← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 71

Sashe 11

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsoro ne yakamata, idonta yayi tsilli-tsilli tana Kallan sa,duk da bata sanshi ba,yanda taga ransa ya6aci tsaf zai iya aikata abinda yafada,wani tsoron ne yasake shigarta, gashi cikin dare ne kartaje haka kawai yakasheta a banza awofi, bare taga yanda yake da kyau, bata Sani Bama ko aljani ne, to sune akace suna shigar mutane su shigo cikin su, gabanta ne yafara faduwa ganin yanda ya matso kusa da'ita kamar zai shige mata jiki

Batare datace masa komai ba ta sunkuya,dogon gashinta ne ya dawo fuskarta sakamakon sunkuyawar da tayi,yasake rufe mata fuska, kwalin taliyar ta d'auka tayi ciki.

Kallan ta yayi yaga yanda uban hips dinta yake juyawa,girgiza Kansa yayi, yafara magana cikin zuciyar sa, inaga fa yarinyar Nan ba mutum bace, yar qaramar yarinya da'ita Amma ta mallaki abubuwan more rayuwa, Kuma inba aljana bace tayaya yanda yakewa mutane kwarjini Amma ita baiyi mataba Sai rashin kunya take zuba masa? Kaiii Gara yayi sauri yabar gidan, idanma aljanar ce to aniyarta tabita,cikin sauri yafuto daga gidan, Aisha kuwa tana ajiye kwalin taliyar tashige cikin Dakin Hajja da sauri gabanta yana faduwa, runtse idonta tayi, Amma shi take Gani a'idon zuciyarta yanda ya matso kusa da'ita ya nuna ta da hannu, yake zare mata ido, dak! dak!! Haka gabanta yake faduwa, Allah yasa ba Gamo tayi ba, Allah yasa ba aljani ne yabude mata idoba.

Sai wajan karfe hudu saura suka gama, har suka koma hotel kuwa jikinsa a sanyaye yake,maganganun yarinyar ne suke masa yawo a zuciya,saida yayi nafila sannan yayi sahur ya kwanta, da asuba kuwa tunda suka tashi basu koma bacci ba sukai shirin komawa Abuja

Da asuba Abbah yana tashin su Aisha sahur, saiyaci Karo da kwalin taliya guda daya, Wanda Aisha tashigo dashi, mamaki ya kamashi, jiyake kwali ne, Amma yana ta6awa yaji nauyi, Hajja tana futowa itama ta tsaya tana Kallan sa, fita yayi daga gidan saboda hayaniya da yaji tana tashi awaje, yana zuwa bakin kofar gida yaci Karo da sauran kayan,fita yayi daga gidan inda yaga mutane Ana tsatstsaye kowa yana fadar Albarkacin bakinsa, wannan yace yaji tsayawar motoci to yayi tunanin Yan fashi ne shiyasa yaqi futowa, wannan yace kaza wannan yace kaza, haka de, Abba yajuyo yashigo da sauran, anan yaga duk mutanan gidan sun tashi, Hajja ta Kalle shi tace "mamuda ashe Wai kaji ita Me sunan qawa taji lokacin da aka ajiye kayan tafuto fitsari lokacin, to Kuma Wai kafin taje bakin qofar har Wanda ya ajiye yatafi, bataga kowa ba, shine tashigo da guda daya taji tsoro kartaje ko aljannu ne" (😲)

Murmushi Abba yayi yace "ba aljannu bane Hajja, Ina Yaron Nan Dan kasuwar Nan? Me sunana?"

Hajja tace "waye Dan kasuwa Kuma?"

Yace "shugaban EFCC da'ake maganar sa a gidan redio yana raba kayan abinci gari-gari, ai shi nake nufi, to wai shine ya aiko wasu mutane suka raba mana muma"

Fashewa da Kuka Hajja tayi tana goge hawaye da gefen zaninta, cikin kuka tace "Allahu akbar, Allah yasaka masa da alkhairi, Allah yabiya masa buqatunsa na alkhairi, mamuda kaima bancire rai zakayi kudi ba, kaima Naka kudin yana Nan tafe" (😂)

Aisha ta harareta tajuya tad'auki buta da brush tayi bandaki, har Bayan gama sahur dinsu,zancen aketa maimaitawa, Garin chamo babu sunan Wanda yake yawo saina MAHMUD WAKILI 👌🏻

******

Bayan sun koma Abuja Kai tsaye office suka wuce, saida yarage wasu ayyukan sannan yatafi gida, Bai nufi part dinsu ba, saboda yasan Idonsa idon munirat to yau babu batun daga qafa awajansa, kwana ukun Nan Dayayi jiyake kamar yayi shekara uku ne batareda mace ba.

