← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 71

Sashe 45

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri Aisha ta sunkuyar da idonta qasa, wannan tonon silili na Hajja har Ina? Da alama batasan waye wannan yake tareda mama ba, da tasan shine Shahaab dabata mata wannan tonon asirin ba.

Ahankali kuwa ya kalli Hajja yace"nima haka tamin Hajja, ranar Dana kawo muku abinci da Azumi rashin kunya ta dinga zubamin, saura kadan ma ta dungure min kai na...."yaqarasa maganar cikin sigar tsokana.

Aisha ta d'ago ta daka masa harara da fareren idonta tareda murguda masa d'an qaramin bakinta,yana ganin abinda tamasa yafaki idonsu Hajja ya motsa fatar bakinsa yasakar mata kiss ahankali,karaf akan idon Abba (🤭🙆🏻‍♀️🙈)
Aisha kuwa tana ganin abinda yayi tayi sauri ta sunkuyar da idonta, Abba kuwa cikin sauri ya kawar da Idonsa yayi murmushi cikin ransa yace"dole yarinya tadinga bijiremin tadage lalle Sai Kai"
Ummah da mamaki yagama kamata ta kalli Shahaab tace"wanne irin abinci kake magana bawan Allah?"

Abba ya kalli Ummah da Hajja yace"wannan fa Mahmud Wakili ne, Wanda yaturo da Azumi akayi Rabon abinci agarin Nan?"

Hajja ta kalli mama tanuna Shahaab tace"wannan shine Mahmud dinki?"

Cikin sauri mama ta daga Kai tace"shine Aysha, shi kadai nahaifa, inde kinji Ana cewa Mahmud Wakili to Mahmud dinane, ashe de alqawarin mu nasaka sunaye ya tabbata, Rabon abinci Kuma babu Wanda yaturo, shida Kansa yazo, a lokacin nariga na fidda rai da ganin Aysha Sulaiman, sainayi masa magana akan yazo jihar Jigawa yagina gidan marayu, ko Allah zaisa watan watarana Yaya, kokuma jikokin Aysha zasu kasance a gidan, ta wannan hanyar ne zan iya taimakonta saboda bansan inda zan ganta ba, Nasaka anyi cigiyar duk a banza,Bayan yazo sunyi maganar aikin shida Gwamnatin Jihar, saiya raba kayan abinci, to kunji dalilin zuwansa Nan Garin, dama shine Wanda nake dashi Wanda zai tsayamin akan nemanki, toshi tunda yaji nace masa muddin naganki Sai na aura masa yarki, Tofa shikkenan yayi biris da maganar neman naki, saboda bayason nabashi wadda bayaso, yad'auki son duniya yad'ora wa matarsa, shi Dan boko, ba zaiyi wa matarsa kishiya ba, Amma dayake Allah yaso kamashi, saiya saka masa son Aisha, soyaiya ta kamashi dumu-dumu, Idonsa yarufe,ya manta da batun Qin qarin aure,Sai gashi da Kansa yazo min da maganar inzo in nema masa auren Aisha, inkikaga yanda yake son Aisha saikiyi mamaki, harfa company yabata, Alokacin da akayi kyautar na tambayi abokinsa wacece Aisha? Nasan tare suke qulla komai, Amma Shima saiya 6oyemin, akace mama ai jinake dake yake, waini za'a yiwa wayo, Amma da aka 6oyemin din Sai gashi de anzo wajena inzo neman aure, to Dama mun samu Sa6ani da takwarar tawa, sainace zanzo inbata haquri, ashe ni Allah ne yayi zan hadu dake...."

Tajuya ta kalli Shahaab tace"idan baka auri yar qawata ba ai gashinan zaka auri jikar qawata"

Cikin sauri Hajja tace"kamfani fa kikace Aysha?shiyasa da yarinyar Nan tadawo tazo da kudi ajakarta tace mana Wai me gidan ne yabata naji tsoro, saboda kar ace daga zuwa aiki yarinya ta qwacewa matar gida Miji, saide Kuma bakisan wani abu ba, ai ita takwarar Taki akwai Wanda takeso, tad'auki son duniya ta dorawa wannan jarababban yaro(😳)
Uban Nata har dukanta yayi akansa, saboda Dafarko akwai Wanda mukeso mubata inusa, yarinyar Nan tunda tahadu da wannan saurayi ta bijire tace lalle saishi, ita batason inusa, to yanzu ma idan muka bata Mahmud din naki muna Nan dake wannan Yaron zai dawo yaqara hure mata kunne, qarshe tazo tace bazata auri Mahmud dinba, Amma wata kusan ai tafi wata, shi wancen saurayin biro yabata shikkenan ta rikice akansa, Amma ga Wanda yabaka kyautar kamfani banda rashin Hankali me akai-akai wani biro? Aini idona idon Shahaab, hakuma ce zata rabani dashi, Kuma infada miki yaqi futowa fa? Shirme ne kawai irinna takwarar ki"

