← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 34

Sashe 21

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 1-6 Posted by ANaM Dorayi on 12:26 PM, 12-Sep-15 Under: SANADIN BOKO ." Kuka ya sake sarkeni, na ci gaba da cewa, "Shekara 3 da doriya yana min dawainiya da sunan zai aureni, kuma Wallahi Baba fyade ya min." Megadi ya ce, "Kuskurenki shine zuwan da kika yi gidan nan, ki kiyaye zuwa gidan samari ko dakin samari. Yanzun kije ki yi hakuri, in ba haka ba zaki jawa Iyayenki matsala. Kin san masu kudin nan ba duka bane suke da tsoron Allah, 'ya'yansu su ne 'ya'ya na wasu tamkar dabba suka dauke su. Shi Munnir sau nawa yana samuna yana rokona shi da abokansa wai in kai musu kudin gaisuwa gidajen 'yan matansu a matsayin nine Ubansu." Na ce, "Baba ka je?" Ya ce, "A'a ni nasiha na musu dan nima inada yara da jikoki. Tunda haka samarin yanzu suke yi, su kai kudin gaisuwa don su bata yarinya. In ta'ki su ce aurenta zasu yi. Na san koda ban kai musu ba sun je sun samu wani, kuma ya kai musu, kila ma sun cimma burinsu, don haka ki je kiyi hakuri ki kuma kiyaye gaba." Na ce, "Na gode." Ko da wasa ba zan ce maigadin nan ina da ciki ba. Tahowa na yi ina mamakin kalaman Munnir, wai ya taimakeni ne don bukatarshi, dama haka halin maza ya ke? Dama Munnir mayaudarin 'yan mata ne? Tafiya nake amma sam ban dauki hanyar gida ba ko cikin mafarki ai ba zanje gida ba. Zuciyata ta bushe na share hawaye na na nufi Babban titi. Kwatsam! Sai ga Yayana Umar ya sauke wani a mashin, cak na tsaya don mun riga mun hada ido. Cikin mamaki ya ce, "Hafsa daga ina haka?" Gabana ya fadi matuka, amma sai na kanne banda wata damuwa na ce, "Na zo ne yau ko gidama ban karasa ba, gidan su wata na zo." Ya ce, "Wacce watan?" Na 'kirkiro 'yar dariya, "Yar ajinmu ce ta yo mana gaba da kaya to na zo kuma bata karaso ba." A take karyar tazo min, ya ce, "Hau na kaiki gida." Muna cikin tafiya ina tunanin ban so na hadu da Yaya Umar ba, sai ya jeho min tambaya, "Hafsa sai na ganki duk a hargitse, fuska a kumbure kamar kin sha kuka." Gabana ya yi mummunar faduwa amma don kada ya ganoni na ce, "Kukan lafiya? Ka sam zaman mota, kuma baccina na sha har na gaji." Ya ce, "Irinku ne ake sace wa, nan da Kano kin hangame baki kina bacci,." Na ce, "Cikin kwanakin nan ne bamu samu bacci ba saboda karatu." Ko Inna abinda ta soma tambaya ta shine lafiya? Cikin dariyar da bata kai zuci ba na ce, "Lafiya Innarmu." Na shige daki na kwanta kan gado.Jim kadan Ummi kanwata ta shigo da kwanon alala ta ce, "Anty gashi." Na amsa na aje. Ummi ta tsaya tana kallona, ina zaton dan wasan da na saba yi mata ne taga ban mata ba. Inna ta shigo, "Wai Hafsa lafiya na ganki kwatsam! Kuma kina zuwa kin zube a gado?" Ban san yadda aka yi maganar ta zo min ba, sai dai kawai naji ina bata amsa, "Innarmu gajiyar mota ce, kuma dama bani da lafiya ne. Can ma muna ta sintirin asibiti shine aka ce in zo gida in nemi na hausa." Cikin fargaba da Tausayi ta ce, "Ashsha, me ke damunki?" Sai kurum na ji bakina ya ce, "Shawara da Basiri." Ta jinjina kai, "Sannu, Allah ya sauwake, jiki da jini haka ne. Ta ce ci alalar." Ta daga murya, "Ummi! Ummi!!" Yarinyar ta shigo da gudu. Inna ta ce, "Kira min Baban gida in aike sh dattawa ya hadowa Hafsa maganin basir da shawara." Ta kwance habar zaninta ta ciro kudi naira dari 3 da ashirin ta ce, "Ungo ka hau mota ka je layin dattawa gurin masu magungunan gargajiya ka siyo mata maganin shawara da na basir." Ya ce, "To." Ya amsa ya fita. Bani da damar in ki sha domin Inna tsareni take, a cewarta tun ina karama bana son magani. Duk lokacin da zan sha ina sha da niyyar cewar Allah ya sa cikin nan ya fita amma shiru, sai ma tsananin amai da ya karu gareni da kuma kasala. Tausayin Inna yana sani kuka, in naga irin fadi-tashin da take yi gurin neman min magani.Wata rana ina kwance dakin Baabah amai ya sarkeni na tashi da sauri kafin na bude kofa na soma sheka shi. Baabah ita ce ta taimaka min na gyara jikina ta kuma kwashe aman. Har na kwanta ta ce, "Hafsa!" Na ce, "Na'am." Na tashi zaune, ta ce, "Zo nan." Na mike na bita can kuryar daki ta ce, "Hafsa ki fada min tsakaninki da Allah me ke damunku?" Gabana ya yi mummunar faduwa, zufa ta keto min na ce, "Me,,,,,me kika gani?" Ta ce, "Hafsa na ga wasu alamu da suke nuna kina da ciki, menene gaskiyar hasashena?" "A'a bani da komai." Tayi-tayi da ni in fada mata gaskiya amma na dage kan cewa bani da komai, don haka ta kyaleni tare da cewa, "Shike