Sashe 51
Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tace"may be saboda rashin lafiyar kane,wacce qasa zamu tafi ne nida Hajiya Zaliha, saboda hado kayan lefen takwara?"
Kafadunsa yadaga yace"duk inda ya muku mama, na tambayeta tace na Nan qasar takeso"
Mama Tace"A a, bazai iyuba, saide asiyo komai acan abunda babu Kuma Sai Asiya anan din"
Yace"toshikkenan Allah yakaiku lafiya"
Kafin tayi magana momy tayi sallama cikin falon itada munirat, lokaci daya Shahaab yature hannun mama datake bashi farfesu, fuskarsa ta sauya,yanda kasan bai ta6a yin dariya ba haka yakoma, yad'ora kafa daya Kan daya, yad'auki computer sa yaci gaba da aikin dayake, ganinta ne yasa gaba daya yaji komai yafita daga ransa
Mama ta Kalle su Bayan sun qaraso tace"sannunku da zuwa"
Momy tace"yauwa Hajiya Aisha, Ina wuninmu?"
Cikin sakin fuska mama tace"lafiya kalau Alhamdulillahi" ta kalli munirat da kanta ke qasa tace"munirat?"
Cikin sauri tace"ina wuni mama"
Mama tace"lafiya kalau munirat, Kuma yanzu munirat dankun samu Sa6ani keda mutumin naki saiki tafi gida maimakon kizo ki sanar Dani?"
Munirat ta daga Kai ta kalli Shahaab, taga Hankalinsa yana kan computer ko kallon inda suke baiyi ba,Sai taga yaqara yin wani kyau yakoma kamar bashi ba, yanda ya daure fuska kad'ai yasa taji wani irin kwarjinin sa yashige ta, cikin sauri tayi qasa da kanta
Momy kuwa baqin ciki ne ya kamata, banda munirat tana son Yaron Nan babu abinda zaisa tazo gidannan, idan dukiyar ce ai sun samu abinda suka samu a qarqashin sa, yanzu saboda Allah a matsayin ta na mahaifiyar munirat yadaga Kai ya kalleta ma ya gagara, bare tayi tunanin samun gaisuwa,ajiyar zuciya tayi tace"Hajiya Aisha ayi hakuri Dan Allah,kinsan halin 'Dan yau, ka haife shi baka haifi halinsa ba,ni nafi tunanin anshiga tsakanin Mahmoud da munirat ne, banda haka yanda yarannan suke son junansu yaushe har Mahmud zai iya sakin munirat,tunda yafara neman aure de kema kinsan iyayen yarinyar bazasu zauna ba, dole zasu shiga su fita domin araba Mahmud da matarsa,abinda yaji tana waya akai Kuma asalin abun ma badake take ba, da wata mata take,tana so tad'auki nauyin wani film na ita matar, saboda haka ga yarinya Nan nadawo da'ita, yayi hakuri ya maida ta dakinta tunda akwai sauran igiya guda daya"
Mama ta kalli momy tace"Wato Hajiya zan'iya daukar komai akan baqar magana Amma banda cin zarafin qawata, wannan yarinyar da Shahaab yake nema jikar qawata ce danayi shekara da shekaru Ina nemanta, kinga kuwa ni nake da alaqa da Aisha,nasan halin qawata, batasan ma akwai malaman tsubbu a duniya ba bare taje tasa araba Mahmud da munirat, koba wannan Bama bai kamata kice Wai anshiga anfita tsakanin sa da munirat ba,wannan kamar daukan haqqi ne tunda ba Gani kikai da idonki ba"
Munirat ta kalli mama cikin sauri, dama Aisha jikar qawar mama ce? Qawarta datake 6ata ran Shahaab saboda ita,? qawarta datake sa ta ajiye soyaiyar datakeyi wa Shahaab tayi masa cin mutunci saboda yaqi Nemo mata ita? Inhakane Kam dole ran mama ya6aci, tunda akan wannan qawar Tata harta iya 6ata ran danta na cikinta, to kuwa babu ran Wanda bazata 6ataba, cikin 6acin rai momy tace"to Hajiya Aisha menene laifi danna fadi haka?ranar wanka ba'a 6oyon cibi, yakamata ki fadi abinda yake ranki Kai tsaye, Nima na fadi nawa inyaso asan inda za'a Nemo maslaha, Munirat fa ta fadamin komai, tacemin tun farko kece kika daure masa gindi yanemi yarinyar,ni Ina ganin dama can kin Riga kinsan jikar qawar kice, shiyasa qarfi da yaji saida kikasan yanda kikai kika cusa masa ra'ayin yarinyar, Kuma wannan de ba soyaiya yake mata ba, sha'awar ta yake, banda haka Yaya za'ayi ace daga ta6a nonon yarinya shikkenan saiya dage saiya aure ta,? soyaiya guda daya ce, Kuma ita Mahmud yakewa munirat sannan...."