Cikin sauri Abba da yasan komai yayi qasa da Kansa, Aisha kuwa murmushi tayi Shikuwa Shahaab yana jin haka yayi qasa da Kansa, yaude yakawo Kansa wajan Hajja Sai ta Allah Kuma.

Mama tayi dariya ta kalli Hajja tace"to yanzu ai gashinan yafuto, Mahmud din nawa Aishine Shahaab din"

Cikin sauri Hajja ta zaro idonta(😳) tace"Shahaab?"

Cikin sauri yayi qasa da Kansa yafara Sosa qeyarsa, Ummah kuwa dariya ce ta kamata, Sai yanzu ne ta gane dalilin dayasa tun dazu yake sunkuyar dakai, ashe suruki ne dakansa.

Mama tayi dariya tace"to yanzu mun futo Aysha, Sai abamu auren Aisha"

Hajja tayi dariya tace"narasa ma mezance wallahi"
Tajuya ta d'akawa Aisha duka abaya har saida tad'an yi qara, sannan tace"dan gidanku kinaji inata zuba ko zunguri na bakyayi ba?"

Ummah tayi dariya tace"Hajja Ai zancen yaqare"

Mama ta kalli Shahaab da Kansa ke qasa tace"narasa gane wannan kunya daka aro ka yafa wa kanka Shahaab, agida fa sassafe kazo min falo ka zauna kanaso muyi muzo gidansu Aisha, yanzu Kuma gamu a gidan Amma kakasa kallon Aishan ma, to ai shikkenan ga abokinka Nan, saika bashi haquri ka nemi auren awajansa, yau aboki yazo wajan abokinsa neman auren yarsa"

Dariya sukai gaba dayansu, Abba yace"nikam babu komai wallahi, dama komai an ai katashi ne cikin rashin Sani, Amma komai ai yawuce, Allah ya nuna mana lokacin ya basu Zaman lafiya"

Ummah tace"Amin-Amin, aimune da godia Hajiya, Allah yasaka da alkhairi anata dawainiya damu, bagamu ba, baga yaran muba, Allah yasaka da alkhairi"

Mama tace"duk abinda Shahaab yamuku ai Kansa yayi wa, idan zai dauki duniya yabawa jinin Aysha Sulaiman, wallahi banida damuwa, yayiwa wasu ma bare Kuma Aysha? Aysha ai mahaifiyar sa ce, yanda nake da iko akansa itama haka take dashi"

Tajuya ta kalli Aisha tace"takwara ta matso kusa Dani mana,Allah sarki kullum saita dinga Cewa a kakarta ta daukeni, ganina take kamar Hajja kakarta, ashe kuwa yarinya da gaske take nidin kakarta ce"

Murmushi sukayi, Aisha ta taso ta zauna agefen mama kanta sunkuye aqasa, Hajja tace"Aisha kenan, sarkin tsiwa, waini Kam Aysha Mahmud dinki yaransa nawa yanzu? Ni nawa Mahmud din Aisha ce ta farko, saikuma jabir yana qasashen waje Mahmud dinki ya turashi karatu, sukenan su biyu"

Jikin mama ne yayi Sanyi, ahankali tace"wadannan jikokin naki su zan kalla Nima ince ga jikokina, saboda har yanzu Allah bai Bawa Shahaab haihuwa ba, shiyasa na damu akan yaqara aure, saboda likitoci sun tabbatar lafiyarsa kalau, shikuma yaqi yayi auren ko Allah zaisa Shima muga yayansa, to yanzu de Ina fatan idan akayi auren da Aishan, ko Allah zaisa ita tasamu cikin"

Hajja tace"ciki kuwa,insha Allah anayin auren zata samu,auren yanzu da anakai yarinya zakiga tasamu ciki kamar Dama abakin qofa tayi tuntu6e dashi?yo Allah natuba jikar qawata jummai fa watanta Tara cif-cif ta haihu, idan kikai lissafi zakiga inajin a ranar damuka Kai yarinyar a ranar tasamu ciki, shegiyar jaraba duk ta cika mazan, dama akan ga6a suke, shiyasa anakai musu yarinyar suke haike mata...."(🙈🤭)

Ummah najin haka tatashi Dasauri tace"bari azuba muku ruwan alwala naji Ana Kiran sallar magrib"

Shahaab kuwa kunya ce ta kamashi cikin sauri yadan Sosa Kansa, Shima abban cikin kunya ya kalleshi yace"muje masallaci yalla6ai"

Aikuwa cikin sauri yatashi suka fice.