Sai Bayan Ansha ruwa yaga lafiya lafiya yakai azumin sa, sannan yatafi part din nasu, a wannan Daren munirat tagane kurenta, domin kuwa taji jiki yanda ya kamata
Saide abun mamakin shine kwata kwata baiji wani canji awajanta ba, tana nan kamar de yanda yatafi yabarta,ko kadan bai samu gamsuwa ba, shiyasa Bayan yahuta saiya sake nemanta Bayan wasu awannin, Amma idan yasake maimaita wa dinma duk hakan yakeji, yayi tunanin idan yayi dayawa hakan zaisa yaji shi zam-zam, to Amma sai yaji sa6anin haka.
A 6angaren munirat kuwa tayi tunanin yanda yadage yake abu daya tun farkon dare har tsakiyarsa yaji tayi masa dadi ne, saboda Shahaab irin mazan Nan ne Wanda suke shiru yayinda suka kasance da matansu, tun tana amarya takeso ta rikitashi ta karya wannan dabi'ar tasa taqin yin kukan dadi, Amma duk yanda takai da gyara haka zata jishi shiru, shi Dan sumbatun Nan ma ba yayi, bata saniba dadin tane baikai yayi kukan ba kokuma haka dabi'ar sa take, dataga sun kwashi shekaru masu tsawo Ahaka, kawai saita sallama, tabarshi a hakan dabi'ar sa take, shiyasa yanzu ma bata kawo komai acikin ranta ba, saide Bayan komai ya gama wakana ta isheshi da kukan kissa, shikuma Nan da Nan ya lalace wajan lallashin ta, ko kadan baison abinda zai 6ata ran munirat.

******

Yau satin su daya da dawowa daga jigawa, Amma tunani d'aya yabi yadameshi, yana son ya yakice maganganun da yarinyar tafad'a masa Amma yakasa, 'Dan qaramin tsaki yasaki, yafi awa daya a kwance a gadon mama, so yake tadawo yaji duminta Amma taqi dawowa tana can tana kula da Abincin da ake rabawa sadaka,Lumshe Idonsa yayi yana jin dadin yanda sanyin esi yake ratsa jikinsa, ko kadan bayajin wahalar azumin, sake sakin wani tsakin yayi Bayan tunanin yarinyar yasake fad'o masa, alqur'ani yadauka yafara karanta wa ko zai kawarda tunanin a ransa.

Sai gab da shan ruwa mama tadawo, alqur'anin ya ajiye ya dawo ya kwanta akan cinyarta, Kallan sa kawai tayi takasa magana, wani lokacin idan yayi mata wani abun kamar qaramin yaro, babu yanda zatayi dashi tunda shi kadai gareta, dan haka ta share shi tad'auki remote takamo tashar Sunnah TV tana kalla, saida aka Sha ruwa sannan suka dawo falo, anan ya tarar da munirat tana hada fruit salat, suna zama kuwa ta ajiyewa kowa nasa, wannan Karon mama batayi halin Nata ba, kawai dauka tayi Tasha, kodan saboda azumi ne yasa kwana biyu tayi shiru oho.

Bayan ya dawo daga sallar tarawih ma wajan mama yawuce, har lokacin suna tareda munirat, Sai wajan karfe goma sukayi mata sallama suka tafi part dinsu.
Kai tsaye dakinsa yawuce yayi wanka sannan ya kwanta, so yake yayi bacci da wuri, to Amma saide me? Dan qaramin pink lips din yarinyar yake tunowa, yasake tuna yanda take tafiya da sauri zatakai kwalin taliya cikin gida gaba daya hips dinta wani irin juyawa yake, yatunada dogon gashinta Wanda yafara daukan hankalin sa.
Meyasa ta tsaneshi? Meyasa take hamdala ga Rabbi saboda yace mata shi Yaron Mahmud Wakili ne? Hakan yana nufin akwai abinda ya yi mata, Kuma take neman sa ido rufe Amma bata sameshi ba, laifin meyayi dahar take fada masa cewa Shima ya kamata atuhume shi? Meyasa ta tsaneshi har haka? Wata zuciyar tace dashi yakamata kasan dalili.

