Sashe 8
Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mai aiki tafice daga falon, mama ta kalli munirat tace "duk inda kissa take ni banason ta, nida ba namiji ba tayaya za'a min kissa nakasa ganewa? Dacan baki ta6a zuba min abincinba, Sai yanzu? Babu uwar da kike tsinana min a gidan Nan munirat, shiyasa Nima nafi ganin mutunci da qimar wadda take kula Dani akan ki, koba komai ita zata Dauko abinci na takawo min tunda tasan banason Zaman dinning, zata zauna ta dinga matsamin qafafu na saboda kumburi, zata zauna Dani tayi fira Dani ta debemin kewa idan d'ana baya Nan, duk abinda zakumin yanzu daga ke har mijin naki ai duk a banza, tunda Shima gashinan a zaune yakasa nemo min Qawata, Amma da neman 6arayin Gwamnati ne jikinsa yana rawa zaije yakamo su, anan yafi qarfi, saikace Gwamnatin ce ta haifeshi baniba"(🤭🙆🏻♀️)
'Dago Kansa yayi zai bata haquri ta dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu, "dakata Shahaab, banason jin komai...idan kuma zayyanomin abinda kata6a yimin zakayi danka wanke kanka saboda rashin nemo min qawata dakayi to Shima Bana buqatar ji, to mema kata6a yimin? Fadamin abinda kata6a yimin abaya, saina biyaka, barema nikam mekata6a yimin a duniyar Nan ne Shahaab?"(😂)
Girgiza Kansa yayi da sauri yace"A a, banta6a yimiki komai ba mama, kiyi hakuri"
Bata sake magana ba daga Nan, abincin da yar aikin tazuba mata ta d'auka tafara ci, munirat kuwa cikin ranta mamakin masifar mama take, akan wannan shegiyar qawar Tata da babu Wanda ya Santa, dannata ma datake mutuqar so bataqi ta6ata masa rai ba
******
Washe gari maqocin su Hajja Alhaji Audu yasake aiko musu da kayan Azumi sadaka, buhun shinkafa three brothers Dan madaidaici, da madara qaramin gongoni da siga kusan kwano biyu, Abba yafita da Kansa zaije har gida yayi masa godia, dama ya kammala sabon gidan mansa daya Gina akano, Mekai ashirin, Amma ba'a kaiga bude shi ba, duk saiya hada yayi masa Allah yasanya alkhairi tunda yazo Garin, dama Ana tunanin gobe za'a tashi da Azumi, gashi babu abinda suka siya a gidan, Sai Hajja ce take cewa zata siyo musu shinkafa awajan qawarta jummai ko kwano goma ce, Amma gashi sama taka sun samu wannan kyauta, sukam Dame zasu sakawa wannan bawan Allah?
Ummah tace "Hajja Dama wallahi babu komai a gidan Nan, Bari adiba Sai adafa"
Hajja tace "sosai kuwa, Mesunan qawa tashi kinemi wuqa kibudeta ki dauka kidafa mana, saide mu qaro macaroni da yar taliya ko guda biyar biyar ne Kuma"
Aisha tatashi ta kama buhun ta bude, Nan da Nan kuwa tadafa musu, aka zubawa kowa da Mai da yaji, suna cin abincin Hajja tace "Mesunan qawa wannan shinkafar Taki tadahu kuwa, three brothers cefa, Amma kinyi mata tahuwar three sisters"
Aisha datake hada gumi tace "tadahu mana Hajja, kede kinfi son kiji shinkafa tayi luguf, kodan ke tsohuwa ce, haqorin duk ya mutu"
Kafin Hajja tayi magana Ummah ta kalli Aisha tace "Dan Allah kicire hijabin nan, kewai bakya jin zafi ajikinki ne? Sai hada uwar zuffa kike Amma bazaki cire hijabin ba?"
Hajja ta kwashe da dariya tace "Wanne dare ne jemage bai Gani ba?"
