← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 71

Sashe 50

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu musu yafara furta"i luv you, I luv you.....saida yafada sau d'ari cif, kamar yanda ta buqata, sannan yace"nagama"

Ajiyar zuciya tasaki Tace"ka fanshi kanka,to ya gajiya?"

Ahankali yace"Alhamdulillah, but nagaji sosai maaamah, please kizo"

Cikin sauri tace"ina?"

Yace"kizo yanzu....wajena....inason tausa"

Murmushi tayi tace"aiban iyaba"

Cikin sauri yace"aizan Koya miki, Amma nafison kimin iya cinyoyina"

Cikin sauri tarufe fuskarta taqi bashi amsa, yace"kinji? Zakimin?"

Cikin sauri tace"zan mintsineka idan kasake fadamin haka"

Murmushi yayi yace"wacce qasa kike so aje ahado miki kayan lefe?"

Sai taji tambayar tasa tazo mata a bazata, har yanzu idan yayi wani abun mamaki ne yake sake kamata, Amma idan ta tuna da Mahmud Wakili take tare, saita daina mamaki, ajiyar zuciya tayi tace"nanan qasar ma yayi"

Cikin sauri yace"no, kifadamin qasar dakikeso Sai ahado miki,kinga bamuda isasshen lokaci dayawa"

Ahankali tace"ni bansan na inane yake da kyau ba, nabaka za6i, kayimin duk abinda Allah yahore ma, Amma karka takura kanka, kayi abinda Allah yahore ma kawai"

Wani irin sonta yaji yasake shiga ransa, yar qarama da'ita Amma sai Hankali, cikin jin dadi yace"toshikkenan za'a kawo insha Allah,please kiss me Maaamah, Ina kewarki"

Tace"kaiii, tayaya to? Waima Ina matarka kakirani a'irin wannan lokacin?"

Yace"tana dakinta, nide kimin abuna"
Yaqare maganar cikin sigar shagwa6a.

Ahankali tace"to tayaya?"

Yace"Ahakan"

Ahankali ta juya ta kalli Hajja, taga bangon Dakin take kallo tana bacci, ajiyar zuciya tasake yi sannan ta Lumshe idonta tasakar masa kiss tacikin wayar

Lumshe Idonsa yayi, cikin sigar rad'a yace"please maaamah cigaba, karki dena kinji...."

Ahankali taci gaba da kissing din wayar akai-akai yana jinta, jiyake kamar shi takeyi wa,babu musu Shima yafara maida mata, lokaci daya taji yanayin ta yana neman sauya wa, cak ta tsaya ta daina abinda take yi, Idonsa a Lumshe yace"why?"

Cikin shagwa6a tace"ni
... Nifa...uhm ni wallahi..."

"wani iri kikeji?"

Ya katse mata maganar Tata ta hanyar jefa mata wannan tambayar, babu musu tace"um"

Murmushi yasaki yace"Nima haka nakeji, shiyasa na matsu naganki acikin gidana, matsayin matata, mekikeso nayi Miki a rayuwa Maaamah?"

Cikin rashin Sani tace"kamarya?"

Fillonsa yasake rungume wa yace"kome kike so kifadamin"

Cikin shagwa6a tace"ni kainakeso"

Cikin jin dadi yace"sai Kuma me?"

Cikin jin nauyi tace" Sai waya idan Allah ya hore "

Murmushi yasaki yace"waya kike so?"

Cikin sauri Tace"eh"

Yace"kibari idan muka tafi Dubai honeymoon saiki za6i wadda kike so"

Ahankali tace"to"

Yace"todan sake min kiss din sainayi bacci kinji?"

Wani irin kukan shagwa6a tasaka masa, Wanda ita kanta batasan ta'iya shi ba,Adede lokacin Ramadan yadawo Dakin, ganin hakan Shima yasa yayi murmushi cikin sauri yace"to shikkenan,naji... Na haqura,Kidena min kuka, mayi magana gobe,please kiyi addu'ah"

Ahankali tace"to"tareda Lumshe idonta, kiss yasakar mata ta cikin wayar me ratsa jiki, sannan yakashe wayar.

Ahankali ta ajiye wayar itama, tafara shafa addu'ah ajikinta, Hajja tasaki ajiyar zuciya tace"ummm qarshan duniya yazo, irin wannan sumba azahiri qiri-qiri munaji muna Gani fisabilillahi kamar ba 'ya'yan hausawa ba?mesunan qawa kina masa irin wannan shagwa6ar ba waya ba ko duniya kikace kinaso ai dole yabaki"(🙆🏻‍♀️🙈😳😲🤭)

Lokaci daya Aisha ta runtse idonta,😖 shikkenan Kuma Hajja taji komai(🤦🏻‍♀️)

Please kuyi haquri da wannan ba yawa, mu hadu zuwa yammah insha Allah🙏

Shahaab littafin kudi ne, ki biya naira 300 kacal ki karanta halak dinki, muddin kika karanta baki biyaba wallahi tallahi nabarki da MAHALICCINKI ban yafeba🙅💁

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN tareda shedar biya ta wannan number 08033300034

Mrs Usman✍🏻

Page 40

"wannan d'a na Aysha da jaraba yake,yazo Nan yasaki agaba da naci ko Ina yabar matar tasa?"