Bata qarasa maganar datake ba Shahaab yayi jifa da computer sa dake kan cinyarsa, cikin 6acin rai ya kalli momy sannan yafara kokarin tashi tsaye, cikin sauri mama tasa hannu ta riqe shi, tajashi yakoma kan kujera ya zauna, munirat kuwa hawaye tafara ganin yanda momynta ta lalata komai, cikin sauri itama ta riqe hannun momynta.
Cikin 6acin rai momy ta kalli Shahaab dayake huci tace"fitsararre dukana zakayi ne?idan ma bazaka maida ta dakinta bane menene abun tasowa haka kamar hayaqi zaka iyo kanmu? sanin kanka ne munirat haqurin zama take dakai, meza'ai da namiji juya, marar haihuwa?a wannan lokacin shekara biyar tayi yawa zaku rabu saboda rashin haihuwar ka, Amma haka ta zauna dakai shekara da shekaru duk da tasan baka haihuwa, Amma ita kowa yasan gadon haihuwa tayi,ai rufa Maka asiri take, kaje ka auri yarinyar kagani idan zata Iya zama dakai Ahaka baka haihuwa"
Hannunsa ya dunqule waje guda,yarasa meyasa mama ta riqe shi, yaso ta rabu dashi da tuni labari yasha bam-bam,wayar sa yadauka yayi danne-danne sannan yayi jifa da wayar.
mama ta runtse idonta cikeda dacin zuciya sannan ta kalli momy tace"kingama?"
Munirat ta Fashe da Kuka tace"momy kin 6atamin komai, inason Mahmud momy Amma kinzo kin rusamin farinciki na,mama Dan Allah kiyi hakuri sharrin shaidan ne, Dan Allah mama ki hanashi auren Aisha, wallahi nayi alqawarin zan gyara komai, zanyi masa duk abinda yakeso, Amma Dan Allah mama karki barshi ya auri Aisha, wallahi banason ganin da Aisha, saboda Ina ganin tane a matsayin wadda tashigo cikin rayuwar mu tayi mana katangar qarfe nida Mahmud"
Mama ta Girgiza kanta ta kalli momy tace"idan kun gama zaku iya tafiya,Mahmud de d'anane, to bazai maida munirat ba tunda babu dole, Kuma kusa aranku INSHA ALLAHU Sai kunga 'ya'yan Mahmud da idanunku"
Kafin momy tasake magana sojoji guda biyu suka shigo bisa umarni Mahmud, kallansu momy sukai daya daga cikin su Yace"Hajiya please go out"
Cikin sauri momy ta Kalle su, sannan ta kalli Mahmud, Shikuwa Mahmud baice komai ba, dayan sojan yakai hannu yana kokarin ta6a momy yana fadin "idan bazaku fitaba zamu iya fita daku"
Cikin sauri munirat tafice tana share hawaye, momy ma tabi bayanta tana d'ura ashar.
Saida yaga fitarsu sannan yahade hannayensa waje daya, yad'ora goshinsa akan hannun nasa daya hade, mama tasaki ajiyar zuciya ta kalleshi tace"wannan dalilin ne yasa naso tun farko ka qara aure matarka ta haihu akan idon munirat Sai tasan cewa lafiyarka kalau itace juya, to soyaiya ta rufe Maka ido kakasa gane Ina na dosa, banda rashin mutunci kije ki fadawa mahaifiyar ki qarya da gaskiya sannan kizo Nan kinamin kuka inyi haquri?, inda ace Aisha ta bayyana da wuri wallahi da ko zaka mutu ita zaka fara aura,nasan cewa nida Aysha mun wuce qawaye saide yan'uwa, danhaka koda jikar ta tayi Maka Gorin haihuwa kanta tayiwa tunda kun Riga kun zama daya"
Jin yayi shiru ne yasa takai hannu tata6ashi, yana d'ago Kansa taga hawaye yana zuba A'idonsa,(🙆🏻♀️)
cikin sauri tace"subhanallah...."
