← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 71

Sashe 63

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi yayi Shima sannan yakamo hannunta suka futo dayan hannunsa d'aukeda wata yar qaramar jaka dasuka taho da'ita.

Kasancewar saukar dare sukayi basu fita ko'inaba, wanka sukai sukaci abinci sukai sallah, sannan suka kwanta, harta fara baccin Nata taji shi yana lalubeta, haka tayi haquri tabarshi yayi abunsa, Amma ta tabbatar yanda yake wannan kururuwar jin dadin dole Dakin dake kusa dasu zasu jiyo su.😲🙊

Suna gamawa zazza6i Sabo ya rufeta Sai karkarwar Sanyi take,ya dauketa suka shiga toilet yana fara yimata wanka tafara kwara amai Mai ban mamaki, so Sai take amai duk ta fita a hayyacinta har hakan ya tsorata Shahaab, daqyar suka gama wankan, suka dawo d'akin har zuwa lokacin karkarwa jikinta yake har idonta yayi jajir,jikinta yafara goge mata da ruwa har zazza6in yafara sauka, can Kuma bacci ya dauketa, Sai Alokacin yasaki ajiyar zuciya sannan yazuba mata ido yana Kallonta, a wannan dare Shahaab bai runtsa ba, yana zaune yana gadinta Sai gyangyadi dayake yana daga zaunan.

Sassafe suka nufi Asbiti Bayan angama yimata gwaje gwajen komai suka bata gado aka daura mata ruwa, shikuma Dr. Yakira Shahaab zuwa office dinsa, Bayan sun zauna cikin farinciki yake sanar dashi matarsa tana d'aukeda cikin wata biyu.

Cikin farinciki Shahaab yad'ora hannunsa akansa, ya hargitsa sumar Kansa tareda fadin"wayyo Allah na"😂

Sai yayi qasa yayi sujjada yana qara godewa Allah, sannan yadawo kan kujera ya zauna, Dr ya kalleshi da mamaki yana tambayar sa bai ta6a haihuwa bane? Kai tsaye yabashi labarin tsawon shekarun daya dauka yana neman haihuwar, daga qarshe yake fada masa yasake duba Aisha dakyau kode cikinne yasa kwata kwata batason sex, ga yawan bacci, sannan Kuma idan sunyi sex din tana amai.

Murmushi Dr yayi yana yimasa qarin bayani akan duk alamomin cikin ne,duk lokacin datake baccin abarta tayi baccin ta, amai Kuma bazata daina ba saide in cikin ne ya danyi qwari, Amma zata rage yi idan sukayi kokari wajan bata magungunan dazai rubuta musu, maganar sex Kuma cikin ne bayaso, dole zai daga mata qafa zuwa Nan gaba kadan.

Cikin farinciki Shahaab yabashi hannu suka sake gaisawa sannan yatashi yakoma Dakin da Aisha take, agefen gadon ya zauna yasaka hannunsa cikin Nata, tareda dora dayan hannun akan cikinta yana shafawa, kallon ta yake sosai kamar yau yafara ganin ta, yanzu shine yayiwa Aisha ciki? Kenan lafiyarsa kalau kamar yanda likitoci suka fada? Hawaye ne yazubo daga Idonsa, kamar zararre yafara magana shi kadai "zan zama uba, Aisha zata haifamin Dana na kaina, ya Allah na gode Maka"

Sosai yake hawaye, yasake shafa cikin Nata sannan yace"kai,in namiji ne kasani, In mace ce kisani zamu fara fada daku, tunda kunzo min da bidi'ah bakwaso Daddynku yaji dumin mommy ko? To sainayi, rigimamman ciki kawai "

Duk wannan maganganun dayake hawaye ne suke zuba daga Idonsa, cikin sauri yad'auki wayarsa yakira mama, Alokacin suna tareda Hajja, cikin rawar jiki ta dauki Kiran nasa Dama jira suke suji sakamako, yana jin ta d'auka yace"mama"

Gaban mama yayanke yafadi tace"nashiga uku Shahaab meyafaru naji kana kuka? Meyasamu Aisha?"

Cikin hawaye yace"mama Aisha tanada ciki, da gaske ne mama, mama yanzu shikkenan Nima lafiya ta kalau ko?ankusa adenamin Gorin haihuwa ko mama?"

Itama kukan farinciki tasaki, tafara fadin"Alhamdulillah, Allah abun Godia Ina Aishan?"

