← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 71

Sashe 17

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri ya ruqo hannunta, sannan yamiqe tsaye, yazare wayar Hajja dake hannunta, yasaka mata kudin cikin tafin hannun, sannan yayi danne danne a wayar kamar yana neman wani abu, yabata wayar tareda cewa "kisai ice-cream"

Daga haka bai qara cewa komai ba yajuya yatafi cikin sauri,saboda shi harga Allah kunyar bata kudin yake, kudin yayi qanqanta dayawa.

Aisha ta riqe kudin ta bishi da kallo, harya shiga mota, suka tashi, akan idonta, cikin zuciyar ta tace "nikam inani Ina wani ice-cream, banta6a Sha Bama"

Ahankali ta juya ta nufi masallaci jiki a sanyaye kamar kazarda qwai yafashe wa, tunani take aranta Yaya za'ayi ta nuna wannan kudin agida? Tace musu wa yabata? Duk da bata dubaba tasan kudi ne masu yawa,tana wannan tunanin harta ta'isa masallaci, bata samu mafita ba

******
Suna cikin tafiya Ramadan ya Kalle shi yace "kaganta ne?"

Kai tsaye yace "Eh"

"tafada ma abinda yasa tazageka?"

Dan qaramin tsaki yasaki yace "Shirman tane kawai"

"Yaya sunan tane yarinyar?" cewar Ramadan

"I don't know"
Yafada a gajarce

Murmushi Ramadan yayi, cikin ransa yana fatan ace su sake dawowa Garin

Bayan sun idar da sallar Kai tsaye gida ta wuce, Hajja tana cikin dakinta, Ummah Kuma tana Dakin Abba, danhaka saita wuce Dakin Ummah, da wayar Hajja ta haska ta duba kudin, gabanta ne yafadi, lokaci daya ta zaro idonta waje tace "dubu biyar?"

Tunda take, bata ta6a riqe kudin daya Haura dubu biyu ba, Amma yau gashi Wai ita aka Bawa dubu biyar, Tome zatayi da wannan kudin? Tasan cewa idan Ummah ko Abba suka Gani kashinta ya bushe, hatta Hajja ma saita tambayeta waye yabata wannan uban kudin?

Wani tunani ne yazo kanta, tasan babu me bude mata asusunta, koda tace umma ta d'auka toba ta6a mata kudi take ba, Dan haka cikin sauri tatura kudin cikin asusunta sannan tafuto ta wuce Dakin Hajja

******
Bayan sun koma hotel sunyi shirin kwanciya, yad'auki wayarsa yakira wata number, Bayan mutumin yadaga wayar Shahaab yace "Alhaji Inuwa akwai wani case din gidan Mai na wani Alhaji Audu, I don't know who his father... Please kadubamin file dinsa menene abunda yake faruwa"

Alhaji unuwa yace "Angama yalla6ai, yanzu hakama Ina office akwai aikin danake, Bari aje yanzu yanzu aduba"

Kashe wayar yayi batare daya ce masa komai ba

Baifi minti talatin ba dayin wayar su Sai gashi Alhaji unuwa yasake kira, cikin ladabi yace "yalla6ai file dinsa baya wajan mu, anturashi Abuja, abinda bincike ya tabbatar kenan"

Ahankali yace "ok" tareda kashe wayar

Addu'ah yayi ya kwanta tareda Lumshe Idonsa, Sai yanzu ne yake jin wata irin nutsuwa tana shigarsa, wadda shi Kansa baisan dalili ba.

Washe gari suka koma Abuja, Kai tsaye office suka wuce dagashi har Ramadan,magana yayi a duba masa file din Alhaji Audu, aka duba aka Gano, sannan suka kawo masa, saida yaduba yaga shine file din da aka kawo masa kwanaki yace akai shi wani office din suduba

Kar6a yayi sannan yabawa Ramadan yace suje suyi binciken dazasu akan file din, idan sun gama saisu sanar dashi.

Kasance war kwana daya baizo office ba Sai ayyuka suka taru suka masa yawa, Bai koma gida ba Sai Bayan sallar la'asar.

