Sashe 8
Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
boko,Primary 5 Umar yake lkcn da ni ma aka sani. Babanmu bai cika biya mana kudi Makarnta ba, don bai cika samu ba.Amma in yana da shi yana ba mu,ganin haka ne yasa Innarmu ta kama sana'a. Gyada take soya mana ni da Yayana in lkcn dafaffiya ne kuma ta dafa mana da wannan muke samun rufin asiri. Cikin haka Yayana ya gama Primary aka kukata ya shiga Junior. Kwanci tashi nima na gama primary, sai dai lkcn ne Baba ya ce Bokona ya isa haka, izifina ishirin a Islamiya ya ce da na sauke za a min aure. Innarmu ta ce ina, yanzun kai ya waye ko ita tayi makarantar gaba da primary balle 'yarta. Sun yi hatsaniya hr abokinsa makocinmu Baba Garba, ya saka baki kan cewa Baba yayi hakur ko aji 3 in yi wato karamar Sakandire. Baba ya ce, shi kenan,amma fa ba ruwan shi, ko yana taka kudi ba zaya ba ni ko na fensir ba. Abubuwa suka kara yi wa Innarmu yawa, ga Yayana Umar kudin jarabawa yasa makarantar tsaya. Sai dai karen mota ya koma yana yi wa wani mu2m a layinmu,kasuwa-kasuwa.Inna ta zaunar da ni ta ce Hafsatu,kin san yanda zamu yi? Na ce A'a na me? Ta ce, na karatunki, kina so ko? Na ce "Tab so kai ba ki ga su Saliman ajinmu na su suna ta zuwa, ta ce to dagewa za ki yi zan dinga alala da safe ki dan zaga. Sai kuma ki zo ki dauki gyada, na ce Innarmu ni wlh Na gaji da talla,wata rana mu2m ya yi ta yawo a ki sayar ta ce sakarya kin zaga tas za a saye. Asusu zan yi riba ko nawa aka ci sai mu zuba kafin gama zangon farko mun tara kudin da za ki shiga, na ceto,gwangwanayen gyada muka fafe wasu tayi alala.Nan da nan ya kare, Ta dafa min gyada na dauka ta ce maza Hafsatu, Allah ya bada sa'a kin ji, kan lkcn Ismaiyya ki saida. Na ce to, Ta ce bn da wasa fa, don na san ki, na ce to.Wasa kam inadashi,kowa ya sani har na gama primary duk report card dina ba wanda ba a rubuta min na cika wasa ba, a haka kuma nake karatuna. a haka kuma nake karatuna haka kuma na dage da talla na wata ranar litinin ina tafiya nice har baban titi na tsallaka, sai ga wata yarinya tana tallan kwakumeti, tace ke ina kike zuwa? Na ba ko ina yawon talla nake. Tace zomuje (governmeet college) ana cinikin gyada in yan makaranta suka tashi nace, to muje tafiya ce sosai har gidan gwamna ta nuna min. Muna isa agajiye muka zauna gin din bishiyoyi ga yan talla nan kala-kala har da masu gyada babu abin da yafi mun dadi irin yanda naga yara nata wasa saboda yan makaranta basu tashi ba. Masu carafke masu yar gala gala nayi, wasu na tayin ziro-ziro duwatsu na tsinta nima nashiga yin yar carafke, batare da na huta ba koda dalibai suka taso nan kowa yasaki wasa suka shiga saida kayansu, ni ko ban damu ba na cigaba da wasa na sai da takowa ta kare sanan aka shiga siyan nawa. Washe gari nacewa innarmu a kara mai makon mudu hudu a dafa biyar. Yau ma wasa na dora haka nan sai da ta kowa ta kare don su suna zaune, a gaban kayan su niko ina can ina wasa na. Zuwa yanzu na saba da dabar hanya zuwa (government college) wata rana ina zaune kan duntsen da na dasa a matsayin abin zama na, gaban tirena hannuna zarene ina ta wasa dashi na hada injin nikan barira inata yar waka ta. Sai naji magana kusa dani ance ke gyadarki ba ta saida wa bace? Ba tare da na dubeshi ba nace ta saidawa ce mana,ya ce, "Sa min daya a leda sarkin wasa." Na ce, "Zaba." Ya ce, "Zabar min." Sai lokacin na kalle shi na dan kara zare ido saboda kyawun shi. Haka nan ba Uniform a jikin shi, kenan ba dan Makaranta ba ne. Na mika mishi ya ciro wani farin kyalle ya shinfida akan jijiyar bishiya ya zauna ya soma cin gyadar. Ni kam kallonshi nike a raina ina cewa, "Dama 'yan gayu suna cin gyada?" Ya dube ni, "Ki yi wasanki mana kada ki sa na kware." Na dauke idona daga bisani na tashi, na soma 'yar gala- gala ta. Yana lura da yadda kowa ke tsaye kan kayansa banda ni, da ya mi'ke zaya tafi ya ce, "To sarkin wasa ga kudinki." Sabuwar naira biyar ya bani a mike, a rayuwa ta babu abinda ke burgeni irin sabon kudi, na ce, "Amma na gode, kalleta kar-kar bazan kashe ta ba." Ya ce, "Mai zaki yi da ita?" Na ce, "Ajiyewa zanyi ba zan sashi cikin asusu ba bare har na lankwasa ta." Murmushi yayi sannan ya ce na bashi daya. Ba bashi