Sashe 19
Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Acan gidansu mama kuwa hidima tayi yawa, kamar Wanda ake dan qaramin biki, mama tana zaune tana ganawa da mutane masu zuwa yimata barka da sallah, kudi ne masu yawa agefen Dan qaramin fillon kujerar datake Kai, duk Wanda ya tsugunna ya kwashi gaisuwa idan yatashi tafiya haka zata dauki kudin tabashi, Shahaab kuwa bata ganshi ba, tasan yana can waje yana Fama da nasa mutanan, abinci ma bai samu damar zuwa yaci ba, Kuma tasan munirat bata nemeshi akan hakan ba, to itama dasuke zaune gida daya batazo ta gaishe taba bare tayi mata barka da sallah, batasan wacce irin mata Allah yabawa Mahmud ba, kafin tagama tunanin Nata yashigo cikin falon Nata yana Sanye cikin manyan Kaya farare tas,shadda ce dataji dinki Mai kyau da tsari, yasaka babbar Riga, hatta takalmin qafarsa fari ne, yayi mutuqar kyau kamar ka sace shi ka gudu, kasancewar baya saka manyan Kaya kullum Sai suit, Sai hakan yaqara qawata kyan halittarsa, Sai tashin qamshi yake Mai dadi, yana qaraso wa kusa da'ita duk mutanan falon suka tashi suka fice, Kallan sa tayi cikin farinciki tace "masha Allah, Mahmud kayi kyau sosai, yanda kake da kyan Nan Allah yabaka kyakykyawar amarya ku haifomin kyawawan jikoki"
Inda Dane tafada masa hakan bazai ji dadi ba, Amma yanzu wani irin murmushi yayi, tana cewa kyakykyawar amarya, itace ta Fado masa, baisan Ina yarinyar ta kwaso kyau irin haka ba, saikace aljana, cikin murmushi yace "Amin mama, dafatan kinyi sallah lafiya"
"Alhamdulillah Shahaab, ya munirat? Tayi sallah lafiya?"
Cikin mamaki ya kalleta "kamarya? Batazo bane?"
Tace "a a, nida ba nice na haife ta ba, Yaya za'ayi tazo ta gaishe ni, Amma nasan idan mahaifiyar ta tana cikin gidannan bazai iyu a kwana atashi, taqi zuwa ta gaishe ta ba"
"mama kiyi hakuri, zanyi mata magana"
"a a, rabu da'ita, inda Sabo ai yaci ace nasaba da halin munirat, dama kaina ke jira, inaso kasiyomin ticket,gobe zanje marad'i ganin dangin babanka, idan zakaje Kuma saika siyo mana mutafi"
Cikin sauri yace "a a mama, kijeki, ni jigawa zanje"
Cikin mamaki tace "jigawa Kuma?"
Sai yanzu ne ya gane irin Shirman Dayayi, cikin sauri yasake cewa "Eh... Eh.... Ina nufin akan aikin gidan marayun Nan"
Ajiyar zuciya ta sauke tace "to Alhamdulillah, nayi tunanin wani abun ne yataso"
Ahankali yace "a a, Amma mama kwana nawa zakiyi kidawo? Kwana uku yayi?"
"haba Shahaab , har yanzu de kana Nan da halinka bakason inje unguwa in zauna? Kwana biyar nakeso nayi, idan kajini shiru Kuma to sati daya zanyi"
Cikin ladabi yace "to shikkenan mama, Allah ya dawomin dake lafiya,saimu fita goben Nima gobe nakeson wucewa"
Tace "Allah yakaimu, tashi muje nabaka abinci"
Babu musu yatashi suka nufi dinning
Bayan yagama cin abinci fita yayi daga gidan, baije part dinsu ba Sai Bayan ya dawo da daddare, baiyi wa munirat maganar mama ba, yasan Bayan fitarsa zataje su gaisa, abinda bai saniba kuwa shine mama ko idon munirat bata Gani ba, washe gari karfe goma suka shirya shida mama suka tafi, Bai fadawa munirat inda zaije ba, yadai fada mata cewa sunyi tafiya shida mama, mama tayi tunanin Dasafe kafin su tafi munirat zatazo, shiru shiru bata zoba harta fidda rai, haka motoci guda biyu suka rakasu Airport, mama ta wuce Niger, shikuma yawuce Jigawa.
