Sashe 4
Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama tayi kuka tayi kuka kamar ranta zai fita, har kwantar da ita akayi a Asbiti, anan ne aka Gano tana d'aukeda ciki na wata uku, haka taci gaba da Kula da cikinta,tasamu mutane amintattu suka tayata kula da dukiyar mijin Nata,kamfanin sa dasuke Nijar tasa akai gwanjon su,Alokacin da cikinta yakusa haihuwa saita shirya tatafi Saudia,acan ta haifi danta namiji kyakykyawa Mai Kama da mahaifinsa sak, ranar suna taso sakawa Yaron sunan mahaifinsa, to Amma data tuna alqawarinsu itada qawarta Aysha Sulaiman bompai, saita sakawa Yaron suna MAHMUD, mutane suke kiransa da MAHMUD WAKILI, ita kadaice bata fadar sunansa, saboda Dan fari ne, Sai take masa alkunya take kiransa da SHAHAAB.
A India yayi degree dinsa na farko, ya karanci bangaren medicine
Haka mama ta hanashi aikin asbiti duk da yanaso, ta dorashi akan harkokin mahaifinsa, kasancewar yanada hazaqa hakan yasa Nan da Nan yasan kan harkar, dukiyar Kuma tasake ha6aka,daga baya Kuma yatafi malesia yayi karatu akan harkar kasuwanci, hakanne yasake bashi damar gogewa akan harkar kasuwancin nasu,sannan ya dawo Nigeria yayi wani karatun afannin economic, daga Nan yafara aiki da hukumar efcc, yafara da matakin karamin ma'aikaci, har Allah yasa sukaga kokarin sa akan aiki dakuma jajir cewarsa,shugaban qasa ya nad'ashi shugaban hukumar, baya had'a kasuwancin su da aikinsa, aikinsa daban, harkar kula da dukiyar da mahaifinsa yabar masa Shima dabam, Kuma yana kula da hakan yana taka tsantsan akan duk wani abu dazai hada aikinsa dakuma kasuwancin sa, yana samun wannan matsayi yahadu da munirat, tanada samarinta sosai, Wanda suka sota tun tana qarama, suka Sha wahala Akanta, suka hidimta mata, Amma tana ganin Shahaab yafuto a matsayin jerin masu neman aurenta saita liqe masa, harma soyaiyar datake masa ta danne tashi soyaiyar, ta Kuma zabeshi a matsayin Wanda zata aura, acewarta yafi sauran samarin Nata nagarta.
Mama bataso yanemi yarinyar ba,taso ace yasamu yarinya da batasan waye Shiba, batasan kudinsa ba, itace zatayi masa soyaiyar gaskiya, Amma tana ganin idon munirat tasan cewa idon yarinyar abude yake akan son kudi, ta fahimtar dashi Amma soyaiyar munirat din data Gani acikin Idonsa yasa tarabu dashi ya aureta, abokan mahaifinsa suka shige masa gaba, Nan da Nan aka bashi ita, kasancewar sa Babban mutum Kuma sananne a qasar.
shekarar su Tara kenan da aure, haka Kuma a tarihin aikin nasu shine matashi na farko daya dade a matsayin shugaban hukumar, ba'a dade da dorashi ba ya auri munirat,a dadin shekarun sa a matsayin shugaba, a dadin shekarun aurensa, gaba daya shekarun sa 39, yayi aure yanada shekara talatin a duniya, Amma babu Wanda zaice yayi wannan shekarun kasancewar yanda yake motsa jiki, yake Kuma kula da jikin nasa, yasan cewa da yana candy yayi aure to tabbas da yanzu yarinyar sa kokuma yaronsa zaikai shekara Ashirin kokuma shatara,to Amma gashi har yanzu shiru babu haihuwa, Kuma yaga munirat abun baya damunta, shikuma yanason yaga yanada yaronda zai gajeshi koda ace baya Raye, kamar yanda Shima yagaji mahaifinsa.
Shahaab bai iya soyaiya ba, idan yanason mutum Tofa yana sonsa, da gaske yake saka mutum acikin zuciyar sa, shiyasa munirat tayi Kane Kane acikin tasa zuciyar, yanason mace Mai gashi, asali ma shine abinda yagani awajan munirat haryaja ra'ayin sa akanta, Bayan sunyi aure yagane gashin dokine take sakawa, maimakon ya hanata saiya qyale ta taci gaba da sakawa saboda Shima yanaso.