Mama tayi murmushi tace"kinga Kin kori yaran naki, gaba d'ayansu sun watse"

Hajja tace"Allah nake fada miki haka mazan suke, watama da za'a yi jinkiri adan daga Daurin auren to da a gidansu zai fara rage zafi, wannan fitina har Ina?"

Cikin sauri itama Aisha ta silale tayi dakin Hajja, tanajin mama ta cewa Hajja"aikuwa Shima dannaki Ina tunanin haka yake, Dan mahaifinsa ba sauqi, idan kikaga yanda yakebin takwarata da kallo Sai abun yabaki tsoro,shiyasa nake jin tsoro kar aure yazo abawa yarinya magunguna Tasha yazo yayi 6arna"

Hajja tace"to Aysha itada zataje gidan kishiya akaita haka babu Dan tsumi?, itama matar tasa ai kinsan kintsawa zata sake yi"

Mama tace"Eh da wannan Kuma,toki bata maganin Mai kyau da inganci, inkanada kyau saika qara da wanka, yanda yake rawar jiki akan takwarar Nan tawa Gara yajita da zaqinta"

Haushi ne yakama Aisha, wannan mutanen basuda damuwa wallahi, dama de halinsu ne yazo daya shiyasa abotar tasu ta Dore, Wai mutum ake cewa yayi zaqi saikace wani chocolate(😂)

Ruwan alwala da Ummah ta gabatar musu a buta, shine ya katse musu zancen nasu, Kuma ko ajikinsu Ummah tana jinsu suke wannan maganganun, Kuma ahakan ita surukar su ce(😂).

******

Su Abba suna fita kofar gida sukaga cincirindon mutane suntaru a kofar gidan, cikinsu harda Mai Gari, mamaki yakama Abba, kafin yayi magana maigari ya kalli Abba yace"mamuda yanzu Yara suke fada mana anga Mahmud Wakili agidanka, shine mukayi gayya mukazo mu shaida, saikuma muyi musa godia akan abun alkhairi daya aiko mana kwanaki"

Shahaab yana jin haka yayi murmushi yace"babu komai baba, Bana buqatar godiar ku, ai komai Dan Allah nayi, Allah yaqara hore mana domin mu samu qwarin gwiwar taimakon naqasa damu"

Gaba dayansu suka amsa da ''amin'', daga Nan Kuma suka babbashi hannu sukai musabaha suka wuce masallaci gaba dayansu.

Bayan su Hajja sun idar da sallah aka kawo wutar nefa, Dakin Hajja suka koma gaba d'ayansu har Ummah, Aisha ta zubowa mama abincin data gama dafawa me miyar kaji, ta zauna tafara bata abincin kamar de a Abuja, tanacin abincinta fanka tana fifitasu, Hajja ta kama ha6a tace"ikon Allah,kaga wani sabon Salo yanzu Aysha abincin ma abaki takwarar Taki take baki? Shiyasa fa idan Naga Aisha tana cin abinci nake tunawa dake, komai kina yinsa kamar yar sarki, Kuma Sai akayi dace kinyi kudi, mulki Kuma Sai Allah"

Murmushi mama tayi tace"ai Aysha, shiyasa kullum nake qara godewa Allah, Shahaab yana sona, yanamin biyaiya yanda bakya zato, shida Kansa yake nemomin Mai kula Dani, Kuma duk cikin Wanda yake kawo min nafijin dadin aikin Aisha fiye da kowa, saboda itace take min komai tsakani da Allah babu 6oye-6oye, tana kulawa Dani kamar Nina haife ta, cin abinci Kuma Aysha ai Yanzu na rage yanga, tunda Wakili yarasu na watsar da Gayu, yanzu Shahaab ne yake wannan cin abinci kamar bayaso, haka zai Sani agaba wataran lalle saina bashi abinci dakaina, nikuma ince Ina matarka, jeka ta baka"

Hajja tace"ai shikkenan,idan akai auren saita dora daga inda ta tsaya"
Chapter 45 · 0% Book details