Sannan tamatsa kusa dashi tajashi jikinta tana bubbuga bayansa alamar lallashi, Sai Alokacin yasaki wani irin kuka mecin rai, sosai yake kuka harda shashsheka,cikin sigar lallashi mama tace"menene abun kukan Kuma?"
Cikin kuka yace"mama da gaske ni juya ne Bana haihuwa ko?da gaske itama Aisha zata gujeni saboda rashin haihuwa ta?zatace narabu da'ita ko mama?" ya qarasa maganar cikin hawaye
Cikin sauri tajashi jikinta ta rungume shi sosai, saboda gaba daya ya karya mata zuciya, batasan lokacin dataji qwalla tacika mata idonta ba, cikin sauri tasa hannu ta goge, sannan cikin lallashi tace"mahmuuuud" taja sunan nasa, sannan taci gaba da cewa "waye yace Maka baka haihuwa?ni lafiyar Dana kalau,kana haihuwa, idan ka auri Aisha zata Haifa Maka Yara dozin-dozin,insha Allah kunayin aure Aisha zatasamu ciki, shiyasa nake baka maganin Sanyi ai, akwai sanyin dayake Hana mutum haihuwa, idan ma kanada shi maganin zai taimaka Maka wajan warkewa Sai kaga andace,kayi hakuri kadena kuka kaji?"
Tafadi hakan cikin lallashi
Cikin sauri ya Girgiza mata Kai sannan yazare jikinsa daga Nata yace"to mama kibani maganin zansha ,jiya ma baki Bani ba"
Murmushi tayi tatashi tad'auke masa computer tarufe ta, sannan ta wuce kitchen tafara hada masa maganin tana dariya, yau Gori yasa Shahaab dakansa yana neman magani, Amma ranar data bashi har wani yamutsa fuska yake shi ala dole bayason shan maganin, abinda bata saniba shine wannan maganin na qarfin maza data bashi shine yasa yake yatsina fuska, saboda shi yasan cewa yanzu hakama da qarfin sa🙊🙈
asalima tun munirat tana d'akin ta idan yayi kwana biyu zuwa uku bai nemeta ba Tofa suna haduwa babu sauqi, akan irin haka har taimakon Dr. yanema, to Amma Kuma ita mama bata Sani ba, gashi Sai sake d'ura masa maganin take, tana sake tunzurashi(🙈)
Maganin takawo masa na sanyin,babu musu yadauka ya shanye, cup din ta dauke sannan takai kitchen Sai gata ta dawo da tsumi, shima bashi tayi, saida yayi kamar zaiyi kuka sannan ya Kar6a Badon yaso ba, yashanye, mamaki yakama mama, hakan yana nufin maganin tsumin datake bashi shine bayaso, to meyasa bayaso? Wata zuciyar tace Gara de yasha koma lafiyarsa kalau, yanzu yanzu aka gama yimusu Gorin haihuwa, Gara ta tsumashi dakyau yanda zai dinga aiki babu kama hannun yaro, duk da tasan cewa yawan yin wannan abun bashine yake kawo cikin ba.
(banyafewa wadda ta karanta min littafi na free ba)
******
Da daddare yana kwance a falon dake part dinsa, kallo yake yana Dan daddana waya, yayinda yad'auki fillon kujera yad'ora akan cikin sa, kiran wayar Hajja yayi,Bayan sun gaisa yace"maamah bata kusane?"
Hajja tace"Aisha nasani ba maa-mah ba, shegen iyayi da kwainane ku ala dole Yan zamani bazaku kira sunayen ku ba,ina uwar taka? Bata wayar zanyi magana da'ita"(😂)
Kwanciyar sa ya gyara yace"kikira layinta mana, ni banida Kati bazaku cinye min sauran na cikin ba,magana nakeson yi da maamah"
Hajja tace"to Bari kaji inzaka ce Aisha ma kafada,bata Nan tatafi dutse, bansan Kuma ranar da zata dawo ba,inta dawo ma bazan bata wayar ba saboda damuna kuke Kuna hanani bacci"
Cikin sauri yace"tatafi dutse?Kuma kika Barta tatafi bata kirani ta tambayeni ba?"
Cikin sauri itama tace"andaura auren ne?Shahaab kafita daga idona in rufe, inbansa andaga auren Nan ba kace niba Hajja A'i bace"
Cikin sauri yace"shikkenan, ni Allah yabaki haquri saida safe"
Cikin sauri yakashe wayar, yasan Sarai zata Iya aikata wa, Gara yakashe wayar yabarta da hatsaniyar ta.