ya ci rabi ya bar saura, na ce, "Ji fa baka cinye ba." Ya ce, "Na koshi." Da zai tafi ya kuma bani sabuwar naira goma wai in bashi canji na ce, "Wai don Allah kai kuwa a ina kake samun sababbin kudi?" Bai amsa ba yana ta kallona. Na ciro tsohuwar biyar na mika mishi. Ya girgiza kai, "Ba na amfani da Tsohon kudi." Na ce, "Saboda mene?" Bai amsa ba ya ce, "Gobe zan amshi gyada." Na ce, "Toh"Ku san kwana 2 ban ga mu2min ba, sai ranar 3. Yau ma shigar shi ta 'yan gayu kamar kullum. Ya amshi gyada zai tafi ya kuma bani sabuwar 10. Na ce a, ka manta ne kana bi na canji? Ya ce haka ne, to rike wannan don ni in na ciro kudi bana maida su. Na ce ko? Tab, amma dai sun maka yawa ne ko? Ya dube ni ba alamar wasa, ya ce "Mu ne ai muke kera su. Na zaro ido ina kallon shi, cikin matukar mmk "Kana nufin ku ke buga kudi? Ya sake dubana, kwarai kuwa, na Maida hankalina duk a gare shi. Ka ce kana da su lodi? Ya saka hannu cikin aljihu shi ya ciro sabababn dal 'yan naira ashirin da goma-goma na zaro idanu. Tabbas yanzun na yarda na ce kai ko kaji dadinka, ina ma ni ce. Ya ce da me za ki siya? Na ce na farko zan biya kudin makarantana, kuma na dinga sai mana kayan dadi da su nama da mota, su mashin.Kai komai sai na sai mana. Ban lura ba, ashe shi kam dariya na ba shi, ya ce to ai ni kin ga duk na siya abubuwan da ki ka ce, na yarda kam, shi yasa gaka nan dan gayu da kai, ka ta6a zuwa kasar waje? Ya sake darawa, sannan ya ce eh, da yawa ma. Ya tafi ina ta kallon shi. Sa'a da Zaituna wadanda muke tafiya tare dasu, da na basu labarin dan gayun nan na ce ashe sune suka buga kudi kin yarda suka yi. Suka ce to in shi ne me zai kawo shi nan yana karyawa? Na ce shi ne ya fadamuku karyawa yake yi? Suka ce min tun yaushe suka san shi a nan Makarantar. Na ce ko dai yana koyarwa ni na yarda su ke buga kudi, Ga sabbin kudi nan dami a gunsa, Lura da su Sa'a suka yu cewa ba zan yarda da su ba sai suka bar ni. Sau dai suka ce min ni wawiya ce, sai ka ce bn yi zaman aji ba, sunan na gama aji 6 bn san komai ba, na ce naji din. Su Innarmu a da Baba na kuke ina ba su labarin dan gayu mai buga kudi, amma wai sai suka ce zolayata yake yi, nayi duk wani kokari na wai don su yarda da ni cewa gaske ne,amma sun ki. Sai dai na dauki alwashin zan masa tambayoyin da zai gamsar da su. washegari jumma‘a ba mu cika jimawa ba, saboda ana sallah juma‘a a masallacin da ke kallon makarantar amma kin bin su Sa‘a nayi na fake da cewa sai gyada ta ta kare. In tashi yan makaranta tuni sun watse ina ina zaune gaban gyada yar ragowa ce ma, sai kalke kakle nake. Can na hangoshi zai shiga makarantar, ya sanye da wani ubansun yadi fari kar hatta takalminshi da hular kanshi. Duk da yau ce na soma ganin shi da manyan kaya ban kasa ganeshi ba. Da gudu na bishi ina cewa tsaya tsaya ban san sunan shi ba bare na kira. Shiko bai san dashi nake ba a haka mukayi nisa cikin makaran tar sai dai wani ya lura shi nake bi sai ya tai maka ya tsai da mun shi. Na lura yaji mama kin ganina yace, sarkin wasa ina zaki haka? Na tsaya ina haki saboda gudun da nasha yace sannu na ce yauwa, dama kai nake ta jira zan tam bayeka ne. Yace na me? Nace wai dan Allah da takarda kuke yin kudi? Yayi dariya har hakoranshi farare suka fito yace eh, da takarda ne to in na baka zaka iya yi min saboda mutane sun kiyarda ne dani in nace naga masu buga kudi sai ace karya ne zolayata kake yi. Yace zanyi maki in kina so nace innaso kai, to da wace irin takarda kuke yi? Yace ta rubutu nace gobe zan duba jaka ta da in dauko. Yace ba ayi fa da tsohon littafi ko kina son tsohon kudi ne? Nace a a taf na fison sabo yace to shike nan ki kawo sabo nawa za abuga maki yawan kudin? Nace zaka iya min dubu malala gashin tunkiya? Ga mamaki na sai naga yana dariya har da rike ciki nima na soma dariyar ya numfasa ya ce,in ban da abin ki sarkin wasa wane ne ya san yawan malala gashin tinkiya, Na ce to ko dai nawa ne ina so yanda dai ishe ni na gama karatuna. Ya ce,wai dama nan kin yi karatu? Na dube shi, ba na fada maka ba cewa na gama primary? ya ce ban ji ba lokacin da ki ka fada,yanzun JS1 za ki shiga? "Eh tallar da nake ai kudin rijista muke nema, kaga in ka bugo min kudin na daina talla,