← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 34

Sashe 22

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nake ceki sai da nayi Allah wadai da shugabannin da muke dasu. Asibiti ka mar wannan ace likitoci mata basufi uku ba, ga mata nan sun kusa 100, wata mata dake kusa dani tace min tun asubahi suka zo nan tayi sallah. Amma har yanzu ba‘a zo kanta ba. Ina ganin rashin kula da ba ayi da likitocin shine dalili da yasa basu zuwa aiki. Haka muka yini a gurin, amma baba ya dage sai munga likita. Muna shiga ya bashi kati likita ya tambayi meke damuna?Kafin nayi magana baba yace yata ce, munzo ne ayi mata gwaji kotana da juna biyu. Likita yace bari yaji ta bakina, ya tambayeni meke damuna? Nace basir da shawara, yace yaya kikeji a jikinki? Nace amai da zazzabi. Kama hannuna yayi ya duba, nan take ya bamu wata takarda wai muje amin gwaji nayi fitsari na kawo. Nan take sakamako ya fito baro baro ina da ciki nurse bata fada muna ba, ta dai bamu sakamakon mu kaiwa likita. Lokacin zuciyata ta gama bushewa, na mekawa Allah komai. Mun shiga yana rubuta muna wani magani, sai da ya gama sanan ya duba. Ya kali baba, tana da miji? Baba yace a a likita yasake kalona, amma ke kinsan kina da ciki? Wata muguwar faduwar gaba naji, tamkar yau nasoma jin cewa inada cikin. Baba yace tanada ciki ko? Yacigaba da rubuta wata ta karda yana cigaba da cewa tana dauke da ciki. Abinda sakamako ya nuna kenan. Amma kuje ayimata (scan) don kusan ko wata nawa ne inna kawai na kallah wada ta kafa min idanu sun kada sunyi jajajir,Baba ya ce a"a bama bukatar sai tayi hoto,dama tabbacin cewa akwai cikin muke son sani, tunda akwai shi kenan. Ya kalli Innarmu,bana bukatar sai na sake tuna miki komai daga ke har ita. Ya fita abinshi. Inna cikin kuka ta ce, Hafsa haka zaki min? Hafsa na dace da wannan sakamakon? kin min adalci kenan? cikin kuka nima na ce kiyi hakuri Inna, wlh fyade Munnir ya min. Ta ce, karya ne, ki min shiru. Ta dubi Likitan da ya zuba musu ido,don Allah Likita ka taimake ni ka cire mata cikin nan. Da saurin Likitan ya mike tsaye cikin murya mai karfi, fita anan domin nan ba asibitin zubar da ciki ba ne. Muka fito muka nufo gida, Inna na fadin Hafsa kin cuce ni kin kuma cuci kanki. kafin mu isa gida tuni Baba yaje yayi fadan shi a tsakar gida kamar yanda ya saba, muna isowa kowa sai kallonmu yake yi. Muna shiga yazo ya ce ya va mu zuwa da safe mu fice, yanzun ma don dare ne. Mutane na ta bashi hakuri,amma ya ce to wane hakuri zai yi? Dan ya ce mata in haka ta faru a bakin aurenta, kuma ta yarda. Ranar inna kasa fadan nata tayi, duk da matan gidan da suka cika a kofar dakinmu. Ni kaina kasa min fada tayi sai kuka da take shara6awa. Mun kule can daki, can cikin sulusun dare na tashi dan bacci taya dauki Inna na fice. Bayan na kwashe duk wani abuna mai mahimmanci, Baban titi na mika ina tafiya ba tare da tsoro ba. Daf! da Asubahi naji wata mota suna cewa kano ne? na tsaida su na shiga duk da cewa ba ni da ko sisi,saboda ragowar kudina na mikawa Inna tun zuwa na, wato kudin wayata. Sai da muka dau hanya suka ce dari biyar zan ba da, bn yi mng ba, don haka sai suka zata na yarda ne. bakwai da 'yan mintuna muka isa Gyadi-Gyadi, suka ce kudina, na ce bani da kudi,don Allah su taimaka min. Nan kwandastan ya hau ni da zagi, ni dai kallon shi nake yi. Direbn ya ce, in je amma nan gaba in banda kudi in dinga magana tun kafin na hau mota, don ba kowa zai iya kyale ni ba. Na ce na gode.Sai lokacn kuma na soma tunanin ina zan je? Wata zuciyar ta ce bakina karanta littattafan su Anty Fauziya D. Sulaiman da su Anty Sadiya ba? Ai suna fadin cewa in yara sun gudu su kan je wani gidan a rike su a taimake su. To suma ai sa rike ki in kin je ki zauna da sy za su fahimce matsalarki don suna rubutu kan haka. Amma sai wata zuciyar tace, ki je gurin Likita nan, ban san lkcn da na tsaida dan mashin ba, na masa kwantace muka tafi. Ta fito kenan zata ofis sai gani, ta ce a'a Hafsa ce .da safen nan? Na ce eh, Anty ga shi ma bani da kudin da zan ba mai mashin din. Ta zuge jakarta tana cewa, nawa ne? na ce,daga Gyadi- Gyadu ne ba muyi ciniki ba, ta bashi dari biyu,naga dai ya bata canji, amma bn san ko nawa ba ne, ta ce daga ganin ki ba wata nasara amma shiga ciki. Sai da ta huta bayan ta dawo sannan na fada mata