← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 34

Sashe 33

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

unguwarsu da kuma dan lbr ta haka rahama tace unguwarmu daya, sannan ita daliba ce a Poly yanzu haka tana HND dinta ne. Iyayanta fa mutanen kirki ne? Rahama ta danyi din sanan tace eh yace ta taba aure ne? Kuma shadad dan tane? Nan take zufa ta karyo mata, amma bata da amsar da ta wuce eh ya jijiga kai, dama nayi zaton danta ne duk da batayi kama dashi ba sun rabu da mijinta ne ko ya rasu ne? Nanma tace eh, yace Allah sarki inaga shiyasa bata son hulda da maza, dama ance mace in mujinta ya rasu kafin ta manta da wuya. Iyayan ta din sunan layinku? Rahama tace eh, a a karatu tazo suna kaduna. Gurin aikinmu daya ne super market ne, yace to zan iya samun number dinta? Rahama tace wai gaskiya yallabai sai dai kayi hakuri, in na baka number ta zai iya zama sanadin rabuwar mu kwata-kwata. Ya dan yi shuru yana nazari, Rahama tace duk yanda kake tunanin hafsat ta wuce nan. Yace amma ina zaton bakinki naji yana fadin tana da saukin kai da dadin zama, kuma bata da fada? Rahma tace gurinmu mata ba, amma game da maza sam bata da sauki, ta tsani namiji ta kijinin ace anason ta sanan bata son taimako daga namiji, ko wannen abu 3nnan ba taso. Yace to me tafi so? Rahama tace abinda tafi so shine kada kashiga harkarta, in kuma kashiga kayi tsananin dace ta kula ka to kada ka tam bayeta ko wace irin tanbaya, sannan kada kace kana sonta, ban san me zakayi ba ta saki jiki da kai ba, don naga maza da yawa wanda suka sota amma dole suka hakura rashin sakin fuskarta yasa maza suna tsoranta. Da zaka hakura da ya fi maka lada don ko taji hau shin abinda MC yace mata a gurin bikinmu inda yace ku miji da mata ne. Abubakar yace niko sai naso ace gaske naji dadi maganarsa. Rahama ba zan iya hakura da hafsat ba don ina jin wani abu game da ita wanda ban taba jinshi a wata yarinya ba ina zaton shine so. Su Rahma suka sa dariya sagir ya nisa yace lalle sonka din nan ya iya jan rigima ya fada inda zaku sha wahala Abubakar yace sona yayi daidai don yasan bama ra‘ayin mata marasa aji wadanda ke bin maza da kansu suce suna so zanje in gwada sa‘a ta kafin na bar kano zanga yada zamuyi. Sukace Allah ya taimaka yace kasan ban sami daurin aure ba so bansan gidansu rahama ba bare insan nasu hafsa din. Yace bari inje in nuna maka daga nesa suka fita suna dariya ba tare da yace komai ba shi tuni ya manta da menene a gabanshi ko da sagir ya nuna mashi sai yace ba yanzu zanje ba sai gobe da safe. Ni kam tuna ranar da muka dawo daga bikin rahama kulin shadad bashi da magana sai ta uncle dinshi tun ina jin haushin shi ina mai fada har na dawo lallashinsa, saboda har lokacin yana fama da zazzabi nakan lallabashi da cewa kayi hakuri zai zo ya daukeka ranar cikin dare har da cewa to anty kirashi a waya nace to ka bari sai da safe yanzu yayi bacci, cikin kwana ukun nan da kyar na samu ya manta da maganar uncle sai jifa-jifa. Da safe yana sanye da kayan makaranta ni kuma nayi shirin gurin aiki. Yau bani da lecture da safe don haka gurin aiki zanje dama ka‘idar da manaja ya bani kenan dan a daidaitanmu yana jira, shadad ya fita da gudu ni kuma na kule dakin na fita. Ina rufe gida naji muryar shadad yana cewa anty ga unclena anty na wai wayo baya na datse kwado, ilai kuwa yana tsaye jikin wata yar kyakyawar motar blue kiran kanfanin (toyota) sanye da t-shirt da wando jeans baki, riga baka da ratsin ja. Ta kalmin kafarshi baki ne sauciki. Na dauke fuskata daga kalonshi bacin nayi fuskar shanu shadad wanda tuni ya daneshi, murna yake yana cewa unclue kazone? Da ma anty tace indaina kuka zakazo, takaici ya kamani. Shi kuma sai ya dubeni anty antashi lfy? Ba tare da na kaleshi ba nace kalau na daga labuln dan a daidaita na shige. Sai naji yana cema dan a dai daitan, ungo nan malam kaje sai bayan kwana 2 ka dawo tun da nazo ni zan rinka kaisu kafin in tafi. Ya mika mushi yan dubu dubu sababi fil guda 3 ya amsa yana cewa na gode yalabai to sai zuwa yau she zan dawo yace nan da kwana hudu haka nace sannu da karfin hali menene gamina da kai? Da har zakaso ka min iko? Bai ce kala ba ya juya. Na cema dan a daidaita sahu muje na leka nacewa shadad zo mutafi ko nayi tafiyata. Mutumin ya kaleni shima fuska a kame ki fito muje ban san sanda nace to ubana! Sai kazo ka jani ya kara matsowa saitin dan a daidaita yace ka sauketa katafi abinka. Sai