← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 34

Sashe 9

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ina gama secondry har ta gaba in je in fara aiki. Ya ce "Wane aiki ki ke son yi,? Ina nufin me ki ke son ki zama? na daga kaina sama ina nazarin ya ma ake ce musu? Ya ce ba ki san me ki ke so ki zama ba? Na ce, "Ya ma mutanen da ke yin labarai a Talabijin ko Rediyo? Ya ce, " Media ki ke so? na ce yawwa, haka zan zama 'yar media,yayi murmushi, to ni zan wuce, ina kayanki? Sai lokacn na tuna da tirena da kudina cikin ledar gwangwani, na ce to sai gobe. Na tafi ina waiwayanshi, ina cewa kai,wannan mu2min dan gayu ne,ga kamshin turare yana yi. Ranar Litinin tsawo naga ta min,yau kam d murna na iso,na nutsu ban yi wasa ba,saboda wata zuciyar da ke ce min in ya ki zuwa fa, ga shi na zo da sabon littafina, ba karamin damuwa nayi ba da na ga lkcn tafiyarmu yayi ban gan shi ba. Ina kulle gwangwanaye sai gashi, na ce hr na cire rai, ya ce ai zan zo, na ciro littafi na ba shi, tare da cewa wannan takardar ta isa? Ya ce eh, na ce na gode, na mika mishi gyada tare da cewa na rage mishi ne. Ya ce ya gode ya tafi. kai, kuruci dangin hauka, nifa tsakanina da Allah na yarda suke buga kudi. Daga ranar ban kuma ganin shi ba, Kusan sati 2 hr na soma tunanin ya gudune da kudina kun ji shirme. Wata ranar Jumma'a ranar za a yi wa dalibai hutu hr cikin Makaranta muka shiga muna ta ciniki,mun saida mun fito sai na hango shi tsaye gurin zaman mu. Da sauri na isa gurin shi, me bugakudi......
Chapter 9 · 0% Book details