← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 71

Sashe 18

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kuka tace "yanzu abunda akemin a gidan Nan hakan adalci ne? Ni banida ikon siyo abinda nakeso kullum saide asiyo abani? Mama tayi Kane Kane akan komai nikuma anmaida ni saniyar ware"

Ajiyar zuciya yasaki, baice da'ita komai ba,Dan qaramin towel din hannunsa yad'ora a lallausar fatarsa datake shinning,saida yagama goge jikinsa sannan ya zauna abakin gadon dab da munirat

Ahankali yace "munirat... Mama mahaifiyata ce, nayi tunanin yanda na dauki momynki a matsayin uwa, kema hakane,wani lokacin rikicin mama harda na tsufa, ni abinda nasani arayuwata shine inason mama, Kuma inason duk abinda takeso, karki manta dede da second daya banta6a ganin fuskar mahaifi naba saide a photo, mama itace komai nawa, itace uwata, itace ubana, tamin gatanda ko mahaifina yana Raye abinda zaimin kenan, duk lokacin da mama ta 6ata miki rai kidauka momy ce ta6ata miki, babu yanda zakiyi da'ita, a koda yaushe inaso ne kitayani yimata biyaiya nasamu narabu da'ita lafiya.... Ta hanyar biyaiyar danake mata ne zaisa inshiga aljanna munirat, nikaina nasan wani lokacin Rikici ne kawai irinna mama Amma a hakan nake goyon bayanta Dan in rabu da'ita lafiya, Amma ke kin kasa gane hakan, idan momy ce ta zazzageki wazaki kaiwa qara? Babu Wanda Zaki fadawa saide ma kibata haquri, to inaso kidauki mama kamar momy, idan kikamin hakan kingama min komai munirat.... "

Jikinta ne yayi Sanyi Bayan tagama Sauraron kalamansa, lokaci daya ta sauya kukan Nata ya dawo na kissa, cikin wani irin Salo tace"ainima Bahaka nake nufi ba, Ina kuka ne akan irin wariyar da mama take nunamin, yanzu wannan kayan waye zai dinka min insaka su jibi? Ai Yanzu ni a ganina mama ta wuce ace itace zata dinga siyo mana Kaya, a matsayi na namatarka ainice yakamata ace nasiyo mana, ita Kuma mama ta huta, ni bansan meyasa mama bata sona ba"

Runtse Idonsa yayi, bayason jin kalmar Nan datake fada akan mama, cikin sigar lallashi yace "yanzu me kike so?"

Ahankali tace "ni wannan kayan basumin ba, Kuma momy ma ta dade da dinka irinsu, saide nabawa ma'aikata su, inyaso nida momy muhaqura"

Ahankali yace "a a, ki dauki kudi acikin briefcase dina, saiki siyo muku Wanda kike so, shikkenan?"

Cikin murna da farinciki tace "eh, nagode my Dear"
Tafadi hakan tareda rungume shi ta manna masa kiss akan lallausan lips dinsa.
Cikin wata irin murya yace "Bari mana munirat azumi fa"

Murmushi tayi, tazuba masa wata irin hararar masoya, sannan tafice daga d'akin.

Mutara zuwa anjima, insha Allah zaku samu update 🙏🏻

To Aisha de tace ta yanke alaqa tsakanin ta da Hajja😂

Ko Yaya za'a qare akan takardun filayen mama? 🤔

Bazan tsaya Ina Allah ya'isa akan novel ba, Amma duk wacce ta karanta min littafi batareda ta biya ba nabarta da mahaliccinta, saboda nide ban yafe mataba

Mrs Usman ce ✍🏻

Page 19&20

Atamfa ce turmi uku da wani yadi irinna maza Mai kyau agaban Ummah da Abba, Bayan Ummah tagama Gani tace "mukam kasan ba zamu samu dinki yanzu ba, saide Bayan sallah mesunan qawar Hajja sai takai mana, Amma Naka Dana Jabir bansani ba ko zaku iya samu"

Aisha datake kwance akan gadon Ummah tana Kallan su batace musu komai ba, har yanzu idan tatuna fad'an da sukai da Hajja jiya ranta sake 6aci yake, kullum sukai fada da'ita saita sako iyayenta aciki.
Kafin Abba yayi magana Hajja ta doko sallama cikin d'akin, kallanta yayi yace "Hajja sannu da zuwa"

