada Abba, tace "kifuto kiyi abinda aka sakaki mana"

Futowa tayi tana mita qasa qasa, "asara tanawa Kuma, aikuwa itace tasai asara tunda batada qanqara Kuma basu kawo wuta ba, kullum mutum yana abu daya, idan baya gindin murhu to yana wajan Tatar kunun Aya, kwana biyu da mukai fadan ma ni harna huta"

Hajja datake jiyota tana mita tace "to mesunan qawa idan baki tacemin ba waye zai tacemin? Ko mamuda zansa ya tacemin ayar?, saboda wa nake sana'ar? Saboda auren ki ne"

Aisha batace mata komai ba,haka ta tatace mata kunun ayar tsaf, takai mata shi gabanta, Hajja tabata kujera tace "sannu me sunan qawa, zauna anan to"

Zama tayi cikin shagwa6a tace "Allah Hajja nikidena min zancen aure na"

Murmushi Hajja tayi tace "to shikkenan yawuce, yanzu de shawara Zaki Bani, sonake nasiyo tinkiya ko Rago, da Dan kudin Dana Tara na ciniki, idan Allah yasa jabir yasamu gurbin karatu, Sai a siyar da'ita abiya masa kudin makaranta, idan Kuma auren ki yariga karatun nasa tashi, Sai a siyar acika ayimiki kayan daki Mai kyau, Amma ke Yaya kika Gani? "

Ummah dake zaune wajan Abba tayi murmushi duk da bata ji amsar da Aishan ta bayar ba, cikin ranta tana mamakin shaquwar Hajja da Aisha

Da yammah Hajja tasa Abba yasiyo musu kifi, da kanta tashiga kitchen din nasu tana dafawa, saboda tasan cewa me sunan qawa yau taje makaranta Kuma tagaji, Aisha datake duba jarabawar Yara kasancewar sun kusa hutu sakamakon gabatowar watan azumi, tace "Hajja me kike dafa mana ne?"

Cikin tsokana Hajja tace "Kifi ne qwaya biyu nake dafawa bawani abun kasawa a faranti bane"

Itama Aisha tace "Alhamdulillah tosaikici daya kibani daya"

******

Zaune yake akan wasu lafiyayyun kujeru masu laushi a balcony din falon Mama, Wando ne ajikinsa three quarter, da wata Riga yar qarama wadda ta kama jikinsa, kana hango yanda faffadan qirjinsa zuwa jikinsa yayi wani layi layi, dantsan hannunsa yafuto sosai, coffee ne a gabansa Amma yakasa Sha ya zubawa sojojin dake shawagi a harabar gidan ido, azahiri su yake kallo, Amma badini tunanin rashin haihuwar sane yake damunsa, yayi tunani sosai, amma yarasa mafita, maganar Babban abokinsa Ramadan Wanda yaje Italy yake shirin dawowa jibi, itace take masa yawo acikin qwaqwalwar sa, (Yakamata ka qara aure Shahaab, mutum baya cire rai da Rahmar Allah,tsawon shekaru kaji shiru daga bangaren munirat why not kasake auren wata yarinyar ka gwada kagani ko zaka dace? Wani lokacin idan ta cikin gida ta dade bata haihu ba Ana auran ta biyun idan tasamu ciki zakaga itama dayar Allah yabata idan da rabo, sannan karka kuskura ka nunawa yarinyar dazaka aura kanada kudi, tahakanne zaka samawa yayanka uwa tagari....)
Chapter 5 · 0% Book details