Aisha tayi shiru, duk yanda takai da Bawa Hajja martani yau kasa mayar mata tayi, taga alama idan tayi magana to tsaf Hajja zata tona mata asiri akan abinda taga tana kallo yauda safe, haka ta kama hijabin tacire,lokaci daya taji iska me dadi tana shigarta, tsefaffan kanta me tsawo da qyalli Sai kad'awa yake saboda iskar datake shigarsa
******
Da daddare yayi shirin tafiya masallaci sallar magrib, Sanye yake da jallabiya ruwan toka, Sai carbi ahannunsa, baisaka hula ba, Amma jallabiyar tasa tayi mutuqar yimasa kyau,fatarsa tayi wani irin fresh, yana ganin musulman sojojin gidan suma suna alwala, da aqafa yake tafiya Amma yau mota yahau, kasancewar akwai kwalayen alqur'ani dazai raba, ko Allah zaisa yasamu Lada saboda gobe za'a kama azumi, Ana idarda sallar magrib din yatashi yafara Rabon alqur'ani, mutanensa suna tayashi.
Limamin masallacin ne yayi masa addu'ah, Sannna yafara yin wa'azi kafin lokacin sallar ishsha'i, wasu mutane ne guda biyu dasuke zaune asahun bayansa, yaji suna zance qasa-qasa, da alama ba'a Garin sukeba, zuwa sukayi, gaba daya Sai hankalin sa yabar kan wa'azin da akeyi, yakoma kansu, dayan yaceda dayan "yanzu Mansur kaduba kagani yanda masu kudi suke jin dadi a wannan Garin? Amma kwata kwata basa taimaka wa talakawan dasuke wasu qauyukan, kaduba kaga haduwar wannan masallacin fa, ni idan nasamu Nan ma ai naji dadi, wannan shi ake kira aljannar duniya"
Wanda aka kira shi da Mansur yace "wallahi hakane zakarai, kaga fa har kyautar alqur'ani ake bayarwa, mukam Bana zamuyi azumi a dadi, tunda ba yanzu zamu koma arewa ba, gashi babu zafi, ga ruwan sama, can Kuma Sai zafi"
Zakarai yasake yin qasa da murya yace "wallahi saida nazo Garin Nan nasan cewa bazan mutu acikin wahala ba, gaskiya kudi yayi, saboda yanzu rashin kudi yayi yawa, marasa qarfi suna buqatar taimako, inda ace masu kudi zasu dinga taimaka musu Aida sun samu Lada, wani ma baisan irin addu'ar da za'ayi masa ba, qarshan ta wani yana masa addu'ah kaga Allah ya amsa masa, saboda kowa da irin baiwar da Allah yabashi, wancen azumin fa, gidan wani maqoci na, kullum gero sukeci, safe rana dare, shine abincin, idan aka Sha ruwa kuwa farau-farau suke hadawa, dayake Ina Dan taba sana'ar qanqara to shine Nima nake Dan taimaka musu, Amma wallahi kafin akama azumi geron ne, haka cikin azumin ma de shine abincin "
Jikin Shahaab yayi Sanyi kalau, yanzu acikin wannan qasar ne za'a samu masu cin gero da azumi? Kuma Ahaka suke rayuwa?
Har aka idarda sallar Isha'i, yana wannan tunanin a ransa, daya koma gida ma suna yin dinner mama taga kamar hankalin sa baya kan abincin, kawai de yana cine
Shikuma tunani yakeyi a ransa, mutum yaci gero da Azumi?
Mama kuwa Kallan sa take,tun daga fuskarsa har zuwa faffadan qirjinsa, tambayar kanta take Anya kuwa Mahmud lafiya kalau yake? Kokuma bashida lafiya? Kwata kwata Bahaka mahaifinsa yakeba,saboda idan de bata manta ba, lokacin da sukai aure idan babansa yafara abu daya saita gudu(🙈)
Kuma idan de Shima ubansa yabiyo, to jarabar sama kadai zatasa matarsa tasamu ciki duk dade haihuwa tsari ne na Allah, to Amma shi shiru kakeji da alama de ba qalau din yakeba, duba da yanda yatsani ayi masa maganar qarin aure.
Ruwa yadauka yasha, Sannna yad'auki tissue ya goge bakinsa, zuwa yanzu yagama yanke shawarar rabawa talakawan wasu garuruwan kayan abinci, ko Allah zaisa Shima wani yayi Masa addu'ah Allah yabashi magaji, Kallan munirat yayi, ya qifta mata ido alamun yana jiranta, Sannna yayiwa mama sallama yatafi part dinsa
Bayan sunyi shirin bacci yaja munirat jikinsa ya rungume ta,ganin kamar baida damuwa yasa ta bijiro masa da maganar ten million din Dayayi mata alqawari zai bata.
