Sashe 38
Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tashi yayi yakoma can Gefe, cikin shagwa6a yace"mama kibawa wannan yarinyar takawo min mana"
"wacce yarinya Kuma Shahaab? Inada wata yar ne Bayan Kai?"
Saida yasake yin qasa da murya sannan yace"wannan yarinyar fa....me kula dake "
Mama tasaki Dan qaramin tsaki tace"wai Aisha kake nufi? Shahaab tayaya zan turo ta lagos Bayan bata ta6a zuwa ba? Koba haka Bama agabana jiya kasa yarinyar Nan kuka, idan tazo inda kake Kuma ai sai duka"
Murmushi yayi yace"shikkenan mama, Bari nakira Ramadan din"
Wayar yakashe, yadokawa Ramadan kira, yana dauka Yace"Ramadan wasu takardu nakeso kaje gida kadauko ka kawo min su lagos kokuma kabawa wani daga cikin ma'aikatanmu yakawo min"
Ramadan yace"abokina wallahi Bana gida, madam ta matsa, muntafi yankari, tana so tayi kallo"
Runtse Idonsa yayi, ahankali yace"jarababbe kullum kana gida, ai hutu yaqare saika dawo bakin aiki"
Murmushi Ramadan yayi yace"abar kaza de acikin gashin ta"
Wayar yakashe yasake Kiran mama ta d'auka tace"zaizo?"
Yace"mama baya Nan, yaje Bauchi state"
"tunda kadage Sai yarinyar Nan ta taho de nasan ko yana Abuja abinda zakace kenan,ka fadawa matarka takawo takardun, Sai akawo"
Cikin murna yace"to mama"sannna yakashe wayar
Daya daga cikin sojojin gidan yakira, ya turashi part dinsu sannan ya turawa munirat text, Bayan taga text din saida tagama shan qamshin ta, sannan ta Dauko tabashi, shikuma yaje ya kaiwa mama.
Mama tasa aka kira mata Aisha adaki, Bayan tazo tace"Ki shirya zan aikeki yanzu, zaki kaiwa Mahmud wadannan takardun"
Cikin ladabi ta amsa mata, Sannan ta juya daki, tana tafiya mama ta dauki wayarta tadubo mata wasu dogayen Riguna Masu kyau, tayi oder, Bayan Tashirya tafuto mama tace"zauna akwai kayan daza'a kawo miki yanzu"
Zama tayi tareda fadawa cikin tunani inane mama zata aiketa itada ba ko'ina tasani ba, wani form mama tabata tace"Aisha ga form din banki nasa an kar6o miki, kicikeshi, idan ansamu lokaci saikuje kiyi bvn abude miki bankin"
Cikin ladabi tace"to mama nagode, Allah yasaka da alkhairi "
Cikin jin dadi mama tace" Amin ya Allah "
Sun Dan dade suna jira sannan aka kawo kayan, mama tad'auki ledar tabata tace" to gashi kije kisake shirya wa saiki futo kutafi "
Har qasa ta sunkuya ta karba cikin murna tana yiwa maman godia.
Kai tsaye d'akin Takoma tafara bude kayan, cikin farinciki tasaki wani irin ihun murna tareda fadawa kan gadon, dogayen riguna ne Yan Dubai masu kama da abaya har guda biyar,Sai jaka da takalmi guda bibbiyu, wadda tafi daukan Hankalinta ta d'auka wata baqar abaya wadda akayiwa adon stone a hannu dakuma Qasan a bayar da qirjinta,gaban madubi Takoma tasake taje dogon gashinta, ta daure shi, sannan tasaka rigar, fuskarta babu kwalliya ko kadan kawai lipstick tad'an shafa alips dinta, tayafa mayafin a bayar, tad'auki jakar ta riqe ta kalli kanta a madubi, lokaci daya gabanta yafadi saboda gaba daya ta sauya kamar ba'itaba, ita kanta tasan zuwan ta Abuja ta sauya nesa ba kusa ba.
