Sashe 21
Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari ya shirya yatafi Abuja, tun ranar dayaje wajan Aisha har sukai waya da daddare, baisake kirantaba.
Yana zuwa gida kuwa munirat Sai Gani tayi Ana shigowa da jakarsa cikin falonta, cikin mamaki tafuto daga kitchen hannunta d'aukeda apple, tace "a a, my Dear daga Ina haka babu sanarwa? Harkun dawo?"
Zama yayi akan kujera tareda dora fillo akan cikin sa yace "nide nadawo, Amma mama tana can, Sai nanda 4 day's zata dawo, bata fada miki bane?"
Cikin yaqe tace "Dama...dama....ba Niger kuka tafi tare ba?"
Girgiza Kansa yayi, sannan yad'auki remote yana kokarin sauya Tasha, yace "tatafi ita kadai ne, nikuma naje Jigawa"
Gabanta ne yayi mugun faduwa, tarasa meyasa yake zarya a wannan qauyen, zama tayi akan hannun kujerar daya kwanta tace "Wai kana nufin Kai kadai katafi jigawa? Dan Allah my dear mekake yi a wannan qauyen ne? Wajan wa kake zuwa?"
Cikin mamaki yadago kyawawan idanunsa ya kalleta, sannan ya maida Kallan sa TV yace "to sarkin kishi, naje ganin aikin gidan marayu ne"
Haka kawai taji zuciyarta taqi yarda da maganar tasa, cikin tsananin kishi tace "idan ma wajan wata kaje, to wallahi kafada mata nafi karfin kishi da yar qauye, mijina yafi qarfin ta"
Murmushi yasaki tareda janyo ta tafado Kansa, dankwalin kanta yacire,gashin dokin datake sakawa yasakko kan fuskarta, kwata kwata yanzu jiyake gashin datake sakawar baya birgeshi, yafi son irinna Aisha, ahankali yad'ora kannata akan faffadan qirjinsa ya rungume ta tsamm ajikinsa tareda Lumshe Idonsa, wannan kishin datake yi akansa, saiya tuna masa da Aisha, sake rungume ta yayi yanaji kamar Aishan ya rungume (🙆🏻♀️🤭)
munirat kuwa ganin irin rungumar daya mata yasa tayi shiru tareda yin luf a qirjinsa, dama akusa take, saboda kwana biyun Nan abuqace take dashi.
Cikin jin dadi yace"waye ya'isa yaja da uwargida? Um? Fadamin me kike so?"
Dukda itama idonta a Lumshe suke, saida jikinta ya danyi Sanyi kadan, duba da yanda koda yaushe burinsa shine tafada masa metake so? Kuma tasan cewa inda tafadi wata buqatar to babu tantama yimata ita zaiyi, ahankali tasake qanqameshi ajikinta
******
Ummah ce da Hajja suka dawo daga gidan Alhaji Audu, Bayan sunje sunyi wa matarsa murna akan gidan mansa da aka saki, suna zama Hajja ta kalli Abba dazai fita tace "mamuda kaje kayiwa Alhaji Audu murna kuwa akan gidan mansa?"
"eh naje tunda safe, saide Allah yaqara kiyayewa gaba"
Aisha tana jinsu gabanta yafadi, hakan yana nufin kenan da gaske Shahaab, ya fadawa ogan sa maganar gidan man Alhaji Audu? Kenan da gaske shidin Yaron Mahmud Wakili ne? Wani irin farinciki taji ya kamata, wayar Hajja ta d'auka zata kirashi, Sai Bayan takira taji wayar tasa akashe, a fili tace "Allah ya dawo dashi watarana Sai nayi masa godia"
Hajja tace "me sunan qawa zoki siyomin Goro a gidan iya hansai"
Futowa tayi, fuskarta d'aukeda murmushi tace "kawo kudin"
Kudin tabata, Aisha ta kar6i kudin ta duba da kyau, sannan tace "Hajja riqe ashirin dinki, kudin Nan bazai kar6u ba"
Hajja ta bude baki ta kalleta tace "to kawo insauya miki wannan din Sai mamuda ya rufata a qirjinsa yana yawo" (🤭🤣)
Babu musu tabata, saida ta sauya mata, sannan taje tasiyo mata Goron takawo mata.
Yau Kwanansa biyar da dawowa Abuja, mama kwanan ta takwas a Niger
Kiran wayarta yayi, yasan duk inda take yanzu de jirginsu yakusa tasowa, Bayan ta d'auka yace "mama kun kusa tasowa ne?"
