← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 34

Sashe 32

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 1-09 Posted by ANaM Dorayi on 12:23 PM, 18-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Don itama haushinta nakeji ba don bukin ta bane wa za ya hadani da wayanan gardawan. Cikin fada nace wai meye ne kika dame ni da kira, ina hanya in kuma zaki matsa min sai na juya gida abina. Tace mai da wukar Allah ya baki hakuri, da ma ruwan da ake shekawa ne nace bari naji ko kin koma gida ne saboda ruwan sai direban su sagir yazo ya daukeki. Nace na hutar dashi, gani nan zuwa na kashe wayata tare da tsaki.Harabar hotal dam yake da jama‘a, ko ince motoci jama‘a sun cika holl din suna tsayawa na kama kofar zan buduwa. Ashe daga gaba ne direbab zai bude mu. Yana budewa na fita, sanan na nufi ciki mai surutun tsiya nan shadad ba tare da na kalesu ba na nufi wata yar baranda ina ta yi mashi fadan irin surutun da ya dinga tsugawa acikin motar, sai ya bale mun da kuka yana fadin.uncle! Uncle!! Nace yi min shuru ko in mareka, sarkin shishigi, bai daina kukan ba, na na ciro wayata na kira rahama gani nan fa ba zan iya shiga ba, mutane sunyi yawa. Ta ce mun ganki kin tsaya ga Aisha nan tazo zata taho dakegurin mu tare zamu shiga. Nice a gefen amarya sauran kawaye suna bayan mu,haka nan ango da abokan shi suna biye da mu, ina reke da hanum shadad, wanda har lokacin bai daina gunjin kuka ba, muka shiga. Kidan da ke tashi kamar zai fasa kwanya yasa naji tamkar in bar gurin kai tsaye. Wani mai dauke da abin magana yace, ango da amarya sun shigo, kowa da amininshi zai zauna, sagir ya zauna gefen shi wanan mutumin, ni kuma ina gefen Rahama tare da shadad ta dube ni, mutuniyata wa ya taba ki ne, naga fuskarki ta kasa boye fushinki, nace uhm! Ke dai bari, abokanan muijinki ne wlh, sai kuma shadad yaron nan ya kular dani yau. Tace to dan saki fuskar mana saboda guri ya kayatu, kisan fushinki zaisa gurin ya dishe. Na harareta tare da dan murmushi, tace ko kefa. Sagir yace ranki yadade, ya gajiya? Na nace tana gurinku ya jama‘a? Yace gasu muna tare nace Allah yasa alheri, da ganan na maida hankalina gun mai abin magana, yace za mu kira baban bako kuma baban abokin ango don yayi mana jawabin maraba tare da dan fada mana wanene sagir. Sai dai kafin nan babar kawar amarya hajiya hafsat sai ta bude mana taro da adu‘a, na kali rahama tace please, tashi kawai. Na mike cikin natsuwa na isa gurin na amshi abin maganar. Shadad yazo ya rikeni yana kuka, sai wai abokin ango ya taso ya daukeshi. Bayan n gama adu‘a na dora da karanbanin nawa, ina bawa jama‘ar da ke gurin nan shawar kada suyi liki, almubazaranci ne ga duk mai sha‘awar ya burge ango da amarya su dan ka musu a hanun su, amma ba dole bane kuyi yanda nace,sha wara ce. Na koma na zauna, bayan sun bini da tafi. Shiko da zaije yin jawabin maraba tare da shadad yaje yana rike da hanunshi. Cikin jawabin ne naji yana jaddada maganata cewa abinda na fada yayi kyau, don haka ba‘a son liki, duk wanda zai lika yazo ya ba ango ko amarya a hannusu. Wanan ma yasa aka kashe rawa da za‘ayi, rahama ta dinga yi min dariya wai a gaisheni da karfin hali har ta sanima na dinga dariyar. Sagir cewa yayi nazo na hanasu rawa, to wane rawa zasuyi ba liki? Nace tai makonku nayi ai rawa haramun ce ko? Haka aka ta gabatar da abubuwan da za ayi har lokacin da akayi sanarwar ango da amarya tare da da masu tayasu zama dan dibar abinda suke son ci da kansu, kasancewar dibi da kanka ne za ayi a gurin. Muka hadu muka jeru amarya tana biye da ango yayinda ni kuma nake biye da abokin nashi, shi kuma yana dauke da shadad a kafada tamkar wani danshi. Ango yasa abida yake so sai fruit ya ce ko zaki tai maka min? Inji abokin ango tamkar ince a'a amma sai nace me zan sa maka? Ganin yana sabe da shadad yace ki samin ko menene, zan ci. A raina nace kaji dashi, ba tare da tsayawa tunani ba ko mai hanu na yakai shi nake zuba masa, sai da na shake plate din sannan na bi bayanshi da plate 2. A gabanshi na dire tare da samashi cokali, na koma ma zaunina. Sai kurum naji sarkin surutun nan wato mai rike da abin magana yana cewa, kai gaskiya ango da amarya kun burge ni, kun zauna da aminan ku kuma mata da miji har da dansu, to yace ke amarya yaya bakiyi koyi da kawarki ba kema ki zuba ma ango da kanki? Kai abokin angon nafa yi maka murna, matar kada kayi mata kishiya, dubi yanda ta cika maka plate da kaji da kifi