Gyara kwanciyar sa yayi ya dawo yana kallon p.o.p din 'Dakin, tabbas inason jin dalilan yarinyar,gashi tanada masifa Amma da alama tanada tsoro, tunda tsawa d'aya kawai yayi mata, yaga idonta yayi tsilli-tsilli kamar ace kyarat ta gudu,idan ita din marar kunyar gaske ce to tsayawa zatayi ta fuskance shi yafada, itama ta fada, ya tuna yanda take zare ido cikin tsoro, baisan lokacin da wani irin murmushi ya qwace masa ba, cikin zuciyar sa yasake cewa yar qarama...
Yasake sakin wani murmushin har dimples dinsa yana futowa, a fili yace "me qaramin baki kawai...."

Munirat data dade da shigowa Dakin tana fesa turaren sa,cikin iyayi tajuyo ta Kalle shi tace"My Dear ni d'in?" (😳🙊)

Firgigit yayi ya dawo cikin hayyacinsa,yasaki wata nannauyar ajiyar zuciya, yaushe tashigo Dakin bai Sani ba?
cikin salon basarwa yace"yes"

Tareda miqa mata hannu yana daga kwancen.

(kaii jama'ah, shegiya yaudara 🙄)

Babu musu ta qarasa tana wani irin taku tana karkad'a jikinta, hakanne yad'auki hankalin sa, har me aukuwa ta auku, tayi tunanin zaiyi mata godia Bayan komai yagama wakana saboda dazu dazun Nan tagama shan wasu magunguna data siya wajan qawayenta, a jikin maganin ma saida akai kashedi idan kinsan kinada kishiya to karkiyi amfani dashi Dan Zaki gigita maigida.

Shikam Shahaab daqyar yasamu yayi released, zuwa yanzu Kam yariga ya saduda,ya daina qorafin komai, danhaka yauma bai nuna mata komai ba.

******

Zaune suke da Hajja, tunani take a ranta hartana cizon yatsa, Sai yanzu ne takejin haushin kanta kan rashin maidawa wannan mutumin martani.

daya ce mata ogonsa ne ya aiko shi, meyasa bata maida masa martani tace yaje ya fadawa ogan nasaba?
Takaici yazo wuyan ta ya tsaya, Sai yanzu haushin kanta duk yabi ya isheta, mutumin datake nema ruwa ajallo Kuma yanzu tasamu Damar da saqonta zaije gareshi Amma tayi watsi da damar ta.

Hajja dake Gefe tace "me sunan qawa yau me Zaki dafa mana a gidan?"

Taji shiru, ita kuwa Aisha tunani ne yayi Nisa batasan ma Hajja tana yimata magana ba.

Saida Hajja tata6ota tace "mesunan qawa!"

Sannan ne ta kalleta, Amma batayi Mata magana ba, cikin sauri Hajja tace "idan de akan naqi yimiki kitso ne kika fara gaba Dani har Ina miki magana kina qyaleni to dauko mataji nayi Miki, saikiyi gabar da mamuda ko Hadiza"(🤭)

"Hajja menene Kuma ummah da Abba na suka miki Zaki sakosu aciki?"

Hajja tace "kidauko nace, ni banason mita wallahi, dama azumi ne yasa nace bazan miki ba, saboda ranar Bana Gani sosai yunwa tasa duhu duhu kawai nake Gani"

Tashi tayi ta dauko mata matajin tabata, sannan ta zauna suka fara, manyan kitso suka fara guda goma, kasancewar gashin baida cika saide tsawo, Sai yarfe hannu take saboda zafi.

Jummai ce tashigo gidan tasamu waje ta zauna, Bayan sun gaisa tace "Hajja babu Dan sauran abinci awajanku nabawa jikana"(😂)

Hajja tace "Ina zamu samu sauran abinci jummai, muda ba Yara ne damu ba, Hadiza ta daina haihuwa, danma mamudan nawa jarumi ne gashi harda yaransa biyu, Amma ni har nayi zamani na nagama aishi kadai na Haifa, tundaga Kansa ko 6atan wata ban qara ba, Amma shi kinga yayansa biyu "

Jummai tace"um aikuwa mamudan naki ya'iya haihuwa jummai, ga 'Ya'ya nan kyawawa kamar yayan larabawan labanu"
Chapter 11 · 0% Book details