Futowa tayi zuwa wajan mama, tundaga nesa mama ta qare mata kallo cikin ranta tace"masha Allah "
Aisha tanada kyau, babu Wanda zaiqi Aisha, gata yarinya qarama ga Hankali, Kuma batada girman Kai kasancewar ta yarinya Sai yanda akai da'ita akan komai, saboda idonta bai bude da sanin rayuwa ba, tana wannan tunanin Aishan ta qaraso ta tsugunna awajanta tace"mama nafuto "
Mama tace" masha Allah takwarata kinyi kyau, toga wannan takardun zakije lagos ki kaiwa Mahmud "
Cikin sauri ta d'ago ta Kalle ta"mama lagos Kuma? Ai bansan hanya ba"
Murmushi mama tayi"nasan bakisan hanya ba Aisha, ajirgi Zaki tafi, direba zai kaiki Airport, sannan Kuna sauka a lagos ga wayata Zaki tafi da'ita saiki kirashi kifada masa kinzo"
Hankalin tane yadan kwanta sannan tace"to mama"
Tareda karbar takardun da wayar, direba ne yashigo mama tayi masa bayanin komai daga Nan suka tafi.
Suna zuwa Airport yahadata da wani, cikin kulawa da girmamawa mutumin ya kalleta yace"muje ko"
Aisha tayi mamakin yanda ake bata kulawa awajan kamar yar wani, itade tasan bakowan kowa bace face yar gidan mamuda da Hadiza, Amma sauran mutanan dake wajan kowa Kallan yar gidan Mahmud Wakili yake mata, duba da yanayin shigar ta, dakuma kalar fatar ta, uwa uba yanda ta riqe babbar wayar mama qirar iPhone tana Kallan pictures, kai kace wani abu muhinmi takeyi, tunda ta zauna babu Wanda yayi kasadar qaraso wa inda take, saboda kallo daya zaka mata kasan cewa irin yayan masu kudin Nan ne Wanda ake 6atasu Ana basu manyan wayoyi suna abinda suke so, bata Jima da zama ba jirginsu yatashi zuwa lagos, acikin jirgin de duk Wanda yayi mata kallon qwaqwaf, zaisan atsorace take, kamar ace kyat tazura da gudu, Amma Kuma yanda take kallon window tad'an basar, Sai hakan yasa babu hankalin Wanda yadawo kanta, tunanin rayuwar ta take Wai yau itace a jirgi a dalilin wa dalili ta, basu dauki tsawon lokaci ba suka sauqa a lagos,miqewa tayi tsaye tana daukan takardun, saide dayawa daga cikin mutane kowa yana dauke da jakar Kaya ne, Sa6anin ita da kawai takardu ne a hannun ta Sai yar qaramar handbag dinta, shiyasa kowa kallo daya zaiyi mata yasan cewa lalle yar wani ce, tafiya daga ke Sai takardu? (🤔)
Ita kuwa ko ajikinta saboda batasan yanayin ma yanda ake tafiyar ba, wajan sakkowa daga jirgin ma ahankali ta sakko harta futo cikin mutane kamar yanda taga kowa yanayi, wayar mama ta dauko ajaka Takoma Gefe.
Dakanta ta rubuta number,Nan da Nan kuwa sunansa yafuto,MY SON, wayar na shiga yadauka cikin sauri saboda Dama jira suke tun dazu, cikin sauri yace"mama anbata ne?"
Cikin sanyin murya tace"nazo,Ina filin jirgin"
Murmushi amsar ta tabashi, cikin jin dadi yace"Welcome Baby, bani 5 minutes kinji"
Tace"to"
Tana nan a tsaye tsawon wani lokaci saiga kira yashigo wayar, tana dauka direba yayi mata magana akan yazo daukan ta ne, fada masa inda take tsaye tayi, shikuma ya qaraso suka tafi, basu dade suna tafiya ba suka qaraso cikin Babban company, suna tsayawa driver yace"ga hanyar dazakibi Nan"
Ta'amsa masa,sannan ta nufi hanyar tana tafiya, daga can nesa ta hango shi a tsaye agaban wata qofa, yayi kyau sosai cikin suit Amma babu jacket, hannunsa duka biyu zube cikin aljihun wandonsa, ita yake qarewa kallo yayinda bugun zuciyarsa yake sauya wa, Sai yanzu ne yayi danasanin zuwan ta, haka ta taho da wannan shigar tundaga Abuja kowa yana qare mata kallo? Lokaci daya yaji wani irin kishi ya kamashi, ahankali yajuya yashige cikin office din, Aisha kuwa tana ganin shigar sa cikin ranta tace"yayi kyau kamar saurayi"
Ta qarasa wajan kenan zata shiga, wani Dan sanda yataho da sauri yace"ke Ina Zaki shiga?"
