← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 71

Sashe 69

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace" idan kanaso fin hakama"

Cikin jin dadi yace"thank u maamah"

Yasaka hannu ya daukata suka shige toilet, sabon wanka sukayi, sannan Aisha tasake gyara Dakin suka shirya suka dawo falo Daddy yana hannun Shahaab, ita Kuma ta wuce fridge tadauko chocolate tana Sha, kallo suke cikeda farinciki gaba dayansu, harda Daddy Wanda kawai hasken TV ya zubawa ido yana kallo.

Ranar basu koma part din mama ba, itama batayi jajensu ba, tana can tareda Hajja,har dare Shahaab yana naniqe tareda Aisha, Bai daga mata qafa ko dayaba ranar.
Washe gari takama weekend yana gida, Bayan sunyi wanka sun shirya part din mama suka nufa,Bayan sunci abinci Aisha ta nufi kitchen tad'auko ice-cream roba guda ta zauna tanasha, shikuma ya amsa waya yafita, Bai dawo gida ba Sai Bayan azahar, yana zuwa yaga mama tana cewa Aisha"sakashi a jikin ki yaji dumi sosai"

Zama yayi yace"lafiya? Meyasame shi?"

Kafin su bashi amsa Yaron yasaki atishawa, mama Tace"wallahi yanzu yanzu fa kawai Naga yanata atishawa kode kun kwana da esi a kunne ne?"

Cikin sauri Aisha tace"mun kunna kam"

Ran Shahaab ne yayi baqiqqirin yace"babu ruwan esi,yanzu haka sanyin da aka dinga dura masa ne"
Yaqare maganar yana daukan Daddy yatashi yana jijjiga shi.

Mama tace"sanyin me Kuma?"

Cikin damuwa yace" mama dazu Ina shirin fita Ina kallonta da uwar robar ice-cream Sai Sha take ko tausayin Yaron Nan bataji, may be sanyin ya zuqo daga nononta"(🤭)

Mama ta jijjiga Kai tareda sakin ajiyar zuciya, taga alama al'amarin Shahaab gaba yake yi akan Yaron Nan, inajin Nan gaba saiya Hana Aisha kyakykyawan motsi saboda Daddy.

Aisha ta kalleshi tace"yanzu Uncle wannan Dan ice-cream din da Nasha shine zai saka shi mura? Bafa duka na shanye ba, Dan kadan Nasha ko mama?"

Tajuya tana tambayar mama.
Bai saurari abinda mama zatace ba yace"ungo taso ki goyashi, ai d'umin runguma yayi masa kadan, zoki goyashi idan yaji d'umin ki sosai may be yadena atishawar"

Mama ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah Kuma tanaso taga me uwar Dan zatayi (🤔😄)

Cikin sauri Aisha tace"d'azu d'azu nagama goyashi, wallahi nagaji,ka kira me aiki ta goyashi"

Cikin sauri ya kalleta, fuska daure yace"ki goyashi mana"

Dan qaramin bakinta ta turo gaba sannan tatashi ta juya masa baya, yad'ora mata Yaron tagoyashi, sannan tafara jijjiga shi, Sai a lokacin yasaki wata irin ajiyar zuciya yanemi waje ya zauna, har zuwa lokacin mama bata ce musu komai ba, tana zaune tana ganin ikon Allah, Aisha kuwa daga gaji da tsaiwa saita nemi waje ta zauna, tana dora duwawunta akan kujera Daddy yasaki kuka, Sai atishawa, gaban Shahaab yafadi, cikin sauri ya kallesu, ganin yanda yake kallonta yasa tasake tashi tsaye, tana tashi Daddy yayi shiru, falon tafara zagayawa tana Dan jijjiga shi, cikin akasi inda ta cusa towel din goyon yafuto, aikuwa Daddy yayi baya zai fad'i (😲🙆🏻‍♀️)

Ita de mama tana zaune, Amma batasan Yaya akai ba Sai ganin Shahaab tayi yayi wata irin super, Sai gashi agaban Aisha, Aisha tayi wata irin zabura ta tsorata, cikin tashin hankali yace"ki riqeshi dakyau mana,kinga kawo Shima, dama can ba qaunar goyon kikeba, kawo shi, Dan idan nabar miki Shima Zaki iya yarda shi, Kuma ko bemiki mita a ransa ba Nima sainayi"