Bangaren munirat Kam Bahaka bane, rashin haihuwarsu baya damunta, kullum qawaye take biyewa suna kawo mata magungunan mata Kala Kala, dayawa daga cikin su batasan Dame aka hada akayi suba, kudi Kuma duk lokacin data so samu tana samu awajan mijinta, wani lokacin saita tsokano masa sha'awar sa cikin kissa zata Fashe da Kuka, yana tambaya abinda take wa kuka zata fada masa kudi takeso Kuma gashi account dinta yayi qasa, shikuma jinsa cikin wannan yanayin yasa zai bata kudade, Sannna ne zata bashi hadin Kai su Raya Sunnah yanda ya kamata
Shahaab yana yiwa mama biyaiya, tun tasowarsa yana qarami ita yake Gani, itace take masa komai,baisan mahaifinsa ba, mama itace komai nasa, tana sadaukar da Nata farincikin akan nasa, yana kiyaye duk wani abu dazai sata 6acin rai, yasan cewa Sarai batason munirat, akwai lokacin daya tambayeta meyasa batason munirat Kai tsaye tafuto tafada masa cewa matarsa kudinsa tagani shiyasa ta aure shi, sannan akwai alqawarin dasukai itada qawarta cewa zasu hada yayansu aure, Kuma yasani muddin Aysha ta bayyana Tofa saiya auri yarta inde mace ta Haifa, idan Kuma ba mace ta Haifa ba shikkenan.
Tun daga lokacin idan tasashi yayi wani kokari akai Dan agano qawarta, Sai yayi mursisi da batun, saboda bayason maganar hadin auren Nan datake yi kokadan.
Akwai lokacin data dameshi akan maganar, Amma Shahaab yaqi yayi mata binciken, tayi zuciya tafice tabar gidan a hanya kidnappers suka saceta (😂)
Saida yasha wahala kasancewar sa sannane yasa hukumar tsaro ta qasar tabashi hadin Kai har saida aka kamota daga hannunsu, tundaga lokacin ya zubawa gidansa tsaro, sojoji ne suke gadin mama, banda Yan sanda dasuke Gefe suma suna nasu aikin.
To dayaga de mama da gaske take, shine yabada sanarwa a kafafen sadarwa dakuma yanar gizo, ganin yanzu harkar yanar gizo kowa yanayin ta, shiyasa yayi tunanin za'a iya samun labarin qawar ta mama, abinda bai saniba shine Hajja A'i Kam vivo gareta itama screen din duk ya Fashe, wannan gidan ta abincin dazasuci sukeyi, bata yanar gizo ba(☹️)
To ganin haka yasa hankalin mama ya kwanta, Amma idan ta tuna qawarta, ranar haukace masa take, tun yana bata haquri harya dawo Shima yazama kamar ta, ya dinga zigata, to saita sauko su zauna lafiya.
Tsawon wannan shekarun munirat ko 6atan wata bata taba yiba, data fahimci hankalin mama dakuma shi Kansa Shahaab din yana kan haihuwa, saita shiga damuwa, akan yanda suke nuna son haihuwar, danhaka Sai take jinyar qarya, dasu amai, mama da Shahaab hankalin su yatashi, suce taje Asbiti taga likita ko ciki ne, saita kar6i maqudan kudade awajansa daga baya Sai tace ai ba ciki bane, tayi haka yakai sau uku, mama kuwa tariga tagane kawai kudin yarinyar takeso, bawai Shahaab din ne da haihuwar suka Dame taba
Tarasa Yaya zatayi, aure tsawon shekara Tara babu ciki, but ita hakan bai dameta ba saboda tana cikin daula, ko neman magani batayi, shikuma duk lokacin daya shirya yatafi Saudia Tofa addu'arsa daya ce akan Allah yabashi haihuwa, ita kuwa mama burinta guda biyu ne, nafarko taga qawarta, na biyu Kuma taga Shahaab ya haihu.
Duk juma'ah Ana bada abincin sadaka a gidan, kunu, abinci, dakuma bread tareda nera Dari biyar, wannan Kuma aikin mama ne, tana bada sadakar ne saboda Allah yakaiwa mijinta dakuma ahlinsa ladan.
Ta bangaren Shahaab kuwa lokaci zuwa lokaci yana yin tasa sadakar, Amma yafiyi lokacin zuwan azumi, yana sauke farashin kayan da kamfanonin sa suke sarrafawa domin talakawa su iya siya.