Da daddare Bayan yagama komai, yad'auko wasu takardun mama na wasu filaye daya siya mata da kudin ta daya saka hannun Jari awani company, takardun sunkai guda goma, yasan cewa idan yabata kudin ma cewa zatayi ya ajiye, shiyasa yayi dabara yasai mata manyan filaye dasu, daya Bayan daya yagama dubasu, zai dauke kenan Sai aka kira wayarsa, yayi mamaki ganin Kiran daga office dinsu ne, Bayan ya dauka suka tabbatar masa cewa wannan file din daya basu sungama bincike akansa, tabbas kudin Alhaji Audu ne, ba kudin sata bane, ya saida wasu kadarorin sane, sannan ya Gina gidan man, umarni ya basu cewa atura file din zuwa kano, Sai asakar masa gidan mansa.

Wani irin farinciki ne ya kamashi Bayan yagama wayar, shi Kansa baisan dalilin yin farincikin ba, maganar tace tafado masa Arai, "kanaji ko Yaron oga... Mahmud Wakili bashida mutunci"

Murmushi yayi, yamiqe tsam yashige toilet domin watsa ruwa, kwata kwata ya manta bai dauke takardun filayen mama ba.
Munirat data shigo Dakin domin kawo masa coffee,taci Karo da takardun azube atsakar d'aki, juyawa tayi ta kalli cikin Dakin kamar tana tsoron wani zai ganta, tsugunna wa tayi tadudduba takardun taga na filaye ne, mamaki ya kamata, ta ajiye coffee din hannun ta, ta sake duba takardun dakyau, take hudubar mahaifiyar ta tafado cikin ranta, cikin sauri ta dauke takardun manyan filaye guda biyu, sannan tayi gaggawar ficewa daga d'akin batare data ajiye masa coffee dinba.

Shahaab kuwa ya dade yana wanka sannan yafuto jikinsa daureda towel, hannu yasa yadauke takardun batareda yasake dubasu ba, Kai tsaye yabude wata yar qaramar akwatin sa ta adana sirri, yasaka takardun agefen inda ya ajiye ribbon din daya siyowa Aisha,kallon ribbon din yayi na Yan seconds sannan yasaka wasu numbers yarufe akwatin, ya shirya tsaf, sannan yafada kan gado tareda daukar wayarsa, number daya dauka a wayarta yakamo ya zubawa ido yana kallo, cikin zuciyar sa yace "ko tayi bacci yanzu?"

Har zai kirata saiya fasa, Tome zaice mata?
(nikam nace idan ka kira ma dandalewa zakayi da Hajja 🤣)

Ahankali yace "idan taji labarin Mahmud Wakili yasa ansaki gidan man Alhaji Audun nasu, nasan zatayi farinciki" fillo yaja yarungume a qirjinsa, da wannan tunanin bacci me dadi ya dauke shi, saida yatashi sahur mamaki ya kamashi yau meya hanashi neman munirat har yayi bacci shi kadai? (🤔)

******

Zaune suke atsakar gida, Aisha da Jummai suna tsince shinkafa, jummai ta kalli Hajja tace "Amma Hajja A'i wannan 6arawo naku da rashin kunya yake, Dan tsabar rashin mutunci ga mamuda yana kwance atsakar gida Amma har ya'iya dirowa cikin gida irin wannan me tsaro?"(🤣)

Aisha takwashe da dariya tace "infada miki iya jummai nice nafara jinsa lokacin daya shigo, Ina tsugunne aqofar bandaki naji kamar andiro ta cikin bandakin, aikuwa nayi tsilak natashi nadawo kusa da Abba"

Jummai tace "ahaf, to inaga Dama yasaba shigowa yana muku dauke dauke, Amma naso kun kamashi, da Sai mun Tara masa jama'ah"

Kafin su bata amsa daya daga cikin jikokin ta yazo Yakirata, daga Nan tayi wa su Hajja sallama tatafi gida.
Hajja tacewa Aisha"nikam da 6arawon Nan yashigo ya kwashe min kudin qanqara Aida bazanyi azumi ba gobe, wuni za'ayi Ana yaiyafa min ruwa"

Ummah data futo daga daki tace "Gobe jajiberan mutane Sai shiri suke yi, azumi yatafi kamar yau muka d'auka"

Aisha tace "au Wai Ummah da gaske gobe jajiberan kasuwa zataci kenan?"

Hajja tace "insha Allah jibi zamuyi sallah, mun kusa muhuta, gobe Kuma kasuwa zataci, inada cinikin qanqara gobe"

Aisha tace "dole ki riqe lokacin kasuwa ai, saboda kina samun kudi, larabawa suna kuka azumi zai tafi, kekuma murna kike jibi zakiyi sallah"

Hajja tace "ke suma kukan munafurci suke, wannan wahalar azumin idan dan'adam yakaishi lafiya ai abun azo har gida ayi masa barka ne, insha Allah jibi sallah"

Aisha tace "Wai Hajja waye yacemiki jibi sallah? Idan kuma ba'aga wata bafa?"