Kallan Aisha yayi datake bacci hannunta cikin nasa yace"gata Nan bacci take mama,mama na damu Aisha dayawa ashe cikinne baiso, Sai yanzu da Dr. Yake fadamin Nima na tabbatar dahakan"
Mama data gane inda maganar tashi tasa gaba cikin farinciki tace"baiwar Allah kenan,ashe shiyasa take tahowa Nan,kanaji na ko Shahaab, kakula da'ita sosai karka bar wani abu yasamu yarinyar Nan, kakula sosai idan angama dubata saiku shirya kutaho"

Murmushi yayi sannan ya goge Hawayen Idonsa yace"mama ko quda bazan Bari yata6a Aisha ba, babu abinda zai samu cikin Nan insha Allah"

Yana fadar haka yakashe wayar, yakira Ramadan ya sanar dashi Aisha tasamu ciki, cikin wata irin qara Ramadan yace"what? Wai Dan Allah da gaske kake?"

Cikin farinciki yace"da gaske Ramadan, yanzu haka muna India, munzo Asbiti,Ramadan ashe da Rabon Nima zanga gudan jini na kafin na mutu?"

Ramadan yace"yanzu kagane matarka tada itace bata haihuwa kenan kokuma har yanzu kaida munirat Sai Allah?"🤔

Cikin 6acin rai Shahaab yace"ni Ina cikin farinciki karka 6ata min raina malam"

Ramadan yayi murmushi yace"tuba nake oga,gaskiya duk lokacin da akai haihuwar Nan muna da Babban taro,Allah de yakaimu lokacin Kuma ya sauketa lafiya"

Cikin farinciki yace"idan kace taro ma ai daya kenan,Amin ya Allah de, Allah yakaimu lokacin lafiya,Amma kanajin abinda Dr yace saide in haqura da'ita zuwa wani lokaci Wai cikin bayason abunnan"🙊

Ramadan ya tuntsire da dariya yace"inajin ustaz ko ustaziya zamu samu, Kai kaji wani fi'ili na ciki ko?"

Shahaab yayi murmushi yace"wallahi kuwa, Toya zanyi"

Fira sukaci gaba dayi cikin tsananin farinciki yana bashi labarin abubuwan datake masa Kala Kala duk Sai yanzu ne Shima Kansa ya tabbatar cikinne yasa ta hakan.

(SHAHAAB littafin kudi ne, inde kika karanta batare kin biya ba, ban yafeba, nabarki keda ALLAH)

******

Hajja ta kalli Mama tace"cikinne ko?"

Mama ta goge Hawayen idonta tace"shine wallahi, aikuwa Bari su dawo mukuma saimu fita wata qasar afara siyo kayaiyakin haihuwar"

Hajja ta zaro ido(😳)
Tace"nashiga uku,tun yanzu?"

Mama tayi murmushi Tace"A a Gara muje,idan bamu fara siyowa yanzu ba yaushe zamu je?"

Hajja tasaki dariya tace"kai, nikam zanga wannan haihuwa taku wanne irin so za'a yiwa abinda aka Haifa, Bari inkira iyayenta in fada musu"

Tafadi hakan tana dannawa Ummah kira.

Shahaab kuwa farinciki ma hanashi komai yayi, kawai wasa yake da hannunta yana tunanin Ina zai Sakata saboda farinciki? Da ruwan yaqare shine yacire mata, tayi bacci sosai, tana tashi ta ganshi a zaune yana zuba mata murmushi, addu'ar tashi daga bacci ta karanta idonta akansa,tace"Uncle karfe nawa kuwa, da alama na Dade Ina bacci kuma banyi sallah ba, inaso inyi sallah "

Tafadi hakan tana qoqarin tashi, cikin jin dadi yace"Bari nakai ki toilet kiyi alwala"

Cikin sauri Tace"A a zan iyafa, banajin zazza6in yanzu, kalau nake Jina"

Yace"A a, banaso ki wahala, Baby na ya wahala, zan kaiki"

Cikin mamaki tace"Baby Kuma?"

Murmushi yayi sannan yace"sosai,Dr yace namiki ciki har cikin yayi wata biyu,ashe Nima zan iya yiwa mace ciki da gaske?"🤔😂

Fillon dake gefenta ta d'auka tafara dukansa dashi yana karewa yana dariya,cikin farinciki yariqe Fillon yace"to karya nayi? Nine namiki ciki, kema kin kusa zama uwa, kidinga Bawa babynmu nono,mudinga yimasa wasa, Shima yayi mana.... Saime kekuma kike so?"

Cikin shagwa6a tace"Uncle..."

Hannayenta yariqe yace"nagode Aisha,Allah yasaka da alkhairi, Allah ya saukeki lafiya,Aisha mezan baki a duniyar Nan Wanda zaisa kiji dadi?"