Shiru Aisha tayi takasa bata amsa

Taci gaba da cewa "ai kina Jina Sarai,kishirya gobe dutse zamu tafi,akwai wajan wadda zan kaiki 'yar'uwar jummai ce, munyi waya tace nakai ki gobe, bansaniba inaga 'Dan gyare gyare zatasa a miki"

Sai a lokacin tace"Allah yakaimu"

Sannan ta ajiye wayar agefen fillo tashafa addu'ah tareda juyawa ta kwanta.

Saide baccin kwata kwata yaqi zuwa, tunanin sa ne yadawo mata Sabo fill,tanajin yanda yanayin ta yake sauya wa zuwa sha'awa, lokaci daya dukiyar fulaninta suka fara yimata qaiqayi, haka tayi haquri har batasan lokacin da bacci ya dauketa ba.

******

Shima a nasa 6angaren Lumshe Idonsa yayi, ya tabbatar cewa inda tana kusa dashi, babu abinda zai Hana ya kaiwa boobs dinta hannu, ya matsu sosai, halin da yake ciki yayi masa zafi dayawa, yadaiji lokacin da Ramadan ya dauro alwala yazo yacire kayan jikinsa ya kwanta, Amma shi Kansa baisan inda Hankalinsa yatafi ba, yana rungume da fillo kawai juya Kansa yake ahankali, Ramadan ya juya ya kalleshi duk da cikin duhu suke saida yaga halinda yake ciki, tausayi yabashi, yadaisan ba ciwon kan da yakeyi ne yasa shi haka ba, saboda ciwon Kai ba zaisa mutum ya rungume fillo haka cikin yanayi ba, ajiyar zuciya yasauke yace"kayi haquri mana, ai ankusa, Kuma....bata Nan, dasai kaje kaganta may be kasamu relief"

Ahankali yace"gara da batanan ai,Gara da Bana ganinta,because komai ma zai iya faruwa idan Ina ganinta"
Ramadan ya Girgiza Kansa yace"kuma da hakan ma,kadinga azumi kafin lokacin, zaka Dan samu sauqi ko Yaya ne"

Cikin sauri yadaga masa Kai batare da yace komai ba, daqyar bacci yayi nasarar dauke shi.
Asubar fari yatashi yashige wanka kasancewar yayi mafarkin ta tana masa tausa,Sanadin haka yaji shi jalaf... Dole saida yayi wanka sannan yatada kabbarar sallah, saida ya idar yafara lazimi sannan yaji za'a shiga sallar asuba, Ramadan ya tasa, Shima ya'iyo alwala sannan suka wuce masallaci, basu dawo gida ba saida gari yayi haske, suna zuwa Ramadan yahada masa tea Mai kauri yasha tareda magungunan sa, sannan suka kwanta, sosai Shahaab yayi bacci yanda ya kamata kasancewar bai samu yayi baccin ba da daddare, Sai wajan Sha daya da kwata na safe yatashi, Alokacin har Ramadan yayi wanka ya shirya yana kwance yana kallo, Shima tashi yayi yashige toilet yayi wanka, sannan yafuto ya shirya, sosai yaji shi garau kamar bashine jiya baida lafiya ba, ko kadan bayajin ciwon komai yanzu, Kai tsaye part din mama suka wuce, tana zaune afalo tana ganinsu tatashi tanufeshi, hannayenta ta miqa ta riqe fuskarsa tana fadin"yaya jikin Naka?tun dazu nake zuwa Naga Kuna bacci Baku tashi ba"

Murmushi yayi yariqe hannayenta data kama fuskarsa dashi yace"naji sauqi mama, Ramadan yabani magani Nasha, banajin ciwon komai yanzu"

Cikin jin dadi tace"Alhamdulillah"

Tajuya ta kalli Ramadan dayake kallon su yana murmushi, har yanzu yarasa gane waye yafi son wani acikinsu?
Mama Tace"Ramadan muje kuci abinci"

Bayanta sukabi, Kai tsaye suka wuce dinning, saida suka gama cin abinci suka danyi firar duniya, sannan Ramadan yawuce gida, Shikuwa Shahaab Kansa yad'ora kan cinyar mama, duk masu aikin dasuke zuwa wajan ta idan suka ganshi mamaki suke, Babban mutum kamar shi Amma har gobe kamar yaro yake awajan mahaifiyarsa, ganin masu yimata sallamar ba qarewa zasuyi ba yasa yatashi yashige dakinta yaci gaba da kallon acan.