Hajja tace "ke Bari kiji, duk masifarki daga gobe de mungama azumin Nan, ke koba'a gamaba nikam na sauke, Kuma babu uban daya Isa yasa nayi, ai kowa kabarinsa daban"

Aisha tace "yanzu ma babu Wanda yahanaki saukewa, walakiri ne zai kamaki yadinga jibgarki kekadai babu me cetonki Sai Allah...."

Lokaci daya Hajja A'i tafashe da Kuka, ihun datasa ne yaja hankalin wasu samari daga waje suka shigo gidan sunyi tunanin mutuwa akayi, Ummah kuwa cikin ranta cewa take innalillahi wa inna ilaihirraji'un, yau Kuma abun na Hajja yatashi, tambayarta samarin suka farayi waye yamutu? cikin kuka Hajja tace "yanzu munzali, nime sunan qawa zatayi wa fatan walakiri yakamani da jibga kamar wata kafura"

Kafin su munzali subata amsa ta juya ta kalli Aisha tace "insha Allah babu abinda walakiri zaimin, fatan ki yaqare akan Hadiza da Mamuda..."

hawaye ne ya taru a'idon Ummah, ahankali ta juya ta shige cikin dakinta, sumasu munzali suka Bawa Hajja haquri sannan suka juya

Aisha kuwa harara ta zubawa Hajja, sannan ta wuce Dakin Hajjan kaitsaye, duk wani kayanta dayake Dakin Hajja yau saida tafitar dashi tas..., ko dankwali bata Bari ba, ta wuce ta maida shi Dakin Ummah, Ummah tana kallanta batace mata komai ba, ahankali ta zauna abakin gadon ta kalli mahaifiyar Tata tace "Ummah Dan Allah Kidena kuka saboda wannan tsohuwar, kiyi hakuri insha Allah ni nariga na yanke alaqata da Hajja, hakan bazata sake faruwa ba"

Ummah batace da Aisha komai ba, abinda tasani shine idan tabiye mata suks taru suka zagi Hajja, to Ana jimawa zasu shirya da Hajjan, menene amfanin ka daurewa yaro gindi? Ita kanta tasan cewa haifar Aisha kawai tayi, Amma duk wata wahalar ta da rainon ta Hajja ce tayi, shiyasa suka shaqu, koka shiga tsakanin suma kaine zakaji kunya.

******

Kayane masu mutuqar kyau da tsada azube agaban mama, dubasu tayi sosai sannan ta ware wasu, wayarta dake gefenta ta d'auka takira Shahaab Wanda ya dawo daga wajan aiki yake shirin shiga wanka, yanaso yatafi masallaci wajan tafsir, cikin ladabi ya dauka kamar yana gabanta, munirat data gama debe kayan daya cire Sai jinsa tayi yana fadin "to mama, gatanan zuwa"

Cikin zuciyar ta tace "kome take buqata Kuma? Jarababbiyar tsohuwa kawai"

Kallanta yayi yace "kije inji mama"
Daga Nan yawuce toilet.

Bata dauki dogon lokaci ba ta wuce wajan mama, tana zuwa mama tabata kayan data ware tace "ga kayan sallarki Nan, wannan Kuma ki aikawa tsohuwa, inji Dan Albarka Mahmud Wakili"

Maganar tamata ciwo, domin kuwa wani qullutun baqin ciki ne yatokare mata maqoshi, ahankali ta daga mata Kai, cikin ladabi tace "to mama mungode, Allah yaqara Arziqi"

"tun kafin kizo Arziqi Kam Dama can yana qaruwa, ke kanki Arziqin ne ya janyo ki, tashi kibani waje"

Wannan Karon munirat batace komai ba, tatashi tatafi.
Tana zuwa Kai tsaye d'akin sa ta wuce ta zubar da kayaiyakin akan gado, sannan ta zauna aqasan gadon tafashe da Kuka, yana futowa daga wanka yaganta tana kuka, ya kalli kayan dake kan gado, sannan ya dawo da kallon sa gareta yace "menene yake faruwa?"
Chapter 17 · 0% Book details