Wannan Karon ma a hotel ya sauka, tunda yamma yake shirin tafiya wajan ta, Amma idan ya tuna maganar Ramadan cewa akwai Wanda suka sanshi agarin, Sai yaji wani irin taqaici,yanason yaganta dawuri kodan yasata agaba yadinga kallonta harya gaji, shi Kansa yarasa meyasa yake murna da zumudin zuwa wajan ta.
Da daddare wata shigar yasake kamar ta jiya, manyan Kaya yasaka harda babbar riga, saide jiya shigar fararen Kaya yayi, yau Kuma light blue ne, shi Kansa daya kalli Kansa a madubi saida ya jinjinawa Hajja data iya auren kyakykyawan babansa Dan Nijar har Allah yasa Shima ya'iyo kamar baban nasa, saikuma yayiwa Allah godia bisa ni'imomin Dayayi masa, turare yafara fesawa kamar wani sabon ango, sannan yasaka face mask,yafuto a gurguje yashiga motarsa, rabonsa da driving harya manta, Sai yake jin wani irin nishadi a ransa, yana tafiya ahankali yana Sauraron yanda gidan Radio suke labarai na gaishe gaishen sallah, Ahaka harya qarasa cikin Garin, yau Garin yaga Yacika da mutane Kuma ga manyan motoci Nan alamun duk wasu wanda basa zama agarin ma sunzo gida bikin sallah, a'inda suka tsaya rannan shida Ramadan yauma anan yayi parking, face mask dinsa ya danja qasa, sannan yad'auki wayarsa yafara Kiran number ta, saida yaji tashiga sannan cikin ransa yace "yanzu da wayar akashe take Yaya zanyi? Ahankali yasake cewa" Sai inje gidan inyi sallama idan mungaisa dasu infada musu wajan yar qarama nazo"(🤭)
Saida wayar takusa katsewa sannan yaji an dauka, ahankali kamar Wanda yake rad'a yace
"inajiranki a kofar gida"
"waye?"
Shine abinda tace, cikeda tsananin mamaki
Kai tsaye yace "SHAHAAB"
gabantane yafadi harsaida tasa hannu akan qirjinta, idan bata manta ba mutumin dayazo da Azumi yakawo musu kayan abinci har yace mata shi Yaron Mahmud Wakili ne, shine Shahaab, toba rannan yazo ba? Meya dawo yi wajan ta?
Kafin tagama tunani taji yace "I'm waiting for you"
Sannan ya katse wayar, ahankali ta dauki dogon hijab dinta Wanda yazo mata har qasa,haka tafuto daga d'akin kamar kazarda qwai ya fashewa, Ummah na banda ki danhaka ta kalli Hajja tace "Hajja inada baqo a kofar gida, zanje wajan sa daga Nan natafi gidansu Walida, yanzu zan dawo"
Hajja zuciyar ta daya tayi tunanin Inusa ne, Kai tsaye batare da tantama ba tace"ki gaishe ta"
Tana futowa qofar gida ta hango motarsa, Kai tsaye wajan ta nufa, tana zuwa ta Qwanqwasa masa glass din motar, ahankali ya sauke glass din, yana ganinta gabansa yafadi, cikin zuciyar sa yace "yasalam!"
Sannan yabude motar yafuto, ganin wajan babu mutane sosai yasa yakama hannunta yajata ta dayan site din, samun Kansa yayi da bude mata motar, sannan yasaki hannunta ya kalleta tareda nuna mata cikin motar yace "Bismillah"
Kallan sa tayi,tana mamakin yanda Babban mutum dashi Amma yake bude mata mota, yakamata ace tatakawa mutumin Nan birgi akan yanda yake riqe mata hannu kamar wata matarsa, kallansa tayi wata zuciyar tana hanata shiga, Amma ganin shi din Babban mutum ne, a shekaru ma zai iyayin na Abban ta, Saitayi Bismillah tashiga, rufewa yayi, sannan ya zagaya yashiga shima ya zauna tareda rufo motar, juyowa yayi yana fuskantar ta,Kallan ta yafara kamar zai had'iyeta, fuskarta babu kwalliya Amma saiyaga tamasa kyau sosai, cikin ransa yace "yar qarama Kyakykyawa".