Tace "sannu mamuda, a zaune kuke?" bata jira amsar dazai bata ba tad'auki jakar kayan Aisha, Aisha tana ganin haka ta juyar dakanta Gefe ko kallon Hajja batayi ba, Hajja ta kamo hannunta tace "tashi mutafi mana mesunan qawa, duk fadan da mukai dake ai Bama raba makwanci, Amma jiya har kayanki saida kika kwashe, meyayi zafi haka? Tashi mutafi madubinki yana Nan nasake goge miki shi kiji dadin Kallan Kallan da kike" (🤭🙆🏻‍♀️)

Cikin sauri Aisha tatashi, ganin irin kato6arar da Hajja takeson yimata agaban Abba, Wai mutum da abunsa danya kalla shikkenan Hajja ta dinga magana daya, saukowa tayi daga gadon tana tura baki gaba, suka futo daga d'akin Kai tsaye suka koma cikin Dakin Hajja.

Suna zama Hajja tace "yanzu mesunan qawa abinda kikai ya kamata kenan? Ki hadani da walakiri, aiko maqiyi na bazai min irin wannan fatan ba"

Aisha tayi shiru batace mata komai ba, Hajja tasaki ajiyar zuciya tace "shirya muje kasuwa musiyo kaji da d'an kayan miya muzo mu gyara gobe Sai ai miyar sallah dasu"

Tashi tayi tad'auki hijabin ta tasaka sannan cikin qasa-qasa da murya tace "muje"

******

Yana zaune a office dinsa Bayan yagama ganin mutanan office din nasu Wanda suka masa sallama saboda tafiya garuruwan su hutun sallah, Shima tunani yake Ina yakamata ace yaje ya huta?
Itace tafad'o masa, to kode ziyara zaiKai matane? Mamakin Kansa yake, duk lokacin dasuke samun hutu irin wannan babu abinda yake tunawa illa munirat, yanda zai dauketa sutafi wata qasar suje Sud'an huta sannan su dawo, Amma yau kwata kwata yakasa tunawa da'ita, cikin zuciyar sa yace "tunda ba sonta nake ba menene zai dameni dannakai mata ziyara?, to Amma idan naje mezance mata? Wancen Karon akwai dalilin daya kaini, Amma yanzu fa?"

Afili ya furta "babu dalilin zuwan" duk yanda zuciyarsa taso hanashi, haka yaqi yarda, ahankali yad'auki wayarsa yadubo number ta daya d'auka ranar dayaje, batareda tunanin komai ba ya danna mata kira.

******
Suna futowa daga gida sukaga wani me adedeta, cikin sauri Hajja tace "Tsaya! tsaya!! d'an sahu"

Tsayawa yayi, Aisha tace masa "kasuwa zaka qarasa damu"

Yace "ba haya nake yi ba"

Cikin sauri Hajja tace "haba kaikuwa yaro, Nima nasan ba hayar kakeyi ba tunda mukam agarin Nan Ina mukaga wani adedeta sahu, saboda Allah zaka kaimu saina baka 'yar nera hamsin kasayi gasara Kasha ruwa da magariba"

Murmushi yayi yace "tokushigo"

Shiga sukayi, sun fara tafiya kenan wayar Hajja tad'auki qara, cikin mita tace "Kai wannan jaraba da yawa take, da ranar ma baza'a bar mutum ya huta ba?"

Aisha tace "to idan ba'a kiraki da rana ba cikin dare kike so a kiraki?"

Cikin mita tace "aikuwa koma waye bazan dauka ba,da azumin zanji koda Kiran waya?" tafadi haka tareda kashe wayar

Daga nasan bangaren mamaki ne ya kamashi, kamar fa rejecting din Kiran akayi? Metake da wayar zata katse masa kira? Wata zuciyar tace "kasani ko game takeyi?"
Ahankali yace "may be" sannan yasake Dialing number, wannan Karon Kiran yana shigowa Hajja tasa hannu zata kashe Aisha tace "Bani In dauka"

Babu musu Hajja ta bata wayar, ahankali cikin zazzaqar muryarta tace "Hello Salamu Alaikum"

Atsaye yake, Amma yanda yaji muryar Tata tana neman kashe masa jiki, saiya nemi kujera ya zauna tareda Lumshe Idonsa

A 6angaren Aisha kuwa dataji shiru saita sake cewa "Ba'a jinane? Wake magana ne?"