kila abinda ka fi so kenan, wanan ya nuna ko a gida ba a barinka da yunwa. Sai kurum naji gurin ya dau tafi. Da sauri na dubi plate din, lallai kam kaji ne da kifi, sai dan cosilo a gefe, na dubi fuskarshi yana dan murmushi. Rahama da sagir kuma dariya naga suna ta shekawa nan take na hade rai tare da kin kai komai bakina. Shiko shadad sai uban cin naman nan yake yi, shi da mutimin tuni gurin ya rikice da ciye ciye kowa na diba da kansaRahama tace to kici mana,nace mata ke ni nama koshi, ba yan haka ma ni ba zan iya cin komai a taron nan ba, kowa yana kallona. Haka nan bayan an tashi duk na matsu naje gida domin magariba ta yi, ina so inyi sallah sai dai tun da muka fito banga shadad ba, ban ga mutumin nan ba. Nace rahama ina suke? Tace suna cikin jama‘a in dan jira. Can nesa na hango wani shago naje na siyo ruwan naira 10 nayi alwala, nasami gefe dama da hijabina a jaka, nayi sallah ta. Rahama tazo tana ce min sun dawo? Nace ke zan tam baya, ina mijinki? Kune kuka sanshi ku zaku nemo shi. Takira sagir tace sun ko dawo? Hafsat tana son zuwa gida. Yace a'a na kira wayarshi kuma a kashe, tace a a to ina ya shiga? Kai kana inane? Yace gani nan kusa da shago ina kallon ku ai. Muka nufi girin ango, hankalina ya tashi da rahama take fada min wai wayanshi a kashe.rahama ta dubi angon ta tace, ba kace min bako ne ba? Yace eh amma kano ba bakuwa bace a gurinshi. Ki kwantar da hankalinki, yauwa gasu nan zuwa ma, duk muka kai duban mu gurin shi. Yana rike da hanunshi, shi kuma yana reke da leda. Suna tafe suna yan zan tukansu har suka isko mu, nace kai ka cika shegen yawo, ina kaje? Na finciko shi yace anty munje masalaci ne da uncle, ba kin ce mun wai in dinga sallah a farkon lokacinta ba? Nace naji ni dan Allah wuce muje na dubi rahama sai watarana, tace dinner din fa, anjuma karfe 10 naja tsaki ke kinsan ba zan iya wanan galafirin ba, gara ke sai dai nazoo. Sagir yace ki bari a kaiki don Allah, gari yayi sanyi ga duhu, nace nagode, sai anjima nayi gaba.Wani daga cikin abokan da suke tsaye wanda har dashi muka shigo motar nan da zamu zo, ya dubi rahama yace kai wanan kawar taki ta cika masifa, ita ba kyau ba rahama tace a a kada ka zagar mun kawa masa‘udu, hafsat bata da masifa,tana da kirki sosai na jima banga mace mai saukin kan hafsat ba, ita dai abu 3 ta tsana a rayuwarta, inko mutun ya kiyaye ba mai jin su. Ni da ita bamu taba yin fada ba koda munyi sai dai ni ni na ta sababi na amma bata biye min. abubakar lamido yace yanzu kai kaga masifarta? Ya dubi masa‘udu masa‘udu yace au yanzu duk abinda take maka baka gani ba? Yace ni kam me tamin? Bata min komai ba, duk abubuwan da takeyi sun matukar burgeni. Ya dubi rahama, ni kam in tambaye ki? Rahama tace ina jin ka, yace amma dai ba matar aure bace ko? Rahma tace a a daga nan bai sake magana ba. Duk abubuwan da Abubakar Lamido ke gani daga hafsat bai taba ganin wani aibunta ba, tunani 1 ya dameshi, ina ya santa? Shi dai yasan cewa koda a hanya ne ya taba ganin ta. Anashi ganin Hafsat ta san mutuncin kanta shiyasa take wanan dabi‘un. Acikin masauki ya kasa zaune da tsaye, baisan meyasa ya damu kanshi da dabi‘un hafsat ba, bai taba ganin mace da ta burge shi irin ta. Yasan daga ganin halayenta za asha wuya kafin a samu soyayyar ta, duk da bashi da tabacin sonta yake ko burgeshi take. Ya dai san ko ma dai menene ya damu da ita. Kafin kwana 3 ya damu da son sanin wacece ita? Alwashi ya sha ma kansa ba zai bar kano ba har sai yasamu cikaken labarinta, wanda yasan gurin rahama ne kadai zai san haka, haka a rana ta 4 ya kira sagir yace gashi nan zuwa, zaya ci dinner tare dasu. Duk da tulin kayan da aka tara a gaban shi na lashe-lashe da tande-tande, sam basu dameshi ba, ya dubi sagir cikin hausarshi na fulanin yola ya ce, nikam ka bani dama inyiwa amaryarka wasu tanbayoyi game da kawarta nan sagir yace wace ba dai hafsatba? Bai san da lilin fadiwar gaban da yaji ba, haka nan bai san lokacin da kalma ta fito daga bakinshi ba, tana da miji ko? Ya tsare sagir da idanun shi masu kama da na mata.Sagir ya ce bata da miji, amma fandarrarun halayenta ne zasu gundire ka, yace bana zaton haka, yanzu dai nafi so ka min izinin zantawa da matarka, yace to ya kirata tazo ta zauna tare da cewa ba dai har ka gama cin abincin ba?Yace ai kafin abincin ya samu shiga nikam sai naji batun kawarkinnan hafsa. Rahama ta dubeshi da sauri tace me kake son sani game da ita? Yace
Chapter 32 · 0% Book details