Ta6e baki tayi tace "to Shahaab matar gida ta tsaneni saboda Allah Ina Naga ta dawowa?"
Shiru yayi, cikin ransa yace "to akwai matsala kenan"
Mama kuwa dataji yayi shiru taci gaba da cewa "matarka bata sona Mahmud, tun cikin azumi Rabon danasa ta a'idona, ranar sallah ma batazo inda nake ba, awayama bansamu matsayin data kirani tamin barka da sallah ba,haka dazanyi tafiyar Nan, batamin Allah yakiyaye ba, yau kwanana takwas awajan dangin mahaifinka nanma batamin waya ba, Nima Kuma anan duk lokacin dasuka tambayeni Ina matarka Sai ince musu bansan inda take ba, saboda Allah idan tana Sona ai zata zo Niger din tayi bikona, Amma zanyi maganin ta, Dani take zancen"
Ran Shahaab idan yayi dubu Toya 6aci yau, yanzu abubuwan na munirat har yakai haka? Mahaifiyarsa? Idan yafara Bawa mama haquri qara tunzurata zaiyi, Gara yabi da'ita yanda takeso, inyaso ita Kuma munirat, su gauraya shi da'ita.
Ajiyar zuciya ya sauke yace "eh gaskiya hakane mama, kinada gaskiya bakya dawo ba, inda ake sonka ai Nan kake zuwa"
Mama tace "ato, Nima abinda nagani kenan, ni yanzu na tattara munirat na zubar, Ina dalili?Gara inyi zamana anan"
Cikin sauri yace "a a mama, ba za'ayi hakaba, kiyi hakuri, ni zanzo indaukoki, idan kowa yaqiki aini bazan qikiba mama"
Tace "yawwa, Gara kazo dinma, kazo ka nuna mata Nina haifeka"
Yace "angama mama"
Sannan sukai sallama, munirat ce tafado masa Arai, kina zaune gida daya da mahaifiyata Amma kikasa zuwa ki gaishe ta? Meyake damunta ne?
Agogo ya kalla karfe shadaya na safe, waya yayi atanadar masa ticket din tafiya jigawa.
Tashi yayi yafara zuba kayansa a wata yar qaramar jaka, yasan idan yaje Niger bazai iyu su barshi ya dawo a ranar ba, dole zai musu kwana biyu, daga Nan saiya taho da mama, Amma kafin Nan zaije ya kaiwa Aisha biro dakuma ribbon din daya siyo mata daga Saudia.
Saida yagama hada komai har ribbon din yana cikin jaka, sannan munirat tashigo Dakin, ganinsa da Kaya yasa ta tambayeshi, "my dear Ina zakaje?"
Fuskar sa babu alamun wasa yace "jigawa"
Ranta ne ya6aci jin inda zaije, gashi bataga fuskar yimasa ihu ba.
Gaba daya ya tamke fuska kamar ma haushinta yakeji, Shikuwa Shahaab abinda tayiwa mama ne yasa yake jin inda yana duka Toda ya rufe munirat da duka yau, da niyya yaqi 6oye mata inda zaije, saboda yasan ta tsani yaje jigawa, yarasa dalilin ta akan hakan.
Ko Kallan inda take baiyi ba yafice yabar mata Dakin, yana fita driver yadaukeshi, Biron Dayayi order Nan suka fara zuwa ya Kar6a, sannan yawuce Airport, basu dade da zamaba jirginsu yatashi, har yanzu jin ransa yake adagule, Bayan jirginsu ya sauka wani driver ne yasake kaishi hotel, Sai Bayan yayi wanka ya huta ne sannan yayi order abinci, spoon biyu yayi, yaji abincin babu teste, tureshi yayi, sannan yafada kan gado yakira Ramadan kozai bashi shawara akan abubuwan da munirat takeyi akan mama,Amma wayarsa akashe.
Dafe Kansa yayi, yarasa meyake masa dadi, Aisha ce tafado masa, ahankali yasake daukan wayar Yakirata.
Bugu daya, Hajja ta dauki wayar,batayi magana ba yaji tana cewa "ke ungo wannan wayar, inajin inusa ne, dankare da shegiyar rowa, har yanzu baikawo miki kudin barka da sallah ba, tayaya ma zan dauke ki nabashi?"(🤔)
Bakinta ta turo gaba, cikin shagwa6a tace "Kai Hajja Dan Allah, to Ina ruwanki da kudin dazai Bani? Naga baya Nan yaje dutse"
Hajja tace "oh... Ai jinake rowar samarin zamanin ce tatashi"
Cikin daki tashige, saida ta kwanta akan gado sannan tayi qasa da murya tace "Hello"
"who is Yunusa?"