nan. Dama ke nake tunanin zaki bani hadin kai domin Innarku ba zata fahimce ni ba na sani shi yasa na miki magana." Na ce, "Ni fa kalau na nake." Don haka sai ta rabu da ni. Kafin sati 2 duk 'yan gidanmu sun gane halin da ake ciki, amma banda Innarmu sam bata lura ba bata zata ba, ba kuma ta tsammanin haka zata faru ba, 'yan tsegumi har cewa suke mata, "Yaya 'yar boko da jiki?" Haka ta ce, "Da sauki." Tana washe baki ita a dole an gaishe ni. Sannu a hankali zance ya soma fita makota sai gashi ana shigowa dubani, niko ko yaushe ina cikin Hijabi. Baabah Maimuna ita ce ta shigo dubani yau kawar Innarmu ce kut da kut ta kalli Innarmu, "Kin san zancen da yake yawo unguwar nan?" Ta ce, "A'a." "To 'yan gidanku sun fita suna yada cewa Hafsa ciki ta yo." Inna ta mike cikin tsananin tashin hankali, "Wane dan sharrin ne? Wallahi zan iya maka mutum a kotu." Maimuna ta ce, "Saurara kiji, kafin ki fita kiyi wata magana soma tuhumar ta tukunna." Innarmu ta ce, "Haba Maimuna, sanin kanki ne Hafsa bata da rawar kai irin na 'yan iska, sharrine kawai za'a mata. Kin san bani da hakuril dole sai ba ni ba'asni wanda ya mata wannan sharrin." Maimuna ta ce, "Don Allah ki bar zancen nan." Amma Inna bata saurareta ba ta fita tana fada, wai yaya za'a yi ta bar wannan zancen ana kallon 'yarta a matsayin 'yar iska! Kai tsaye sashen su Asabe ta nufa tana fadin, "To munafukai magulmata masu zuwa lahira da kokon dambu! Za kuce 'yata cikine da ita, to aniyarku ta biku. Kuma Insha Allahu 'ya'yanku ne zasu yi ba tawa ba. Kanta aka fara ciwo da za'a mata sharri?"Kuma in sha Allahu yayanku ne zasuyi ba tawa ba kanta aka fara ciwo za a mata shairi? Asabe tace aina kika ji? Mu nan dai ba wanda ya san haka inna tace rufe min baki munafukai, to nazone in muku gar gadi zan maka mutun a kotu, sai ta fito mun da wanda ya fada mata. Ade tace maganar gaskiya ki bin ciki yarki dan muma a makota mukaji. Inna tace ahaf na san duk inda aka zaga aka zago kune zaku fadi wanan maganar, kuma zaku amsa kiran alkali,gida ya hautsine baba ya shugo yana tambayan ba asi, babah tace a a yar rigimar yara ce ba sai kaji ba. Nufinta kada yaji don tasan in yaji sai yabi duddugi amma jin zantukan sun cika gidan har makota sun soma zagayowa, ya fito dan jin ba‘asin tun bai karasaba ya soma jin muryarsu Ade na cewa an dai fada maki kije ki tuhimi yarki, ba kizo ki tasamu kina zagi ba. Ki dau mataki tun kafin lokaci ya kure miki, in shairi a ka mata sai kiji dadin kaiwa kotun. Asabe ta kara da cewa, inko kin tafi yanzun kya iya zuwa kiji kunya. Ya iso gurin yace zo, babah ta malam na kiranki don Allah kiyi hakuri ki bar zancen nan, wanda ya fada ba don kansa ba. Ta nufo daki inda baba ke kiranta, ina kuryar gado tare da fatan Allah ya dauki raina yanzunnan. Baba ya dubeta, to in kin gama fadan kira min yar bokon yar taki inna tace saboda Allah malam daga ciwo sai ayi mata sharri? Ca wa fa sukayi tana da ciki yace ai ba abin mamaki bane kira min ita. Hafsa zonan, na fito kishirya mutafi asibiti inna tace malam asibiti suna bada maganin basir ne? Acan makarantarsu fa sunyi na asibitin sun gaji shinefa sukace ta taho gida ayi na hausa. Yace to ai ba matsala bace wanan, matsalata in tabatar da zargin da ake yi mata inna tace ai! Malam kaima ka yarda za ta iya? Yace kwarai kuwa, yace ita ba mutum bace? Ya ba kanshi amsa yacemutum ce kuma baliga mai lafiya, don haka yanzu da bayanin likita zan yarda da duk abinda zakuce. Nan take tsoro ya kamani hankalina yafi da tashi. Inna tace je kushirya kutafi asibitin inma har har danine sai muje. Yafita tare da cewa ina jiranku waje. Nace inna kice masa don Allah mu bar zuwa asibitin nan kinji? Tace a a ki shirya kindai san halin babanki, in ba‘aje likita ya wankekiba bamu da zaman lafiya, nace inna mudai mu hakura ba sai mu barsu da Allah ba, masu cewa inada cikin? Tace shin hafsat kodai kina da cikin ne?nazaro ido nace a a ni bani da komai tace to shirya muje, garuwa ki daureye jiki nace to a ban daki tamkar in haure yar gajeruwar katangar mu in gudu, domin na san yau idan mukaje asibiti asiri na yagama tonuwa. Yau auren iyayena zai rabu na shiga 3! Nan wata zuciyar ta fada mun ba laifina bane, in bisu inje asibitin inyaso duk yanda Allah yaga daman zai faru dani shikenan, sai in rungimi kaddara. Afili nace Allah ya isa munnir asibitin dutse muka je, baba shine ya yankar min kati suka tura mu gurin da zamu ga likitan mata. Duk da halin da
Chapter 21 · 0% Book details