Cikin rashin Sabo da shiga waje irin wannan tace"ciki zan shiga"
"kamarya ciki zakishiga, Ina I'd card dinki?"
Bude kofar da akai ne yasa ta kalli kofar, Mahmud dinne yafuto ya kalli Dan sandan, sannan yayi mata alama data shigo cikin office din, cikin sauri Dan sandan ya russuna yace"kiyi haquri Dan Allah, kinji"
Aisha batace masa komai ba, tabi Bayan Shahaab suka shige, suna shiga wani irin Sanyi ya bugeta, Babban office ne Mai d'aukeda manyan dinning table guda biyu, daya kalar baqi ne, dayan Kuma milk ne, a shimfide yake da carpet tareda wani dogon esi a tsaye daga Gefe, ga wata uwar plasma a jikin bango, Sai manya manyan pictures dinsa guda biyu a manne abango, mutane hudu ne a zaune a dogon table din, dukansu suna Sanye da suit, kallon ta suka tsaya yi, cikin ladabi yace"ina kwananku"
Cikin sauri suka amsa mata, Shahaab kuwa ya daure fuska yasa hannu ya kar6i takardun tare nuna mata dayan table din da hannu alamun ga wajan zama, zama tayi tareda zubawa TV ido, inda ake haska yanda yanmajalissa suke meeting akan yanda za'a qara inganta tsaro aqasa, Shima zama yayi, Amma shi fuskantar mutum hudun yake, takardun yaduba sannan ya basu suka fara dubawa suma.
Saida yaga hankalin su yakoma kan takardun sannan yatashi yadauko mata wani Babban tire me d'aukeda flask din ruwan zafi, da Green tea, da madara da bournvita da Nescafe dakuma suger Dan kwali, ya ajiye a gabanta, sannan yad'auki qaramin glass cup da spoon yajefa mata green tea din guda daya acikin cup din,ya sunkuya kamar zai bata, yayi qasa da murya cikin sigar rad'a yace"meyasa kika futo da wannan kayan?"
Itama cikin qasa da murya tace"mama cefa tabani"
Girgiza Kansa yayi, sannan yace"kihada tea Kisha"
Daga masa Kai tayi, shikuma yajuya yakoma dayan table din dasuke zaune, ganyen shayin tacire, tamaidata cikin kwali, ta zuba madara kusan cikin cup din, ta bude bournvita Shima tazuba dayawa, sannan tazuba ruwan zafi tadamasu da kauri kamar chocolate sannan tafara Sha,(😄)
Shahaab dayake kallon ta ta gefen Idonsa cikin ransa yace"quruci dangin hauka... Ko tsoron ciwon ciki batayi
Tanajinsu daya daga cikin su ya kalli Shahaab yace"mutum Dari ne a jikin takardar mu,za'a basu horo acikin camp Bayan an sallami masu bautar qasa"
Yajuya ya kalli na gefensa yace "kayi waya da masu kula da camp, nawa zamu basu tsawon sati daya?"
Cikin sauri yace"aini already munyi waya dasu, sunce abada ko nawane, shine nake Gani why not mubashi kudin Dan kadan, inyaso kowacce Sai a sallameta da dubu ashirin ashirin?"
Shahaab dayake sauraron su yace"amma idan akai haka lissafinmu zai rushe, lissafin da mukai last time kusan million biyar zamu kashe,abashi kudinsa kawai yanda ya kamata, sukuma matan tsawon sati dayan da zasuje suyi a camp din Nan za'a Koya musu cake,popcorn,dakuma donut, ranar dasuka gama abawa kowacce injin aiki dakuma jarin dubu goma,dole za'a rage yawan masu Zaman banza babu sana'ah agari"
Daya daga cikin su dayake rubuce rubuce ya d'ago yace"duk da haka de kudin yafi million biyar, saboda a Kwai kudin abincin su,abinsha, sutura dakuma fetir din daza'a siya saboda kunna inji daddare, sannan matar Nan daga wata qasa zata zo domin training dinnan, itama dole za'a saka kudin sallamarta aciki"
Dariya suka saka gaba daya, daya na gefen yace"wallahi wannan Yacika qaqalo abubuwa"
Aisha data gama shanye hadin madararta, tazuba ruwan zafi a cup din Dan kadan tahada tea dashi marar madara tafara Sha ahankali, cikin zuciyar ta tace"kowa kata6a yacema babu tayi yawa Amma su gasu suna qirga millions"