Aisha kuwa jitayi motar wani irin sanyi, ga qamshi yana tashi, ahankali ta kama yatsun hannunta tana wasa dasu, kanta yana qasa, ko kadan takasa kallansa,wani irin kwarjini yayi mata musanman yau data ganshi cikin manyan Kaya, tana ganinsa ta Qasan idonta yanda ya zuba mata Ido kamar yanason Gano wani abu a fuskarta, Itakam tana zaune ne, Amma azahiri gabanta faduwa yake, saboda bata taba shiga mota mekyau irin wannan ba tunda take a rayuwar ta, acikin motar ma Kuma da wani namiji, ganin har yanzu yakasa yimata magana yasa tace "Ina wuni"
Saitaji yayi shiru,ahankali tad'an d'ago kanta ta kalleshi tace "Ina wuni"
Cikin sauri ya dawo hayyacinsa, ajiyar zuciya yasaki sannan ya gyara zamansa, ya kalleta cikin qasa-qasa da murya yace "Lafiya"
Daga Nan babu Wanda yasake magana, kusan minti takwas shiru, taga babu abinda yace, Sai aikin kallonta kawai yake,ahankali ta motsa d'an qaramin lips dinta tace "zan'iya tafiya?"
(tab! yaufa Ana zance anan😍🤣😂)
Amnah El Yaqoub ✍🏻
Page 21&22
Cikin sigar rad'a yace mata "meyasa?"
"gidansu Walida nakeso naje Dama, inaso ta rakani shago"
"what will you buy?"
Kai tsaye tace "biro"
Mamaki ne ya kamashi, gata de yar qarama, Kuma tatashi acikin qauye, Amma tana danjin Dan qaramin turancin dayake mata, samun Kansa yayi da cewa "muje na rakaki?"
Cikin sauri ta kalleshi, tab, Ina zata Iya tafiya dashi acikin Garin Nan, ai kowa kallon dazai mata daban, ahankali ta girgiza masa kanta alamun a a, sannan tasa hannu zata bude motar tafita, cikin sauri yamiqo hannunsa yad'ora akan Nata hannun da nufin hanata fita daga motar, juyowa tayi ta kalleshi har kusancin nasu yayi kusanci tana iya jiyo daddadan qamshin turaren dake tashi ajikinsa, ganin kamar tana tsorace dashi ne yasa ahankali cikin sigar lallashi yace "kina jin tsoro nane?"
Girgiza masa Kai tayi, ahankali yasake cewa "to meyasa kike son ficewa daga motar?"
Ahankali tace "toka matsa mana"
Wani irin murmushi yasaki, sannan yadauke hannunsa dake kan Nata hannun, sosai yayi mamakin furucin ta, ita yanzu tsoro take kartaje yayi mata wani abu, Sai maganar Tata tabashi dariya saboda shi yar qaramar yarinya yake ganin ta, babu yanda za'ayi yayi mata wani abu makamancin Wanda take tunani, yana jin nishadi atare dashine idan yana tareda ita, Sai yake ganin ta kamar wata 'yarsa, inda ace a gidansa take bayajin akwai yarinyar dazata nuna mata gata, to Amma Yaya zaiyi? Allah bai bashi haihuwar ba.
Cikin murmushi yace "Na matsa, shikkenan?"
Kallan sa tayi, taga yanda dimples dinsa suka futo, Sai taga yayi mata kyau, ahankali tace "to intafi?"
"meyasa kike son tafiya ne? Kinsan tundaga Ina nazo wajanki? To tundaga maiduguri"
Zaro idonta tayi,(😳)cikin mamaki tajuyo tana fuskantar sa batama San tayi hakan ba,tace "maiduguri? Tome kazoyi Nan Garin?"
Sosai yaji dadin yanda tafara sakewa dashi, cikin farinciki yace "wajanki nazo"
Tace "wajena Kuma?,to meyasa?"
Yace "wancen Karon nazo natafi, ban tambayeki sunanki ba, shine nazo kifada min yanzu"
Cikin tsananin mamaki tace "sunana kawai? Saboda sunana kayi wannan doguwar tafiyar? aikuwa da matarka taji dalilin zuwanka wajena, dasai tayi fishi dakai"
Cikin mamaki yace "waye yace miki inada mata?"
Tace "aikai babba ne, nasan kanada mata, da Yara"
Jikinsa ne yayi Sanyi, haka kawai saiya samu Kansa da fada mata gaskiya "banida Yara"
Cikin tausayawa tace "to Allah yakawo masu Albarka, insha Allah watarana matarka zata haihu"
"Wai waye yace miki inada aure ne? Ni banda aure, very soon de nakeson yin auren"