Back to story 👌🏻
******
Jigawa
Aisha ce take sallah, Hajja na gefenta tana Jan carbi, ta kalleta tace "mesunan qawa kiji tsoron Allah, wannan ba sallah kikeba, sallah batafi minti goma ba an idar"
Aisha batace mata komai ba, Sai abincin ta data Dauko tafara ci,batare data cire hijabin jikintaba, qwaine guda daya akan abincin Nata Wanda qawarta Walida tabata, Hajja taleqa kwanon abincin Aishan tace "Menene wannan nake Gani aciki?"
Cikin gatse tace "gishiri"
Hajja tata6e baki, Sannna taja bakinta tayi shiru tana kallon yanda gumi yake jiqa mata fuska, har gashin gaban goshin ta ya kwanta yayi luf-luf dashi, Amma Dan masifa Taki tacire hijabin jikin Nata, bacci ma wani lokacin da hijabi takeyi, tarasa Ina mesunan qawa tad'auki wannan dabi'ah
Wani yaro ne yayi sallama yashigo gidan yace "Hajja A'i abani kunun Aya na nera Dari"
Tace "idan Sadiya ce ta aikoka kakoma kace mata akwai kudin rannan ma"
Yaron yajuya yatafi, baifi minti biyar ba Sai gashi ya dawo, yace "Wai tace babu,bakya Binta bashi"
"au haka tace?, to shikkenan taje na rataya awuyanta, kawo Darin abaka"
Kudin yabata, Aisha tamiqe ta bude Dan qaramin fridge din Hajja tabashi kunun ayar, yatafi
Jabir ne yashigo gidan, Bai nufi wajan Ummah ba Kai tsaye rumfar dasu Hajja suke zaune yaje, ya kalleta yace "Hajja Dan Allah kisiyar min da wayar ki dubu uku"
Tace "kawo dubu biyar de saina baka"
Dariya yayi yace "wayarda batafi dubu uku ba?"
"aikuwa bazan siyar ba saide dubu biyar"
Aisha ta Kalle su tace "kawai kabata dubu ukun in taga Dama ta kar6a kokuma tabarshi"
Hajja ta yatsina fuska tace "yo Ina yaga dubu ukun ma?"
"Arziqi Aina Allah ne, Shima wataran zaiyi"
Hajja najin wannan furucin na Aisha saita Fashe da Kuka, da gudu umma tafuto daga daki tana tambaya "Hajja meyafaru kike kuka? Keda waye?"
Cikin kuka tace "nida mesunan qawa ne, nariga nadade da sanin me sunan qawa d'auka ta take a matsayin sa'arta, tunda taga ta girma tafara nono shikkenan ban'isa inyi magana ba acikin gidannan, saide in fad'a itama tafad'a,inda ace nasan haka halin yarinyar Nan yake tun farko daban Bari ansaka mata sunan qawata ba, saboda Bahaka halin qawata yake ba, saide in uwarta ce take Koya mata rashin kunya"(😂)
Ummah tanajin haka tafara hawaye, duk lokacin da fadan Aisha da Hajja zai tashi, to akanta take hucewa, Kuma ita bata Isa tahana Aisha zuwa wajan Hajja ba, Kota hanata ma Sai taje, Kuma ko tayi zuciya taqi zuwa inda Hajja take to Hajjan da kanta take zuwa sutafi
Ganin Ummah na kuka Sai hankalin Aisha yatashi, menene laifin Ummah anan daza'a ce itace take Koya mata rashin kunya, cikin 6acin rai ta kalli Hajja sannan tace "niba abinda Ummah ta take koyamin, gaba daya halin me sunana nabiyo, haka kawai antashi ansaka min sunan matarda banma santaba, qila ma tamutu" (🙆🏻♀️)
Abbansu ne yashigo gidan dawowarsa kenan daga rumfarsu inda yake aikin facin tayar mota Kota machine, kukan Hajja ne yaqaru, cikin kuka ta kalli Aisha tace "ta Allah ba Taki ba, insha Allahu qawata tana nan da ranta, Kuma tana bayyana zan tattara kayana intafi inbar miki gidan ubanki"
Abba ne ya kalli Aisha yace "ke rufemin baki anan, marar kunya kawai"
Sannan ya kalli Hajja yace "Hajja Dan Allah kiyi hakuri Kidena kukan Nan, mesunan qawarki batada Hankali yarinya ce Kidena biye mata Kuna sa'insa Dan Allah"