(banyafewa Wanda ya karanta batareda ya biyaba)

******

Tafe suke da Hajja hannun Aisha d'aukeda kayanta, duk inda suka wuce Sai an gaishe da Hajja, tagaban shagon inusa suka wuce yataso da sauri suka gaisa da Hajja, Sai kallon Aisha yake qasa-qasa, yaso ace ita kadai ce dasun 'Dan zanta, suna wucewa Hajja tace "mesunan qawa mubi titi kawai,zaifi sauri"

Aisha tace"haba Hajja, aqasa ma Ana miki irin wannan gaisuwar idan muka hau titi Kuma ai sai ta Allah"

Hajja tace"ai nafiso inganni atitin Ana Hajja A'i, Ina d'aga hannu Inacewa na'am"

Dariya Aisha tayi tace"Saikace wata 'yar siyasa?wallahi bazamubi titi ba"

Haka suka dinga tafiya ta lungu da saqo har suka qarasa inda zasuhau mota, basu dade da zuwaba suka samu mota suka wuce dutse, Bayan sunje gidan sun huta Hajja tayi haramar dawowa gida, inda taqara yiwa Aisha fada akan magungunan ta na Sanyi ta dinga Sha kullum kartayi wasa dashi, matar mesuna Anty Mariya itace taraka Hajja, sannan tadawo gidan, sosai takejan Aisha da zance harta saki jikinta suke dan firarsu, washe gari tafara yimata gyaran jiki safe da Kuma yammah.

******

Yau Kam da shirin office yatashi, har mamaki yabawa mama yanda yake kokarin kula da aikinsa, inda wanine wannan rashin lafiyar tasa saiya dauka mata hutu awajan aiki, ko abinci baici ba saboda azumi daya dauka,yana kokarin shiga mota aka fara ruwan sama kamar da bakin kwarya, haka yashige suka wuce saide babu damar gudu, awajan aikin ma sunyi mamakin ganinsa duba da yanda Ramadan yake fada musu cewa bayajin dadi kwana biyu, sosai yayi aiki ranar,su kansu ma'aikatan sunsan Mahmud Wakili yadawo aiki, saboda yanda yasa aka riqe mutane basu tafi gida akan lokaci ba, Amma duk da hakan sun riga shi tafiya gida, shi bai tashi ba Sai yamma lis, koda wasa baiyi gigin Kiran Aisha ba, yasan cewa yana jin muryarta zai shagala ya manta da komai, Kuma ga azumi dayake, shiyasa ya tsaya tsayin daka wajan ganin yayi aikin yanda ya kamata, hakan ne yasa Hankalinsa yakoma kan aikin, Bayan yadawo gida wanka kawai yayi, ya shirya cikin qananun Kaya, wandon Jeans dakuma qaramar Riga wadda tayi masa mutuqar kyau,lokaci daya ya rikide yakoma tamkar saurayi Dan shekara talatin da uku, yasa hannu yad'auki system dinsa yayi wajan mama,zama tayi akusa dashi ta ajiye masa takardun companyn daya Bawa Aisha tace"Shahaab kayan Nan sunyi Maka kyau sosai kodan basaka qananun kayan kakeba?kullum daga suit Sai suit, manyan kayan ma basakasu kake ba"

Murmushi yayi baice mata komai ba, itama tasan ba lalle ne Dama ya tanka ba, danhaka tace"ga wannan takardun, ka ajiye mata awajanka, idan tazo saika bata"

Hankalinsa yana kan computer yayi murmushi yace"to mama"

Tace"bakaci abinci bafa, gashi ankusa Kiran sallar magrib, kaje office kawuni kana aiki, yanzu kadawo gida maimakon kahuta Kuma ka dora dawani aikin"

Tsayawa yayi da abinda yake yace"azumi nake yi,saide ahadamin tea idan nadawo daga masallaci Kuma zanci farfesun kaza medan yaji"

Cikin sauri tace"to" sannan ta wuce kitchen, Dakanta tahado masa tea din, sannan tasa me aiki tayi masa farfesun kaza, a gabansa ta ajiye masa tea din Sai turiri yake, saida ya jira aka kira sallah sannan yasha tea din, yawuce masallaci, baidawo ba saida yayi sallar ishsha'i, mama ce Dakanta tafara bashi farfesun, ta kalli yanda yake neman cinyewa, cikin jin dadi tace"kaida bakason yaji meyasa yau kakeci?"

Yace"mama banajin testing abakina, shiyasa"
Chapter 50 · 0% Book details