← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 34

Sashe 13

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

hankali, kina fa da masaniyar ina da burin tsayawa takara a siyasa mai zuwa, ko kin manta? Kin san cewa abokan gaba za su iya fakewa da wannan su ci zarafina har suyi nasarar kada ni? Ta ce to yanzun yaya za'ayi? Ya ce bani Yasir din a waya, ko ba ya kusa? ta ce ba ya kusa, ka kira layinsa. Yasir ya daga kiran wayar Mahaifinsa, ko gaisawa ba su yi ba ya jeho masa tambaya, gaya min gaskiya kai ne kayi cikin? Yayi shiru, fada min na ce kai ne ka min shiru? Uban ya fada cikin daga murya. Yasir ya ce "Dad ba zan kara ba, Mahaifina ya ce, Ok kai ne kenan? Ya ce Tsautsayi ne. Alhjn yayi shiru yana nazarin abn yi. Can yaja tsaki, in ka kuma ranka zai 6aci fiye da zatonka. Abn da zan maka sha mmki, kila ma kayi zaton ko ba ni ne na haife ka ba. Ya ci gaba da fada. In ma ba iskanci ba duk nawa ka ke 25 years amma ka iya jarabar mata? Yasir ya dinga ba wa Mahaifin shi hakuri, Alhjn ya ce shi kenan, ya kira Hjy Mairo ya ce, kada su shiga kotu, su nemi sulhu duk yanda aka yi su fada mishi. Washegari da kanta taje ofishin shugabar kungiyar don neman sulhu. An kira Dakta Hindu sun zo tare da Asabe, sharadin 2 suka gindaya wa Hjy Mairo, aka c ta za6i daya.Na farko ko dai dan nata ya auri yarinyar bayan ta haihu, na 2 kuma in ba zai aure ta ba, to zai dauki nauyin cikin tun daga yanzu hr zuwa lkcn da za a haife shi a yaye shi. Daga bisani su dauke shi. Hjy Mairo ta nemi saukin Asabe ta rike danta za su ci gaba da mishi komai,amma shugaba ta ce a'a ba za su yarda ba, domin Asabe in ta samu miji aure zata yi. Ba zai yiwu ta tafi da dan wani gidn wani ba. Nan ta take ta kira mijinta ta mishi bayanin komai, ya ce su dauki za6i na biyun in yaso zasu yi shawara in ya dawo. Ta ce to. Nan dai aka yi dogayen rubuce-rubuce, kowa yasa hannu Daga nan ta tafi........
Chapter 13 · 0% Book details