komai, tace to ke yanzun menene burinki? Na ce ni da zan samu wani dan aiki in dauki nauyin kaina ba tare da na sake neman taimakon kowane da naminji ba, zan so haka,amma da wuya tunda takardun sakandire kawai gare ni, ta ce amma bn san hikimar guje ma iyayenki da ki ka yi ba, musamman mahaifiyarki wadda ta gwada miki kauna. Da kin bita kun gudu tare ko kwa tsira tare. Na ce Aunty ina tsananin jin kunyar mahaifiyata. Ba zan iya zama da ita ba. A halin yanzun itama nasan ta dauki hanyar gidansu, da wane ido zan kalle su? Ta ce to yanzu ina son ki zauna nan mu ga yanda za"ayi. Ni da Asabe mun zama 'yan gidan Doctor Hindu, ita ke mana awo da komai, magunguna duk ita ke ba mu. Cikin haka hr muka shiga watan Haihuwarmu ko na ce haihuwar Asabe. Ta kawo min kaya jarirai yayin da Asabe aka kawo mata daga gidan su Yasir. Doctor ta ce, Kin gani kin hana mu dauki mataki da kema yanzun dole su ringa yi miki komai. Na ce, Bar su kawai Anty, Ni yanzun ba n da burin da ya wuce in haihu lafiya, ina so in tsaya da kafafuna ko Allah zai taimake ni in dawo da iyayena farin cikin su. Ina tuna kannena, musamman Ummi, Nasan Baba kishiyar Innarmu bata da mugunta, zata rike su amma nasan ba za su yafe min ba, Matsawar suka ji cewa ni ce na kashe auren uwarsu da ubansu. Doctor ta ce kada ki damu, Insha Allahu za ki dawo musu da komai. Asabe ta haihu'ya mace, kyakykyawa. Duk da 'yan gidan su Yasir da shi kan shi ba su zo ba, amma sun aiko da komai hatta ragon suna. Sannan suka ce ta sa ma 'yarta sunan da take so. Doctor ce ta bada shawar a saka sunan mahaifiya Yasir wato Maryam.A cewar Likitar, zai fi girmama yarinyar duk lkcn data koma gare su. ... A ganina matsalar Asabe mai sauki ce, don mahaifiyarta har duba ta tazo sa6anin ni da ban san halin da nike ciki ba? suma ba su san in da nike ba, Mai aikin Doctor ita ce ke mata wanka., Kwanci tashi ni ma(E .D. D) na ya cika har ya gota, amma shiru ba batun nakuda bare haihuwa, Ranar Litinin tana min gwaji ko na ce awo, ta ce yaran nan naki fa yayi girma da yawa ga shi kin kasa kwantar da hankalinki jininki kullum kara hawa ya ke yi. , Yanzun ya wuce ka'ida ina miki tsoron afkawa cikin matsala, kin kasa daukan kaddara. Kuka ya kwace min Anty zan so in mutu a gurin haihuwa nan, shi ne kawai burin zcyta. Likitar ta ce dama mun saba fada, duk lkcn d zan miki awo,mugaye fatan d ki ke yiwa knki kuwa da kina da kambun baka da yanzun kin lalace., Na ce Allah isa tsakanina da Munnir Ta ce " Ameen. Amma yanzun na fi so ki kwantar d hnklnk kin ji? Na ce to. Wasa- wasa gani na kara sati 3 ta ce in na kara kwana 3 za a yi min akin. Talata Doctor ta tafi wani taro a brnin Tarayya, ranar ce kuma na soma nakudar Haihuwa. Haka na kwna na yini, mai aiki tana kula dani, bayan magriba ta shigo fada ta hau mu da shi me yasa b muje asibiti ba? Ni kam na galabaita matuka,gado aka turo aka dauke ni, zuwa cikin asibiti, amma haka na sake kwana dole ayi min aiki. dn hk Likitar tasa a min shiri a sani a dakin tiyata.Tare da taimakon wani Likitan suka yi nasarar ciro min katon yaro namiji. Hakika na matukar shan wahala, kusan kwana 3 ban sami kaina ba., Sai a rana na 4, din ranar har na tashi an jingina min filo. Likitar ta kawo min yaron. kai na kauda domin a ganina shi ne silan raba ni da iyayena. Ban ta6a ganin fushin Likitar ba a iya zamana a gidanta sai yau. Ta ce, Dauke shi ki ciro nono ki bashi . Na fashe da kuka Anty ban yi aure ba kada ki sa in ba shi nonona su fadi, ba zan ba shi ba. Ya ya za'ayi ya raba ni da iyayena, na ci gaba da kuka, ta ce ke rike shi kafin in zabga miki mari. Shi ina ruwan shi? Shi ya samar da kan shi ko samar da shi ku ka yi? Don me za ki ga laifin shi ? Da ba ku aikata abin da ku ka aikta ba da Allah bai samar da shi cikin mahaifarki ba, ganin irin kukan da nike yi yasa ta koma lallashina, bayan na dauke shi. Babansa ya juya masa bya, kada kema ki zama kin juya masa, Kina nufin ba za ki rungumi kaddara ba? da lallashi ta shawo kaina na ciro nono yana sha ina kuka. Satina daya na gargije, muka koma gida., Ba a yanka ragon suna ba, sai dai na ce ma Anty duk sunan da ya dace ta sa mishi ta ce a sa mishi SHADDAD. sunan wai yana mata dadi. Har ta kara da cewa da Allah ya nufe ta da aure ya bata da sunan da zata sa masa
Chapter 22 · 0% Book details