Mamaki yakama Aisha,Kallonsa tayi cikin 6acin rai tace"tayaya zan yarda d'ana aqasa uncle?Dan Allah kadinga saukaqewa kanka damuwa akan Daddy"

Maimakon yabata amsa saiyace"waya sanima ko mintsininsa ake, yaro tun dazu daga kuka Sai atishawa"
Kallonsa tayi da sauri ta Girgiza kanta ta nemi waje ta zauna ta dora qafarta daya Kan daya tareda d'aukan remote, Shima Yaron yafara jijjiga wa,da yaga jijjigawar ba zatayi ba saiya dorashi a bayansa yafara zagaye falon da Yaron, Hajja data idar da sallah tafuto daga d'aki taga Shahaab da goyon Daddy tace"yau kaine da rainon?"

Cikin sauri yace"Hajja ruwan Sanyi ta dinga d'urawa Yaron Nan, gashinan Sanyi nema yake ya kamashi"

Hajja tasa hannu ta kar6eshi tace"kawo shi mugani"

Babu musu yabata shi, sannan yanemi waje ya zauna kusa da Aisha, mama tasaki ajiyar zuciya tayi murmushi ganin yanda suit din dake jikinsa harta fara tattarewa daga baya saboda wannan Dan goyon Dayayi, Sai wata zufa yake hadawa kamar wanda yayi tseren gudu(😂)
Ganin ya zauna kusa da'ita ko kallo bai isheta ba yasa yasake jin wani irin haushi, yasaki qaramin tsaki nanma Aisha ko juyo wa batayi ba, yasaka hannu ya fizge remote din hannunta, Sai Alokacin ta kalleshi ta kawar da kanta itama tana Girgiza qafa alamun akusa take, Hajja kuwa da batasan wainar da mutanan falon suke Toya waba saita shige daki domin shafawa Daddy man kad'e ajikinsa.

Haka rayuwar take tafiya yau dadi gobe babu dadi, Hankalinsu kwance suke rainon Daddy, idan kaga Shahaab da Aisha sun samu Sa6ani to akan Daddy ne, kokadan bayason abinda zai ta6a Yaron, mama kam idan yana wani abun saide ta zuba masa ido tana Kallonsa kawai, wani lokacin ko wankan Daddy ake haka zai zauna yadinga mita shide Adinga yimasa wankan Ahankali, haka suka dinga Haquri dashi har Daddy Yacika wata hudu, kwata kwata ba zakice Yaron watansa hudu ba saboda yana samun kulawa ga nono ga madara, uwa uba ga abincin Yara da'ake bashi, shiyasa suka fara zaunar dashi Kuma daram yake zama, Amma duk wani abu dayake gefensa inde hannunsa zaikai wajan, to yanzu zaiyi ajalinsa, kokadan hannunsa baya zama waje daya, idan Shahaab yadawo daga wajan aiki haka zai zauna akusa dashi yadinga yimasa hira kamar wani me Hankali, wasa kuwa idan yacire kayan jikinsa yadauke shi suka dinga wasa afalon saide Aisha ta jiyo sautin dariyar su, wani lokacin tayi musu vedio wataran Kuma ta dinga kallon su tanajin farinciki acikin ranta.

Har zuwa lokacin Hajja tana gidan,idan sungaji da Zaman gidan itada mama haka zasuyiwa Shahaab magana yasa a fitar dasu wani wajan Sudan Sha iska su dawo, ahankali ahankali rayuwa take tafiya har Daddy yafara rarrafe, tunda yafara rarrafe mama ta Dena ajiye wayarta aqasa, idan tea aka kawo musu saide su riqe a hannun su, baya ta6a zama shi kadai, idan kuwa aka jishi shiru babu 6arna to yasamu wani abun ne yana lalata shi, shine zakaji shi shiru, gaba daya falon mama yazama kamar falon renon Yara uku saboda yanda aka baje masa kayan wasa, haka zai zauna daga shi Sai pampers yana wasansa afalon, suma masu aikin gidan inde sunzo falo Tofa Sai sunyi masa wasa zasu wuce, ganinsu dayake yau da gobe yasa baya musu qiwa, saide in baiga wani yashigo falon ba, yanzu zai fara daga hannu yana kuka alamun yanaso a dauke shi.