Ahankali tace"zuciyarka Uncle"

Idonsa ne yakawo ruwa, lokaci daya hawaye ya zubo daga Idonsa, Kallan ta yayi yace"nabaki, kin Riga kin sameta, har abada takice, babu Wanda zan yi fatan nasake Bawa Bayan ke"

Cikin sauri ta rungume shi, tafara bubbuga bayansa alamun yayi shiru.

Bayan kwana uku suka dawo Nigeria, afalon mama suka Yada Zango, Aisha Sai ciye ciye take itace rake, itace d'ata, saikuma alale irin wadda takeso, Shahaab kan yanzu komai tayi, tadena bashi mamaki, mama kuwa ta Rasa inda zata saka Aisha taji dadi, a ranar takira Hajiya zaliha take fada mata matar Shahaab tasamu ciki, saita shirya zasu fita siyo kayan Baby, acikin satin kuwa suka tafi China itada Hajja dakuma Hajiya Zaliha, saida sukai sati biyu sannan suka dawo niqi niqi da Kaya harda su keken Hawa na Yara.😲

Har zuwa sati ukun Nan Shahaab bai nemi Aisha ba, ita kanta tasan cewa ba qaramin so yake wa wannan cikin ba, inbanda ciki waye ya'isa yahana Shahaab wannan abun?🤔
Sosai ta Jinjina masa, kwata kwata ya kauracewa saka turare saboda ita, yadena kusantarta, bashida aikin komai sai Wanda zai sata farinciki, tsananin kulawar dayake bata ne yasa tasake jin soyaiyar sa tana sake shiga ranta.

Yau satin su hudu da dawowa daga india, watan cikinta uku, daga Saman mararta kuwa ciki harya fara tasawa,tunda Shahaab yaga haka, yahana Kansa sukuni, bata Isa ta kwanta rub da ciki ba zai fara fada, murmushi kawai take tarabu dashi da gyara kwanciyar Tata.

Yau da daddare Bayan sunyi shirin bacci ta kalleshi taga duk jikinsa yayi Sanyi, Idonsa yayi jajir kamar marar lafiya, Kallonsa tayi tace"Uncle lafiya?"

Cikin wani irin yanayi na buqata ya kalleta yace"maamah....inashan wahala, natara dayawa maamah, ni wannan wasan Bana jin dadinsa kamar dayan"

Ajiyar zuciya ta sauke tace"yanzu fa lafiya ta kalau Uncle, idan zakayi kazo kayi, ni banajin komai yanzu"

Cikin kulawa ya kalleta yace"a a, kirufamin asiri maamah, Dr yace cikin ne bayaso, idan Kuma nayi a kazo aka samu matsala fa? Inason cikin Nan kamar raina maamah, banason abinda zaisa yasamu matsala ko yar kadan ce"

Cikin tausayawa tace"to yanzu haka zamu zauna?"

Yace"zan tambayi Dr tukunna, idan naji na gamsu da bayanin nasa Sai muyi"

Tace"to Allah yasa mudace"
Ta kwanta rub da ciki abun ta tafara bacci, Shikuwa yana zaune yana aikin tunani, yana juyowa ya ganta ta kwanta akan cikin, aikuwa da gabansa yafadi, cikin sauri yace"maamah!, maamah tashi mana, wacce irin kwanciya ce wannan?"

Tashi tayi, ta gyara kwanciyar Tata, ta kwanta akan hannunta nadama, Sai a lokacin yasaki wata irin ajiyar zuciya, sannan ya matsa kusa da'ita Shima ya kwanta(😂)

Cikin dare tana tsakar bacci taji shi yana fadin"maamah!"

Ahankali ta bude idonta kadan tace"na'am Uncle"

Yace"tashi ki gyara kwanciyar ki,kar Babyn Nan yasamu matsala tunda kika kwanta yanzu karfe biyu ko juyi bakiyi ba, gyara kwanciyar ki"(🙆🏻‍♀️)

Babu musu ta sake juyawa ta kwanta akan hannunta na hagu tana mita acikin ranta, sunci gaba da bacci gab da Asuba yafarka ya Kalle ta sannan yace"maamah!"

Tace"Um Uncle"

Yace "tashi kidan gyara kwanciyar ki, maamah tun dazu fa Dana tasheki Ahaka kike"

Runtse idonta tayi😖😖, sannan ta bude, ahankali tatashi zaune, tasaka hannunta ta kunna fitilar gefen gadon, sannan tace"Uncle"

Yace"na'am"

Akaro na biyu tasake cewa"Uncle"

Yace"Na'am maamah"

Akaro na uku tasake Kallonsa tace"Uncle"

Yace"Na'am"
Chapter 63 · 0% Book details