Aisha tace "na'am?" alamun bata jishi ba
Cikin wani irin 6acin rai da tsananin kishi yace "nace waye Yunusa?"
Bakinta ta turo gaba kamar yana ganin ta, cikin shagwa6a tace "saurayi nanefa"
Cikin masifa yace "maaama, ni kike fadawa saurayinki ne? Waye ma yabaki damar dazaki dinga magana da maza? Waye yace ki saurare shi?"
Har yanzun bakinta yana gaba, tace "Hajja ce"
"okay kina sonsa kenan, yar qarama dake samari zasu fara zuwa wajan ki, kema Kuma har kulashi kike tunda gashinan har wayama kunayi ko?"
Tace "nito ya zanyi?"
Baqin ciki ne yasake kama Shahaab, Yakirata danya danji sauqi Amma gashi yasamu wani baqin labarin, cikin masifa yace "look... Maama You know what? Idan nasake jin kince min saurayinki ne, Sai ranki ya6aci, karatu zakiyi, babu wani aure da zakiyi, ko shekara Dari kikai babu aure bazaki Rasa mijin aure ba"
Cikin sauri tace "eh bazan Rasa ba Amma ai saide Tsoho"
Cikin sigar lallashi yace "kenan kina son saurayinki, bazaki rabu dashi ba ko?"
Murya can ciki tace "to ai Shima yana sona, Kuma yanason Hajja"
Wata irin wawiyar ajiyar zuciya yasauke, domin kuwa amsar data bashi ka kadai ta'isa yasa ya gane cewa ita din ba lalle tanason Yaron ba, duk dade bata futo fili tafada masa tana son inusan ko bata sonsa ba, lalle ya kamata yad'auki mataki akan Yaron koma waye shi, bazai iyu yana abota da yarinya wani Kuma daban yazo yana soyaiya da'ita ba, a ko'ina abota gaba take da soyaiya 🙄🙄
Ahankali yace "kina gida ne?"
Tace "um..."
"Anjima zanzo, kibar wayarki awajanki,"
Tace "to"
Har zai kashe, saiyace "fishi kike Dani?"
Cikin shagwa6a tace "nifa ba fishi nake ba, bakaine ba kake tamin fada..." tana fadar haka Sai kuka
Dafe Kansa yayi, cikin qasa qasa da murya yace "shikkenan to yi hakuri, nadena, shikkenan?"
Tace "eh, saikazo"
Kashe wayar yayi, yana mamakin yanda kuka baya mata wahala, kamar wanda take zaune cikin tsofaffi, kokuma yarintace take damunta waya Sani.
Allah Allah yake dare yayi yatafi, jiyake kamar yana kan qaya, dazaran yatuno da maganar Yunusa Sai yaji sabon 6acin rai acikin zuciyar sa, wata zuciyar tace tokai menene abun damuwa tunda ba sonta kake ba? A fili yace "Bana sonta, Amma duk da haka ai tayi qanqanta da soyaiya yanzu"
Haka yadinga zirga zirga yakasa zaune, yakasa tsaye, dare nayi, yad'auki hanyar garinsu, tun kafin a shiga sallar ishsha'i yaje Garin, inda yasaba ajiye motar sa anan yayi parking yauma, Kiran wayarta yayi, wayar na hannunta, tana dauka tace "Gani nan"
Wajan Ummah taje, saboda Hajja tafita gidan qawarta jummai, cikin nutsuwa tace "Ummah zanje gidansu Walida na kar6o saqo nadawo"
Ummah tace "karki dade, kinga dare yayi"
Tace "to Ummah, sannan tafuto, a kofar gida taci Karo da Hajja, tace"Hajja natafi gidansu Walida yanzu zan dawo"
Hajja tace "konazo narakaki?"
Cikin sauri tace "A a nayafe"
Hajja ta wuce cikin gidan tana mita, Aisha kuwa Kai tsaye wajansa ta nufa, yauma dakansa yafuto yabude mata motar, sannan tashiga yarufe, Shima yashiga ya zauna tareda rufe motar, kanta aqasa tace "Ina wuni"
Cikin wata irin murya yace "maama"
Tace "um"