Tunda Shahaab yatafi lagos Kwanansa biyu bai dawo ba, yau yana hanyar dawowa yakira Aisha yace tahada masa cake idan yazo zaici, gashi su mama basa Nan, Kuma tunda taji Yakirata yafada mata hakan tasan cewa to bayason na ma'aikatan gidan ne, ta kalli Daddy dayake wasa cikin motar wasan Yara, ta dauke shi ta goyashi suka shige kitchen tafara aikinta tana masa magana kamar wanda yake jinta, Shikuwa gwarancinsa yake ma yana saka hannunsa abaki, Bayan tagama hada komai tasaka butter da suger tana mixing tace"Daddy na d'an Albarka yau ai zaka barni in yiwa Abbanka cake ko?"

Tadauko qwai tafasa taci gaba da mixing, Hankalinta yayi kan abinda take batayi aune ba taga Daddy yaja fulawar data ajiye ya kwaro musu ita kansu, lokaci daya ta tsorata tasaki qara saboda zubar fulawar kawai taji, shikuma qaran data saki ne yasa ya tsorata yasaki kuka Kuma ya qanqame bowl din yaqi saki, baqin ciki yakama Aisha(😖).

Tunda yashigo kitchen din ya tsaya abakin qofar kitchen din yana kallonsu, sosai tayi masa kyau da goyon Daddy musanman da yaji tana masa magana kamar Dame Hankali take magana, ganin aikin da Daddy yayi mata yasa ya tuntsire da dariya yafara yimusu vedio, juyowa tayi ta kalleshi da fuskarta data cika da fulawa tafashe da Kuka, qaraso wa yayi kitchen din ya qwace bowl din hannun Daddy sannan ya kunce mata shi, kuka take sosai cikin kukan tace"kana ganin abinda yamin fa, ya 6are baki yanamin kuka kamar bashine yamin laifin ba"

Cikin jin dadi ya janyo ta jikinsa ya rungumesu gaba daya, sannan yafara kad'e mata fulawar yana lallashin ta, daqyar yasamu tayi shiru sannan yace"ai nine nace amin cake din, to abarshi tunda Daddy yahana"

Cikin shagwa6a ta kalleshi takai masa Dukan wasa a qirjinsa.

Da daddare suna zaune a part dinsu suna kallo, Sanye take cikin rigar bacci tana kallon film din da ake haskawa, agefe daya Kuma waya take da faty tana sanar da'ita ansaka ranar bikin ta, shikuma Shahaab yana zauna aqasan kafet yana aiki a computer, yayinda Daddy yake Gefe yana wasa, saida tagama wayar sannan ta kalli Shahaab tace"Uncle ansaka ranar bikin faty fa, nanda wata shida"

Hankalinsa yana kan aikin dayake yace"Allah yakaimu, Amma Ina tunanin zuwa lokacin Bama Nan ai, inaso muje umara gaba dayanmu, dasu Ummah dasu Hajja, daga Nan Kuma zamu je muga jabir"

Cikin farinciki tace"Uncle Saudia zamu tafi gaba dayanmu?"

Yace"insha Allah"

Cikin jin dadi taje ta rungume shi tasakar masa kiss tace"wayyo Allah, Amma naji dadi uncle, mungode Allah yasaka da alkhairi yaqara budi"

Cak ya dauketa yadorata akan cinyarsa yace"Amin, idan kinyi waya da qawar ki ta jigawa kifada mata Faisal yamin magana yanaso inje gidansu in nema masa aurenta"

Fari tayi da idonta tace"wai Walida?"

Kansa yadaga mata yana sake gyara mata gashin kanta, cikin jin dadi tace"zan fada mata, Bari inkirata ma yanzu"

Tafadi haka tana qoqarin tashi daga kan cinyarsa, cikin sauri ya riqeta yace"Haba madam"

Murmushi tasaki kafin tayi magana yafara waigawa falon yace"ina Yaron Nan yake ne?"

Tashi tayi daga cinyarsa tace"inaga wasa yake"

Shima tashi yayi yana nemansa, acan suka hangoshi yana rarrafe yana bin ball dinsa yanaso ya dauko ta, cikin sauri Shahaab yadauko shi suka dawo kan kujera suka zauna ya kalli Aisha yace"yazaki barshi yana rarrafe a tile maamah?"

Tace"to Uncle akan cinyata zaiyi?na'isa in Hana Daddy rarrafe?tayaya ma zan San yatafi?"

Goge wa Yaron qafa yakeyi, sannan yadora mata shi akan cinyarta yace"ki kula dashi karki sake barinsa yana rarrafe a tile please,Bari in Dauko takardu adaki"
Chapter 69 · 0% Book details