kawai mai a daidaita yace kiyi hakuri yar uwata, ki sauka ban tankashi ba bankuma sauka ba,gani nayi zamuyi latti nace yanxu kai malam haka zamuyi da kai? Duk tsawon lokacin da muka dauka yau kace bazaka kaini ba? Yace to Alhaji ne yace ki sauka ai, kuma ni bansan dangantakarku ba kada in shiga hurumin da banawa ba. Nace to bawata dan gantaka a tsakanin mu, asalima ni ban sanshi ba da muna da alaka da baka gan shi ba ko sau daya? Yace ki sauka mana nasan duk yanda akayi kunsan juna. Ganin zai bata min lokaci sai na sauka na dauki jakata nace shadad ya wuce muje, a mota yasaka shi amma ya tada mota sukayi gaba. Na tare mai mashi muna ciniki yazo yace mai mashi tafi abinka, in ka dauketa zaka gamu da hukunci... kafin ya rufe baki yaja mashin ya kara gaba. Na kaleshi nace me kake nufi dani? Yace gurin aiki zan kaiki kawai,nace banaso dan Allah kai mayene? Yace a'a ni ba maye bane, to bin me kake min? Nifa ba yar iska bace. Yace nasani ai, to dan Allah kafita hanyata, in kanawa darajar mahaifinka. Yace don girman Allah ki shiga motar nan mu tafi, kada shadad yayi latti, sannan inaso ki bani lokaci nazo mu dan tautauna, nace bani da lokacin da zan iya baka, ka fita harkata please, nacigaba da tafiya. Ranar dai a kasa na tafi gurin aiki, shikuma sukayi wani guri shida shadad, nasan sai dai suyi tambaya amma shadad ba zai iya gane makarantar ba, ganin nakusa bansha wahalar hawa abin hawa ba na karasa, takwas ta gota ina shiga ishak yace yau bamakaranta kenan? Nace eh, gashi ma nayi latti, musa yace manaja kuwa yazo yananan ya zagaya ciki nasan sai yayi maki surutu, nace uhum sai dai yayi tunda dai latti na riga nayi shi.Ina zama yana isowa, ban ko kalleshi ba na jawo takarda dake kan teburina zan fara duba abubuwan da suka fita da safen nan, sai ya ce, "Kin san zaki zo da safe me yasa zakiyi latti?" Na ce, "Abin hawa ne ban samu ba." Ya ce, "Amma ai ba'a wahalar mai ko?" Na ce, "Kamar yaya?" Ya ce, "Ballantana ki ce ana wuyar abin hawa." Na ce, "Akwai abin hawa mana." Ya ce, "Baki da kudi ne?" A kagare na ce, "Ina da shi." Ya ce, "Ok kin soma gajiya da aikin kenan?" Na san shi sarai zai iya cewa ya koreni, kuma dai Allah ya sani da aikin na dogara, don haka nace, "Tunda ba halina bane lattin amin uzuri." Ishak yace ayi mata hakuri Sir. Ya ce, "Kune kuka iya bada hakuri ita bata iya ba ko? To ba zan mata uzuri ba, sai dai in taimaka mata." Cikin sauri na ce, "Bana son taimakon kowa sai na Allah, nace dai amin azuri." Ya ce, "To ki je gida ki huta na sati 2 don ki koyi yadda zaki dinga zuwa aiki." Muryarshi muka ji ya ce, "Uzuri za'a yi mata manaja." Ya dubeni har na mike, "Koma ki zauna. Manaja akwai uzuri a rayuwa, ko tana latti?" Ya ce, "A'a ranka ya dade bata dai da mutuncine, in banda rainin hankali tana fada min akwai abin hawa kuma tana da kudi amma ta zo latti?" Ya ce, "Duk da haka ka mata azuri da tace baka san dalilin ta ba, so tayi zamanta." Na dube shi ina mamakin karfin halinsa, sai naga ya nufi Ofishin manaja na ce kila ya san shi ne. Ni dai na zauna na ci gaba da aikina. Ina jin Musa da Ishak suna mitar rashin mutuncin shi.Abubakar ya dubi Manaja ya ce, "Ka daina yiwa mutane haka, musamman na kasa da kai, a rayuwa dole ne mutum ya dinga hakuri, yanzun kasan uzurin da ya tare ta?" Manaja ya ce, "Yallabai yarinyar nan bata da mutunci sam!" Ya ce, "Ko zan iya sanin halayen ta marasa kyau?" Ya ce, "Na 1 bata da fara'a ga kallon banza, kuma ta fi karfin kace zaka taimaka mata sai ta hau bala'i, ina ce sakin fuska ma abu ne?" "Ni kuma hakan ya birgeni." Abubakar ya katseshi, "Ban ga laifinta ba, don ta kare mutuncin ta. Shi kenan sai ya zama zubar da mutunci don bata saki fuska ba?" Manaja ya yi 'yar dariya, "Yallabai yarinyar nan fa in ma sonta kake ka hakura don ba zata baka hadin kai ba, in mata kake so 'yan gayu isassu na debe kewa sai in kawo maka su. A ina ka sauka?" Abubakar ya ce, "Na fada maka ina son ta ne? Ko na fada maka ina son mata ne? Inma matan nake so ai baka fini saninsu inda zan same su ba, ina maka nasiha ne ka daina wulakanta na kasa da kai, in dai suna yin abinda ya dace." Ya ce, "To zan kula Yallabai -ya ci gaba da cewa- Ya hajiya? Ai mun yi waya da ita jiya tace matake fada min kana Kano zaka shigo ka duba abubuwan dake tafiya." Abubakar ya ce, "Kwarai kuwa, bari in duba takardun. Fito min da su." Ya jima sannan ya kammala ya fito, Manaja yana biye da
Chapter 33 · 0% Book details