Hajja tace "maganinki kenan, kina ganin number special kece mecewa Zaki dauka, baki Sani Bama ko masu shan jini ne"

Dariyace ta kamashi, Kuma bayason taji shi, Sai yayi sauri yakashe wayar, yana cikin murmushi Ramadan yashigo office dinsa, cikin mamaki yace "Abokina lafiya?"

Saboda Rabon daya ganshi yana irin wannan farincikin harya manta, ahankali ya girgiza masa Kai, sannan yace "nothing"

Aisha kuwa dataji an kashe wayar, saita Bawa Hajja wayarta, me adedeta yace "Hajiya Kidena futowa da waya fa, kinganni Nan, to yau -yau dinnan nafuto daga gidan yari, Kuma satar waya ce takaini, gobe sallah idan kinsan ma zakije wajan idi toki tafi da paper da biro duk Wanda yace kibashi number ki saiki bashi paper ya rubuta miki, kema ki rubuta masa, saboda zamuyi patroll goben"

Cikin sauri Hajja tasake qanqame Jakarta, tace" innalillahi.... Aikuwa Gara daka fada mana Kai 6arawo ne, tsaya ka saukemu anan "

Cikin dariya yace"mama ni bazan muku komai ba, inda zan muku da tuni na zubar daku, kawai de fada muku nake ku kiyaye "

Cikin tsoro tace"to mungode, Kuma zata kiyaye, kasan jikar tawa farinjini ne da'ita kamar kudi, Yanzu haka me Kiran ma inka bibiya mashinshi nintane".

Suna zuwa kasuwa ya saukesu, Bai kar6i kudin su ba, godia suka masa sannan suka shige suka sayi abinda yakawo su, sannan suka juyo gida,ummah ce ta gyara kayan miyan jabir yakai wajan niqa, Aisha Kuma ta gyara kajin ta soya su, Hajja Kuma tadafa musu jallop din macaroni da sauran man da Aisha tayi suyar kajin dashi, sannan sukai wanka suka zauna kowa yana jira Asha ruwa.

Washe gari sallah, karfe bakwai da rabi Aisha da jabir da Hajja A'i suka shirya suka tafi masallaci wajan sallar idi, aqafa suke tafiya ahankali suna tafe kowa bakinsa d'aukeda zikiri, jabir yana Sanye da yadi ajikinsa medan sauqin kudi, Hajja ma taci atamfar ta sabuwa wadda ta dinka da kanta, Aisha kuwa atamfar da inusa ya dinka mata, itace ajikinta, sun sanya sabon hijabi iri daya itada Hajja, Wanda Hajjan ce ta dinka musu.

Suna zuwa masallacin Hajja ta dubesu tace "ikon Allah, dama wannan ne sabon masallacin da'aka Gina?"

Jabir yace "shine Hajja, ga wajan mata can, saiku qarasa, idan an idar kujirani zanzo mutafi"

Hajja tace "to ni yanzu wannan danqareren masallaci da Bismillah zan fara shiga kokuwa?"

Aisha da taqaici ya kamata ta juya fararen idonta tace "Da zagi Zaki shiga, haba Hajja, wani lokacin kidinga abu kamar wata tsohuwa"

Murmushi tayi tace "Allah sarki, mesunan qawa menene Kuma yarage? Tsufa kan ai mun tsufa, saide fatan Inga takwararki, Kuma incika da Imani"

Hannunta Aisha taja batare datace komai ba, suka shige cikin masallacin, sallaya ta shimfida musu suka zauna, basu sake magana ba kowa zikiri yake cikin ransa,basu dade da zama ba wani mutum yazo yana kar6ar sadaka, Hajja ta bude gefen zaninta tabashi nera Dari, Aisha tayi murmushi tareda jijjiga Kai, cikin ranta tace "lalle Hajja yau take sallah"

Bayan sun idar sun koma gida, anan sukaga har Ummah takusa kammala abinci, Aisha ce tacire hijabinta ta kama mata aikin, Nan da Nan suka gama, mutane Sai shigowa suke anata gaisawa, masu shagunan caji Sai kunna waqa suke a mp, Bayan sunci abincin Aisha tayi wa Ummah magana tana so taje gidansu Walida, abinci Hajja tabata tace "kafin ki wuce kishiga ki kaiwa jummai abincin Nan"

Kar6a tayi sannan ta wuce.

******
Chapter 18 · 0% Book details