Kallan ta yayi, "idan kina buqatane yanzu, to nayi Miki izni kibude loka ki dauka, ten million din Kuma tunda nayi Miki alqawarin baki to zan baki, but ba yanzu ba, akwai abubuwan dasuke gabana yanzu"
Rantane yayi baqiqqirin, Amma dayake yar duniya ce, bata nuna masa ba, saima kissing din wuyansa data hauyi, alamun furucin nasa yayi mata dad'i, dayaga tana neman janyo masa ruwa, saiya rungume ta yayi mata rad'a a kunne, yasan cewa idan tatada masa Hankali ma wahala kawai zaisha, saboda kwana biyun Nan gaba daya tasauya masa, jinta yake tamkar abinci ce medadi Amma Kuma babu Maggi da gishiri acikinsa(😲)
daga Nan yayi bacci, munirat kuwa, kasa baccin tayi, baqin ciki ne fall ranta, Sai gab da lokacin sahur bacci me dadi ya dauketa, shi kuwa tun qarfe uku da rabi yatashi yafara nafilfili, yana roqon Allah yasadashi da alkhairin dayake cikin wannan wata Mai Rahma daya kama yau
Sai shine yatashe ta tahada musu abunda zasuyi sahur dashi, shikam kawai baqin tea yasha, Bayan ankira sallah yafice masallaci.
Dasafe yana tsaye gaban mirror din dakinsa, agogo yake daurawa ahannunsa,kamar kullum yana Sanye cikin suit wadda ta kar6i fatar jikinsa, ya maqala waya a kafadar sa yana magana cikin aji
"Ramadan kayi magana da MD na company yahada manaTrella ta macaroni da taliya guda goma "
"yanzu ake buqatar trella goman?"
"no, cikin satin nan nakeso agama hadawa, Sai kayi magana da Baba yahuza, zai hadaka da mutanan dazasu dauka, Sai araba duk garuruwan daya kamata"
"ok to shikkenan, jiya naje ganin sabon company, komai yayi kyau sosai Abokina, Sai aiki ake wuta-wuta,da alama kana buqatar sa yanzu ne cikin qanqanin lokaci"
Murmushi yayi, Bayan yagama daura agogon yace "A a, ni Bani zanyi amfani dashi ba, akwai wacce zan Bawa, zan Bawa wata wadda Takeda mutuqar muhimmanci awajena"
Munirat data qaraso cikin Dakin nasa hannunta d'aukeda brief case dinsa, tasaki wani murmushi Mai qayatar wa Sannna tashigo cikin Dakin, tasan cewa itace, ta Kuma San Bayan ita, babu wadda Shahaab zaiyi wa wannan kyautar, Nan da Nan taji duk wani 6acin rai datake ciki yakau, bacin ran Data kwana dashi Daren jiya taji yatafi.
Ganin munirat din tashigo dakinsa yasa yakashe wayar, bayaso ko kadan tasan shirin dayake akanta, yafi son saide taga yabata takardun companyn
******
Hajja ce zaune cikin inuwa tana wanke jarkokin kunun Aya, tunda ankama azumi yau, tofa tarufe yin kunun Aya Kuma, Aisha na gefenta tana tsefe kalbar da'akayi mata wadda duk jelar tagama warware wa, ta kalli Hajja tace "Dan Allah Hajja kimin kitso, kullum saide amin kalba, ni wallahi nagaji kitso nakeso"
Hajja tace "haba 'yar Nan, kika Bari saida muka dauki azumi Sannan Zaki kama Kai ki tsefe saboda kina tutiya Hajja A'i ta'iya kitso, aikuwa saide kije maqota a miki"
Kafin Aisha tayi magana wani yaro yashigo gidan yace "Hajja A'i Wai inji jummai idan kinada yar ashana kibata zata hura wuta"
Hajja tace "wacce irin ashana Kuma da wannan safiyar ko bata dauki azumin ba ita?"
Yaron yace"bansani ba "
Tace" kace mata banida ashana, saide kwalin ashanar idan tana so saikazo ka kar6a mata, saita nemi ashanar awani gidan "
Aisha tace" Hajja Dan Allah nikiji Dani "
Tace" ke bazan miki kitso yanzu ba, kanki yayi santsi dayawa, tsautsayin dayasa kika tsefe shi zaisa ki kitse abinki da kanki "